Showing 135001 words to 138000 words out of 223329 words
kalleta yana ƴar dariya, “Hindatu ko iya haka muka tsaya kin sami amsarki akan Adnan, dan kinji dai abinda yace, sunansa Abdul-Mutallab Kabeer Abdul-Mutallab Shira. Ba Abdul-Mutallab Hindatu Umar Kaita ba. Ballantana yanzu muka fara wasan ni da ke wlhy, dan sai na tabbatar miki ke kaɗai kikazo gidan nan badasu ba”.
“Kabeer Shira!”.
Ta faɗa a tsawace.
Shima Baffah a fusacen yace,
“Yes! I am. Hindatu Kaita!”.
Ganin yanda Baffah da Mammah sukai ɗin ya tayarma Mommy da Momie hankali, shi kansa Huzaifa ƙarjinsa sai bugawa yake dan tamkar AK yake bayason hayaniya, barshi dai da shegen surutu shima yafiyi ga wanda ya sani sosai. Farah kuwa ai sake tsurewa tayi dan bata taɓa tunanin haka Baffah yakeba. Kallon mutum mai sauƙin kan tsiya take masa.
“Dan ALLAH kuyi haƙuri ni banga abin tashin hankali ananba Yaya”. Mommy ta faɗa hankalinta tashe tana dawowa kusa da Baffah.
A fusace Mammah ta miƙe tare da kama hannun Farah da duk jikinta ke ɓari. Ta duba Baffah da manyan idanunta da har ƙwalla suke tarawa dan bala'i. “Banzo Nigeria da niyar yin fitina da kai ba Kabeer, amma tunda har kace ka shirya muje zuwa. Ina mai tabbatar maka bazan bar ƙasar nanba sai da yarona, sai kuma nasan uwar data haifa wannan ɗan da shi. In ko har aure ka ɗaura masa da ita aka samar da shi sai ya saketa, na haɗa da yaron kuma na wuce, dan yazama nawa shima”.
Wata ƴar dariya ce ta suɓucema Baffah babu zato, ya shafa kan Little yanayin kayarsa hankali kwance. Kafin ya ɗago yana nuna mata little. “Wannan shine tunani mafi gurɓata da kika taɓayi a rayuwarki Hindatu, kinsanfa ance abin cikin ƙwan yafi ƙwan daɗi. Dan haka ki sani wannan da kike gani zuciyata ne da duk ma wanda yake rayuwa a gidan nan. Kinsan kuwa raba zuciya da gangar jiki abune mai wahala ga ɓarawo. Amma tunda kema kin shirya wasan muzuba, ɗan halak ka fasa. Sai dai ki sani wasa zamuyi da basira bada hauka ba. Ki cire wannan shirmen a ranki ki nutsu waje guda wajen farautar dawo da Abdul-Mutallab gareki, nima zanyi farautar ganin ya dawo gareni daga shi har Maryam (Adilah) sannan kuma na haɗa da ɗan jikallena abin cikin ƙwan”. Ya ƙare da wani salon ɗage mata gira ɗaya.
Da ƙarfi ta rumtse ido da cije baki, harshenta har harɗewa yake wajen ambaton, “Muje zuwa mana, kaima kasan Hindatu, nama ƙwata ada da kake jin kanka Kabeer Shira balle yanzun. Wlhy saina tabbatar maka dani Hindatu bakatsiniyace ƴar asali”.
“Kika dai sata. Kamar yanda nima sai na ƙara tabbatar miki dani Kabeer jinin bauchi ne gaba da baya babu gauraye”.
Fuuuuu Mammah taja hannun Farah dake kuka dan duk a firgice take suka fice. Dama tun jiya da dare suka iso a hotel sukai masauki.
“Amma Yaya miyasa zaka biye mata? Kasan fa Hindatu dama can ƴar zafin kai ce. Dan ALLAH karku saka yaranku a rikicinku, gashi ma harda jiƙa da shi baima gama saninkuba da ƙyau har yanzun”.
Murmushi Baffah yayi yana kallon little. Hankalinsa kwance yace, “Zai sammu ne Bilkisu. Zafin kan Hindatu kuwa zan sauke mata shi a wannan karon dan na fita itama ta sani. Wasu dalilaine kawai yasa na barta ko a can baya ɗinma”.
