Showing 162001 words to 165000 words out of 223329 words

Chapter 55 - Makauniyar Kaddara Hausa Novel Complete

21 Nov 2024

1197

ganin Number aunty Zakiyya ya sakashi yi kamar bazai ɗagaba sai kuma ya ɗaga ɗin batare da yayi magana ba.
      Cikin sake fusata daga can Mammah tace, “Abdul-Mutallab nasan kana jina”.
     Runtse idanunsa yay da cije lip ɗinsa na ƙasa. yay ƙoƙarin daidaita kansa wajen faɗin, “Am sorry, bansan ke bace ba”.
       “Ai yanzu ka sani, na kiraka ne na gargaɗeka, wlhy ka taɓa musu yarinya sai ranka yay mummunan ɓaci, dan nayi alƙawarin wannan auren sai na tsinkashi wlhy, saboda haka karma ka ƙwaɗaitama kanka abinda zai dameka daga baya na faɗa maka”.
         A bazata ya saki murmushi mai sanyi da kai hannu ya shafi kansa, dan tana gama faɗa ta yanke kiran bata jira amsarsa ba. Ajiye wayar yayi yana miƙewa gaba ɗayansa idonsa akan Zinneerah dake cuɗa yatsunta cikin juna tana cigaba da kukanta  harda shashsheka.
      Batare da tunanin kanta ya nufoba sai ganinsa tai ya hawo gadon sosai, filo ƙarami ya jawo daga gefenta ya kishin giɗa, dan ɗaura gwiwar hannunsa ɗaya yay ya tallafe kansa da tafin hannun yanda yake iya kallonta da ƙyau, sai kuma ya saka yatsunsa biyu na ɗayan hannunsa ya tallafo haɓarta yanda zasu haɗa ido.
      Suna haɗa idanun kuwa tai saurin son maida nata dake kwarar da hawaye amma ya hanata wannan damar. Sai kawai ta shiga sake matso hawayen. Dan irin kallon ƙurullar da yake yima fuskar tata ne yake ƙara ƙarya mata zuciya ga kwarjininsa daya cika mata idanu.
           “Shi wannan kukan ba'a gajiya dashi?”. Yay maganar da muryar lallashi data sakata ɗago idanu ta sake kallonsa, yanda yay ɗan yi luuu da idanun nasane ya saka tsigar jikinta tashi, cikin harɗewar harshe tace, “Yayanmu!”.
       “Uhmyim ƙanwata”. Ya faɗa yana sakin haɓar tata da janye hannunsa daya tallafe kansa shima yana gyara kishingiɗar tasa da matsowa daf da ita yanda takejin har saukar numfashinsa shima yanajin nata.
     Ganin yanda ta kasa ci gaba da maganar sai juya yatsun hannunta take a cikin na juna ya sashi ɗaura hannunsa akansu yana kallon zanen baƙin lallen da ja dayay matuƙar ƙyau a kansu, “Kuka ga amarya a ranar da aka kawota gidan miji cikar kamalace da bayyana adon mutuncinta, sannan kuma tarbiyyace da nuna tsantsar soyayya ga iyaye, sai dai idan yayi yawa yana gundurata. Karki damu da neman amsar duka tambayoyinki, a hankali zaki samu amsarsu. Inason mutum mai biyayya akan umarnina, banason hayaniya, banason taurin kai, banason ƙarya. Duk wanda zan rayu dashi inhar zai kiyaye waɗannan zaiji daɗin zama dani fiye da yanda yake zato. Bana yanke hukunci ga mai laifi da sauri ko cikin fushi har sai na bisa mataki-mataki wajen fahimtarsa da dalilinsa. Mun sami juna a yanayin da banso ba, sai dai ba hakan na nufin zanyi sakaci da damata bane, komu samu tsaurin idon bijirema hukuncin ALLAH dana iyayenmu, dan sun cancanci sadaukarwa koda ace mu zukatanmu basa buƙatar hakan, ina ƙyautata miki zato bisa ga wasu dalilaina, dan haka sai kiyi ƙoƙarin tabbatar mini da hakan”.
