Showing 219001 words to 222000 words out of 223329 words

Chapter 74 - Makauniyar Kaddara Hausa Novel Complete

21 Nov 2024

1217

da nasiha mai ratsa jiki, kafin ya duba AK da yay kicin-kicin da rai. “Abdul-Mutallab ayi haƙuri, a cigaba da haƙuri a ƙara haƙuri. Ita ƙaddara haka take babu abinda ya isa tsaidata ga bawa. UBANGIJI ya riga ya hukunta faruwar hakan a garemu tilas. Hakan jarabawa ce. Maganar tone-tone bama ta tasoba tunda anyi komai ya wuce sai ayi haƙuri kuma a sake kafa sabuwar rayuwa. Ga Farah nan ta dawo cikin iyalinka. Ina fatan zaku manta da komai ku ringumi junanku kuyi haƙuri. Darajar haƙurin da zakuyi sai ALLAH ya ƙara muku kwanciyar hankali da farin ciki kaji”.
       Kan AK a ƙasa yace, “Dady taya zan zauna da wadda bata amshi laifinta ba, girman kai ya hanata neman yafiya ga wadda suka zalunta duk da rawar gani data taka wajen hana katsewar igiyar aurenta”.
     Shashshekar kukan Farah ne ya fito, tace, “Wlhy ba girman kai ya hanani neman gafarar Zinneerah ba kunya ce kawai da nauyin girman laifin da aka aikata mata, duk da ALLAH shine shaidata ban sanma wadda aka sakama ciki ba. Amma inajin nadama da kaico da kawunanmu saboda son zuciya. Zinneerah ki yafe mana domin ALLAH badan halinmu ba. Duk da nasan munzo a makare ga neman gafarar taki. Amma dan girman ALLAH ki gafarcemu, gwiyawunmu bisa ƙasa........”
      Sauron katseta Zinneerah tai da faɗin, “Haba aunty Farah, wlhy ni ban rikeku ba tun a waccan ranar komai ya wuce a gareni. Sai dai muyi fatan ALLAH ya yafe mana baki ɗaya. Ya kuma bamu zaman lafiya da haƙuri da juna”.
      Da amin duk suka amsa. Yayin da AK ya ballama Zinneerah harara. Murmushi kawai tayi ta ɗauke kanta. Shima AK ɗin gafararsa Farah ta nema, duk da dai bai kulataba bai kumace uffanba. Uncle Ahmad dai ya ɗora musu da sabuwar nasiha data ƙara sanyaya jikinsu.
    Da ga ƙarshe ya rufe taron da addu'a suka tattara suka tafi aka bar Farah anan.
       Tashi Zinneerah tai zata barsu AK ya dakatar da ita wai ta haɗa masa ruwan wanka. Kafinma ta nufi ɗakin shi ya shige. sai taji duk babu daɗi ga Farah zaune ko kallonta baiyiba.
      Tayi tunanin Farah zata ɓata rai, sai taga kawai ta bisa da kallo tana murmushi da share hawaye a kaikaice. Ta maido dubanta ga Zinneerah datai shiru kanta a ƙasa ta kasa tashi. “Mamin Abdul kije karya ga kin ɓata masa lokaci, sai dai ki sake roƙamin shi gafara dan ALLAH, da kuma keys ɗin sashena”.
       “Kiyi haƙuri dan ALLAH aunty Farah komai zai wuce. Kinsan dai halinsa kinma fini sani. Keys kuma suna wajena ma bara na ɗauka miki”. Tai maganar tana nufar hanyar ƙofar fita. Da sauri Farah ta dakatar da ita tana miƙewa. “A'a kinga jeki ki cika umarninsa zanje na jiraki a general falo”.
        Kai Zinneerah ta kaɗa mata kawai cike dajin nauyi ta nufi ɗakin nasa. A cike fam ta iske AK da haushi. Kamar jira yake tana shigowa ya balbaleta da masifa wai ta wulakantasa bayan ya faɗa mata bukatarsa. Hankalintane ya tashi dan faɗa sosai yakeyi.
       Ganin abin karya juye mata yasata faɗawa jikinsa ta manne bakinsu waje guda ta shiga lallashi ta hanyar da yafi buƙata. Ai ko saigashi yay bulum harma yana neman zurmawa. Da ƙyar ta ƙwace kanta ta na masa dariya. Ƙwafa yay da fadin, “Zan kamaki ne ai, zakimin bayani dalla-dalla tunda na fara zama abokin wasanki”.
    Ita dai shigewa toilet tai tana masa dariya.

