Showing 216001 words to 219000 words out of 223329 words

Chapter 73 - Makauniyar Kaddara Hausa Novel Complete

21 Nov 2024

1171

yana faman shafa kawunan yaran. Ta zare hijjab ɗin nata tana nufar falo ɗakko ruwa duk da ta tabbatar sai yaci abincin nan ko zuwa anjima ne.
    Da kallo ya bita harta fice. Ya sauke ajiyar zuciya yana mikewa daga wajen su Amaan ɗin.
    Tsaye ta samesa gaban mirror yana saka turare. Tana ajiye ruwan ta juyo da nufin masa magana taji anyi cak da ita sai gado. A tare ya faɗa da su yana magana cikin kuneneta. “Wai sokike dai sai na miki kuka yarinyarnan. Sai wani ƙwalele kikemin ni da kayana”.
    Siririyar dariyar data nema zautashi ta saki tana cusa kanta a wuyansa da shaƙar ƙamshinsa itama. Babu shiri ya lalubo bakinta dake ƙamshin strawberry freshener ya manna nasa a ciki. A zalame yake, dan haka cikin zalamar ya shiga sarrafata shima, itama kuma tana amsarsa da zalamar dan koba komai tayi kewa.
     Sai da tafiya tai nisa sosai ta gama shagala a hannunsa da salonsa sai ga idon madam ya raina fata ta koma raki daga karshe. Inama AK ke wani jinta shi a wannan yanayin. Sai da ya more duk ƙwalelen kwanakin da akai masa shima sannan ya koma lallashi yana mata dariyan mugunta.
    Kamar yanda tai hasashe kuwa suna kimtsa jikinsu sai da yaci abinci waishi duk ta sakashi jin yunwa. Murmushi kawai ta dingayi dan dai al'amarin nasa yakanfi ƙarfinta wani lokacin, babu abinda ya damesa ɓaro mata zance yake kansa tsaye kamar ba yayansun nan sarkin mazurai da tsare gida ba. A yanzu haka idan su Jamal na tsogumi akansa sai taita dariya kawai dan tasan dai mazuran iya na waje ne. Itama dai sai da tacin danya tsiyayeta tas ga yaransa a gefe da nasu suma.