       Hannunta ɗaya ta zare daga cikin nasa a hankali ta share hawayen da suka jiƙe mata fuska.
     “Good” ya faɗa yana tashi zaune daga kishingiɗar da yayi. Sauka yayi gaba ɗaya a gadon Zinneerah na binsa da kallo ta ƙasan ido da ƙoƙarin ganin ta shanye hawayen dake shirin sake zubo mata. Akwatin daya gani a gefe ya ɗakko, ya ɗaurashi a gadon tare da buɗewa. Da kayan barci dake sama ya fara cin karo, batare da damuwaba ya ɗakko na saman kawai ya maida ya rufe. Takowa yay ya ajiyesu gabanta fuskarsa a tsuke kamar yanda ta santa, cikin rashin sakewarsa yace, “Ki tashi ki sauya kayanki ki kwanta”.
     Daga haka ya juya ya nufi ƙofa. Da kallo ta sake binsa tana share hawayen da suka ziraro mata. Yana fita ta ɗaura hannu duka a kai tana sake fashewa da kuka. A fili tace, “Na shiga uku ni Zinneerah ina ni ina zaman aure da Yayanmu? Wlhy yafi ƙarfina, matarsa tafi ƙarfina bazan iya da bala'inta dana Mammah ba”.
    Sai kuma ta zame ta kwanta tana jan numfashi dake sarƙe mata a ƙirji da ƙyar. Tabbas bazatace batason Yaya Abdul-Mutallab ba, dan ya cancanci zama abinso ga kowacce irin mace ciki harda ita da a yau zata iya kiran kanta mai sa'a ma, amma tasan yafi ƙarfinta ta kowanne fanni na rayuwar duniya, duk da tasan zata iya finsa a lahira itama wannan hukuncin ALLAH ne. Miyasa MAKAUNIYAR ƘADDARA zata rasa a inda zata jefata sai cikin rayuwarsa?. Ta inama zata fara kwatanta zaman aure dashi itako?.
             “Idan nace bana son abu sau ɗaya to a kiyaye mini, inba hakaba zan ɓata ran mutum kamar yanda ya shirya ɓata nawa”.
     Ta tsinkayi muryarsa a bazata batare data san ya sake dawowa ɗakin ba. Zumbur ta miƙe zaune da kwasar kayan barcin daya ajiye mata tana sauka a gadon batare data yarda ta kalli ko sashen da yake ba. Kamar ƙyaftawar ido ta afka toilet ɗin ɗakin.
        Tea cup ɗin hannunsa ya ajiye a bedside drawer yana ƙoƙarin zaro wayarsa datai alamar shigowar saƙo. Ganin no ɗin aunty Zakiyya ta sakashi buɗe saƙon dan yasan Mammah ce.
       _Ina ƙara tabbatar maka karka taɓa yarinyarnan Abdul-Mutallab, dan zaka gamu da ɓacin raina da baka taɓa ganiba a tsahon shekarun rayuwarka talatin da huɗu_.
       Murmushi ne ya suɓuce masa, yaɗan girgiza kansa da faɗin, “Mammah problem”. Akan laɓɓansa. sai ma ya kashe wayar baki ɗayanta ya ajiye ya ɗauka lap-top ɗinsa daya shigo da ita ya shiga hidimar kunnawa dan akwai abinda yake son yi daya shafi business ɗinsa da wani abokin harkarsa mai turo masa kaya daga dubai...............✍
   