     Da taimakon su Saliha Farah ta gyara sashenta, Zinneerah takai mata abinci da kanta tana sake mata sannu da zuwa. Dan harda yara taje mata. Jawosu Farah tai jikinta ta rungume ƙwalla na cika mata ido. Little kam daga jikin Zinneerah ya makale yana gaisheta. Duk yanda taso yazo gareta yaƙi dole ta haƙura. Anan ta bar mata Amaan da Anam suka fita ita da little tana masa faɗa.
        Buɗar bakin yaron nan sai cewa yay, “Mami ni bana sonta...”.  Baima rufe bakiba ta make bakin har yana fashewa. Ta shiga masa masifar da ta kai har AK dake falonsa fitowa dan suna a general falo ne tsaye.
       Kallon yanda bakin little din ke jini yana kuka yayi. “Lafiya? miya miki haka harda fasa baki?”.
       Ranta a ɓace tace, “Idanma ya sake maimaita abinda ya faɗa wlhy haƙwaran zan zubar ƙasa. Dalla matsamin na wuce mara mutunci”. Ta faɗa tana turesa tai shigewarta sashenta.
      Da kallo AK ya bita ransa a ɓace, dan ya tsani ana dukar masa yara itama kuma ta sani, yakance ko laifi sukai ta zaunar dasu ta musu nasiha bawai dukaba dan baya magani. Hannun little ɗin ya kama suka shige sashensa yana tambayarsa miyayi mata?.
     Abinka ga yaro saiya maimaita abinda ya fadama Farah ɗin. Faɗa shima yay masa da nasiha akan karya sake itama Momy ce. Yaron sai yace bazai sakeba ya kuma bashi haƙuri. Tare da cewa bara yaje itama Mami ya bata haƙuri.
     Cayay ya barta idan sun dawo salla saiya rakashi ya bata.

Haka kuwa akai bayan sun dawo salla sashen Zinneerah ɗin suka shiga shi da little. Acan ɗakinta na ƙurya suka sameta ita da Saliha suna magana. Saliha ta gaishesa ta fice. Zama yay bakin gado little kuma yaje gabanta ya durƙusa. “Mami kiyi haƙuri bazan sakeba dan ALLAH”.
    Shiru tai masa tamkar batajiba sai da AK ɗin yace tunda ya baki haƙuri ba kuma sai ya wuce ba.
      “Yayanmu so kake na haƙura gobe ya sake kenan? Shi ɗan karamin nan dashi har yasan wani cewa baya son mutum?”.
      Kuka little yasa mata yana ƙara bata haƙuri hannayensa riƙe da kunnuwansa. Nanma dai baki AK ɗin yasa harta haƙura. Little ya fita ya barsu a ɗakin saboda aikansa da tayi wajen Saliha.
      Mikewa tai tana ninke abin sallar da take kai zaune, AK dake binta da kallo yace, “Kemafa masifanki yayi yawa”.
     Baki ta kumbura gaba amma batace komai ba. Hakan yasa AK kamota ta faɗo jikinsa. Lips ɗinta ya ɗalla da yatsunsa yana faɗin, “Dan wulakancin kin fasamin bakin yaro harda jini”.
    Murmushi tayi tana cusa kanta a ƙirjinsa da faɗin, “Kaga gobe idan zaima wani rashin kunya sai ya tuna da wannan ai”.
      “Uhmyim, to ai ba ƙyaleki zanyiba sai na rama masa”. Yay maganar yana ɗaura lips ɗinsa kan nata. Daga hukunci aka zarce soyayya. Daga karshe dai sai da aka kai gayin wanka...........✍
    

*_Dan ALLAH ku saka ɗan uwana addu'oinki na yinin yau, ya ɓata an rasa inda yake kuma babu labarinsa. ALLAH ya bayyanashi, ya karama mahaifiyarsa damu nutsuwa. Ya kuma tsaresa a duk inda yake. Ya bashi kariya daga abokan banza ko miyagun mutane. Tare da sauran al'ummar musulmi baki ɗaya_*😭🙏🏻


*_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*

Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.

