Showing 159001 words to 162000 words out of 223329 words

Chapter 54 - Makauniyar Kaddara Hausa Novel Complete

21 Nov 2024

1173

Iska yaɗan furzar kansa a ƙasa. “Mahma wlhy nima ban saniba”.
    “Kamarya baka saniba, a ruwa ake shan ciki balle kace mana itama acan tasha?”. Aunty Zakiyya tai magana karon farko tun shigowarsu a hasale
         “Tabbas ba'a sha, amma inaga itakam dai acan ta shashi. Dan ni dai ban taɓa tarayya da wata mace bayan matata ba ALLAH shine shaidata. Sannan ban taɓa ganin yarinyarnan da idanuna ba sai a gidan nan. Amma kuma tabbas na yarda Abdul-Mutallab ɗa nane, ina kuma kan binciken ta yadda aka samar dashi insha ALLAH”.
      Shiru falon yayi tsahon lokaci, sai Uncle Ahmad da wani tunani yazo masa a zuciya dan shidai shedane akan AK bai iya ƙaryaba yace, “Abdul-Mutallab maganar nan ba wadda mutane zasu ɗauka bace balle su fahimceka. Amma sai nake tunanin ko kun taɓa yunƙurin yin wannan dashen na zamani da aketa nusar al'ummar musulmi rashin anfaninsa?”.
      A karon farko AK ya ɗago ya duba Uncle ɗin nasa da rinannun idanunsa. Hakama Mammah da aunty Zakiyya a razane suka dubi Uncle Ahmad har hakan ya bama Mahma da Hajiya iya mamaki. Da sauri AK ya girgiza masa kansa. “Wlhy Uncle ni ban taɓa son hakanba dan bayama birgeni, na tabbatar idan ALLAH yaso zai bani, da bai baniba kuma ƙila haka shine mafi alkairi a gareni”.
       Cikin jinjina kai Uncle Ahmad yace, “Na yarda da kai Adnan dan baka taɓa min ƙaryaba, sai dai wannan al'amarin na buƙatar bincike, musamman ga matarka kota taɓa wannan yunƙurin aka samu kuskuren ɗaukar sparm ɗinka aka saka ga ita yarinyar bada sanin ku ba ku duka tunda wannan matsalar kan faru saboda son zuciyar wasu likitocin, kokuma daga likitocin matsalar take baki ɗaya”.
       Wani irin mugun tarine ya sarƙe aunty Zakiyya har sai da aka bata ruwa. Ita kanta Mammah sai zufa take gogewa a kaikaice. Cikin rawar murya tace, “Hakan bamai yuwuwa bane, tayaya za'ai yunƙurin hakan shi bada saninsa ba, kuma shi da ke a london yarinyar na ƙauyen katsina taya ya hakan zai faru, yadai zauna yayi tunani ko wani akasi ya taɓa faruwa”.
       Hajiya iya da zuciyarta keta kaikawo da nazarin kowa a wajen tace, “Inaga to wannan maganar babbace gaskiya, mu ajiyeta a yanzu idan an gama biki lafiya saimu yita a tsanake, dan yanzu haka ga Huzaifa nata kirana kunsan ana jiranmu a wajen walimar can”.
       Baffah da shi kansa tunanin zuciyarsa ya fara canjawa daga akalar zargin Ak da yake har yanzu zuwa zancen ɗan uwansa cikin gamsuwa yace, “Hakan shine dai-dai Inna”.
      Tabbas a wannan gaɓar suma su Mammah sunfi buƙatar tsayawar zancen su sami dama da sararin yin nazari, dan haka duk suka amince. Sai dai basuso zuwa wajen walimarba Mahma ta takura musu akan saifa sunjeta dole ko shima AK ɗin zaiji sanyi a ransa ai.
      Gudun zargin wani abu daban daga AK yasasu yarda zasuje. Dan ya tsatstsare su da idanunsa da gaba ɗaya suke a birkuce da abubuwa kala-kala da shima baisan adadinsu ba.

