Showing 1 words to 3000 words out of 81675 words

Chapter 1 - Likitan Zuchiya Hausa Novel Complete

[29/04 12:05 pm] 🔳◾◼▪💙: `☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
☆We the best ☆

Email:[email protected]
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Labari me tab'a zuciyata.... Karatu cikin harshen hausa... Tafiya cikin nutsuwa da tunani me kyau... Yanayi na d'aukar hankali..... Soyayyar gaskiya me tafiya da qauna Zallah....
Bani da lokacin b'ata lokaci akanku dan kunsan dawa kuke... Da marubuciyar data nishad'antar daku cikin Novel nata na Y'AR QAUYE KO Y'AR BIRNI.... MASEEFAR SOO... Birnin masoya... SADEEQ.. Amakirci na... SAMAREEN BANAH.... HAYATUDDEN..

*Ban yarda kina budurwa ko kina bazawara. Ko kana saurayi. Koka tab'ayin Aure Ku karanta min littafi ba. Nayi shine kawai DON Ma'Aurata🙉 ba dan Kuba...*

Jaruman cikin labarina....
ADAMSY
NUFAISAT
TAUDAT
MUSLEEMAT
RAHMA NALELE Auntyn Luv☆
Junior Ramadan nah👌🏻

” بسم الله الرحمن الرحيم


☆page 01☆

ADAMSY Likitan zuciya... Aka rubuta ajikin allon bangwan dazai sataka da cikin ofishin nasa..
Da rikicewa wata Yarinya me sanye da kayan asibiti farare (Norse) take kwankwasa k'ofar ofishin nasa..
Kyakkyawan mutum ne.. Wanda ya had'u tako ta'ina. Shekarunsa bazasu wucce 33 ba. Saidai idan kagansa zakayi tunanin d'an shekara ishirin da shidda ne. Yana sanye da rigarsu ta likitoci kan kujerar da take mallakinsa. Yana da dogwan hanci me d'auke siririyar fuska wacce take da fad'i kaɗan.. Ma'ana dai anan shine fuskarsa baza'a kirata da ririya ba kuma baza'a kirata dame fad'i ba. Tana dai tsaka tsaki..
Sannan yana d'aya daga cikin mutanan nan waƴanda sudai baza'a kirasu da dogayeba. kuma baza'a kirasu da gajeru ba.. Saidai yana da ɗan ƙiba kaɗan.. Wacce bazamu kirata dame muni ba.
Sannan yana da faɗin ƙirji me ɗaukar hankali..

Yana da San ƙamshi yana da San tsafta. Yana da San kwalliya. Yana da San gaye. Yana da San abu me kyau. Yana San gaskiya. Yana San mutum me bin ra'ayinsa. Yana San wulɗa da mutanan kirki. Yana San matarsa San gaskiya. Yana san iyayansa. Yana San yara so me tsanani. Yana San temakwan su. Yana San temako arayuwarsa. Yana San mutumin da yake San shiga al'amuransa. Yana San sana'arsa ta ceton rai da kasuwancinsa da yakeyi
Ga Y'a mace kuma. Yana San mace me SHAGWAƁA. Me kirki. Me nutsuwa. Me San KWALLIYA. Me tsafta. Me kissa. Me iyayi. Me iya kalaman qauna. Me nutsuwa yayin da yake jinta. ME IYA GIRKI...
Baya San rainin hankali da wulaƙanci haɗi da munafunci.. Mutum ne me aji!!!. Aji!!!! Fah😳. Irin sosai d'innan.👌🏻
Baya shiga harkar daba tashi ba.
Sam ADAMSY bashi da yawan abokanaye.. Saidai ko'ina ya shiga afad'in garin KADUNA sanshi ake. Ƙaunarsa ake. Jinsa ake.... Saboda halinsa nagari ne. Me kyauta ne. Me tsausayine. Me kwantar dakai ne agun duk wani mutum Wanda yasan ya girme masa ya haifesa.. Toh ADAMSY yana da halin bashi girmansa..
Wannan kad'an kenan daga cikin halaye na ADAMSY..


