Showing 81001 words to 84000 words out of 223329 words

Chapter 28 - Makauniyar Kaddara Hausa Novel Complete

21 Nov 2024

1210

aka cika mana gida”.
     Dariya Zinneerah tai tana faɗin. “Kai Granny bammafa fara miyanba”.
       “Amma kuma ga ƙamshi ya cika ko ina”  Hajiya iya ta faɗa tana buɗe tukunyar data saka kifin nan dake fidda ƙamshi mai daɗi a cikin manja. “Masha ALLAH miyar mi zakiyi?”.
       “Granny ɗanyen kalkashin nan dana gani da zanyi”.
       “Eh lallai kinyi tunani mai ƙyau, dama ɗazun Rahi tazo dashi wai ko zamuyi amfani dashi a gidanta suke ɗan shukashi”.
     “Aiko gashi yayi ƙyan fita Granny. shiyyasama ya birgeni. Kuma ta taimaka ta tsinkesa tun daga can yankawa kawai zanyi yanzu nasa a wuta”.
      “To bara na tayaki yankawa saiki haɗa miyar”.
    Babu musu ta bama Hajiya iyan, tunda dama tanason ɗan haɗa masa ko fruit salad ne haka da ɗan coconut juice idan zata iya. Ganin kifin ya mata yanda takeso ta zuba kayan miyarta a ciki da daddawa ta ƙara rufewa. Inda suke ajiye kayan fruit taje ta ɗauka komai dai-dai misali ta ajiye gefe, ta ɗauka kwakwa ta fasata itama ta ajiye gefe. Komawa tai ga miyarta taga kayan miyan yaɗan soyu, saita zuba ruwa ɗan kaɗan da kayan ƙamshi da magi amma ba star ba dan yana hana miya yauƙi. Da duk abinda take buƙata na saka miya ƙamshi ta saka ta maida ta rufe a binta da sake maida wutar can ƙasa. Dai-dai Granny ta gama yanka mata ɗanyen kalkashin. Amsa tai tana mata sannu da godiya. Granny ta bita da kallo tana murmushi. Madaidaiciyar tukunya ta samu ta saka kalkashin nan dan babu zancen wankesa shi. Tasa ruwa kaɗan da kanwa ta barsa a buɗe wutar naci daidai misali.
    Fita Granny tai dan an kira sallar isha'i, ita kuma tahau gyaran fruit salad ɗinta dan ɗan kaɗan zatayi ba yanda aikin zai mata yawaba. Saiko gashi ta gama a ƙanƙanin lokaci, tasa flavor na gwaba dana strawberry ta motsa. Kaɗan ta ɗan-ɗana, jin zaƙin ya mata dai-dai ta ɗaukesa tasa a fridge ta dawo wajen miyarta da dudduba. Komai yayi, kalkashinma ya dahu, kashe gas ɗin tayi ta koma wajen gyara kwakwar da zatayi juice itama, tabar kalkashinta dayay kauri sosai yana hucewa. Hakama miyar kayan miyanta tayi kauri yanda ko an haɗata da kalkashin bazata tsinkashiba. Sai da ta kammala haɗa coconut juice ɗinta ta saka a fridge shima sannan ta tattara kayan data ɓata ta wanke tsaf sannan tazo ta juye kalkashin cikin soyayyun kayan miyarnan ta motsa da kyau suka haɗe. Ɗanɗanawa tai taji komai dai-dai yanda take fata duk da dai akwai fargaba tare da ita har yanzun.
      “Inno an gama ko?”. Hajiya iya data sake dawowa ta faɗa tana shigiwa. “Eh Granny duk an kammala, amma dan ALLAH ki ɗanɗana wlhy inajin tsoro”.
      “Haba ɗiyar albarka nasanma komai yayi daɗi. ALLAH ya saka miki da kairan ya baki miji nagari dazai riƙemin ke gam, bar wani jin tsoro”. Kanta kawai ta duƙar tana ɗan murmushi. Sai dai a ƙasan ranta tana tunanin ita data haihu a waje ina ita ina yin aure. tafi ganema ta dage taita karatunta har itama ALLAH ya kaita lokacin da zata taimaki kanta da iyayenta......
       “Inno kinga ga naman kai nan da Rahi tai farfesu kafin ta tafi a haɗa masa dashi, sai akai masa gashi can ya dawo har yay wanka yana jira”. Hajiya iya ta katse mata tunaninta. Amsa mata tai da to tana haɗiye ƙwallar dake neman ciko mata idanu.
