Showing 195001 words to 198000 words out of 223329 words

Chapter 66 - Makauniyar Kaddara Hausa Novel Complete

21 Nov 2024

1192

da suke buƙataba. Nasha mamaki saboda yarinyar dana basu babba ce, nasan kowane irin aiki aka sakata zata iya. Dan haka na kasa daurewa na tambayeta duk da inajin tsoro saboda girmanta da kasancewar wadda ta fito daga masarauta. A lokacin bata kulani ba. ta daice naje idan an samu tana jira. Haka na baro gidanta cike da wasiwasi amma bani da mai bani sani sai ALLAH. Anyi haka da kusan wata ɗaya sai ga Hajji Lanti da yara. Da farko dai ƙyawun ita wannan yarinya yasani jin sha'awar kai mata ita, dan nasan masu kuɗinnan dason ƴar aiki mai tsafta da ɗan fasali haka. Cikin amincewar UBANGIJI kuma tana ganinta sai tace tayi, ta kuma ɗauka cikon kuɗina har naira miliyan ɗaya ta bani, duk da dubu ɗari biyar ya kamata ta cikamin. dan munyi da itane akan miliyon ɗayan, nawa dubu ɗari biyu na iyayen yarinya dubu ɗari uku, na yarinya ɗari biyar, amma ban saniba ko jin daɗin samo yarinyar yasata bani ƙarin dubu ɗari biyar, bakuma tamin bayanin ta karanba sai da naje gida na kirata dan duk zatona ko bata kulaba ta bani. Amma sai tace min tana sane. Samun yarinyar dai-dai da ra'ayinsu yasata ƙara mana waɗanan kuɗi mu da iyayen yarinyar. Ta kuma ɗora da faɗamin zasuma yarinyar dashe ne na ciki, idan yakai wata biyu zasu ɗauketa zuwa ƙasar waje har saita haihu musu su sallamota da tagomashin arziƙi, amma wannan sirrine tsakaninmu, ko iyayen yarinyar bataso su sani kawai nace dasu ta tafi turai ne da yarinyar inda take zama da mijinta. Iya abinda ta sanar min kenan ta yanke wayarta. Harga ALLAH na girgiza da zancen sai dai inda aka fi ƙarfi nane bani da damar cewa komai. Kamar yanda ta buƙaci karna bar Nigeria sai aikinsu ya kankama na amince, dan dama kuɗin data bani so nake na koma ƙasar saudia inda dama can nake zaune a da. An yayonine an maidoni rashin kuɗi yasa ban komaba. Gaba ɗaya na mallake kuɗi har na iyayen yarinya dana yarinya da tace, ko Hajji Lanti data kawomin yarinya ban nema ba. Dan na shirya kamfinma ta dawo amsar kuɗaɗen yaran data kawo nabar ƙasar insha ALLAHU. Bayan anyi haka da sati uku inata shirina sai ga wayar hajiya Zakiyya, ta tabbatarmin aiki yayi zan iya tafiyata cikin murnarta. Nima naji daɗi sosai dan dama kayana a shirye suke, hakan yasa kwana biyu dayin magana da ita na wuce saudi-arebia da yara guda biyu. Daga haka ban sake sanin komaiba sai jiya da ƴan sanda sukazo har gida batun kamani. Wallahi tallahi ALLAH shine shaidata wannan shine abinda nima na sani, dan ALLAH ku gafarceni na tuba”. Ta kare maganar tana share hawaye.
        Gaba ɗaya falon ya ɗauka salati ana duban Zakiyya da tai ƙasa da kanta, daka ganta kasan a firgice take matuƙa. Hakama Mammah a ruɗan take amma duk tasan itama akwai sunanta a ciki so take taji ta bakin Zakiyya game da cikin Zinneerah da ita dai harga UBANGIJI batasan da zamansaba.
      Zinneerah kam mutuwar zaune tayi tanabin kowa da kallo kawai tamkar butun-butumi, dan harga ALLAH suna neman rikitar mata da tunani. Ita kanta burinta kawai aunty Zakiyya tayi magana.
     Mai martaba da zuciyarsa har wani tafasa take ya kafe Zakiyya da kallo yana kuma duban Farah dake kuka itama wiwi. A zafafe yace, “To dan uban daya haiheki sai kimana bayani muji lalatacciyar yarinya kawai. Wannan wane irin kafurcine kuma daga ina kika samosa ko kuka samosa tunda dai babu yanda za'ai dashe masu ƙwai basu saniba. Shi ƙwan na wanene? Kuma yaya akai?”.
         Ƙasa ta zamo ta dirƙushe jikinta na rawa, dan tafi kowa sanin wanene mahaifinsu. Inhar kuma tai gigin faɗar abinda ba haka bane lallai zai mata abinda gwamma ta faɗi gaskiyar.