*****
"Yas shigo... Yace da wannan yarinyar da take kwankwasama mai ƙokar
Ahankali tashiga tana cewa.. "Sannu doctor. Dama mahaifiyatace aka kawota yanxu. Shine doctor RAMADAN yace pls kazo kad'an samai hannu.. Yau baya jin dad'ine. Sannan yace dan Allah kayi hakuri yasan lokacin tafiyanka yayi. Danya kiraka baka d'auka ba.
ɗan rintse ido yayi kad'an. Sai hakan ya qara masa kyau..

_Sarki ya tabbata ga Allah. Mamallakin kowa me komai. Allah kabani miji irin ADAMSY. Me kyau. ne me tausayi. me dukiya._ duk da mahaifiyarta ce kwance rai ahannun me dukka. Amman bai hana zuciyarta fad'in wannan kalamai cikin ranta ba!!😌

Ahankali cikin sanyayyiyar muryarsa me dad'in sauraro yace.. "Owkie. Jeki ganinan zuwa..
Da Murmushi akan fuskarta tayimai godiya da ficcewa daga ofishin..
Sauri-sauri gudu-gudu ya saka laptop ɗinsa a jaka tare da ɗaukar wayarsa ya fitto da kulle office ɗin nasa..
Cike da nutsuwa yake tafiya kamar yanda ya saba.. Cikin nutsuwa masu tsaran lafiyansa sukaxo garesa da karb'ar laptop ɗin tasa. Da wayansa. Suka saka cikin motar da yake hawa.
Sannan yace musu baya fitto tafiya bane. Zai d'an duba wata ne a part na doctor RAMADAN Yanxu zai fitto. Ai da ladabi suka mai fatan alkairi yanufi part ɗin doctor RAMADAN

"Bayan doctor RAMADAN ya gama yimasa bayani akan tana da ciwan sugane.. Sai kuma yanxu ya lura Kamar tana da matsala da zuciyarta. Hakan yasa ya nemi saka hannunsa...
Shuru doctor ADAMSY yayi yana duba matar.
Can yace... "Eh. Zuciyarta tafara karɓan wasu sakwanni. Wanda ada bata karɓarsu. Wannan dalilin ne yasa take qoqarin San taga taba me ita wahala. Kafin tabuga.
Zan mata wani aiki da ɗorata akan wasu magunguna.
Idan Allah yaso. Zata samu lafiya. Saidai fah dole ta kaucema waƴancen sakwannin da suke San tarwatsa mata zuciyar tata..
Jan numfashi doctor RAMADAN yayi da cewa.. "Masha Allah. Naga zuciyar tafi buƙatan kulawa ayanxu. Dan haka kagama naka aikin nayi nawa..
"Toh akai min Ita part d'ina... Ya faɗi hakan yana me ficcewa daga gun.
Da "toh doctor RAMADAN ya bishi dashi..

Awa d'aya ya d'auka yana mata aikin. Kafin ya gama ya baro asibitin..

Motoci bakwai ne suke tafiya akan titin..
Uku a baya uku a gaba.. D'aya ƙaramar a tsakiya..
Kaf dukkansu motacin anrubuta.. ADAMSY..
Kina dai gani kinsan dukiya na aiki..

Direct supermarket d'insa suka nufah Wanda yake da girman gaske.
Babuce kawai babu a supermarket ɗin..
Ma'aikata wajen suna ganin tawowarsa kowa ya gyara kansa.. as oga yaxo..👌🏻
ɗan zagaye zagayensa kawai yayi da duba wasu mahimman abubuwa sannan ya kalli wani qaninsa Salim Wanda ya ɗorasa akan al'amuran. Yace dashi... "Ka qara kula sosai da aikinka.. Dan naga kamar kana wasa dashi..
"Insha Allah zan qara kula.. Amin afuwa..
Maida gilashinsa ADAMSY yayi da sakin wani Murmushi ya juya yana bashi amsa da cewa.. "Anyi maka. Dafatan zakayi qoqarin kiyayewa.
"Insha Allah.. Salim ya faɗi cikin sauri da girmamawa..
[29/04 12:05 pm] 🔳◾