      A tsakanin dare zuwa safiya dai sai da Zinneerah ta raina kanta a hannun AK, dan babu kunya ya hanata komawa sashenta yinin ranar shima kuma bai fita ko inaba sai massallaci. Sai dai taje ta ɗauka abu a sashenta ta dawo, su ƴan biyu kam ko ƙofar ɗaki basu jeba suna nane da shi harda little da tunda gari ya waye shima ya taho nan ya tare. Sai da zai wuce islamiyya.
       Babu abinda suke zubawa sai zallar soyayya da nunama juna tsantsar ƙauna a wannan yini. Duk wani motsinta idonsa na kanta. kamar yanda itama dai ta murje nata idon take masa komai dai-dai da buƙatarsa. Sai ta gama ta koma sinne kai wai ita kunya. Hakan na birgesa da sakashi a nishaɗi, dan ji yake tamkar yayi gamo da sabuwar budurwa a haɗuwar farko.
     Washe gari ma duk da ayyukan dake a gabansa tari-tari haka ya lalace wajenta sai bayan azhar ya shirya ya fita. Magribar fari sai gashi ya dawo. Sakawa yay ta shirya ita da yara ya fita dasu wani haɗaɗen joint ɗin cin ƙwalam da maƙulashe, suka shawo ice-creem. Yana ɗauke da Anam tana ɗauke da Amaan. Little na riƙe da ɗayan hannunsa abin sha'awa. Mutane sai kallonsu suke abin birgewa, dan shi kam rashin zamansa a ƙasar sosai yasa bawani saninsa akai a fuskaba da yawa. Sunansa yafi fuskarsa fita ga kunnuwan jama'a. Ganin yanda ake kallon nasu sai kishi ya kamasa ya kuma dinga ɓata fuska. Itama kuma madam ɗin nasa sai kishin ya rufeta ruf saboda yanda ƴan matan wajen ke rawar kai gaban samari dama irinsu AK ɗin duk da suna ganinsu tare da iyalansu (Ƴammata a yi haƙuri inaji daku😂😹😹🙏🏻). Haka dai suka kasance a daddafe a wajen danma vip suke zaune.
Daga nan wajen wasan yara suka kai Little dan duk akwai a wajen duk da dare ne. Ya ɗan hau abubuwa yana maijin nishaɗi harda rigimarsa ta aɗora su Anam. Zinneerah tace wlhy bata yardaba. Bata gama dawowa daga maganin naƙudaba ba'a sata kuka.
Maganarnan ta bama AK dariya. Ya dubeta fuska ɗauke da murmushi har haƙwaransa na bayyana yace, “Haba karki bada mata mana madam, ni har ina murna na sake jefa ƙwallo tsakanin jiya da yau”.
Cikin ƙwaɓe fuska tace, “Wayyo ALLAH Yayanmu dan ALLAH daina min fatan nan ka tausaya min”.
Nanma ƴar dariya yayi da sumbatar goshin Anam dake a hannunsa. “My Sweetheart kinji Mamin ku zata mana buƙulun gambo ko? Ku faɗa mata ku kuna son ƙani da wuri Mammah da Mahma, badan kar ace na cika son kai ba sai nace a haɗo da Uncle Ahmad duk lokaci ɗaya, daga baya sai a bani Mommy na da Gwaggo da Baba suma, sai Abbah kuma ya zama auta”.
Yanda tai sagade tana kallonsa baki a hangame ya sashi dungure mata kai. “Kallon fa?”.
Kai tsaye tace, “Na tsoro da al'ajabi ne ai. Ƴaƴa bakwai fa kake lissafi daga gama arba'in Daddyn Little”.
“Oh kinma ɗauka ni na wasane kenan. Yarinya shirya da ƙyau Shirawa yawa suke son ƙarawa, mu babu ruwanmu da wani tsarin iyali”.
“Aiko na rantse yaji zanzo nayi, danya zan tafi sai nayi wata uku acan”.
Dariya sosai yakeyi yanzu kam. Yace, “Ai wlhy Baba koromin ke zaiyi, kije wajen Granny kuma kin kai kanki, dan ba ɗaga ƙafa zanba harcan zan biki, gara-garama wajen gwaggo, zanji kunya. Amm nasan itama koroki zatai”.
A ranta tace, (Zaka iya wlhy Yayanmu) a fili kam cewa tai, “Wannan zance yafi ƙarfina karka lalatani da ƙarancin shekaruna gaskiya”.
“Lalacewa kuma ta yaushe yarinya, tunda ga ƴan biyuna a hannu ina kallonsu inajin daɗin raina su da babban Yaya takwaran Daddynsa. Zaki gane kuranki bara mu koma gida”.
Jin haka ya sata yin ɓam da bakinta. Shiko ya samu na tsokana har suka bar wajen bayan yama su Yaya Gajeje takeaway ɗin tasu tsaraban na kayan ƙwaɗayi...........✍



*_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*

Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.

*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_

*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_

*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_

*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_

*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_

Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.

Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍






*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*

 *_TYPING📲_*


*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*


_______________________


*Page 69*

...........Rayuwa ta cigaba da tafiya cikin farin ciki gasu Zinneerah, babu abinda zatacema ALLAH dasu Hajiya iya sai godiya, dan itakam sun bata ƙyauta da har abadan bazata daina alfahari da tutuiya dasu ba. Kwananta goma dayin arba'i su yaya Gajeje suka shirya komawa Danya, duk da dai Inna bata warke bane sarai Alhmdllh jikinta yayi sauƙi sosai, dan kullum sai Dr Mahmud yazo safe da dare ya sake dubata. Tana ɗan magana da motsa jikinta, tafiya ce dai babu kam kafafun zuwa gidan malamai sun mutu.
     A ɗan zaman nan gidan Zinneerah babu fashi kullum sai tayi kuka. Musamman idan AK ya shiga ya gaisheta ko aka kawo wani lafiyayyen abinci aka bata, ko Zinneerah ta shiga da yaranta abin sha'awa gaisheta. Balle ta zauna dan su ɗanyi hira ta dinga haɗiyar zuciya kenan kamar budiddigin ƙwaɗo. Little kam baya minti goma bai shiga ɗakin ba inhar yana gida. Dole kuma take kulashi saboda shi babu ruwansa haye mata jiki yake, sai ma idan Zinneerah ta ganine taita masa faɗan karya ƙarisa mata uwa, daya faki ido kuma zai sake komawa, ko ganinta a zaunen ne shike ɗaukar masa hankali oho😂..
           A dalilin zaman Inna maman sadiq kuma tazo gidan sau kusan uku dubata ita da mmn halima. Na kusan ƙarshene sukazo harda mmn sakina da matar naziru da ayanzu suketa zuminci da Khalipha, dan sun zama abokai tunda ba wani girman Khalipha ɗin yayba shima auren gata ne Abba dama yay masa.
    Shatara ta arziƙi AK da Dr Mahmud suka haɗa musu, sannan kuma suka tafi gaba ɗayansu musu rakkiya harda AK da Dr Mahmud dan sunason zuwa su gaida Baba duk da baima jima da zuwa ya dubata ba shi da ƴan uwansa, sai su Meenal da suka maƙale. Tarba suka samu mai ban mamaki daga amaryar baba da dangi, kowa yana sambarka da ƴan biyun Zinneerah dan hada yawon arba'in duk ta haɗa tazo. Ga Sa'a ma na fama da nata laulayin cikin sai fatan sauka lafiya.
      Anan su AK suka barsu zasu kwana biyu, ya juya shi dasu Jamal da Dr Mahmud kowa na kewar matarsa. Da farko little ya maƙale binsu zaiyi, mi kuma ya gani harya shiga motar tama ɗakko masa kayansa sai cayay kuma zai zauna wajan su Anam indai badasu za'a koma Kano ba.
       
      Kwanansu huɗu a Danya Zinneerah da Sa'a suka shiga lungu da saƙo gaida ƴan uwa da abokan arziƙi, duk inda suka gitta sha'awarsu ake ana san barka dan sun zama abin kwatance ga kowa. Alkairi kam duk inda suka shiga sukan ajiye gwargwadon ƙarfinsu su wuce ana saka musu albarka. Baba kansa yana cikin farin ciki da kasancewar ƴaƴansa cikin kwanciyar hankali. Mutane nata zuwa ganin Inna ana yadda mata habaici akan ga wadda ta tsana da gallazamawa nan ta zama silar samun lafiyarta ai.
      Babu bakin magana ga Inna Asabe danya musu murus, sai kukan zuci da haɗiyar zuciya kawai.
    Randa suka cika kwanaki huɗu babu daɗi babu ƙari sai ga Moos'ab yazo kwasarsu. Zinneerah bataso hakaba dan catake zaiyi haƙuri sukai 1week ɗin data roƙa. Amma hakanma sun gode dan batai zaton zai bari ba. Aiko data dawo tasha mitar shi an barsa shi kaɗai a gida kamar mara gata.
         Dariya ta dinga masa da bashi haƙuri. daga ƙarshe tabi hanyar data dace wajen lallashin abinta. Gaba ɗaya gidan yanzu sai take jinsa wani iri da duk suka tafi, sauƙinma ta taho da ɗiyar Yaya gajeje zata ɗan mata hutu mai suna Saliha. Yarinya ce ƙyaƙyƙyawa kuma nutsatstsiya, shekaranta goma kwata-kwata. Tarbiyan yarinyar yasa ta shiga ran AK yace makaranta zai nema mata dan tazo kenan bazata komaba. Sosai Zinneerah taji daɗin hakan kuwa taita masa godiya.
         Bayan sati uku da dawowarsu daga Danya da ƙyar ya barta taje Minna wajen Gwaggo Maryama. Aiko taji daɗin wannan zuwa harda ƴar ƙwallarta. Kwanansu biyu acan suka dawo, Hajiya iya ta sake jajubarta suka tafi bauchi. AK nata fushi batabi takansaba tace yawan arba'in Zinneerah keyi dana aure daya hanata yi.
                Yama zai yi da tsohuwarnan inba yay gum da bakinsaba. Dan yana tankawa zatama iya ƙwaƙulo wasu dangin a wani garin tace Zinneerah taje. Satinsu ɗaya a can suka dawo. Shima kuma sai ya fara musu shirin zuwa Morocco daga can zasu wuce London su ɗan huta tunda little sun sami hutu. Fatansa kuma ya tarkato su Mammah su dawo a maida aurenta da baffah tunda yaga sun sakko an daina faɗan masoya saita waya idan sun kira juna da nufin gaisuwa. Mahma kuwa gida zai saya mata tai zamanta kusa dasu.

