Showing 150001 words to 153000 words out of 223329 words

Chapter 51 - Makauniyar Kaddara Hausa Novel Complete

21 Nov 2024

1182

jata ɗakin da tasa aka ware musu ta ɗora aikinta daga inda ta tsaya gudun karsu cigaba da cinye lokacin a banza.

     Washe gari tun kusan gabannin azhar aka fara karɓar baƙuncin dangin Mmn Sadiq na ɗan-musa a danya. Hakan ya ƙara tabbatarma Inna lallai bikin na gaskene ba wasa ba. Sai kawai ta zauna ta fara kuka rirus ƴaƴanta na lallashinta. Tinene kuwa dariya taita kwasa dan itako ko'a jikinta. Tama nanema Zinneerah ne kamar basuke zuba faɗaba a baya.
         Bayan la'asar itama mmn sadiq ɗin sai gata da tawagar ƴan kano. Gida ko ya sake haukacewa da murna. Ita da Inna suka shiga kallon kallo. Mmn sadiq na ganin tsufan inna da komawarta kamar wata zararriya. Inna na kallon komawar mmn sadiq ɗanya shataf ga ƙyau dajin daɗi da kwanciyar hankali tattare da ita.
    Cikin rashin damuwa da yanda Innar ta tarbesu Mmn sadiq tashiga gaisheta. Banza Inna tai mata dan idan tai magana to lallai bazata zama mai daɗiba. Fitar mara daɗin kuma shine zai zama tabbatar sharaɗin baba a gareta. Haka kawai yasata zaɓar yin shiru, amma tana ƙullama zuciyarta abinda zata aikata musu wanda sai sunyi nadamar dawowa cikin rayuwarta su dukansu.

      Duk wani abinda mmn sadiq zata iya buƙata na abincin da ƴan uwanta zasuci da abinta tazo, hakan yasa suna isowa babu jimawa ta bada aka saya mata icce mai yawa, ta kuma ware kuɗin ruwa. Duk da abin yama baba ciwo baice mata komaiba, dan ganinta kawai sai da ya sakashi share ƙwalla, yanason Hauwa'u matuƙa, ƙaddarar iyakar zamace kawai ta shiga tsakanin su da sharrin Inna.
      Tuni Zinneerah ta shige cikin dangin mahaifiyarta da suka nuna damuwarsu akanyi watsi da lamarinta sunata neman afuwarta. Ita dai nata murmushi ne da tabbatar musu babu damuwa. Daga haka aka shiga shagalin biki.

         Batare da Zinneerah tasan da zuwan su Bahijja ba sai gasu suma kusan biyar na yamma driver ya kawosu, taji daɗi matuƙa dan sune dai ƙawayen dama. Garama isowar ƴan ɗan musa da sakina yasa taɗan samu ƙawaye, Tinene nata ɗari-ɗarin shiga cikinsu Zinneerah ta jawota tare da gabatar musu da ita.
    Sukam babu ruwansu basusan wulakanta mutaneba, hankali kwance suka amsheta babu wani nuna ƙyama gareta ko makamancin hakan.

*KANO*

        A kano ma dai gidan hajiya iya ya ɗauki haramar dangi da abokan arziƙi, dan dole AK yabar gidanma gaba ɗaya ya koma nashi dayasha gyara inda za'a saka amarya dama Uwargidan kanta. Dan ya ƙullama Farah batare data san dawan garinba tanacan katsina suna jiran tsammani ita dasu Mammah.
       Ƙiri-ƙiri AK yace bai yarda da wata dinner da shirme ba. Hajiya iya tasan kishinsa na tsiya, amma batai zaton zai nuna akan Zinneerah da aka aura masa babu neman shawara ba, dan duk da bikin Farah Mammah ta nuna musu iko akansa haka ya hana yin kowacce bidi'a. Ba kuma komai yasa hakaba sai kishi, dan AK nada matuƙar kishi gaskiya abin a jininsu yake kam da gaske.
      Amma duk da haka dai an shirya walima da liyafar cin abincin rana, dan Baffah yace bazasuyi biki lami ba, Khalipha kuma da su Huzaifa suka shirya fati iyakar su mazan kawai dan gayyato abokan AK na kasuwa dana makaranta sukai sosai batare daya sani ba. 
       Abin mamaki kuma sai ga Uncle Ahmad da iyalansa babu zato babu tsammani, sai baffah da AK ne kawai suka san da zuwansu. A take gidan ya ƙara harmutsewa da farin ciki, babu wanda yabi takan matarsa daketa faman yatsine-yatsine, ƴaƴanshi kuwa dake a ɗarare saboda rashin sanin dangi AK ya musu jan ido tunda shi ba baƙonsu bane. Aiko sai gasu sun saki jiki a cikin su Saifudden.
       Hajiya iya kuwa duk da haushin uncle Ahmad ɗin da takeji saita daure ta danne komai dake ranta ta tarbesu da farin ciki da ƙewa. Uncle Ahmad ya rungumeta yana hawaye itama tanayin nata. Daga ƙarshe dai su Mommy suka lallashesu akan suyi haƙuri.
          