      Kafin tace komai Farah da tsoro ke neman gigitata na tsawar mahaifin nasu ta fara rawar jiki da faɗin, “Wlhy Abbah babu ruwana nidai, duk aunty Zakiyya ce ta tsara komai, itace tasa muyi wlhy badan inaso ba......”
       Hankali tashe itama Zakiyyan ta fara magana, “Dan girman ALLAH Abbah ka gafarceni. dan ALLAH kar kayi fushi dani, Baba wambai ka bashi haƙuri dan ALLAH”.
        Aminin mai martaba da suke kira da baba Wambai ya gyara zamansa cikin kasaitar mulki da dattako yace, “Zakiyya kafin azo ga neman gafara ai nakega ya dace musan yaya akai ko? Kinsan mai martaba bayason jayayya, dan haka ki buɗe baki kiyi bayani tamkar yanda suma waɗanan mata sukayi, inaga shine zaifi sauƙi kamar kafin muzo ga gaɓar da kike so”.
      Kanta ta jinjina masa tana sharce hawaye.
         “Kowa yasan Farah dai autarmu ce da tausayinta yasa duk muka ɗauka son duniya muka aza mata, musamman ma ni daya kasance itace kawai ƴar uwata mace, sauran ukun duk maza ne. Farah a Morocco ta rayu hannun kakarmu data baro london, bayan rasuwarta Mammah yayar mahaifiyarmu ta amsheta ta koma da ita london. Tausayin da kowa yakema Farah a cikin dangi shi Abdul-Mutallab ke mata shima. Hakan yasa yafi kowa nuna jin daɗinsa da komawar Farah garesu. Kamar yanda take samun gata daga Mammah haka shima take samu a garesa, ta sanadin hakan shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, daga karshema ta juye soyayya. Kowa yaji daɗin hakan a dangi, dan babu wani ja'inja aka yanke zancen aurensu. Bayan bikin su da kusan shekar biyu babu wani labari koda na ɓatan wata daga wajensu, babu kuma wanda ya damu da hakan sai ni dana farajin damuwa. A wani zuwa da tayi Nigeria na takura mata mukaje Doctor ya dubata, inda mukaci karo da mummunan labarin daya nema zautani, dan ita koma a jikinta saboda ƙuruciya na ɗawainiya da ita a lokacin. Doctor ya tabbatar mana akwai wani tsiro daya toshe bakin mahaifar Farah gaba ɗayanta. Yanda da wahala ace ciki ya shiga, kodama ya shigan bazai zaunaba. Na bukaci ai mata aiki a ciresa idan zai yuwu, sai ya tabbatar mana taɓashi babbar matsalace, dan zata iya rasa ranta, sannan basu da wani maganin da zai iya gusar da shi a yanzu haka dai. Naci kuka sosai na kuma shiga damuwa da tunanin neman mafita ma yar uwata. Da farko dai son ganin jinin autarmu yasani damuwar, amma dalilin shigowar wasu maƙudan kuɗi ga Abdul-Mutallab da zantukan danginsa na ya ƙara aure ya far canja alkiblar tunanina, zuciyata ta fara rayamin idanfa ƴar uwata ta haihu da shi komi ya tara mallakintane ita da ɗiyanta. Idan kuma nayi sakacin hakan suka aura masa wata akwai matsala tunda likita ya tabbatar mana akwai matsala game da mahaifarta ita. Wannan tunanin ya sani ɗaukarta a wani zuwa london da nayi muka fara bin likitoci ba tare da sanin Abdul-Mutallab kosu Mammah ba. Sai dai duk inda mukaje amsar dayace mahaifarta nada matsala, kuma irin bayanin wancan likitan suma suke mana dai. Hankalina ya ƙara tashi haka itama nata, dan haushin rashin damuwarta yasani zama na fahimtar da ita. Nasha takaici ganin daga baya ta nuna ita fa ba komai bane, tunda Abdul-Mutallab na sonta tana sonshi ko bata haihuba babu damuwa, ballema bata fidda ran a gaba su samuba dan bata yarda da maganar likitocinba ALLAH ne maiyi. Duk da gatan da mukema Farah na tsiya nasan tanada zurfin tunani da aiki da hankalinta matuƙa, sai dai banyi zaton zata kasa fahimtataba musamman dana san tanada kishi mai zafi irin namu musamman akan Abdul-Mutallab. Lokacin da suke cika shekaru uku da aure kakarsa ta ƙara bijiro masa da zancen aure a time ɗin sunzo Nigeria tare, hankalin Fara ya tashi matuƙa, dan tanada tsananin kishi”...........✍       