*_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*

Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.

*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_

*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_

*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_

*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_

*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_

Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.

Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍





*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*

*_TYPING📲_*


*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*


_________________________


*Page 52*

...........Gargaɗinsa yasa Zinneerah tana canja kayan tayo alwala da sake naɗe jikinta da lifaya ɗin ta fito duk da kayan barcin wandone har ƙasa da riga, kasancewar rigar guntuwa mara hannu yasa taji bazata iya fitowa da itaba gabansa. Gashi ta cire bra ɗinta dan bata iya barci da ita ciwon ƙirji take sanya mata. Buɗe ƙofar tai a hankali ta fito cike da sanɗa kamar wadda ta aikata wani abu. Ganinsa zaune a saman sofa hasken system ɗin da yake sarrafawa ta haska kamilalliyar fuskarta ya sata satar kallonsa.
         Duk da yaji motsin fitowar tata bai ɗagoba yanata aikin gabansa, ganin ta cigaba da tsiwa yace, “Ɗakko tea gashi can kizo nan”.
         Cike da dauriyar yanda kanta ke mata tsananin ciwo ta wuce ta gabansa ta ɗakko kofin tea ɗin daya ajiye a bedside drawer ɗin, gabansa tazo tana niyyar kaiwa tsuggune dan duk zatonta shine zaisha abinsa sai taji yace, “Zauna anan”. Ya nuna mata gefensa yana cigaba da aikinsa.
      Taji ko tamkar ta kurma ihu, dan duk da kujerar doguwace yazo kusan tsakkiyane ya zauna, hakan yasa inda ya nuna mata ɗin dolene zai basu kusanci matuƙa idan ta zauna. Shiɗin ba abin wasanta bane a kafin yau ma ballantana kuma a yau ɗin da take jinsa a sama ƙololuwa da girma, a can ƙarshe takai zaune tana ɗan gyara lafayar dake neman zamowa.
       Ɗan dubanta yay a karo na farko ya ɗauke kansa ya maida ga abinda yakeyi, “Maza shanye ki bani kofin”.
A yanda yay maganar ya sake tabbatar mata da umarninsa, sannan ko banza ma dai tanajin kunyar, dan dama dawowarsu daga wajen walima ne Hajiya iya ta tilasta mata shan tea ganin bataci komaiba a can sam. Kusan rabi tasha tace ta ƙoshi, bai tanka mataba bai kuma kalletaba yanata aikinsa. Tsahon minta ɗaya ta fahimci baima da lokacinta sai ta cigaba da shan shayin hawaye na ziraro mata, cikin dabara take saka bakin lafaya ɗin tata tana sharewa harta kammala shanyewa ta miƙe da kofin a hannu.
     Tunanin ina zata kai ya sata duƙar da kai ƙasa, muya na rawa tace, “Ina ne kitchen?”. A yanda tai maganar ya tilasta masa ɗagowa ya dubeta na kusan sakan huɗu, ajiye lap-top ɗin yayi gefe ya kamo hannunta ya sake zaunar da ita kusa da shi, kansa tsaye ya janye lafayan data sa har a saman kai da ɗaura hannunsa a saman wuyanta. Sosai jikinta yay zafi. Kansa ya ɗan girgiza batare da yace komaiba ya miƙe tare da ɗaukar cup ɗin ya fice, zamewa tai a hankali ta jingina da kujerar tana lumshe ido da jan ajiyar zuciya, acan ƙasan ranta kuwa fal mamakinsa take da gulmarsa akan ashe yana da ɗan sauƙin kai.
        Tashi tai zaune jin ya sake dawowa, kanta a ƙasa harya ƙaraso ya sake zama a inda ya tashi yana miƙa mata magani da ruwa daya zubo a glass cup, babu musu ta amsa dan tana buƙatar maganin kodan ciwon da kanta ke mata.
        “Tashi ki cire wannan abun da kika naɗe jiki kamar magani kije ki kwanta”. Ya faɗa kansa tsaye yana ɗaukar lap-top ɗinsa ya cigaba da aikinsa. Miƙewa tai cikin bin umarninsa, sai dai gaba ɗaya tama rasa ta ina zata fara warware lafayar saboda tsananin kunya da shakkarsa. Ta saci kallonsa yafi sau goma, ganin shi hankalinsa ma nakan aikinsa yasata juya masa baya da fara warwarewa da sauri-sauri, ko batun linkewa bataiba ta ajiyeta gefenta ta haye gadon taja bargo har wuyanta tana sauke ajiyar zuciya dajan numfashi a gwame.
       AK daba kallonta yake ba, burinsa kawai ya kammala aikin shima ya kwanta dan kansa ya fara ƙarfafa ciwo ya ɗan dubeta jin ajiyar zuciyar data ja da ƙarfi. Ita kam runtse idanunta tayi da fatan barci ya ɗauketa ko zataji sassauci da nutsuwar halin da take ciki a yau. Har yanzu ta kasa daina imagine cewar Yayansu ne mijinta. Ta rasa miyasa su Granny sukai tunanin yin wannan kwamacalar? Inama laifin a bata Khalipha ko Moos'ab, amma maganar ta girmama Yah Abdul-Mutallab matsayin mijinta na aure.
     Da wannan tunane-tunanen barci ya ɗauketa, harya kammala abinda yake ya fita a ɗakin kusan mintuna talatin sannan ya dawo, fitilar ɗakin ya kashe zuwa ta barci, ya nufi gadon ya hau yana ɗan yamitsa fuska saboda kansa dake masa ciwo. Sai da ya zauna yaɗan jingina da gadon yana furzar da huci da lumshe idanu, kusan minti ɗaya sannan ya buɗe da waiwayawa yana kallonta ‘Komanta mai sanyi dai-dai da yanayinta’ ya ayyana a ransa dakai hannu ya gyara mata bargon dake neman toshe mata hanci. Ya mata kallon kusan mintuna uku kafin ya janye idanun nasa da sauke ajiyar zuciya.