*KATSINA*

       Ta wajen su Mammah kuwa yau Farah ta haɗa kayanta tunda safe tace zata wuce kano sabida cimata ƙaniya da Mahma tayi a ɓoye a daren jiya, ta kuma nusar da ita inhar bata daina biyema Mammah da aunty Zakiyya ba to wlhy ƙwaɓarta na gab dayin ruwa. Dan AK zai iya ɗagama mahaifiyarsa ƙafa kodan kasancewarta uwa a garesa amma ita wahala zatasha, ƙarshema ta ƙare da saki idan bata maida hankalinta jikintaba.
     Kalmar sakin nan itace ta rikitata tun a daren ta shiga kiran AK amma yaƙi yin picking call ɗinta, daga ƙarshema ya kashe wayan duka. Wannan ruɗanin ya sata shiryawa da farar safiya tace itafa sai kano.
    Masifa Mammah da Aunty Zakiyya suka shiga mata akan hakan amma taƙi saurarensu tace suyi haƙuri itadai zataje ƙilama ta samo amsoshin da suke zaman jiran nema ga wanda ke musu bincike. Ba ƙaramin haushi abin ya basuba, musamman ma aunty Zakiyya data nuna har a fuskarta, sai dai tai shiru bata faɗi abinda ke bakintaba saboda wani dalilinta.
     Lallaɓa Farah Mammah tasoyi. Ta kamota jikinta cikin lallashi take faɗin, “Haba Farah, kinsan dai komi muke akanki mukeyinsa, bakuma zamuyi abinda zai cuta miki ba. Indai Abdul-Mutallab ne zaiyi fushinsane ya gama ma ya dawo lallaɓaki da kansa. Ni banason ne dangin ubansa su maidaki kamar wata mara gata shiyyasa kikega ina haƙilon nan. Dagani harke taimakon juna mukeyi, banason rasa Abdul-Mutallab a rayuwata, kema kuma nasan bazakiso ki rasashi ba ai. Kuma wannan sakacin namu shi zaisa ya suɓuce mana ɗin dan wannan kakar tasu da Kabeer kansu kawai suka sani, sosuke su rabani da shi”.
      Cikin rashin damuwa Farah tace, “Amma Mammah sai nake ganin kamar bata hanyar da mukebi zamu iya maidoshi garemuba. Kinsan dai yanada taurin kai, garama ki bari na kasance a kusa da shi maybe naji komai dake faruwa sai mu magance cikin sauƙi”.
      Wani alama Mahma taima Farah da ido tana sakin murmushi da ɗauke kanta gefe kamar batasan sunayi ba.
     Cike da masifa Aunty Zakiyya tace, “Mammah dan ALLAH barta taje, itace zatasha wahala a hannunsu ai bawani shege ba, su dangin miji har wani abin kwantarwa kai ne. Wlhy banason dangin miji bakuma zan taɓa sonsuba musamman irin naki. Kina dai ganin duk sadaukarwa da Mammah tayi ta bar karatunta da ƙasar data tashi a ciki ta biyo Abbansa daga ƙarshe mata har uku ya aure sai kace wani bazazzage (zazzagawa😂😜🙏🏻), mi ake da namiji mai shegen aure-aure. Kema idan kikai wasa haka kakarsu zatasa Abdul-Mutallab ɗin yayta aure-aure shiyyasa mukeson baki kariya tunkan faruwar hakan amma kina neman watsa mana ƙasa a ido”.
      Wani irin tuƙukin bakin cikine da kishi ya tasoma Farah, a take tsanar da Mahma ta fara rage mata nasu Hajiya Iya ta ƙara dawo mata sabo, ganin yanda ta fara nutsuwa da maganar aunty Zakiyya yasa Mahma saurin tsoma musu baki.
      Nikuwa da zakuji dakun barta ta tafi ɗin, ta hakanne kawai zamusan mike faruwa? Sannan muji ta tushiyar da aka samar da yaro, tun farkoma da haka kukayi da an wuce wajen, dan irinsu Abdul-Mutallab kwantar da kai sukafi so ga matansu ba shirme da hayaniya ba. Yanda yakeson Farah data lallami kuka bisa ko kuka sakata tabisa ita da kun kamo bakin zaren. Su kuma danginsa wannan kauɗin da kuke sakata tana musu shi zaisa su sakashi ƙara auren dan zasuga tanada ƙarancin tarbiya, tun farko data bisu a yanda sukeso da bahaka ba, kudaiyi tunani gaskiya”.
        Zaram Farah ta miƙe tana faɗin, “Mahma maganarki gaskiyace wlhy, ni dai kuyi haƙuri Mammah bara naje, duk halin da ake ciki zakunaji ta waya insha ALLAH ”.
    Daga haka bata saurari cewarsuba ta fice abinta dan Mahma ma tama driver dazai kaita magana.
    Daga aunty Zakiyya har Mammah sun shaƙa, sai dai yanda Mahma ta haɗe gabas da yamma yasasu kasa cewa komai. Sunaji motar data ɗauka Farah ta wuce badan sunso ba.

