Showing 198001 words to 201000 words out of 223329 words
Takai ƙarshen zancenta tana share hawayen da tun ɗazun basu gajiya wajen kwaranya ba daga kumatunta, dan muryarta har dashewa takeyi dan kuka.
Tsitt falon yayi motsima kowa ya kasa dan al'ajabi, wane irin masifa ne wannan da haɗa boom. dan wannan al'amari na Zakiyya yayi kama da haɗa boom. Dan kawai kinason ƴar uwarki sai ki ƙulla abinda zaki cutama rayuwar wasu.
Kallonta kawai AK yace cike da tsana da takaici. idanunsa sun kaɗa sunyi jajur, hakama jijiyoyin kansa sunyi ruɗu-ruɗu. Hakama Farah kuka take tamkar ranta zai fita, dan tasan dai komai Zakiyya tayine dominta, gashi tun ba'aje ko'ina ba komai ya ƙwaɓe. Kishiyar da take tsoro kuma an mata ta sanadinsu.
Mammah ma kanta duƙe a ƙasa dan tama rasa mi zatace dan tashin hankali da baƙin cikin kanta da kanta, tayaya ta zurma haka da yawa yarinya ƙarama ta ɗana boom ɗin da a ƙarshe yake neman tashi da ita? Tayaya idonta ya rufe haka da yawa ne akan abinda yana a hannunta amma gashi sakacinta ya ta miƙashi ga mai shi?.......
Cikin ƙunar Zuciya AK ya katse tunanin kowannensu ta hanyar faɗin, “Shima cikin da take dashi yanzu na ƙaryane kenan? Randa mukaje asibiti da nufin sake duba lafiyata kune kuka ƙulla?.”
Kasa magana Farah da Zakiyya sukayi. sai Mammah ce cikin kuka tace, “Kayi haƙuri Abdul-Mutallab, tabbas wannan duk laifinane, da ace ban bata goyen bayaba babu yanda za'ai hakan ta kasance. Nayi nadamar saninki Zakiyya, wannan wane irin haline haka da kika nema jefamu a ciki. Har takai na saka hannu wajen cutama gudan jinina ta hanyar makircinki”.
“Dama shi son zuciya ai ɓacin zuciya ne, daga lokacin da kake ganin wayonka ko dabararka zai baka abu to lallai a lokacin ka ɗaura ɗammara da ɗambar rasashi, dan koka samu sai ya suɓuce maka. Kin biyema yara ƙanana saboda wani shirmen banza da wofi Hindatu, yanzu da ALLAH bai ƙaddara yarinyarnan ta faɗo cikinmu ba yaya kenan? Duk da dai sanda sukayi na farko basu sanar miki ba, amma na biyun da'an haifesa fa? Shikam kinada kamasho a ciki ai”. Uncle Ahmad ne ke magana cikin ƙunar zuciya.
Kauda kai AK yayi yana rumtse idanunsa saboda zafi da ƙirjinsa ke masa. ga kansa sai juya masa yakeyi alamar hawan jininsa na neman motsawa. Cikin harɗewar harshe yace, “Uncle idan wancan ya salwanta aiga waninan ma sun sake dasawa. Tunda sunce tanada ciki kuma likitoci sun tabbatarmin babu wani ciki tare da Farah”.
Yanzu kam duk yanda mai martaba da mukarrabansa sukaso daurewa sun ƙasa. Cikin kaushin murya yace, “ALLAH zai sakamin ɓatamin suna da kukayi. musamman ke Zakiyya dan kece kika ƙulla komai, kece kika ɗora ƴar uwarki akan abinda sam babu shi a ranta, ni yanzu bamma san mizance mukuba wlhy, dan yanda nakejin raina zanma iya tsine muku. Amma inason sanin gaskiyar zancen shi cikin da akace tana dashi yanzu, dan nikam kotun musulinci zan kaiku a yanke muku hukunci dai-dai da laifinku”.
Sosai Farah ta fashe da kuka. Ta rarrafo gaban mai martaba ta kama ƙafafunsa da fashewa da kuka. “Dan ALLAH Abba kayi haƙuri, nidai wlhy bazan sakeba, wannan ma kota haufa banaso zanyi haƙuri ALLAH ya bani nawa. Na tuba Abbah dan ALLAH na tuba”.
Banza yay mata yama ɗauke kansa ya maida ga Zakiyya da itama kukan take. “Wai bada Zakiyya nake maganarnan ba?!”
Zabura ta ɗanyi saboda yanda yay maganar a tsawace, ta shiga jinjina kanta da faɗin, “Abba hakane, shima dasawar akai, amma wannan ƴar Morocco ce, kuma da amincewarta itama wlhy”.