        Cikin barci Zinneerah taji kamar an sakata cikin wani abu mai ɗumi da yafi bargon bata kariya daga sanyin da takeji, taja numfashi da iskarsa ta haɗa da daddaɗan ƙamshin turarensa wajen shige mata hanci, gabantane ya faɗi dan tabbas ɗumin yayi kama dana jikin mutum, babu shiri ta buɗe idanu duk da ɗakin babu wadataccen haske kuma kanta na'a ƙirjinsa ne. Ba ƙaramin harbawa zuciyarta tayiba na tsoro, sai dai can wani shashi na gargaɗinta akan karta nuna ta farka zaifi taimakawa tsananin kunya da fargabar dake tare da ita.
     Dole ta ƙarajin zuciyarta da jinin nikinta na cigaba da tsitsinkewa da tsananta sauri wajen gudu. Sarai ya fahimci ta farka, amma sai ya shareta saboda taimakama zuciyarta dake harbawar da har yake iya jiyowa bata salama. Su dukansu sun jima basuyi barciba kowa yana saƙa mai fisheshi, yayinda ɗumin jikinta ke raguwa saboda taimakon daya bata da jikinsa.  Daga ƙarshe dai su duka barcin ya ɗaukesu saboda maganin da suka sha.

_________________★

          A ɓangaren su Mammah kuwa ita da aunty Zakiyya barci sai dai ɓarawo ne ya figesu, sunason zaman tattauna abinda ke musu kaikawo hakan ya gagara saboda Mahma, daga ƙarshema Mahma hukunci ta yanke ita zasu kwana ɗaki ɗaya da Mammah, aunty Zakiyya kuna ta kwanta wajen Farah.
     Wannan abu ya musu ciwo su duka amma babu damar magana. Itako tayi hakane saboda fahimtar take-taken Mammah akan son hana AK nuna kulawarsa ga amaryarsa. Rashin mafita yasa Mammah amsar wayar aunty Zakiyya ta sake turama AK saƙo bayan ta kirasa a wayar ta masa gargaɗin farko. sarai Mahma na lure da ita amma sai batai maganaba ta girgiza kai kawai tana nemawa ƴar uwar tata shiriyar UBANGIJI danshi tafi buƙata a yanzun.

       ★★★★

   Kiran sallar farko ya buɗe idanu kamar yanda ya zame masa jiki, dan ko a london yake a irin wannan lokacin yake farkawa duk asubahi saboda alarm da yake saitawa. Sam barcin bai isheshiba, hakan ya saka idanunsa yi masa nauyi matuƙa amma ciwon kan ya sauka. Akan Zinneerah dake nannaɗe a jikinsa ya saukesu, yanda fuskarta tai wani fayau a barcin ya sakashi nutsuwa wajen ƙare mata kallon kusan mintuna uku, hannunsa dake a saman cikinta ya ɗaga a hankali yakai ga fuskarta yaɗan tallafi kuncinta ta gefe da ɗaura babban yatsansa akan laɓɓanta da suka daɗe suna tsole masa idanu. Yatsan ya shiga zagayawa a kansu taushinsu da santsinsu na masa daɗi, duk dama aɗan bushe suke a yanzu.
          Cikin barci ta dingajin kamar ana shafa mata lips, ga kuma hannunsa da kusan nauyinsa ke a ƙirjinta, ɗan motsawa ta shigayi alamar zata farka, sai kawai ya janye hannun nasa ya tashi zaune tamkar bashi ya aikata ba, buɗe idanunta yayi dai-dai da saukarsa a gadon yana faɗin, “Ki tashi kiɗan watsa ruwan ɗumi zakiji jikin ya saki gaba ɗaya”. Cikin muryar barci yay maganar dan haka ta fita a sanyaye da ɗan kauri kuma.
      Bata iya motsawaba harya fice dan wata irin matsananciyar kunya ke cinta, wai yau itace kwance a gado ɗaya da Yayansu. Jikinsu manne da juna, kai itako ina zata kai wannan abun kunya yau. Da wannan tunanin ta miƙe da ƙyar ta nufi toilet domin yin amfani da shawrsa nayin wanka.
        Tako ji daɗin wankan, dan jinta take fayau saboda zazzaɓin ya saketa, tana fitowa jikinta kawai ta tsane ta ciri doguwar rigar jallabiya a akwatin daya cirar mata kayan barci jiya ta saka, ta ɗauka turare a handbag ɗinta ta fesa sannan ta saka hijjab domin yin salla.
                     Bayan ta idar da ƙyar ta iya zaman yin azkar, tanayi tana gyangaɗi harta samu ta kammala da ƙyar ta sake komawa gadon ta kwanta dan wani irin barci takeji bana wasaba.
     Shima koda ya dawo daga massallaci sashensa ya wuce ya sake kwanciya koma azkar ɗin shi bai iya zaman yiba.
         