     Tafiyar Farah kano da kusan awa shidda wanda suka saka ya musu bincike ya iso gidan. Ko gaisuwar kirki basu bari sunyi dashi ba suka fara jera masa tambayoyi akan aikin da suka bashi. Sanin halin aunty Zakiyya yasa baice komaiba ya miƙa musu takardun hannunsa.
      Mahma data fahimci komai zai iya faruwa ta dakatar da Mahma daga bude envelope ɗin, “Nikam da kun sallamesa ya wuce sannan zaifi”.
    Babu musu Mammah ta miƙe ta ɗakko masa sauran kuɗin aikinsa ta bashi, yaji daɗin haka kuwa ya tafi yana musu godiya, dan ya tabbatar da ace sai da suka duba babu abinda zai samu.

         Aunty Zakiyya ce ta fara cin karo da invitation ɗin walima da za'ai jibi idan ALLAH ya kaimu da liyafar cin abinci, jikinta har rawa yake wajen miƙama Mammah. Itama da taci karo da hoton Zinneerah da AK a take ta miƙe cikin rawar jiki tana kallon invitation ɗin. Wani shegen ashar ta kwaso ta dire akan Baffah.
     Mahma da dariya ke neman kufce mata tai saurin riƙo hannunta tana girgiza mata kai ganin ta doshi ƙofar fita. “Hindatu ki nutsu mana, faɗamin mike faruwa?”.
     “Ai komaima ya faru Addah, ni Kabeer zai rainama hankali, yasan mi yake ƙullawa akan Abdul-Mutallab shiyyasa yace muyi game. Na rantse da ALLAH sai na nunama guy ɗin nan asalin color ɗina. Na shiga uku shikenan ya ƙwacemin yarana. Wlhy bazan bashiba ko sama da ƙasa zai haɗe......”
      “A'a bama sai sama da ƙasa ya haɗeba kwantar da hankalinki”. Mahma ta faɗa tana zaunar da ita a kujera. Amma ina Mammah zillewa take tana botsewa hawaye fal fuskarta wasu na korar wasu. Sai masifa take tamkar zata haɗe harshenta. Tana ta rantsuwar saita maka Baffah kotu akan ƴaƴanta dan bazata yarda ya rabata dasuba. Kuma auren AK ta rantse saita rabashi da Farah kawai zai rayu.
    Aunty Zakiyya ma masifa take iyakar iyawa. Sai dai ita Mahma batabi takantaba dan nata mai sauƙine. Da ƙyar Mahma ta samu ta taushi Mammah akan ta bari sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu suje Kano ɗin suyi nagana da Baffah. Sanin Baffah na matuƙar ganin girma dajin maganar Mahma yasa ta haƙura akan sai zuwa goben, sai dai tanata neman no ɗin AK a kashe, dan dama Mahma ta sakashi ya kashe wayar, baƙon na zuwa ta turama AK text message.