  *_MOROCCO_*

   Wannan shine karon farko na zuwan Zinneerah dangin kakarsu AK, tako sami tarba ta mutunci ga mutanen har taita mamaki, yaranta kowa yana nuna musu so da ƙauna abin birgewa. Yaran Mahma kuwa kamar sun santa dama can, dan janta suka dingayi a jiki ita dasu little. Magana kuwa sai da turanci, waɗanda basaji sai larabci sai dai ake musu tafinta da Zinneerah dan ita dai ba iyawa taiba sai abinda ba'a rasaba na islamiyya, wanda bai wuce gaisuwa ba da kalmomi.
     Satinsu ɗaya cif suka wuce london cike da kewarsu, inda acanma suka sami tarba ga Mahma da Mammah. Kwanansu biyu da isowa Adilah da Huzaifa suka iso suma. Ai fa sai gida ya kacame da farin ciki bakin Mammah tamkar zai yage dan farin ciki. dan itama Adilah fama take da ciki harya fito abinsa.

    Sunsha hutu da soyayyarsu a london kafin su tattaro kuma su dawo gida dansu little sun koma school. Satinsu biyu da dawowa aka maida auren Mammah da Baffah.
        Zo kaga farin ciki wajen yaran gidan, dan koba komai AK ya cancanci su girmama mahaifiyarsa su kuma sota dan shima yana girmama nasu. Ba'a wani tsaya ja'inja ba Mammah ta tarkato kayanta ta dawo Nigeria gidan masoyinta bisa rakkiyar dangin mahaifinsu. 
           Aiko sai ga baffah da mammah an ƙara shimfiɗa sabuwar soyayya, ita da abokan zamanta kuwa sai dai sambarka. Dan tana ƙoƙarin danne kishinta kamar yanda suma suke danne nasu kodan yara da nasihar da hajiya iya ke musu kullum babu gajiyawa. Dan babu abinda zatace da UBANGIJI sai godiya na sake haɗe mata kan family ɗinta da yayi, bayan gwagarmaya da jarabawar data sha a shekarun baya wajen ganin ta haɗesu waje guda hakan bai samuba sai da iyaka tazo.
    Mahma kuma AK ya saya mata gida anan kusa dasu, da yake mutumce maison jama'a saita tarkato ƴaƴan dangi daga kaita dansu tayata zama.

★★★

        Daga haka rayuwa ta cigaba da turawa Zinneerah na cigaba dama AK naci akan dawowar Farah. Duk da yana ɓata mata rai haka take sake dawowa ta ƙara masa maganar.
     Sai gashi a wasa-wasa dai sai da Farah da Zakiyya suka cika shekaru biyu cif da maimartaba ya basu. Zuwa lokacin ƴan biyu babu inda basa zuwa da kafafunsu, yara sunyi ɓul dasu masha ALLAH ga wayo dan sun hau karatun little.
     Naci Zinneerah ta cigaba da masa akan dawowar Farah ɗin yana basar da ita har sai da ta ƙara wata uku akan shekara biyun mai martaba sannan yace mata zaije. Amma babu rana.
    Wannan maganar tasata tunkarar hajiya iya da batun da Baffah a karo na farko. Albarka suka dinga saka mata. Uncle Ahmad yace insha ALLAH da kansa zaije ya ɗakko Farah ɗin.