*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_

*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_

*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_

*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_

*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_

Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.

Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*

*_TYPING📲_*


*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*


_______________________


*Page 70 End😭🙏🏻*

...........Iya ƙokari Zinneerah yi take akan ganin zaman AK da Farah ya dai-daita, dan sai faman fushi yake har yanzu. Itama idan tai maganar sai ya hau fushin da ita. Ya hana taje ɗakinsa balle ta amshi girki. Gudun shiga haƙƙinta yasa Zinneerah riƙa ƙin zuwa ɗakinsa duk bayan kwana biyu, zatai girki ta kuma gyara masa sashinsa amma bata yarda ta kwana ba duk iya masifar da zaiyi. Dan har cikin ransa haushin Farah da yakeji akan al'amarin nan yaƙi barinsa.
      Randa ya fahimci take-taken Zinneerah yayi mata faɗa kamar zai cinyeta, uffa batace da shiba saima kuka da taci. Washe gari sai ya tsiri tafiya Lagos. Kwanansa biyu ya dawo ran girkinta.
      Duk da taji haushin hakan da yayi saita sharesa ta amshesa kamar yanda ta saba daya dawo. Takumabi hanyoyin daya dace ta bashi haƙuri da ƙara roƙonsa akan ya mance komai. A lokacin tana lafe jikinsa.
      Cikin lallashi tace, “Yayanmu nasan daga ni har kai duk an mana laifi, amma idan mukai haƙuri muka mance da komai sai ALLAH muma ya yafe mana kurakuranmu. Shi riƙo baida amfani, sai dai ya dinga zafafa zuciyar mutun da ƙuntata ta. Dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy nasan itama tayi nadama. Ka duba fa yanda aunty Farah ta canja tamkar ba itaba, tayi laushi fiye da zaton duk wanda ya santa”.
        Guntun tsaki yaja da yunƙurawa zai tashi tai saurin riƙosa ta sake naɗe masa a jiki. “Yayanmu Please mana, i beg you”. Ta faɗa cikin tsananin raunin murya.
     Dafe kansa yay da ɗan cije baki yana wani luu da idanu, aɗan hasale yace, “Wai ke miyasa bakison kiga mutum yana hutawarsa ne? Sai kin takura masa da silly zantukanki?. Idan ke zaki iya haƙura kamar bakisan ciwon kanki ba, ni bazan haƙuraba. Ban kasance mazinaci ba amma kullum ana haɗa kai da matata ana min rarraba da sperm a jikin wasu matan dama bansan su ba. Wannan wane irin son zuciya ne da yahudanci?”.
         “Duk nasan ba'a ƙyautaba My Heartbeat, amma Please kayi haƙuri tunda sun amsa laifinsu kuma sunyi nadama. Kodan rahamomi da UBANGIJI yay maka kashi-kashi ciki harda yinka musulmi mai imani daya yarda da ƙaddara da jarabawa. Ya azurtaka da dukiya badan kafi saura ba, ya kuma baka ƙyaƙyƙyawar zuciya da damar sarrafa dukiyar daya baka ta tsaftatattun hanyoyi da babu saɓon UBANGIJI a ciki, wannan ma ba dabaranka bace. Ya baka lafiya a jikinka baka kasance gurgu ba, makaho, kurma ko wani abu daban ba. Zakaji sautin kiran salla, kaji na karatun alkur'ani, kaga ayoyin alkur'anin, ka taka kafarka kaje massallaci, ka daga hannayenka ka roƙa UBANGIJI bukatunka ya ɗauka ya baka babu gajiyawa. Ya cika ƙwaƙwalwar ka da ilimin addini dana zamani danka iya shiga ko'ina cikin duniya babu fargaba. Ya baka nutsuwa da tarin hankali da mutunci ga duk wanda zai mu'amulanceka koda ya fika a shekaru. Ya azurtaka da mata har biyu da ƴaƴa a lokacin da bakai zato ko tsammani ba. Ya bama Baffah da Mammah da Granny tsahon rai kanata ganinsu kanajin farin ciki. Yayanmu duk waɗanan tarin ni'imomin basu isa susa ka yafema duk wanda yay maka kuskure ba koda yakai girman duniya? Haba Yayanmu kaifa shugabane a garemu kuma uba, duk abinda kayi dashi zamuyi koyi muda ƴaƴanmu. Wlhy aunty Farah tanada ƙyawawan halaye kawai anyi amfani da wani raunintane wajen ɗaurata akan hakan. Kai mata afuwa muma sai ALLAH yayi mana. Ka haɗamu ka runguma domin gidanka ya zama tsintsiya ɗaya maɗauri ɗaya. Kagafa yanda take jan su Anam jikinta da soyayya irin ta uwa da ƴaƴa batare da nuna damuwa ba. Ina kishinta dan nima mace ce kuma inason mijina, amma wlhy ina sonta tunda har taso jinina”.
    Ta ƙare maganar hawaye na silalo mata. Sake matseta yay a jikinsa yana bata wasu hot kissis data ƙara tabbatar da yes itama takai mace kuma abinso ga mijinta kuma ɗan uwanta uban ƴaƴanta. Cikin jin daɗin hakan ta sake bashi haɗin kai ya kuma tabbatar mata da ita ɗin mai darajace ta gaske a garesa.
     Koda suka kimtsa jikinsu baice da ita komaiba itama batace da shi ba. Dan tasan idan miskilancin yay miskilanci toshi baya magana da baki sai dai a aikace. Murzar da yay mata yanzu kuma itace amsar komai da furucin bakinsa gareta. Itama hakan ya wadatar da ita dan maimaita maganar bashi da wani amfani ko alfanu sai maida hannun agogo baya.