★★★

         A gidansu Hajiya iya kusan baƙi duk sun tashi da haramar wucewa yau, musamman ma ƴan danya da jikin Tinene ya rikice, dan kwana tai tana sheƙa amai a daren jiya, sai gabannin asuba tai barci. Da safe basu tadataba har suka kammala shirinsu, kusan ƙarfe takwas aka kawo musu abincin kari suda ƴan ɗanmusa da suma suke shirin fitama da wuri dan zasu biya ta gidan mmn sadiq su.
         Zuwa ƙarfe goma duk suka kammala abinda sukeyi, har Tinene ma an tadata ta shirya sai dai ta kasa cin komai duk ƙaunar abinci da takeji a ranta. Hajiya iya data shigo suka gaisa ganin sunta shiri take tambayar badai tafiya da sassafen nanba kamar korarru?.
       Cikin jin nauyinta da girmanta sukace tayi haƙuri zasu tafi haka nan ai anci biki Alhmdllh. Da yawansu sunbar yara a gida kuma.
      Godiya tai musu da addu'oin fatan alkairi, tace su ƙarasa shirin to a fara kaisu gidan amarya. Gwaggo Laritu ce tace, “Hajiya ai dama an barshi kawai tunda jiya munje”.
        “A'a ya kamata kuje gaskiya itama zataji daɗi, jiya duka zuwan minti nawa akai, ku ƙarasa shirin kawai bara naje na shirya abincinsu suma”. Daga haka tai sallama da su ta fice.

   
★★★

    Kusan tara da rabi Zinneerah ta farka, yanda ta ƙarajin ko ina na jikinta ya ƙara saki taji daɗi, gadon ta gyara tsaf, duk da ɗakin ba wani datti yay ba ta fito neman kayan shara. Sosai falon yay mata ƙyau, komai na cikinsa ya kasance ash color da ɗan ratsin pitch kaɗan-kaɗan, sai ƙamshi ke tashi mai daɗi na turaren wuta. Sake fitowa tai inda nanma falo ne da yafi na ciki girma sosai mai ɗauke da bedrooms biyu sai ƙofar kitchen da zakabi ta dining, kalar komai dake a falon ta kasance lemon green and light orange. Fallon babbane dan yafi wanda ta baro, samun kanta tai da leƙa bedrooms ɗin suma ta gani, ɗaya akwai gado a ciki da komai na kayan ɗaki brown da sukai matuƙar ƙyau, dan shima ya burgeta sosai, tana kuma ƙyautata zaton sune ƙoƙarin iyayenta. Har bathroom sai da ta leƙa tana maijin ƙaunar Abba da Baba har cikin ƙoƙon ranta. Daga haka ta fito ta leƙa ɗayan ma. Shikam katifa ce kawai aciki babba sai ƙaramar drawer da mirror. Shima dai ya mata ƙyau ɗin. Ta dining tabi zuwa kitchen, shi kansa dining ɗin abin kallone. Data shiga kitchen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login