★__________★

     Aiko kamar yanda Uncle Ahmad yay alƙawari bayan sati guda da wannan zance batare da sanin AK ba sai gashi tare da Farah. Lokacin suna a barandar gidan su duka da yammaci iskar la'asar na kaɗasu. Boss na zaune yana harkar business ɗinsa a lap-top duk da ma su Anam na hanashi, dan sai hawa masa jiki suke suna ƙirniya. Zinneerah na gefensa tana koyama Little homework.
        Duban Zinneerah yay yana nuna mata Anam data haye masa dokin wuya. “Mami kizo ki ɗauke kakarnan taki kona jehota ƙasa ta isheni ALLAH, ta hanani aiki”.
     Dariya Zinneerah tai saboda yanda yay maganar a marairaice tana kallon uban da ƴar. Tace, “Idan ka jeho Granny ƙasa aiko ka koma Morocco da ƙafa dan takwararta ba ɗaga maka ƙafa zatai ba”.
     Murmushi yay yana sauke Anam ɗin da faɗin, “Madam rikici ba, ai saita saukemin Nigeria a kaina wlhy. Inaga dai bara na haƙura da aikin nan kawai dan ba barina zasuyi ba, shi baffah ma neman rikitamin system ɗin yake”.
     Little daketa tunzura baki gaba ya gaji da homework ɗin yace, “Daddy na ɗakko ball muyi?”.
       “Kokuma kakan ball ɗin ba”. Zinneerah ta faɗa tana nuna masa littafin gabansa. sake tunzura bakin yay yana kallon AK kamar zai kuka. Yanda yay ɗin ya bama AK dariya. Shima sai ya duba zinneerah yana marairaicewa kamar yanda little yayi. “Mami a tausaya mana a barmu mu huta. Itafa bokon nan iyakarta duniya, kuma mu ba dangin mango park ba”.
          Ta buɗe baki zata bashi amsa motar Uncle Ahmad dake tare da Khalipha da Farah ta shigo gidan. Shi AK da farko ma ya zata ko Suhail ne babban ɗan Uncle Ahmad ɗin dan nan ɗin gidan zuwansa ne sosai tunda ya baro Turkey. Dan haka yayma Zinneerah nuni da hijjab ɗinta dake gefe dama ajiye. Sai da yaga Khalipha ya fito da Uncle Ahmad ɗin ya sashi miƙewa tsaye babu shiri. Yana ƙoƙarin nufarsu Farah ta fito a motar. Ta rame sosai ta canja tamkar ba itaba. A take fara'ar fuskar AK ta ɓace ɓat. Sai dai babu damar magana saboda Uncle Ahmad.
        Sannu da zuwa Zinneerah taketa musu fuskarta ɗauke da murmushi. Uncle Ahmad ya ɗauka little yana faɗin, “Uhm babana zoka samin albarka”.
    Shima Khalipha sai ya ɗauka Amaan yace, “Nima taho samin tawa albarkar babana tunda abin hakane”. Dariya aka sanya musamman da Anam taje jikin AK itama ta maƙale. Shi dai ko murmushi baiyiba.
     Ita dai Zinneerah nufar Farah dake kallonsu tamkar tana hawayema tayi tana mata sannu da zuwa cikin fara'a. Yanda ta amsa mata kamar a kunyace sai ta bata mamaki, ta kama hannunta sukabi bayan su AK ɗin da har sun shige ciki.

     Sashen AK suka nufa, sai da ta raka Farah sannan ta dawo ta koma sashenta tasa Saliha haɗa abin sha da motsa baki takai musu, ita kuma ta ɗauka abincinsu na dare da aka girka gaba ɗaya ta nufi sashen nasa. Ta iske Khalipha nata tsokanar Saliha dan mutuniyarsa ce sosai. Bayan ta gama zata wuce ta kirata tazo ta tattara yaran suje. Ɗaukar Anam tayi da tisa ƙeyar little da Amaan suka fita. Itama ta gama shirya abincin a dining zata fita Uncle Ahmad ya dakatar da ita.
       “Dawo ki zauna Inno ai maganar ta shafeki kema”. Dawowa tai babu musu ta zauna.
         Bayan Uncle Ahmad ya buɗe taron da addu'a ya fara musu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login