★★

      Sun isa ƙaton hall ɗin da za'a gudanar da walima and liyafar cin abinci rana daya ƙawatu matuƙa. Ya kuma cika taf da al'ummar MANZON ALLAH (S.A.W). Ga manya manyan malamai da zasu gabatar da lectures. Sashin mata daban na maza daban babu ruwan wani da wani, hakkane ya samama AK nutsuwar da yake buƙatar samu. Suna isowa aka gabatar da addu'oi da suka shafi komai na rayuwa bayan ma'auratan, kafin a fara abinda ya tara mutane.
     Malamai sun ragargaza lectures masu ratsa jiki akan aure da zamantakewar rayuwa data saka jikin mutane da yawa yin sanyi, Zinneerah amarya da duk da basan waye mijin nataba tasha kuka itama, lectures ɗin kuma sun shigeta matuƙa. Lokacin salla nayi aka fita akai sallar zuhur sannan aka dawo aka ɗora dacin abinci, a hakanma dai malamai na cigaba da aikinsu har zuwa la'asar da aka rufe da addu'oin fatan alkairi ga ma'aurata damu da muke a gidan auren sannan aka tashi.

      Da yawan mutane daga nan suka fara kama gabansu, wasu kuma suka koma gidansu AK domin rakiyar amarya ɗakinta da za'ayi da wuri, duk da dai hajiya iya tace ƴan danya bazasu koma a yau ba kamar yanda suka sanar, tace su bari sai ALLAH ya kaimu gobe su da ƴan ɗan musa saisu tafi.
       Sunkiji daɗin haka dan sam garin ba isarsu yayiba. Musamman da kowa yake samun isashen abinci mai rai da lafiya nama har ba'a cewa komai.
     Suna dawowa ba'a zaunaba Hajiya falmata ta hau yima amarya shiri na musamman wanda ya kaisu har bayan isha'i, ana idar da salla ta kammala naɗeta cikin haɗaɗɗiyar lifaya datai mata matuƙar ƙyau kamar ba an Zinnin danya mai tallar riɗi da gyaɗa ba. Daga haka aka miƙata wajen su Baffah da manyan iyaye ƴan bauchi sukai mata faɗa da nasiha matsayinsu na iyaye gareta, sai ga hajiya iya na sharar hawaye kuma, hakama su Meenal kuka rurus suke sha abin tausayi, Sa'a ma sai ta kama kuka dama tasha wani a danya. Tinene kuwa tana kwance rijib babu lafiya dan ko a wajen walima kasa sakewa tayi, danma Yaya Atine nata mata masifa wai harda langwai daga zazzaɓi.
     Yaya Gajeje najinsu dai bata tankaba dan ita tasan mita hango tattare da Tinene ɗin, tanata ƙoƙarin dannewane harsu koma lafiya gida kawai.     
         Bayan an kwashi masu rakkiyar amarya a motoci aka fito da amarya daketa rusar kuka wadda Hajiya iya zatai mata rakkiya har ɗakin mijinta. Aiko Zinneerah na naɗe a jikinta tanata kuka ranta fal fargabar wanda zata tarar matsayin mijin nata har suka iso ƙyaƙyƙyawan gidan na AK da yaji kayan more rayuwa. Duk da yace kar iyayenta suyi komai sai da suka nuna bajintarsu suma gwargwadon ƙarfinsu. Dan kuɗin baba dana abba aka dunƙule waje ɗaya akai mata kaya ƴan ubansu da gara, hajiya iya kuwa dama itace tayi komai na kayan kitchen.
      Ɓangaren ta daban na Farah daban, duk da dai babban falon farkon shigowa ya haɗa ɓangarorin gidan uku, dole ta cikinsa zaka doshi kowanne ɓangare harna mai gidan, amma kuma kowacce a sashenta tanada faluka guda biyu kuma da bedrooms har uku sai kitchen. Tun kafin fitowa mota sai da hajiya iya ta saka zinneerah dake lulluɓe har kanta tana kuka yin addu'a, hakama da zasu shiga babban falon da sashenta.