Sake ɗaukar sallalamu falon yay gaba ɗaya, hajiya iya dake sharar ƙwalla tace, “Gaskiya baku ƙyautaba, wannan zaluncine wlhy dason zuciya. A barshima mutum shi ya yarda yay muku wannan aikin da sauƙi ai, amma kamar yarinyarnan aikun zalunceta. Inda ALLAH bai ƙaddara tamu bace kamar yanda Ahmad ya faɗa harta mutu baza'a daina mata kallon wannan tabon ba. Yaya zakuyi da alhakin wannan yarinyar kawai ma balle na sauran suma, sai dai idan da yardarsu kukayi sukam. Nikam dai ina bayan mahaifinku a kaiku kotun musulinci a bin kadin jikata na rainon cikin da tayi. kuma wlhy ko sama da ƙas zata haɗe ɗannan ya zama nata har gaban abada marasa mutunci”.
A take su waziri suka shiga goyama hajiya iya baya, kowa na tofa albarkacin bakinsa. Mmn sadiq, Abba, baba sune dai basuce komaiba, sai dai duk sai da sukai ƙwallar tausayin Zinneerah harma da AK da little. Sai da ƙyar Baba ya fara magana ganin kowa ya yarda da zuwa kotin.
“Ranka ya daɗe nikam kuyi haƙuri zance wani abu”.
Duk hankalinsu suka maida garesa. Ya ɗan muskuta zamansa yana gyarama little dake a jikinsa kwanciya, dan shi yaune karon farko daya ga jikan nasa, “Kuyi haƙuri nasan tabbas basu ƙyautaba, kuma zaluncine abinda sukayi dan yarinyarnan taga rayuwa mai zafi kala-kala a dalilin cikin nan. To amma Alhmdllh ta wani gaɓar ya zamar mata alkairi. Dan a sanadin samunsa ta sadu da mahaifiyarta, ƙaddara ta ɗakkota ta kawota cikinku da har a yau ya zama sillar bayyanar komai, bugu da ƙari yay mata ƙyauta da miji uban ɗan kuma saboda hikimarsa. Sannan a sanadinsa nima kaina nabar gida harna samu waraka daga kaidin matata, na kuma ƙara aure a yanzu haka matata ta haifamin yara maza ƴan biyu guda biyu tun washe garin da suka koma gida. Waɗanan kaɗanne daga ni'imomin UBANGIJI gagara misali daya lulluɓe Zinneerah dasu a sanadin cikin yaron nan da batajiba bata ganiba. Tabbas duk mai haƙuri zai dafa dutse harma yasha romonsa. Su dai duk sun aikatane akan dalilai biyu zuwa uku. Mahaifiyarsa dalilinta kawai kar ya dawo hanun ubansa ne da rayuwa, sai kuma gashi ya dawo cikin sauƙi. Ita wannan yarinya saboda kar mijinta ya ƙara aure ne, kuma gashi ya ƙara ɗin harma suna zaune a inuwa ɗaya. Ita wannan ƴar uwa tata kar wata tazo ta haihu ba ƙanwartaba. Gashi kuma watan ta haihu ba kanwar tata ba. To idan mukai tsam a nazari zamu fahimci UBANGIJI ya bama kowa sakamako nan duniya dai-dai da shi da tabbatar musu cewar wayo ko dabarar bawa bata kaisa da nasara. duk saurinka kuma saika jirayi zartar da ƙaddarar UBANGIJI gamai ita. Tunda su duk sunyine a ɓoye domin bama kayinsu kariya akan abinda yake gaibu kuma dauɗar duniya amma daga ƙarshe gashi duk sun rasa, kuma wanda sokaso ƙwata daga wajensu ALLAH ya maido musu. A ganina kuma miya rage banda mu barma UBANGIJI ikonsa ya ƙarasa zartar da hukuncinsa. Basai anje kotuba, dan mu dukanmu ALLAH ya haɗamune a ƙarƙashin inuwar zumunci sai muyi haƙuri wajen haɗiye duk wani saɓani da zaizo a garemu duk da kuwa wannan ya banbanta ba abune mai saukiba. Amma idan mun sauƙaƙashi a ranmu sai ya zame mana alkairi kamar yanda ya zamewa Zinneerah. Sai dai kuma su sauran yarenne bamuda hurumi a kansu inhar suma tirsasu sukai ko yaudararsu. Abin na gaba shi annamimin likitan dake wannan aikin ya kamata a dakatar dashi, dan gwara ace ma'auratan dake buƙatar hakan da kansu suka amince suka kai kansu bawai ta irin wannan hanyar dabita wagga ɗiya Zakiyya tabi ba. Wannan al'amarima malamai