      Kular tuwon ta ɗauka tasa kan tire, ta zuba miyar a wani bowl mai murfi na tangaran mai haske, hakama farfesun tasa a ƙaraminsa duk ta ɗora a tiren. Fruit salad ɗin da lemon kwakwar ta fiddo a fridge duk da basuyi sanyi mai tsananiba sunyi dai-dai gamai sha. Fruit ɗin ta saka a bowl fruit salad, juice ɗin kuma tasa a jug da ruwa a wani tiren. Ta kuma gyara ɗan kwalinta cike da ƙarfin halin danne ciwon dake cinta ta ɗauka ta fito ranta fal fargaba.
     Zaune ta samesu shi da matarsa a dining ɗin. Tai sallama ya amsa batare daya ɗago daga latsa tab da yakeba. Farah kuwa bata amsaba saima harara data galla mata na tsananin kishin babu gaira babu dalili da haushin abinda hajiya iya tai mata akanta ɗazun. Ita dai Zinneerah gaishesu tai da masa barka da shan ruwa ta ajiye tiren ta koma ɗakko sauran kayan ba tare data damu da ƙin amsawar tataba.
      Harta gama shirya komai a dining ɗin bai ɗago ya kalletaba. Ta juya zata bar wajen ganin ta gama aikinta taji yace, “Zoki zuba”.
        Dawowa tai da baya cike da ƙarfin hali dan mararta ƙullewa takeyi. Sama-sama take jin tsawar Farah na faɗin, “Kinga dalla kama gabanki zan zuba masa ni tunda inada hannu”. Juyawa Zinneerah tai zata wuce dan taimakontama ita Farah ɗin tayi, amma saita tsinkayi muryarsa a karo na biyu. “Malama ki zubamin abinci nace ko”.
     Jitai kamar ta fasa ihu dan takaicinsu, ta kalli yanda Farah ɗin ke watsa mata harara kamar idanunta zasu faɗo. Shima ta dubesa har yanzu kansa a ƙasa yanata danna tab. Dawowa tayi da baya tunda tasan dai itama matar tasa ai ƙarkashinsa take duk da wannan isar tata da rainin wayo. Batare data sake kallon sashen Farah ɗinba ta fara zuba masa komai tana ajewa gabansa.
       Tana cikin zuba masa lemon kwakwar mararta tai matuƙar ƙullewa. Dole ta ajiye jug ɗin tai saurin zama a kujera tana kifa kanta a teble ɗin dan azaba.
       Karan farko ya ɗago kai ya dubeta. Farah kuma da kishi keci ta daka mata tsawa, “Kujimin ƴar barikin yarinya. bakin gama aikin da aka sakiba miye kuma na zama?”.
     Bata samu amsa daga Zinneerah ba dan bama jinta da ƙyau takeyiba. Shiko tab ɗin ya ajiye da maida hankalinsa gareta cike da nazari, ganin kusan sakan talatin bata ɗagoba yaɗan lumshe idanu ya buɗe akanta. A karon farko na rayuwarsa ya ambaci sunanta cikin muryarsa mai taushi da tarin nutsuwa da rashin sakewa. “Zinneerah are you ok?”.
       Har cikin rai da jini sai da Zinneerah taji fitar sautin sunanta akan harshensa. Ta ɗan ɗago hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarsa ta. “Ba komai Yayanmu kaina ke ciwo”. Ta faɗa tana miƙewa tabar wajen.
     Da kallo ya bita kawai, Farah kuma ta rakata da harara tanajan tsaki da faɗin, “Lallai yarinyarnan idan kikace zakishiga gonata zanko juya fuskarki daga gaba ta koma baya a gidan nan wlhy”.
         Goshinsa ya murza kaɗan, dai-dai yana maida kansa ga abincin. Ya ɗan furzar da huci yana ɗaukar juice ɗin data zuba masa kaɗan a ƙaramin kofi ya kai baki. Duk jarabar da Farah keyi akan Zinneerah ɗin bai ma nuna yasan tanayiba balle ya tanka mata. Sai dai a ransa haka kawai yakejin dariya nazo masa.