Shiru falon yayi zuciyar kowa da fargaba. Musamman ma Momie da ayanzu ta gama sallama ma bala'i da gadarar Hindatu.
Silalewa Huzaifa yayi ya fice, dan abinda kawai zuciyarsa ke basa da wannan game ɗin kafin a farashi Hajiya iya ta dawo gidan nan. Inba hakaba Mammah zata iya bin ta wata hanyar ta sace koda little ne ta gudu dashi idan Ak ya gagareta a yanzun. Wayar Khalipha ya kira.
A lokacin yana kwance zazzaɓi ya rufesa, dan duk yanda yaketa ƙoƙarin danne damuwar rasa Zinneerah hakan na neman fallasa kansa. Amma dai yanata roƙon ALLAH ya rufa masa asiri ya cire masa ita a rai, dan baya buƙatar Yayansu dawowa ya gansa a wannan halin. Ɗagawa yay cikin dauriya, bayan sun gaisa Huzaifa ke tambayarsa ko lafiya?. Cikin dakewa yace masa a barci ya tashi.
Cikin gamsuwa Huzaifa yace ya haɗasa da Hajiya iya, shima kuma ya zauna a wajenta dan maganar ta shafesa. Amsa masa da to Khalipha yayi yana tashi ya fito. A falo ya samesu su duka zaune suna hira da kallo. Ya miƙama Hajiya iya wayar yana sanar mata Huzaifa ne.
Amsa tai cikin tsokana ta fara da faɗin, “Ɗan nema mun shirya kenan? Bandama abinka nima ai bazanso aima autata kishiya ba”.
Damuwar da Huzaifa ke a ciki ta tashin hankalin daya gani ya sakashi cewa “Granny magana zamuyi ni dake da Khalipha ”.
“Lafiya dai ko?”.
“Da sauƙi dai”.
Tsaye hajiya iya ta miƙe tabar wajen zuwa ɗaki Khalipha ya bita. Daga haka Huzaifa ya yanke kiran shi kuma ya kirasu a video call. Bai ɓoyema Hajiya iya da Khalipha komaiba daya gama faruwa yanzun nan. Cikin matsanancin mamaki Khalipha yace, “Dama Nigeria wai su aunty Farah ɗin suka taho?”..
“Gasu harma suna ƙulla game da Baffah. Granny inaga ki dawo gaskiya dan wannan al'amarin ba wasa bane. Na tabbata Mammah zata iya sace little shima, dan nidai yanda ta nuna ɗin na tsorata. Ni kuma wlhy yanda na fahimci Yayanmu nason Abdul-Mutallab banason ta rabashi da shi. Bama shiba koni yaron ya shiga raina. Hakama yaran gidan nan wlhy suna tsananin ƙaunarsa, dan yanda suka shaƙu da shi aduk da ba gidan yake ba ya isa amsa gamai kallo. Khalipha zan turo kuɗi a shiyama Granny tahowa, idan lokacin ganin likitan yayi saita koma”.
Cikin gamsuwa Khalipha ya gyaɗa masa kai kawai. Dan shima ya gamsu da hakan, shi kansa zai bisu dan yasan Yayansu nacan cikin damuwa da tashin hankaki dama gashi ya tafi a birkice.
A ɓangaren AK kam koda ya koma ɗakinsa duk abinda ke faruwa tsakanin Baffah da Mammah yana jiyosa, har game ɗin da suka ƙulla tsaf yaji, mamakin Mammah ya sake kamashi jin kuma little ɗinma ya zama abin harinta bayan ita ta gama bala'i ranar a london.
Safa da marwa ya shigayi a ɗakin yana tunani da nazarin matakin dazai ɗauka akan Farah dan harga ALLAH yana tsoron Mammah ta cigaba da busar masa da idonta akan wannan halayen da sam basa birgesa. Dolene yayi wani abu kafin wankin hula ya kaisa dare.
Ciwon da kansa ke masane ya sakashi tattara komai ya ajiye ya koma gado ya kwanta. Duk da tarin ayyukan dake garesa a yinin yau dan yanason komawa london gobe idan ALLAH ya kaimu baijin zai iya fita a gidan. Maganar komawama babu ita tunda su Mammah sukazo nan ɗin. Dan dole ya haƙura har sai yaga sun koma.