___________★

      A kano kam lafiya lau Farah suka isa. Kasancewar dama shirine tsakanin AK da Mahma kai tsaye gidansa aka wuce da Farah ɗin. Taji daɗin hakan dan bata ƙaunar zuwa family house ɗinsu dama. Ta gwammaci suyi zamansu nan su biyu hartaji gaskiyar zance akan little. Dan ba ƙaramin yaƙi zatai da zuciyartaba wajen bin shawarar Mahma akan ta kwantar da hankalinta wajen AK.
      Shiko AK duk da abinda tai masa naƙin bin umarninsa datai ta koma haka ya danne yay mata tarba data bata mamaki. Daga ƙarshema suka shiga duniyar soyayya. Biye masa tayi da ƙoƙarin danne damuwarta, amma duk da haka sai da ta tambayesa ina ya samu gida?.
     Murmushi kawai yay mata da kissing goshinta, a AK ɗinsa data sani mai tattalinta da bata kulawa ya amsa mata da cewar, “Gidanki ne da baƙyason zuwa, ina fata dai komai ya miki?”.
       Fuska taɗan ɓata tana gyara kwanciya a jikinsa, “My hero ko yamin miye amfaninsa tunda ba zama cikinsa zanyiba, dama ka sayar kayi wani hidimar da kuɗinka danni nanda sati gudama zan koma london”.
     Wani shegen murmushi ya sakar mata da kashe mata ido ɗaya, yace, “Yayi Mrs Shira, nifa shiyyasa kike matuƙar birgeni”.
     Yanda yay mata ɗin ya sakata nishaɗi ta ƙara ƙanƙamesa tana dariya. Da ga haka suka sake komawa duniyar masoya ƙasan ran kowa da abinda ya damesa, sai dai sunata ƙoƙarin ɓoyema junansu bisa mabanbanta dalilai.

         Washe gari tunda safe AK yabar gidan bayan Khalipha da kansa yazo ya kawo musu breakfast, lokacin ma Farah nashan barcin gajiyar murzar juna da sukai jiya, shima sai note ya bar mata suka fice tare da Khalipha.

*_DANYA_*

      A Danya shagalin biki ake na gaske, dan dangin mmn sadiq har safiyar yau zuwa sukeyi, hakama abokan arziƙinta na nan danya sunta zuwa mata baici duk da zuwa yanzu ta wuce da saninsu. Kusan goma na safe sai ga dj da kayan kiɗa dasu Haneef, dama sun haɗa ɗan meeting nasu zasuzo Danya su cashe tunda Yayansu ya hanasu a kano, su dukansu suka taho har Adilah da ƴaƴan Uncle Ahmad da zuwa yau dai sun zama ƴan gari kodan halin su Haneef na barkwanci.
    Sosai isowarsu da dj ya karama bikin armashi, dan a take suka warware sauti biki ya ɗau harama ƴan danya suka ƙara shaidawa. Dan su Meenal da ƴan ɗan musa filin rawa suka shi su Moos'ab suka dinga zazzaga musu liƙi. Yaran gari dana dj na daka wawa. Al'amarin kamar wasa saiga biki yayi armashi, dan ita Zinneerah harma ta faraji a ranta ko Moos'ab ɗin aka aura matane.
    Tayi ƙyau cikin less lemon green da ratsin orange, Meenal ta tsara mata kwalliya ta fito ɗas a amaryarta abin shawa da birgewa. Gyaran da tasha yana nuna kansa a fartarta da ƙamshinta da duk inda ta zauna sai ya cika waje. Ga lalle tasha a daren jiya da yay matuƙar mata ƙyau. Badan tasoba Jamal ya jata har tsakkiyar fili inda su Saifudden suka rufeta da liƙin ƴan ɗari bibbiyu sabbi ƙal. Ai sai bama tasan lokacin data fashe da kuka ba bisa dalilai masu yawa. Hakan da sukai yasa yaya gajeje ma zuwa ta farama Zinneerah liƙin ƴan hamsin-hamsin tana hawayen daɗi, sai ga Sa'a da chewing gum da sweet itama data siya ta fara zazzagesu akan Zinneerah. Aifa sai guri yaɗau ihu da sowa dan sun burge. Gwaggo maryama ma shigowa tai tayi nata liƙin, suma sai ga ƴan ɗan musa suna nuna tasu bajintar kowa dai-dai karfinsa. Wanima naira 100 zaizo ya liƙa mata ya fita.
      Wannan al'amari ya ƙuntata zuciyar Inna matuƙa, har takai ta yanke jiki ta faɗi sai da akai kama-kama wajen kaita ɗakinta. Sai Karima da Atine da Tinene da nunkufurci kecin ransu suka zauna da ita a ɗaki suna zage-zage wai da biyu su maman sadiq sukazo suka kafa bikin ai dama a danya. Duk da wasu a ƴan uwan mmn sadiq ɗin sunji sai basu kulasuba. Dan tunkan su taho an roƙesu kosunzo dan ALLAH karsu shiga sabgar Inna Asabe komi zatayi, dan su dai farin cikine ya kaisu suje ayi a tashi lafiya a miƙa amarya ɗakinta. Da wannan yasa suka sharesu.
    Su Yaya Gajeje kuwa basusan mike faruwaba suna can anashan dj dasu a waje hankali kwance.