          Zinneerah kam tunda takai ɗaki kwanciya tai a sofa tana riƙe mara dan Hajiya iya na bayi tana wanka. Taja kusan mintuna goma a wajen tana murƙususu harta faɗo a kujerar dan azaba kafin Hajiya iya ta fito.
      “Subahanallahi, Inno lafiya kuwa?”.
      Cikin kuka ta nunama hajiya iya saitin mararta. “Ikon ALLAH, nikam dai wannan ciwon mara daga ina? Keda baƙya ciwon mara mai ƙarfi irin haka amma wannan karon da alama ta canja miki sallo. Kinga tashi kije kiyi wanka da ruwan zafi sosai bara na leƙa su Haneef ko sun dawo, bansan ina Khalipha ya kwashesu suka tafiba tun ɗazun.
       Da ƙyar ta amsama hajiya iyan. Sai dama ta taimaka mata zuwa bayin, ta kuma haɗa mata ruwa mai zafi tace tai wankan tana zuwa.

      Ganin yanda Hajiya iyan ta fito da hanzari daga ɗaki Yah Adnan dake cin abinsa hankali kwance matarsa na gefe tana masa hira bayan ta gama bala'in Zinneerah ya ɗago ya dubeta. Tana gab da fita yace, “Granny lafiya kuwa?”.
      Juyowa tai ta dubesu dan ita hankalinta baima kai garesuba. Cike da damuwa tace, “Moddibo Zinneerah ce bata da lafiya. Inason na duba cikin su Moos'ab ne wani yazo ya kaita asibiti kar abin ya ƙara mata tsanani”.
       Shiru yay yana kallonta kamar bazaice komaiba. Ganin Hajiya Iya ta juya zata fita yace, “Granny su da basa nan ki jira na kammala dan zanje wajen Mahmud dama”.
      Dawowa Hajiya iya ta sakeyi tana faɗin, “To Alhmdllh shikenan ma, bara naje ta shirya kafin ka kammala”. Kansa kawai ya jinjina mata yana lumshe idanu da buɗewa alamar amsawar kenan.
         Wani irin kallo Farah ta zuba masa na tsananin takaici da kishi. Muryarta har rawa yake wajen faɗin, “Wai ban ganeba. kaine zaka kaita asibitin kuma?”.
       Idanunsa ya ɗago ya dubeta ya maida ga abincinsa batare daya bata amsaba. A ƙufule ta miƙe tana cewa, “Wlhy to sai dai mutafi tare. Dan bazan yarda ka tafi da wannan shegiyar yarinyar mai kama da aljanu kai kaɗaiba. Ni wlhy bazan iyaba ka shirya mukoma gaskiya”.
     Da kallo ya bita harta shige lungun da ɗakinsa yake. A bazata murmushi ya suɓuce masa ya girgiza kansa da ɗan taɓe baki ya ɗauke kai.
        Harya kammala abinda yake ya miƙe zuwa ɗakin bata fitoba, koda ya shigo isketa yay tana waya. Yasan dai bazai wuce Mammah ko cikin yayuntaba. Dan haka bai tsaya sanin dawa takeyiɗin ba ya shiga toilet. Cikin abinda baifi mintuna uku ba ya fito. Key ɗin mota da ke a bed side drawer ya ɗauka ya nufi hanyar fita ya barta tana wayar har yanzun.
       Yana fita itama ta miƙe ta ɗauka ɗan kwalin abayarta ta bisa tanayin sallama da yayanta da shigowarta ɗakin kiransa ya shigo mata a waya. Shine ta zauna amsawa.