_________________★
Babu wanda yasan mi Huzaifa ya ƙulla. Cikin dare sai ga baƙin london. AK na zaune bisa sallaya yana karatun Al-qur'ani bayan kammala nafilfilinsa ya ɗanji maganganu sama-sama. Mamaki ya kamashi duk tunaninsa Farah da Mammah ne suka kwana a gidan, dan shi da wuri yay barci jiya saboda allura da Dr Mahmud yazo yay masa kasancewar jininsa ya hau sama sosai dalilin ɓacin ran safiyar jiyan. Little ma yau a wajen su Momie ya kwana, tunma fitar da Baffah yay dashi bai sake ganisa ba sai da yamma Huzaifa ya shigo tare dashi duba jikinsa. Da Abidah kuma ta shigo kawo musu abinci ya maƙale mata.
Bai tashi ba sai da yakai inda ya dace, Al-qur'anin ya rufe ya tashi ya fita a ɗakin. Turus ya tsaya yana kallonsu Meenal dake shigowa da kaya, ga Hajiya iya zaune cikin kujera tana shan ruwan da Zinneerah ta ɗakko mata a kitchen. Murmushin kwantar da hankali Hajiya Iya tai masa. Yayinda su Jamal suka shiga gaishesa murya ƙasa-ƙasa dan darene sosai kusan ƙarfe uku ma.
Da ƙyar ya iya ɗaga ƙafarsa ya tako garesu, Zinneerah da sai yanzu hankalintama yakai garesa dan ta juya baya a yanda take tsaye ta ɗan matsa ta bashi hanya murya ƙasa-ƙasa tace, “Barka da dare Yayanmu”............✍
*_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*
Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.
*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_
*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_
*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_
*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_
*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_
Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.
Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*
*_TYPING📲_*
*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*
_________________________
*Page 45*
...........Sai da ya kai zaune sannan ya ɗan dubeta ya kauda kansa yana maidawa ga Hajiya iya mamaki har yanzu shimfiɗe a fuskarsa. Kansa ta shafa tana murmushi. “Mamaki ko?”. Ta faɗa tana kamo hannunsa cikin nata.
Cikin ɗacin murya yace, “Amma Granny yanz......”
“Shiii” ta faɗa tana girgiza masa kanta alamar kar yace komai. Badan yasoba dole yay shiru yana binta da kallo. Barin wajen Zinneerah tayi dan kasancewarsa a wajen yasa taji ya cika mata fili kamar yanda takeji a duk sanda yana a waje. Handbag ɗin Hajiya iya ta ɗauka tabi bayan su Bahijja da har sun shige, barci da gajiyar da take ciki ya haddasama tafiyar tata sanyi sosai fiye da ko yaushe.
Shigowar Khalipha ya sanya Ak dake binta da kallo juyawa ya dubesa. Murmushin ƙarfin hali Khalipha yayi da matsowa ya rungumesa yana jera masa kalmar “I'm sorry yayanmu”.
Komai baice masaba, sai kansa kawai daya ɗan kaɗa yana miƙewa. “Dare yariga yayi nisa, yakamata ku kwanta ku rage gajiya”. Daga haka ya nufi ɗakinsa ransa duk babu daɗi da dawowar tasu, dan shi ba haka yaso ba.
Ƴan gidan babu wanda yasan da dawowar ƴan london sai washe gari, a take suka rikice da murnar dawowar Granny, yayinda Baffah kuma keta mamaki, sai dai dariyar da yaga Huzaifa nayi suna magana da Khalipha ƙasa-ƙasa ya sashi fahimtar sune suka ƙulla komai. Uffan baiceba ya shiga layin ƴan murnar ganin hajiya iya shima.
Sai da duk suka lafa da gaishe-gaishe da tambayar jiki sannan su Zinneerah suka fito suka gaida Baffah suma. Cike da jin daɗi da kulawa yake amsa, dan ƴan kwanakin da sukai acan harsun ƙara canja kala.
Sai da kowa ya nutsa sannan Baffah ya samu zama da Granny shi da Mommy da hajiya iya keta murnar ganinta da kiranta autarta. Yanda Mommy ke nane da hajiya iya sai hakan ya birge Zinneerah har little ɗinta ya faɗo mata a rai da mamanta itama da baba. Murmushi tayi a zuciyarta tana mai begen ganinsu.