        Tun daga ranar ta tattara zancen shirinsa da Farah ta watsar da su gefe kamar bata fahimtar komai. Daga ƙarshe ma cemasa tai ita Danya ma take son zuwa sake duba jikin inna dan duk ƙarshen wata sai sunje dama har da shi da yaran.
    Banza yay mata akan hakan tamkar baijiba har tsahon kwanaki da sukai ɗanyi shariya da juna ita da shi itama. Sai kuma suka koma dai-dai.
    Bata sake masa maganar Farah ba ta zuba musu na mujiya. Tun suna fishe-fishesu har dai takai sun shirya batare dama ta saniba. Sai ganinsu tai ana shimfiɗa shika-shikan soyayya ko kunya babu. Duk da tanajin kishi a ranta haka ta danne ta kauda ido dan karatunta na islamiyya data koma cinye mata kaso mafi yawa na zaman gidan da rana yanzu, ga kuma su Saliha da mama A'i na ɗebe mata kewa sosai.. Dama tunda Farah ta dawo gidan ta canja salon girkin gidan kwana bibbiyu, randa taƙi zuwa garesa yay masifar yay faɗan sai dai ta bashi haƙuri kawai tace ga aunty Farah nan.
        Sai gashi tsakanin miji da mata sai ALLAH sun ɗinke abinsu batare data saniba. Duk da tanajin kishin mijinta haka ta cigaba da ƙoƙarin ganin ta danne kamar yanda itama Farah ke ƙoƙarin dannewa a yanzu, suna kuma girmamawa da mutunta junansu duk da ta girmeta nesa ba kusaba.
        Ya zaunar dasu ya musu nasiha sosai da shimfiɗa sabbin dokoki masu tsauri a garesu. Dukansu sun amsa masa da alƙawarin kiyayewa insha ALLAH.

         Tun daga nan zaman gidan ya canja salo, duk da sunajin kishin junansu haka suketa dannewa kowacce tana nuna bajintarta akan kulawa da shi da saka shaƙuwa tsakaninsu. Ashe Farah har girki ta iya iskanci ke hanata yi ko a baya. Sai gashi yanzu ta zage tanayi, tarema suke haɗuwa suyi dan haka baka iya banbance girkin wance ne inba ka ganta a turaka ba.
         AK ya ɗaukesu zuwa Family house Farah ta ƙara neman gafarar su Hajiya iya. Inda acanma dai nasihar aka sake musu daɗi kamar ya halaka Mammah. Gata ta dawo gidan aurenta ga ƴaƴanta duk suna cikin kwanciyar hankali a gidan nasu auren, ga kuma ƴan jikokinta dan Adilah ma ta haihu. Itama har nasiha tai musu mai ratsa jiki da roƙonsu su haɗa kansu kar taji karta gani, su duka ƴaƴantane bazata fifita wata akan wataba.
      Sunji daɗin hakan sun kuma mata godiya.