Sai da yay sallama a ƙofar ɗakin Hajiya iya ta amsa masa da bashi izinin shigowa sannan ya shiga. Zinneerah data fito wanka ta gama shiryawa cikin baƙar doguwar riga tana kwance a bakin gadon idanunta a lumshe hawaye na zirara. Kallo guda yay mata ya ɗauke kai ya maida ga hajiya iya data ɗakko mata hula da ɗan kwalin rigar.
          “Haka take ciwon kai?”.
  Ya tambaya kansa tsaye kamar yanda ta sanar musu ɗazun. Kallonsa hajiya iya tayi, “Ciwon kai kuma Moddibo? Zinneerah ce zata zauna yima ciwon kai raki kamar haka?. Ita jarumace ai da kake ganinta, tunda ka ganta haka ai abinda yafi ƙarfin ciwon kanne mararta ke ciwo, kuma da ba haka take mataba”.
       Jin abinda Hajiya iya tace ya sashi janye idanunsa daga kallonta ya maida kan Zinneerah data zumɓuro baki alamar bataso Granny ta faɗa abinda ke damun nataba. Baki yaɗan taɓe da nufar hanyar fita yana faɗin, “ta sameni waje”. Daga haka ya fice abinsa ya barsu da ƙamshinsa........✍



*_Sauran inji wani yace kaɗanne gobe na rage mudu😂🤒🤒._*



*_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*

Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.

*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_

*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_

*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_

*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_

*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_

Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.

Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*

*_TYPING📲_*


*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*


*Page 25*
________________________

*ZAUREN GIRKI*

Abinci na *gargajiya* ...Kuka,Taushe,Danbu, Sinasir,Waina
Abinci na *zamani* ...Afang,Edikaikong, Coconut Rice, Ofada Rice
*Garabasa* ...Salads,Pancakes, Plantain mosa, Gyaran nama/kifi kafin girki,Shirin/shinfida abinci kan table.

• A kowane sati,in shaa ALLAAH, za a koyi miya/abinci daya da kuma wani abu ta karkashin *Garabasa* .
• Duk ranar *Lahadi* za fito da sabobin *videos* guda biyu na miya/abinci da na wani abu daga karkashin *Garabasa* .
• Kowacce daga cikin masu koya zasu bibiya video su kwaykwaya su gwada yin abincin bisa ga umurnin *video*
• Kowane ranar *Asabar* za a yi *Q&A* a inda kowa zai samu yin tambayoyi akan *videos* din satin daya gabata, da inda suke neman karin bayani/gyara akan kokarinsu na gwada abincin *video* da kawunansu
• Ga wace taga dama,daga ranar *Talata* za a iya fara turowan *video* ta kokarin da aka yi na kwoyon abincin da aka kwoyar ta *video* na ranar *Lahadi* .
• Inda akwai me bukatan wani fanni na abinci,ana iya hada *aji(Special Personal Video Classes)* musamman domin wannan bukatan.Anan za a shirya live *video* sessions domin cimma wannan burin

• Za a biya dubu biyu *(#2,000)* na watan farko,sannan za dinga biyan dari biyar *(#500)* ta kowane sati ga masu bukatan shiga group dinnan namu mai albarka
• *Zen Commute,account number 0119343451 Union Bank* ,asusunmu
• Duka lokacin da aka biya sai a turomana da hoton teller ko bank confirmation akan wannan number ta *WhatsApp 0817-541-7533*
• Ana iya tuntubammu akan wannan number domin karin bayani; **0817-541-7533(WhatsApp kawai)*                                  
ZA MU FARA ZAUREN GIRKI LAHADIN SATIN FARKO TA WATAR SEPTEMBER,IN SHAA ALLAAH!

*MU TSARE MUTUNCINMU,MU KARE MAZAJENMU...MU KOYI GIRKI!!!*

_________________________

*Page 25*

............“Kajimin ja'iri, basai ka tsaya ka kamata ba kuma? Kinga Inno na tashi muje ni na rakaki”.
        Zinneerah da tonon sililin Granny yasata fahimtar shine zai kaita asibitin tace, “Granny dan ALLAH muje da wani cikinsu aunty Abidah ko su Meenal basai shiba”.
       “Keda kike a wannan halin sai kin zaɓi mai tafiya. Kinga maza miƙe karma ya tafi dan shi ba saiti ne da shi ba wani lokacin”.
      Dole ta miƙe Granny ta kamata badan taso ba. Tsaye suka samesu su duka a jikin mota, shi yana waya Farah na tsaye jingine tana danna tata wayar. Batare da hajiya iya ta damu da ganinsu su biyunba ta buɗe gaban motar ta saka Zinneerah shiga. Sai lokacin suka lura da zuwanta. Farah tabi Hajiya iya dake duban inda Yah Adnan ɗin yake da kallo. “Moddibo kuje dan ALLAH, kasan shi mai ciwo ƙosawa ne da shi”.
       Kansa ya jinjina mata kawai batare daya bar wayarba ya buɗe murfin zai shiga Farah da haushi ya kume tace, “Granny ai sai dai ta dawo baya dan tare zamuje”.
      “Asibitin? A'a idan kin bisu ni motsinwa zanji kuma tunda su Jamal basa nan. Kinga muje ciki muyi hira mai sunan ƴan gayu”. Ta ƙare naganar dajan hannun Farah batare data jira abinda tai niyyar faɗaba.
      Ta cikin mirror Yah Adnan ke kallonsu. Ya danne murmushin dake neman suɓuce masa a fuska saboda rigimar Granny. Daga haka yay horn yana harba motar zuwa gate.