Kamo hannunta Mommy tayi ta zaunar kusa da ita tana faɗin, “Masha ALLAHU, lallai yarona ya iya zaɓe, dan ɗiyar tawa kam badaga nanba”.
Kunyace ta kama Zinneerah duk da bata fahimci inda zancen na Mommy ya dosaba. Sai kuma can gefen zuciyarta ke raya mata ko dai Moos'ab ya faɗa musu wani abune?. Sosai gabanta ya faɗi, taɗan saci kallon Khalipha dake ƙoƙarin fita zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Bata gama kammala tunanintaba ta miƙe ganin kowa ya fice a yaran sai ita kaɗai. Itama ficewa tai tabar su Granny dan taga alamar magana zasuyi.
Kayan barcine wando da riga a jikinta, sai dai ta ɗora hijjab mai hannu a sama kalar pink mai haske daya kai mata har gwiwa, gashi ya ɗau guga dan da zatai salla ta cirosa ta saka.
Fitowarta dai-dai da shigowar AK ɗauke da little a hannu, kamar daga sama taji muryar gudan jininta na ambaton, “Aunty! Aunty!”.
Da sauri ta ɗago ta kalli hanyar shigowar duk da zuciyarta bata yarda da abinda tajin ba. Cikin sa'a kuwa sai a kan little daketa zillo daga jikin AK alamar zaizo wajenta. Shiko yaƙi sakinsa sai ma kafeta yay da idanu kai tsaye hankalinsa kwance.
A hankali ta motsa laɓɓanta wajen ambaton “Little” da mamaki shimfiɗe a saman fuskarta. Ga wani bugawa da ƙirjinta keyi saboda matsanancin kamannin yaron nata da Yayansu da suke ƙara bayyana kansu a koda yaushe. Musamman yau da fuskarsu ke gab da juna kuma little ɗin tamkar ya ƙara girma da wayo.
Duk yanda taso ɗaga ƙafarta zuwa garesu ta amshi little ɗin ta kasa, haka ta cigaba da tsayuwa harshi ya fara takowa a hankali yana nufota. Tsitt falon yayi kowa ya zuba musu idanu ƙasa-ƙasa, musamman su Mas'ood da sukasan mike tsakani yanzun. Su Jamal dai yanda Yayan nasu ke kallon Zinneerah ɗinne da yanda tayi itama ya basu kala suka tsaya kallo dan son ganin mike shirin faruwa.
Gab da ita ya tsaya, batare da yayi maganaba ya kamo hannunta ɗaya ya ɗaura na little akai. Kafin ya saki yaron gaba ɗaya gareta yana motsa laɓɓansa a hankali yanda ita kaɗai zata iya jinsa, itama ɗin sai da taimakon motsin laɓɓansa. “Sai na tsone wannan idanun”.
Sosai taji wani irin shock saboda jin hannayensa da nata na neman sarƙewa waje guda lokacin da yake sake mata little, magarsa da yanayin da ta ji ya sata tura baki da ɗan juya kwayoyin idon dazai tsokale batare da tasan tayiba.
Leɓensa na ƙasa ya wani cije ganin yanda ta tura baki ga idanunta sun fara tara ƙwalla suna wani farfar. Ya saki wani munafikin murmushi da ya nema sakata sakin little ɗin ƙasa yana ja da baya. Da wani irin slow tafiya ya raɓata ya wuce ƙamshin turarensa na sake bugun hancinta.
Babu shiri ta ƙanƙame little jin zai suɓuce mata. Suko su Saifudden suka shiga sunne kawuna ƙasa suna dariyar shaƙiyanci ƙasa-ƙasa. Su Bahijja kuma da basusan dawan garinba bakuna suka saki cike da mamaki da al'ajabin abinda Yayan nasu yayi yanzun, amma ya fiske ya wucesu tamkar baisan da zamansu a wajen ba.