*_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*

Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.

*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_

*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_

*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_

*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_

*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_

Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.

Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*

       
*_TYPING📲_*


*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*


_________________________


*Page 63*

............“A wannan gaɓar saboda yanda ta nuna tashin hankalinta matuƙa sai nayi amfani da damar wajen sake zaunar da ita na nuna mata muhimmanci haihuwarta. Tare da kawo mata zancen dashen ciki. Ta razana matuƙa, ta kuma ce ita dai gaskiya tanajin tsoro, dan tasan Abdul-Mutallab ma ba yarda zaiba. Dan haka kawai mubar zancen na tayata da addu'a dan bazata iya zama da kishiya ba zata iya halaka kanta. Wannan furuci nata ya kuma ɗagan hankali matuƙa, dan nasan zata iya aikata abinda ta faɗan, na kuma tabbatar auren Abdul-Mutallab bazai fasu ba inba danginsa sunga ta haihu ba. Ta kuma nunamin su Mammah ma ba yarda zasuyiba dan abune da kowa yasan malamai na nuna illarsa a addinance dama lafiya ta wani fannin. Ban gusaba wajen zaman cigaba da nusar da ita, tare da kawo mata dabarun da zamuyi maganin kowacce matsala. Na farko karmu bari AK ya sani, ayi komai a ɓoye harta wadda za'a sama cikin ta haihu ace itace ta haihu. Ta tambayeni taya za'ai hakan ta kasance bayan koyaushe tana tare da AK. Na ce mata ta bari zanyi tunani. Bayan kwana biyu dayin maganar na samo mafita a wajen Doctor ɗin da zaiyi aikin, idan an dasama wadda zata raini ciki ita zata fara pretending like pregnant, bayan yakai kamar 3months zata koma zama a Morocco ta hanyar wasu dabaru namu na mata har mai ciki ta haihu a bata ɗanta ta shayar ita da kanta. Cikin tsoro tace amma tayaya hakan zata faru bada yardar su Mammah ba. Niko nace mata Mahma ce kawai za'a ɓoyema gaskiyar zance, amma Mammah da ita za'ai komai. Tacemin ta yaya Mammah zata yarda da hakan?. Nace mata ta hanyar yin amfani da ita akan so da kishin da takema mahaifin Abdul-Mutallab da ganin laifin danginsa da take na rabuwarsu, da kuma ƙin son rabata da ƴaƴanta da shine babbar barazanarta a rayuwa. A lokacin Farah bata bani goyon bayaba, dan tace bata yarda a cutar da kowa ba, musamman ma Mammah da ta ɗauketa daidai da nata ƴaƴan saboda ƙaunar da takema mahaifiyarmu. Sosai na mata masifa ni da Muktar a lokacin, dan shine ya taimaka mana da likutan da zaiyi aikin ma. Da dai mukaga taƙi tanƙwaruwa ta sauki sai itama nabi da ita ta hanyar razanarwa da kshiya har tai laushi ta amince. Tun daga lokacin itama Mammah na fara aiki a kanta, sannan Doctor ya tsarama Farah yanda zamu sami sparm ɗin Abdul-Mutallab cikin sauƙi”.
               Babu wanda mamaki bai nema kashewa a falonba, musamman ma Mammah datai mutuwar zaune akan wannan labari na Zakiyya. Zakiyya ta cigaba da faɗin,