     Ya kuma kaisu gidan mmn sadiq data nuna jin daɗinta sosai itama da dawowar Farah ɗin. Dan dama kullum itace ke ƙara ɗora Zinneerah a kan taita lallaɓasa har matarsa ta dawo su haɗa kai su zauna lafiya. Karta yarda ya guji matarsa akan laifinta itama wataran idan tai masa kuskure koda ba irin wannan ba zai iya gudarta. Dan duk abinda namiji ya ƙware wajen yima matarsa ta farko ke amarya kikaji daɗi har kika zuga ya ƙara fusata kema wataran sai ya aikata miki fiyema da wanda yay mata. Itama kuma ta musu nasiha ta kuma karɓi Farah hannu biyu kamar komai bai faru ba, Farah ɗinma kuma ta mutuntata da gurfana a gabanta ta nema gafararta.
      Mmn sadiq tace karta damu komai ya wuce wlhy ALLAH dai ya kiyaye na gaba ya ƙara musu zaman lafiya da haƙuri da juna. Dan shi kishi tamkar jinin jiki ne ga mace, sai dai idan ta iya sararafashi zataci riba a duniya da lahira. Zafafa kishi a zuciya babu abinda yake haddasawa sai ƙunci da tarin baƙin ciki da kaucema dokokin UBANGIJI batare daka fargaba. Kaɗan daga aikin kishi ya ɗoraka a hanyar zuwa wuta ya sakeka a ciki ya kama wani kuma. Amma daka iya sarrafasa sai gaka ka tsira da mutuncinka da farin cikinka. Ka kuma zama tauraro ga mijin ga kowama, duk mai son ganin bayanka sai dai shi ya wahala kaiko ALLAH yayta ɗaga darajar ka.
     Sunji daɗin nasiharta sosai sun kuma mata godiya su duka. Dan shi kansa AK daya dawo ɗaukarsu yanda ya samesu sunata wasa da dariya sai hakan ya ƙara masa farin ciki dajin ƙaunarsu. Ya dinga kashesu da salon looks nashi da duk yake rikita manyan mata sujisu suna sake dulmiya a tarin sonsa da ƙaunarsa.

      Daga haka rayuwa ta cigaba da turzawa. AK na ƙoƙarin gina adalci a tsakanin matan nasa. Duk ƙwaƙwƙwafinka baka isa banbance wayafi so ba. Ya bar wannan sirrin a ransa da ga shi sa UBANGIJIN daya haliccesa. Idan saɓani ya shiga tsakaninki da shi bazai taɓa yarda ya wulaƙantaki gaban ƴar uwarkiba sai dai kuyi abunku ku kashe ku rufe ke da shi a ɗaki. Ku kuma shirya batare da kowa ya sani ba.
      Idan a tsakanin saune saɓanin ya shiga tunda yau da gobe sai ALLAH sukanyi ƙoƙarin ganin sunyi saurin fahimtar juna kafin abin yay musu zurfi.
      Su Anam gaba ɗaya saboginsu ya koma sashen Farah saboda jansu da take a jikinta. Little ne dai duk yanda taso ya sake da ita yaƙi. Komai zakaga yana yinsa a ɗarare indai tana a waje. Kuma babu abinda take masa mara ƙyau sai ma sakin fuska da ganin ya saki jikin da ita, amma hakan ya gagara. Takansha kukanta a ɗaki da godema ALLAH. Wani lokacin idan AK ya gani ya lallasheta da nuna mata ƙuruciyace kawai ke damun little ɗin zai daina wataran.
       Takance ita badan wani dalili take kukanba dan har ranta ta cire kallon little daga wani sashe na jikinta. Hundred percent kallon jinin Zinneerah kawai take masa. Amma koyaya tanason ya dinga sakewa da ita kamar su Anam.
    Itama Zinneerah abun na damunta dan kulum cikin yima little ɗin nasiha take amma abu ya kasa ƙarewa duk da dai yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login