[29/04 12:05 pm] 🔳◾◼▪💙: `☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. *☾•RAHMA* MUH'MD RUFA'I NALELE..☆

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
☆We the best ☆

Email:[email protected]
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم


☆page 02☆


Gidan marayu matuqan nasa sukayi dashi Kamar yanda suka saba..
ADAMSY duk wata yana kaima gidan marayuwa tallafi.. Sannan kullum Idan ya tashi daga aiki bayan yaje duba wajen kasuwancinsa toh Lalle saiyaxo ya duba yara agidan marayun nan yaga Ko suna lafiya...
Bama wannan kad'ai ba. Kaf yaran dayake temako bawanda bai san shi ba.
Suna matuƙar sanshi da ƙaunarsa..
Yana zuwa wajen dama suna tsaye wajen jiransa. dan haka yana fittowa suka sungumesa suna masu suna murna da farin cikinsu na ganinsa..
Yafi kula yara qanana. Irin waƴanda suke da shekaru uku biyar takwas goma Sha d'aya Sha biyu. Qasa da haka..
Toh yauma haka yana fittowa ya gansu zaune kawai shi suke jira..
Aƙalla zasukai hamsin.
Haka sukazo da gudu suka rungumesa suna murna
Duk sun cukwikwaiya masa kaya..
Saiya ɗaga wannan ya sauke.. Ya ɗaga wancan ya sauke..
Sanda ya gama raba musu alewa as sadaka. Sannan yaba masu kula dasu wasu kayayyaki Wanda yake da tabbacin akullum yaran suna buƙatansu..
Sannan yayi musu sallama ya fito masu tsaransa suka bud'e mai ƙofar mota ya shiga suka rufe kana sukaja motocin..
Basu tsaya yanxu ako'ina ba. Sai'a gidansa..
Gidane Wanda yatara abin duniya.
Gidane Wanda kana kallansa zaka kirasa da aljannar duniya..
Ya haɗu iya kar haɗuwa.
A far fajiyan gidan motucine na alfarma guda uku... Bayan Wanda aka dawo dashi dasu. Da alama wannan na Matar gidan ne.. Wajen parking na motocin kansa abin kallo ne
Dan yana da girman gaske..
_Haka Allah yake ikwansa.. Wasu yabasu wasu kuma ya hanasu. Kaidai karoqesa ya baka na halak ba haram ba; ya baka Wanda zai maka amfani. Wanda zaka bisa akan tsarin addinin musulinci!!!
Ahankali suka bud'emai motar ya fito da karb'ar y'ar jakarsa. Dan dokace baya barin masu tsaran nasa su shigamai cikin gida inda iyalinsa take.
Kawai Idan yana gida toh suma suyi nasu shashin..


"Assalamu-alaikum MESONA
Ya shigo falan da Murmushi akan fuskarsa yana me leqen ta'inda zaiga masoyiyar tasa...
Aiko canya ganota da qawarta suna masu hira cikin farin ciki da qaunar juna....
Lokacin da NUFAISAT tayi ido hud'u da Mijin nata tashi dayi da Sauri tazo ta rungumesa tana me nuna murna da farin cikin dawowarsa...
"Amma sweety banji shigowarku ba...
"Tayaya zakiji. Bayan kina tare da wannan wacce tabi ta kanannad'eki da zaqin baki..... Ya bata amsa da fad'in hakan yana me nuna mata qawarta TAUDHAT..
Da wani yanayi.. da wata shagwaɓa.. Da wani kallo.. tace... "Zaƙin bakinta agareni. bazai tab'a shagaltar da ruhina daga lura da jinka ko kuma ganinka ba...
Kawai kaidai kayarda banjika bane da gasken gaske. 🙂
Murmushi yayi da zareta daga jikin nasa ya nufi part nasa yana cewa. "Na yarda sweetyna.
Murmushi tayi da binsa da kallo. Kana takoma ta zauna sukaci gaba da hira da qawarta tata TAUDHAT BATARE DATA BISHI DAN TATEMAKA MISHI WAJEN CIRE KAYA BA.🙂