sunata nasiha akansa. barinsa yafi alfanu fiye da yinsa. Dan UBANGIJI shine yasan miya gani har bai bakaba, zata iya yuwuwa rashin haihuwar sai yafi zame maka alkairi fiye da yinta. To mizai hana bazaka dogara ga UBANGIJIN talikai harya baka ba kuma?. Sai kuma ina roƙon alfarmar ku taimaka kuje can garinmu ku wanke wannan yarinya agaban al'ummarmu, dan inba hakaba harta mutu wannan tabon na biye da ita. Haka shima wannan yaron bazasu taɓa kallonsa da darajaba dan ɗan shege zasuke kallonsa bayan ba haka bane. Ayi haƙuri da juna ayi sulhu dan ALLAH shine mafi alkairi a garemu fiye da mu tonama kammu asiri kodan kasancewar ku manyan mutane danmu namu mai sauƙine iya garine kawai, idan yazu kuma mukace mun barsa zance ya ƙare. Kuko magauta sun sami abin faɗa a gareku kenan har takai shi yaron ana goranta masa duk da kuwa ba alfasha aka aikata wajan samuwarsa ba kai tsaye”.
Harga ALLAH kowa maganar baba ta sanyaya masa ransa. Kuma kimarsa da darajarsa ta ƙaru a cikin idanunsu, hajiya iya ta shiga jera masa tagwayen addu'oi shi da zuri'arsa kowa na amsawa da amin.
Sai da kowa ya natsa sannan mai martaba ya fara magana bayan yayi gyaran murya. “Ni a nawa hukuncin to Abdul-Mutallab da Sageer (mijin aunty Zakiyya) duk ku saki waɗanan marasa mutuncin, kowacce ta koma masarauta sai sunyi zaman shekaru bibbiyu kafin na barsu su dawo gareku idanma kuna sha'awa kenan, kokuma su sake auran wasu mazan suji, dan masu iya magana sunce idan kai nada tsoka taɓa naka kaji. hukunci na biyu koda na faɗa ko ban faɗaba musilinci ma ya bama wannan yarinya yaro duk da dai malamai sunyi bayani kala-kala akan hakan, dan haka ko da wasa idan kuka ɗauka yaron nan kuka bama Farah matsayin uwarsa ALLAH ya isa ban yafe mata ba idan ta amsa. Yaro na Zinneerah ne har abadan kuma itace zata cigaba da iko da shi matsayin mahaifiyarsa har ƙarshen rayuwarta, kai bamma yarda koda wasa wani ya dangantashi da Farah ba zan ɗauka mataki mai tsauri koda kuwa Abdul-Mutallab ne yayi hakan. Koda alaƙa zata shiga tsakaninta da shi sai dai ta zumunci ko matsar ubansa amma ba uwa ba. Hukunci na ƙarshe idan waɗancan da sukaima wannan ƙullalliyar yazam suma bada saninsu bane to lallai zan kaisu kotu a bi musu kadin haƙƙinsu. Wannan shine hukuncina a matsayina na maihaifinsu”.
Kuka wiwi Farah da Zakiyya keyi musamman akan zancen sakin da mazajenau zasu musu dana haramta mata Little. Dan Farah a yau karo na farko ƙara ganin little yasa ya shiga ranta dan kamar an ɗakko ƙaunrasa mai tsanani an dasa mata a ƙirji takeji.
Babu wanda ya iya jayayya da wanan hukuncin na mai martaba dan shine kawai zai iya zama darasi garesu. Sai dai yanda suke kuka dolene su baka matuƙar tausayi..............✍
*_TYPING📲_*
*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*
________________________
*Page 64*
............Cikin dakiya Baffah yace, “Wannan hukunci naka yayi dai-dai kuma na gamsu dashi nima wlhy, dan haka nima ga nawa hukuncin akan ƴaƴana da Hindatu. Duk da ni bazan rabaki dasu ba amma tabbas zan nesanta rayuwarsu da taki. Daga yau Abdul-Mutallab zai dawo rayuwa a Nigeria, idan har kikaga ƙafarsa a london sai dai harkar kasuwarsa amma bada rayuwaba. Hukunci na biyu anan gurin nakeson a ɗaura auren Huzaifa da Adilah itama ta baro can har abada sai dai taje domin gaisheki ita da mijinta. Hukunci na ƙarshe karna sake ganin ƙafar Hindatu a gidana har abada, idan kuma ta sake shigowa nima zanyi ƙararta........”