        “Bayan wani lokaci na tunkari Mammah da batun ya kamata musan halin da Farah da Abdul-Mutallab ke a ciki game da haihuwa, kar muyi sakacin da dangin mahaifinsa zasu aura masa wata zasu rabamu da shine kawai ya koma hannunsu. Na tabbata wannan kalma ta tada hankalinta matuƙa, dan babu abinda tafi tsana arayuwa kamar ace yaranta zasu koma hannun mahaifinsu. Bayan munyi wannan maganar washe gari taima Abdul-Mutallab maganar a gabana, amma sai ya nuna ɗan ɓacin ransa akan duka shekararsu nawa da auren da har za'a fara nuna damuwa basu haihuba, shi wannn maganar dan ALLAH a barta ALLAH ne mai badawa kuma zai basu lokacin da yaso. Da wannan furucin yabar gidan a zuciye. Hankalina ya tashi, dan gashi saura kwana biyu na baro london ɗin, dan haka na sake sabon zaman fanfa Mammah da kawo mata dalilai kala-kala da suka dinga ruɗa mata tunani itama tana ruɗashi. Tashin hankalin data nema sakashi a ciki ya sashi tattaro Farah suka gudo Nigeria a lokacin bamu sani ba. Sai da sukaje ta kira take sanar mini. Naji daɗin hakan, dan nima a gareni wata dama ce. Dan haka na sake buɗe wutar data harzuƙa Mammah harta kirasa ta tabbatar masa da inhar bai yarda da batuntaba wlhy zata iya tsine masa. Sosai Abdul-Mutallab na gudun ɓacin ran mahaifiyarsa. Dan haka furucinta ya tada masa hankali yace ya amince zasuje idan sun koma london. Still nice dai na sake bama Mammah shawarar suga Doctor Hannafi dake nan Nigeria shima kwararrene a wanna fanin kuma a can london ɗinma yay karatunsa da aiki harna tsahon shekara bakwai. Batare da wani jayayyaba ta kirasa da tura masa address da phone Number ɗin Doctor Hannafi dana bata nima kuma na tattaro na dawo Nigeria neman yarinyar da za'aima dashen. Ta farko bataiminba, dan tanada wayo kuma idonta a buɗe yake, hakan yasa nasa hajiya haule canjamin ita.”
         “Biyayyar da Abdul-Mutallab yake ma Mammah ya sashi ɗaukar ƙafa sukaje ga Doctor Hannafi, wanda dama mun gama tsara komai. Dan haka kawai abinda ya buƙata a garesu shine sparm ɗin sa, ita kuma Farah yay mata wasu gwaje-gwaje kamar gaske. Domin kawai bin umarni Abdul-Mutallab ya yarda ya bama Dr Hannafi Sparm ɗin nan, wanda da shine aka haɗa da ƙwan Farah akaima ita Zinneerah dashen bayan mun tabbatar zata iya. Dan ita bata kai waccan girma da wayo ba, amma yanayinta kawai zaka kalla bama zaka ɗauka a ƙauye ta fitoba dan ƙyakyawa ce. Da wannan karancin shekarun nata mukai amfani wajen yin komai na dashen batare da ita ta fahimci komaiba, dan ALLAH ya taimakemu sanda aka kawo min ita tana cikin halin zazzaɓi sai komai ya ƙara zuwa mana dai-dai muka tafiyar da ita akan treating ɗin zazzaɓin nata. Sai dai kuma bayan dashen muna fata da addu'ar ALLAH yasa ya zauna da kwana uku muka nemeta muka rasa. Hankalina ya tashi matuƙa a wannan lokacin, nama kasa sanarma Farah yanda akai sam. Sai dai munta tararrabin mu da neman yarinya ni da Muktar da Dr Hannafi. Gashi Hajiya Haule ta wuce saudia kuma bani da contact ɗinta nacan balle mu binciki garin da ta ɗakkota. Dr Hannafi ne ya kwantar min da hankali ta hanyar sanar min da wahalama cikin ya zauna, dan bai kai kwanakin da ake buƙatar nutsuwarta a waje guda ba, kawai yanzu dabarar da zamuyi a karasa AK ya bada sparm ɗin nasa kafin su wuce sai a sake yima wata dashen, wannan kuma mu ɗaukama bazai zauna ba kawai, musamman da ko magungunan daya kamata tasha sau daya ta shasu. Na ɗanji sanyi da wannan shawarar tasa, akanta kuma na yanke hukuncin tun karar Mammah da batun dashen cikin. A ranar na kirata, na sanar mata Dr Hannafi ya tabbatar mana AK nada matsalar bama mace ciki, amma za'a iya yin amfani da sparm ɗinsa ai dashe, sai dai matsalar itama Farah nada tata matsalar a mahaifa kuma”.