Yana shigewa ɗakin Hajiya iya su Mas'ood suka shiga tafawa da juna. Khalipha yay ƙasa da kansa yana sakin murmushi da ƙoƙarin kauda komai dake ransa dan yasan dai ta ƙare. Koda ace ya furtama Zinneerah so Yayansu ya nuna yanaso wlhy zai iya sadaukar masa. Ballema ALLAH ya soshi bai taɓa koda nuna mataba duk da kuwa tun sanda ya haɗu da ita a gidan tai caraf da zuciyarsa. Dan bazai saka haɗuwarsu ta farko a lissafi ba, saboda kallon matar aure yake mata. Duk abinda yay mata kuma tausayine a wancan lokacin ba so ba.
Moos'ab ma dai daurewa yake matuƙa wajen danne komai, dan yayi alƙawarin koda yaƙi sai ya cire Zinneerah a ransa ta koma matsayin matar Yaya da ƙanwarsa har cikin zuciya.
Zinneerah kam ƙanƙame little tayi a jikinta da sauri mamakin abinda Yayansu yayi na neman kasheta da ranta. Ta bisa da kallo harya shige ɗakin hajiya iya ko waiwayosu baiyiba. “Aunty!!” little ya faɗa da ƙarfi cikin kunnenta yana bubbuga mata kafaɗa. Babu shiri ta juyo garesa tana sauke tagwayen ajiyar zuciya. Sai kuma ta saki murmushi da lakace hancin little ɗin tana faɗin, “Haba bawan ALLAH kashemin dodon kune zakayi ne? Waya kawoka nan?”.
Bata da mai bata amsa. Danshi little ma dariyarsa ya saki maiban sha'awa saboda lakace masa hanci da tayi, ya kwanta a kafaɗarta yana zagayo hannunsa ɗaya a wuyanta zuwa ɗayar kafaɗarta. Hannunta ta ɗora akan gadon bayansa tana shafawa a hankali da murmushi, murya ƙasa-ƙasa tace, “I miss you my heart, ALLAH ya albarkaci rayuwarka, ya baka kariya a kowanne sakan na agogo”.
A ɗakin hajiya iya kuwa koda AK ya shiga tararwa yay su Baffah na magana. Baffah na zayyanema Hajiya iyan yanda sukai da Mammah. Gaishesu yayi, duk suka amsa masa da kulawa. ya yunƙura da nufin fitowa ya basu waje Hajiya iya ta dakatar dashi ranta a ɓace dajin abinda Mammah tazo tayi.
Komawa yayi ya zauna kansa a ƙasa dan yaƙi yarda ya kalli kowansu, bayason suga damuwar dake kwance a cikin idanunsa.
Cikin kaushin murya Hajiya iya tace, “Ina maka murna da samun yarinyar ƙwarai kamar Zinneerah moddibo, itama kuma ina tayata murna da samunka matsayin miji. duk da har yanzu zuciyata ta gaza hasaso ko tunanin ta yanda kuka samar da Abdul-Mutallab. Amma a dalilin wani bayani da Khalipha yaymin yasani shiga wasuwasi, zuciyata kuma ta ƙara shiga ruɗani da bayanin mahaifinka akan abinda ya faru randa aka sanar maka yaron jininka ne. Sai dai hakan dakai ba shike nuna zan yarda dakai ɗari bisa ɗari ba Moddibo har saina san gaskiyar al'amarin nan. Amma zan cigaba da roƙon ALLAH ya bayyanamin gaskiyar kafin nabar duniya. Ada nayi tunanin barin tarewar Zinneerah harta kammala karatunta na sakandire. Yanzu kuma na canja shawara saboda dalilai masu yawa. Ciki kuwa harda gadaran da mahaifiyarka keson nuna mana akanka da ƴar uwarka, tunda dai ita na fahimci batasan kawaiciba. Kaje daga yau ka fara gyaran gidanka, ka kuma shirya haɗama Inno lefe dan nan da kwanaki goma zata tare”.
Ba AK kawai ba hatta Baffah da Mommy sai da suka ɗago suka kalli Hajiya iya. Cinkin ɗan rawar baki Baffah yace, “Amma Inna karatunta fa?”.
“Tayi a gidansa”.
Ta bama Baffah amsa kai tsaye babu alamar wasa ko sassauci a saman fuskarta. Ɗan ajiyar zuciya Baffah ya sauke duk da shima bawai yana nufin wani dogon zango Zinneerah zata kaiba. Dama