Katsesa Abba yayi (mijin mmn sadiq) “A'a dan ALLAH ayi haƙuri Alhaji Kabeer, ai ko babu komai ALLAH ya haɗa tunda gashi har an fara ajiye jikoki bama ƴaƴa ba. Hukuncin dawowar yara dai yayi amma ita kar ace bazata zo nan ba dan ba'asan mi rayuwa zatai nan gaba ba”.
Wambai yace, “Maganarka gaskiyane Alhaji Abubakar, a daiyi haƙuri Alhaji kabeer a tsaya kan yaran kawai domin ALLAH. Babu yanda za'ai tunda zuminci ya sarƙa a tsakani, koba komai darajar shi Abdul-Mutallab ɗin da biyayyarsa a ɗagama Hindatu ƙafa. Mai afkuwa ta afku, kamar yanda kuma Malam Sulaiman yay bayani ALLAH ya bama kowa sakamakonsa tun a duniya tunda mainakon nasara duk faɗuwa sukai batare da sun ci nasarar burinsu ba. Koba komai ita wannan yarinya MAKAUNIYAR ƘADDARA ta zame mata BUƊAƊƊEN HASKE, ta mallaki ɗa, ta mallaki uban ɗa, sarƙin dake tsakanin iyayenta ya buɗe, sai muyita mata fatan gamawa da rayuwa mai albarka har ƙarshen numfashinta. Su kuma nema gafararta dan alhakinta bazai barsu cigaba da rayuwa cikin salamaba. Suma kuma waɗanda suka sakema ta'asar a nemesu aji ta bakinsu, idan kuma da amincewarsu ne shikenan ai. Sai a tattara a barma UBANGIJI ikonsa. Koda hukuncin mai martaba aka barsu ya ishi rayuwarsu izina. Masu shirin aikata wanan taɓargazar ko ma suka aikata suma sufa sani sakamakonsu naga ALLAH, dan shine kaɗai yasan hukuncin daya dace ga mutane irinsu. Ina amfanin abinda yahudu da nasara suka ƙirƙira da har zai birgeku wajen aikatawa bayan kuna al'ummar musulmai? Koba komai ka nuna rauninka kenan ga jarabawar da UBANGIJI yay maka domin gwada imaninka. Sannan zata iya yuwa shi wannan ɗan ya girma ma ya gallabi rayuwarka, ƙilama yay sanadin hallakaka ko shigarka wuta. Dan ƴaƴa da yawa sune zasu kai iyayensu wuta. Dan haka ya kamata mu kiyaye, dan kana neman haihuwa bai kamata kabi ta kowacce hanya domin samu ba. Hakan son zuciyace da rashin godiyar ALLAH. Domin idan zaka nutsu ga ni'imominsa ya maka ta hanyoyi da dama ba sai ta haihuwa ba, ko musulinci da yayika aciki da soyayyar MANZON ALLAH (S.A.W) daya dasa maka a zuciya kawai aka barka ya maka babban ɗaukaka da rahama. Balle wanima zakaga bayan wannan akwai wasu tanade-tanade da UBANGIJIN yayma rayuwarsa waɗanda shi kansa baima san yawan adadinsu ba. Amma saboda kawai ya jarabcesa da rashin samun ƴaƴa sai ya ruɗe ya fita hayyacinsa. Kaiconmu da wannan shiriritar, nasan rashi ƴaƴa nada zafi a rai da damuwa. Amma duk abinda ka ɗaukesa mai sauƙi sai UBANGIJI ya sake sauƙaƙa makashi kai ma a zuciyarka da ayyukanka. Idan kuma ka dage sai ka samu to lallai San zuciya kuwa ai ɓacintane ga duk mai sha'awa ko buri. Duk wanda basu haihu ba ya ALLAH ka azurtasu da zuri'a masu albarka a garesu, idan ba alkairi bane ALLAH ka sakanka musu da abinda yafi alkairi, ka yalwatasu da tarin haƙuri da juriya a zukatansu”.