         Tunda suka hau hanya baiyi ko tari ba duk da yana jin shashshekar kukan Zinneerah daka ƙudundune kanta cikin ƙafafunta data naɗe sama gaba ɗayanta ta dunƙule a kujera. Sai dai duk kiran wayarsa da akeyi tunda ya gama ta farko bai sake ɗagawaba har suka iso Shira hospital.
     Duk da darene ko ina cikin haske yake kamar ka yarda allura kaga abunka. Sai da ya gama dai-daita fakin yaɗan dubeta ya ɗauke kansa. Wayoyinsa biyu ya ɗauka batare daya mata magana ba ya buɗe ɓangarensa ya fito. Sai da ya rufo murfin ta fahimci ya fita dan haka ta ɗago cike da ƙarfin hali fuska shaɓe-shaɓe da hawaye.
    Tana ɗaura hannunta akan handle ɗin ƙofar da niyyar buɗewa ta fita tunda tasan bacewa zai ta fito ɗinba sai taji ƙofar ta buɗe. Akansa idanunta suka sauka da mamaki, sai dai ganin yanda yaci toka yasata saurin maidawa ƙasa. Gudun kartai laifi ya sata ziro ƙafa ɗaya zata fito ɗayar kuma ta riƙe. Tsareta da ido da yayi ga kuma azabar da takeci yasata sakar masa kuka.
        A ransa yace (sai shagwaɓan tsiya). a fili kam sai ya girgiza kai kawai ya ɗauke kai yana miƙa mata handkerchief. “Malama goge waɗanan hawayen tunda ba satoki naiba”.
         Duk da halin da take a ciki saida tace (bama gara wanda ya satoni da kai ba) amma a zuciya😂. A zahiri kuwa baki ta tura gaba da amsar handky ɗin nasa da keta uban ƙamshin turarensa tahau share hawayen. Shi kuma yay gaba abinsa cikin asibitin batare daya jirataba duk da ya fahimci bazata iya taka ƙafarba dan tun'a gida ya lura dama da ɗingishi ta fito sanda Granny ta kamota.
          Kanta ta ƙara maidawa cikin ƙafafu ta dasa sabon kukan takaicinsa dana ciwo. A haka Nurse ɗin daya turo tazo ta sameta. Itace ta taimaka mata ta fiddota a motar suka fito. Da ƙyar ta taka ƙafar data ƙara riƙewa zuwa cikin asibitin. Suna shigowa a bazata sukaci karo da Khalipha.
       “Kai! Beauty lafiya kuwa? Ke da wa haka?”.
        Bata iya bashi amsaba sai dai ganinsa yasata jin sanyi har cikin rai. Shima bai damu da rashin amsawar tataba ya maida dubansa ga Nurse ɗin. “Sister Sadiya ita da waye sukazo?”.
      Cike da girmamawa tace, “Ogane nidai yace naje na shigo da ita sir”.
    Yasan Yayansu suke cema oga a asibitin. Dan haka cike da mamaki yace, “Yana ina shi ɗin?”.
     “Dr Mahmud office sir”.
“Okay kuje ina zuwa nima”. Ya faɗa yana nufar wani hanya alamar akwai abinda zaiyi.

        Sai da Nurse Sadiya tai sallama aka basu izinin shiga sannan ta shigo riƙe da Zinneerah da ganin Khalipha yasaka kukan nata tsagaitawa. Miƙewa Dr Mahmud yayi yana mata sannu, shiko kansa yana duba wani file bai ɗagoba balle

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login