     Shagali kam dai an shasa sai dai ace Alhamdulillahi, Zinneerah tayi kukan daɗi, tayi na damuwa, tayi na godiya ga ALLAH, ansha hotuna kuma da mai hoto dasu Mas'ood sukazo dashi, zuwa ƙarfe huɗu kuma sai ga motsocin ɗaukar amarya sunzo.
     Kasancewar Zinneerah tasha faɗa wajen iyaye da kakanni tun a daren jiya sai yazam yau sallama kawai aka kaita taima su baba da danginsa. har ɗakin Inna da sai yanzu kowa yasan da faɗuwarta, amma kasancewar ta farfaɗo hakan bai hana su Yaya Gajeje shirin raka ƙanwarsu ɗakintaba. Hardasu Karima mai jego kuwa dan sunce sai sunje sunga uwar da ake nusu fariyya da ita sukam.
    Inna bata hanasuba, dan itama daga ƙarshe catai zataje duk da halin da take a ciki na alamar ciwo. Dan ko gani batayi daƙyau saboda jininta da ya hau sama ƙololuwa dan damuwa da ruɗanin tashin hankalin da take a ciki. Baba zai hanata Gwaggo Laritu tace ya barta. Ai gara taje ta gano komai da idanunta zaifi. Amma yace sam bazatajeba sai daga baya saje da amaryarsa idan ALLAH ya sauketa lafiya. Tamaji da kanta. Badan tasoba dole ta haƙura dan da gaske tana a cikin wani hali dannewa kawai takesonyi dan zuwa taga ƙwaƙwaf. Amma tunawa ga ƴaƴanta nan yasa ta haƙura ta shige ɗaki tana kukan da bataso kowa ya gani.

       Tunda aka saka Zinneerah ta shirya bayan an ɗanƙara mata nasiha take rusar kuka da shiga tashin hankalin tunanin wanene mijin nata. Dan yanda Moos'ab ya nuna mata baiyi kama da miji a garetaba. Sai dai idan suna ɓoyewane har sai taje can ta gani. Kasancewar an turo motoci babu laifi kowa sai da ya samu wajen zama duk da wasu a matse suka tafi, ga kuma motocin ƴan ɗan musa suma sun sake taimakawa. dan a danya har ƴan gayyar soɗi dason ɗakko rahoto sai da sukabi.
     Motar da baba ya kama amarya Zinneerah kuwa ya saka da hannunsa sabuwace dal a ledarta Baffah ya bada a ɗakkota ciki, ita da Gwaggo Laritu da wata Gwaggo Aisha ƴar ɗan musa suka shiga tana tsakkiya, Adilah na gaba kusa da Huzaifa da zai ja motar. Wasu a cikin baƙin ɗan musa zasu wucene gidan mmn sadiq sai zuwa gobe suje suga ɗakin amarya kafin su koma gida. Dan haka motocin ɗaukar amarya sun riga su mmn sadiq tafiya dan su sai da sukai zaman yin sallama da mutane da godiya ga baba sannan suka taho gab da magriba.

Zuwa lokacin motocin ɗaukar amarya tuni sun isa cikin kano har Shira's house, inda Zinneerah keta kwasar kuka har suka iso gidan. Gidan da take zaune a cikinsa matsayin ƴa gata ta dawo a matsayin amarya.
     Hajiya iya da kanta ta fito ta tarbi Innon ta bakinta kamar zai yage dan fara'a. Zinneerah ta faɗa jikinta tana sakin wani sabon kukan. Itama rungumeta tayi cike da farin ciki.
      Ƴan kawo amaryama sun sami tarba ta mutunci da girmamawa. Inda aka saukesu a sashen Mommy dan sassan gidan duk cike suke da baƙi, hatta sashen Uncle Ahmad da matarsa keta baƙin rai sai da hajiya iya ta tura

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login