      A lokacin da ƴan kawo amarya ke shigowa su Mammah suna sashen Farah cikin tashin hankalin sumar da tayi, dan tunda aka taso wajen walima su nan gidan suka nufo kai tsaye, tarbarau tayi da murnarta dan batasan mike faruwaba, kuma ko daɗewa dayin waya da AK bataiba. Sai dai halin da taga aunty Zakiyya da Mammah a ciki ya ɗaga mata hankali ta shiga tambayarsu lafiya? Duk yanda Mahma taso ƙwaɓar aunty Zakiyya da ido akan karta sanar mata sai da aunty Zakiyya da hankalinta ke tashe da zancen Uncle Ahmad na dashen ciki tai suɓutar baki wajen sanarma Farah zancen auren AK. Ko rufe baki batayiba Farah ta yanke jiki ta faɗi a sume.
    ALLAH ya sosu hakan yay dai-dai da shigowar AK gidan a gajiye. Hankalin sane ya tashi matuƙa shima, babu shiri ya tsaida Dr Mahmud da ya kawosa gida. Tofa shine tun lokaci suka rufu akanta da ƙyar suka samu ta farfaɗo Dr Mahmud daya sa aka kawo masa kayan aiki daga asibiti yay mata allurar barci mai nauyi da har yanzu take kanyi bata farkaba.
       Mammah sai masifa take akan wlhy idan Farah ta rasa ranta sai tayima Kabeer abinda bazai taɓa mantawa da ita a duniya ba. Tanayi tana sharar hawaye hakama aunty Zakiyya kuka take rurus dan tana tsananin ƙaunar autar tasu Farah da tausayinta ke damunsu saboda mahaifiyarsu na haihuwarta ta rasa ranta ko ganin Farah ɗin ma batayiba.
     Koda sukaji an kawo amarya Mahma ce kawai tai ƙarfin halin fita tarbarsu kar ace babu kowa a cikinsu tunda ansan suna gidan kuma. Bata nunama hajiya iya komai na halin da ake cikiba ta rungume Zinneerah tana mata barka da zuwa cikinsu. Ita dai Zinneerah ba sanin wacece tayiba tunda kanta a rufe yake, tanata dai sharar hawayenta musamman da taji mutane nata sallama suna ficewa dan ance ba zama za'ai ba. Duk maison ganin ɗakin amarya yazo gobe idan ALLAH ya kaimu ya gani da ƙyau.
     Wannan yasa Zinneerah batasan sanda hajiya iya ta sulale ta gudu ba ita dasu Yaya Gajeje. Kafinma ta farga sai jin hayaniyar tayi ta ɗauke ɗaf daga inda take sai acan harabar gidan take jiyosu.
    Zamewa tai a gadon ta kwanta tare da sake fashewa da wani irin sabon kuka maiban tausayi dacin rai.............✍

*_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*

Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.

*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_

*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_

*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_

*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_

*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_

Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.

Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍




*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*

*_TYPING📲_*


*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*


*_Ashe yau monday😂🤣🙏🏻_*


_______________________


*page 51*

...........Kamar jira ƴan kawo amarya na wucewa Farah ta farka, sai dai a yanayin data farka ɗin yay matuƙar tada hankalin su Mammah, AK daya tuna cewar tana tare da ciki ya cema Dr Mahmud suje asibiti kawai kar a rasa abinda ke cikinta. Mammah ce tai azamar son dakatarwa Mahma ta tsaidata itama ta hanyar faɗin, “Maganar Abdul-Mutallab nakan hanya, hakan shine yafi dacewa kar azo ana dana sani kuma daga baya”.
        Cikin tashin hankali aunty Zakiyya tace, “Mahma kubarta-fa komai zai dai-daita, inaga ya ƙara mata allurar barcin sai mu wuce can gidan da ita dan Abban Ameera ya kirani cewar wanda zai kawo mana key ɗin ya iso yana can yana jiranmu”.
      “Addah abi shawarar Zakiyya ɗin na tabbatar shock ne zata dawo dai-dai idan ta ɗanyi nesa da nan ɗin kamar”.
      Ak dake binsu da kallon mamaki ya dafe kansa dake neman fara masa ciwo, dan shikam dai abubuwan na neman masa yawa gsky. Mahma da wani tunani yazo mata a zuciya tace, “To babu damuwa kai mata allurar kawai sai mu wuce”.
      Kallon AK Dr Mahmud yayi, “Amma ranka ya daɗe karfa allurar tai mata illa, ni bansan ma tana tare da ciki ba da ban mata ita ba, tanada ƙarfi, nayi mamakin ma data farka a yanzu dan allurar mai ƙarfice”.
       Karan farko AK ya saki ɗan murmushi, dan shikam dai zuciyarsa ta fara raya masa wani abu game da yanayin Mammah da Aunty Zakiyya, ya ɗan lumshe idanunsa ya buɗe da gyara tsaiwarsa. Cikin rashin sakewarsa yace, “Kaga yimata ɗin kamar yanda sukace, dan a ganina zamanta a farken yafi allurar zama matsala ga lafiyar tata”.
       Kai kawai Dr Mahmud ya gyaɗa masa, dan shikam dai baimaga wani alamun ciki a jikin Farah ɗin ba. Yana ƙoƙarin haɗa allurar yace, “Amma cikin nata yakai wata nawane?”.
      Shiru Mammah da aunty Zakiyya sukayi, sai Mahma ce tace, “Kamar dai biyar ko”.
     “Biyar fa?”.
Dr Mahmud ya ambata mamaki ƙarara a fuskarsa. Ɗan duban Farah ɗin dake riƙe jikin Mammah tana kuka da wani ɗan fisge-fisge yayi ya ɗauke kansa. Batare da yace komaiba yay mata allurar kawai ransa fal wasiwasi.
     Yana gama mata allurar ko mintuna biyar ba'a ƙullaba barci ya ƙara ɗaukarsa. Kallon AK Mahma tayi da cewa, “Taimaka ka kai mana ita mota Abdul-Mutallab, ku kuma kumuje shima ya samu ya huta”.
       Babu shiri Mammah tace, “Addah ai shine zai kaimu, taya matarsa na wannan halin yaga wani ta hutu?”.
     Murmushi Mahma tayi na takaici, muryarta aɗan hasale tace, “Duk mu da muke tare da ita bai wadatarba sai shi ya kasance a wajen?. Ai ya kamata a tausaya masa ya huta ga kuma yarinya an kawo zai barta ita kaɗai kenan komi?”.
      A take Mammah ta sake tamke fuska matuƙa. Ta kalli AK da yay tamkar bayama jinsu yanata latsa waya. Sai kuma ta maida kan Mahma, “Addah to in hakane muyi kwanciyarmu anan ɗin kawai basai yayi wahalar da kike gudar masanba..”
     “Bazai yuwuba, tunda dai ga gida can da zamu zauna mu kaɗai bamu takura kowa ba, ba'a takuramu ba, can zamuje. Abdul-Mutallab ɗauketa”.
     Yanda Mahma tayi maganar babu wasa a ciki ya sakashi zura wayarsa aljihu ya tako a hankali inda Mammah ke rungume da Farah. Ɗaukarta yay cak ya fita da ita duk da nauyin datai masa saboda yanda jikinta ya saki sosai. Duk yanda Mammah keta kumbure-kumbure Mahma batabi takantaba ta tasasu gaba suka fice suma. Dan ita aunty Zakiyya ma ta ƙagu subar nanɗin dama suje inda takeson amayar da abinda ke a bakinta.
      Aunty Zakiyya ce ta jasu. Suna ficewa daga gidan AK yaɗan lumshe idanunsa da murza goshinsa yana furzar da huci. Sai kuma yay murmushi da girgiza kansa saboda harar da Mammah keta faman antaya masa da gargaɗi da idanu. 
       Juyawa yay zuwa cikin gidan dan shima wani ma zazzaɓi-zazzaɓi ke neman rufesa, sashen Farah ya koma ya kashe komai da maida ƙofar ya rufe, koda ya fito sashensa ya nufa dan yafi buƙatar watsa ruwa a yanzu. 