          “Hankalinta ya tashi, harta buƙaci na haɗata da Dr Hannafi ɗin, na kuma haɗata dashi ya sake mata bayanin daya kamata akan dashen da tsarin da za'ayi. Ta tabbatar masa da zata iya yarda ayin kodan a samu ɗan danginsa su daina harar mata yaro dason mallakesa. sai dai babbar matsalarta shine Abdul-Mutallab, tasan bazai taɓa yarda da hakanba koda zata tursasashi a wannan gaɓar. Cikin dabara Dr Hannafi ya shigar mata da shawararmu na yanda tsarin zai kasance batare da Abdul-Mutallab da kowama sun fahimci hakanba bayan mu. Tace ya bata dama zatai tunani da shawara. Cikin amincin ALLAH sai tai shawara dani, dan a tunaninta bansan komaiba game da dabaran. Babu wani ja'inja na nuna mata hakan shine dai-dai, tare da sake kawo mata dalilaina nima. Sai ko aka dace ta yarda dan nayi amfani da inda ke mata ƙaiƙayi. Amincewar tatace ta zama ginshiƙin tushen aikinmu na biyu, sai dai a wannan karon cikin bayin gidanmu na ɗakko, kuma da amincewarta dana iyayenta, ana kuma gamawa na maidota gidana ina kula da duk motsinta har ALLAH tasa ciki ya zauna ya kai wata biyu da wasu kwanaki sannan Mammah tazo da kanta ta tafi da ita Morocco. Zuwa sannan kuma Abdul-Mutallab da wasu a cikin danginmu sunsan Farah nada ciki, sai dai mun gargaɗi Abdul-Mutallab da sanarma danginsa zancen ciki har sai Farah ta haihu saji hakan zaisa sufi murna ya kuma musu surprise. Ya amince da hakan kuwa sai dai bamusan dalilinsaba. Sai dai ashe kana nakane ALLAH na nashi, dan randa Farah ta baro london da nufin zuwa tai goyon ciki a Morocco wanda tursasawar Mammah yasa Abdul-Mutallab yarda washe gari yarinyar tayi barinsa. Ranar ba Farah kawai ba hatta ni da Mammah sai da mukai kuka wlhy, Abdul-Mutallab kuwa a ranar ya baro london zuwa Morocco hankali a tashe. Shima har kukan yayi saboda ya ƙwallafama cikin nan rai kamar mi. Bayan gama wannan taraddadin bawai na haƙura bane akan ƙudirina. Na cigaba da zungurar Farah da Mammah suna zillewa. Dan kai tsaye Farah tace min alhakin Abdul-Mutallab ne yasa cikinma ya zube. Faɗa mukaita mata a lokacin, amma taƙi saurarenmu. Mun tattara mun ƙyaleta a lokacin danta huta dan naga itama Mammah na neman fara zamemin. Taimakon da ALLAH ya sakemin shine takurawar Abdul-Mutallab ya ƙara aure daga hajiya iya, wanda har takai ga ya ɗauke kafarsa da Nigeria, sukuma suka tura masa ƙaninsa. Tun daga nan na fahimci hankalin Farah baya tare da ita, dan duk wani abinda ya faru tsakaninta da Abdul-Mutallab sai ta kira ta sanarmina lokacin. Abinda na fahimta shine kishin zancen ƙara aurensa na cinta har take ganin kasancewar wani nasa tare da shi zai sa danginsa suci galaba a kansa. Na biyu kuma tashin hankalin Mammah itama na kada Abdul-Mutallab ya komawa danginsa yasa take goyama Farah baya.”
 

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login