Da amin duk suka shiga amsawa, kuma kowa ya gansu da bayanin waziri, saurama suka shiga tofa albarkacin bakinsu. Sai da duk mazan suka gama kace nace Mahma da tun ɗazun al'ajabin su Zakiyya ya hanata tofa komai ta duba su Zakiyyan. “Wannan shine abinda naketa nusar daku amma kuka kasa fahimta, bansan miyasa a mafi yawan lokuta gatan rayuwa da tagomashin arziƙi dake zuwa cikin hannayenmu ke dulmiyar da zukatajen jin muna sama da kowa ba. Zamu iya zartar da hukunci ga kowa, zamu iya taka kowa dan ko anje an dawo babu yanda zaiyi damu. Duk da dai anata maimaita magana ɗaya amma dolene a faɗa. Kun zalunci yarinya saboda kuna mata kallon mai ƙarancin gata, sai gashi UBANGIJI ya biyo muku ta inda bakuyi zatoba ya ruftaku a ramin da kuka tanadi sakata ku kuka afka. Shi kansa Abdul-Mutallab kun cutar dashi ai, gara ace fitowa kukai kuka shaida masa ƙudurinku, idan ya amince fine, idan bai aminceba sai ku bi duk hanyar data dace wajen ganin kun lallaɓasa ya yardan koku haƙura har ALLAH ya kawo mata iyakar da zata samu. To yanzu dai dukma abinda zai faru ya faru. kun aikata a ɓoye ALLAH ya buɗa kowa ya gani, kunyi danku tsare mutuncinku gashi ya zube a idanun kowa. Kunyi don samun haihuwa, gashi an haihu ɗan yafi ƙarfinku dan nima ina bada goyon bayan hukuncin Abdul-Hakim (Mai martaba), kunyi dan gudun kishiya, ga kishiyar nan mai daraja ma kuwa da inhar Abdul-Mutallab ya wulaƙantata koda na second guda bazamu yafe masaba, dan ta cancanci a kula da ita a riritata. Kunyi dan kar Abdul-Mutallab ya suɓuce muku, gashi ya suɓuce mukun ya dawo inda baƙwaso ya rayu dagashi har ƴar uwarsa. Da wannan kawai aka barku ya isheku, dan nidai banga ribar da kukaciba anan sai asarar kuɗaɗenku dana lokacinku da kukayi a banza a wofi, idan kuma wannan baiwa da waɗan can ma basu yafe mukuba to yanzu aka fara wasan. Koda sun yafe muku sai kuma ku jira hukuncin UBANGIJI a gareku dan shi ne yafimu sanin abinda ya cancanta da mutane masu hali irin naku. Hindatu kinfi kowa ganganci matsayinki na uwa, duk da kuwa Zakiyya ce tai amfani da abinda ke damuwarki ta sarrafaki cikin sauƙi kika afka, amma ba komai ya jawo hakanba sai gurɓataccen tunaninki da son zuciyarki. Wanda inada tabbacin son Kabeer ne ɗawainiya dake ba komaiba, girman kai ya hanaki nutsuwa ki nema sulhu da shi sai kike huce komai akan yaronsa da baijiba bai gani ba. Gashi nan ai kin rasa Kabeer ɗin da Abdul-Mutallab ɗin duka harma da Adilah. ALLAH UBANGIJI ya rabamu da son zuciyoyinmu, ya yalwatamu da haƙurin ibadarka. Daga ƙarshe dan ALLAH ina roƙama ƴan uwana gafara a gareku iyayen Zinneerah, ku yafe musu, karkuyi dubi da halayensu da cutar da sukaima ƴarku. Dan tunkan aje ko ina ALLAH ya saka mata. Dan ALLAH ku gafarcesu ko zasu sami sassauci daga raɗaɗin da za'a bar rayuwarsu da shi. Keko Zinneerah bazance ki yafe musu ba, idan zaki iya yafe musu Alhmdllh, idan kinga bazaki iyaba ki barsu da ALLAH zai cigaba da saka miki ta hanyoyi daban-daban kamar yanda ya fara tun yanzu anan duniya. Kabeer da Hajiya Mama (Hajiya iya) kuma dan ALLAH ku yafe musu badan halinsu ba, kodan darajar Abdul-Mutallab dake a tsakani, dan ya can-can-cin yabo yaron nan ta fannoni daban-daban. Duk da kun sakashi a tsakiya game da wannan al'amari a koda yaushe burinsa yaga ya saka farin ciki a zukatan kowannenku koda kuwa shi zai ƙuntata tashi zuciyar. Dan ALLAH muyi haƙuri mu yafi juna kodan shima yay farin cikin da yaketa fata akan kwanciyar hankalinmu”.
Baba ne ya fara jinjina kansa bayan kammalawar Mahma. Yace, “Kinyi bayani mai ƙyau hajiya, kuma nidai ta ɓangarena na yafe musu wlhy, dan koba komai abinda suka aikata ɗin ya zama tsanin nasara ga gudan jinina. Shiyyasa akace idan kaga UBANGIJI ya jarabceka da wani