      ★★★

    A ɓangaren Zinneerah kam kuka taci sosai, sai da Mahma ta leƙo tai mata sallama akan suma zasu wuce, ta kuma ɗan lallasheta da ƴar nasiha sannan ta sassauta. Fitsarin da takejine ya sakata tashi dole ta shiga toilet ɗin ɗakin tayo, tana fitowa ta sake komawa saman gadon ta kwanta dan zazzaɓi takeji yana neman rufeta ga ciwon kai. Ba tare data damu da cire komai ba ta kwanta a haka dajan bargo ta lulluɓa har kanta saboda sanyi da takeji yana ratsata. Ga kuma ac a ɗakin dake aiki ta kasa kashewa.
        Batafi mintuna goma da kwanciyarba barci ya kwasheta sama-sama. A ɗan firgice ta farka saboda ƙarar buɗe ƙofa da taji, ta ƙanƙame jikinta waje guda jin tabbas mutum ne ya shigo. Sai dai ta kasa ko motsi saboda yanda zuciyarta ke wani harbawa da sauri sauri na tsananin tsoron wanda zataci karo da shi a matsayin mijin nata.
      AK da tun shigowarsa ɗakin idanunsa suka fara sauka akanta ya cigaba da takowa cikin ɗakin a hankali sassanyan ƙamshin turaren wutar da ɗakin yaji, da ƙamshin sabbin furnitures dana fenti na rige-rigen shiga masa hanci, a hankali ya sauke ajiyar zuciya yana ƙarasawa gaban gadon sosai. Hannayensa ya tura duka biyu cikin aljihun wandon blue pyjamas ɗinsa har lokacin idanunsa akan Zinneerah dake ƙudun-dune cikin bargo zuciyarta na nemam faso ƙirjinta ta fito.
       “Assalamu alaiki”. Sassanyar muryarsa ta daki cikin kunnuwanta. Sosai ƙirjin Zinneerah ya buga fiye da farko, dan idan har babu kuskure ai muryar Yayansu taji kam. ‘Kai ina ganganne’ ta ayyana a zuciyarta dake raunana.
       “Nasan ba barci kike ba”. Ta ƙara tsinkayar muryar tasa a karo na biyu, a yanzu kam kasa jurewa tayi dole tai ƙasa da bargon a hankali daga saman fuskarta. A hankali ta buɗe idanunta zuciyarta na gudu dai-dai da jinin jikinta dake tsinkewa daga cikin jijiyoyinta. A wani irin firgice ta yaye bargon babu shiri tana miƙewa zaune jikinta na rawa. “Y...y....Yayanmu!”.
      Ta faɗa da wani irin kiɗimammiyar murya dake nuna tsantsar tashin hankalinta a fili. Sosai yanda tayi ɗin ta bashi dariya, amma sai ya daure ko ɗigon fara'a babu a fuskarsa, sai dai idanunsa kafe suke a kanta ko ƙyaftawa bayayi yana ƙarema ƙwalliyar tata kallo, dan zaburar da tayi ta saka lafayar warwarewa daga saman kanta zuwa jikinta. Sai baƙar rigar jikinta mai dogon hannu data lafe da bayyana ainahin surarta da gyaran da fatarta ta samu wajen hajiya Falmata.
           Janye idanunsa dake binta da kallon yayi yana maidawa akan fuskarta, ganin yanda take ɗan ja baya da rawar jiki laɓɓanta na rawa alamar sonyin magana ya sakashi lumshe idanu ya sake buɗewa a kanta yana zare hannayensa daga aljihun wandon barcin nasa. Cikin nuna rashin damuwa da yanayin nata ya kai zaune a bakin gadon yana facing ɗinta. Hannunsa ɗaya yakai akan goshinsa yaɗan shiga murzawa. Sai kuma ya ɗago ya dubeta da birkitattun idanunsa dake rikitata, batare da yace uffanba ya miƙa mata hannunsa ɗaya alamar tazo.
     Kanta ta shiga jujjuyawa tana ƙara nanema fuskar gadon, hawaye na gudu a saman fuskarta kamar an buɗe fanfo. “Yayanmu dan ALLAH kace bakai bane ba”. Ta faɗa cikin tsananin rauni da rawar harshe.
      A karan farko ya ɗanyi luuu da idanunsa da sakin guntun murmushin da ita ko alamarsama bata ganiba, ya ɗan ƙara ware idanunsa a kanta da kai hannunsa ya shafi sajensa dake a kwance luf duk da ba gyaransa yay ba, dan koda yay wankan ma turare kawai yasa da kayan barci ya fito domin dubata. Cikin muryarsa ta rashin sakewa yace, “Bani bane mi?”.
       Cijin suɓucewar baki Zinneerah tace, “Miji!, mijin da aka kawoni gidansa matsayin matars.......”
     Ta kasa ƙarasawa saboda yanda yay bala'in kafeta da idanunsa masu cikar gashi da kwarjini. “Ban cancanta bane?”. Ya faɗa yana cigaba da tsatstsareta da idanu.
    Babu shiri tai ƙasa da kanta kuka na sake kufce mata. Kansa ya ɗauke daga kanta jin wayarsa na vibration, hannu yasa ya cirota daga aljihun wandon barcinsa yana jan guntun tsaki alamar baiso shigiwar kiranba dai. Sai dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login