Can yafitoh falan da wata sabowar shiga. kallo d'aya zakamai kasan yayi wanka ne..
ADAMSY kenan mekatu....
Zama yayi a dining teble
Ga mamakina sai naga TAUDHAT tataso da Murmushi zuwa garesa tana cewa.... "Sannu da dawowa *MIJIN K'AWA*.. Fatan kadawo lafiya.. Allah yasa ba wani Wanda ya b'ata maka rai awannan ranah.. Wajen zaman ka wajen kasuwancinka. Konace a asibitinka..
Da Murmushi yace da ita... "Ba Wanda ya b'atamin rai. Kuma lafiya lau nadawo ga matata.. Fatan dai girkinki agareni yau yafi na jiya d'and'ano..😌
Wani shuqumin Murmushi ta kai masa🤔 da fara zuba masa abubuwan data b'ata lokaci wajen girka masa tana cewa... "Ai akullum qara Neman sani nakeyi. Indai akanka ne. Nayi alƙawarin bazan tab'a bari kakawoma K'AWATA Kishiya akan girki ba......
Lumshe ido yayi lokacin daya kai farfesun kayan ciki bakinsa... Gaskiya yayi dad'i sosai.. Hakan ne yasa daya bud'e idan nasa ya sakar mata murmushinsa me tsada da furta kalmar... "Ki daure ki rayu da qawarki dan bani San nayi missing girkinki
Murmushi taƙarayi da zubamai drink a cup tajuya da nufar aminiyar tata tana cewa.... "Karka damu.. zan rayu da ITA da KAI.. har izuwa qarshen rayuwata...

Rungumarta NUFAISAT tayi da fad'in... "Nagode Aminiyata. Kina kula min da Mijina. Kina kulamin da cikinsa fiye da tunanina...
Nagode sosai fah

"La😀 karki damu Aminiya.. Ai hidima ga Mijinki dani ya dace Idan da kara... Shine fa abin sanki abin qaunarki Wanda kikaso kashe kanki saboda shi. Idan ban kulam miki dashi ba dawa zan kula.
Kawai damuwata d'aya. kyautatawata agaresa. Allah yasa ta maqale cikin zuciyarsa. yaƙi mantawa dani. ta dami zuciyarsa hakan yasa yaqi qara miki abokiyar zama dan ina kishin wata Y'a mace tarab'ar miki miji sanadin girki kawai.😀... TAUDHAT ce me fad'in hakan..

Qara Rungumarta NUFAISAT tayi da cewa. "Nagode... Alamu sun nuna zashi gun Dady... Dan haka kijirasa ya gama saiya sauke ki agida. Tunda yanxu kin fara qin tawowa da motarki...
Jan numfashi TAUDHAT tayi da fad'in "Toh Qawa...
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH*
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. *☾•RAHMA* MUH'MD RUFA'I NALELE..☆

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
☆We the best ☆

Email:[email protected]
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم

☆page 03☆


Yana jinsu ahaka ya gama da tashi ya goge bakinsa da tishu yana fad'in.. "Toh my luv. Kamar yanda kikayi harsashe. Zani gunsu Dady. Kina da buqatan wani abu ne natawo miki da shi...
"Bana da buqatar komai.. Saidai kawai kasauke Y'AR UWA agida dan Allah.
"Angama my luv. Ya fad'i hakan yana me kallan TAUDHAT kana ya ficce daga falan.
"Toh Y'AR UWA Ni zan tafi. Sai Allah ya tashemu lafiya
"Nagode Y'AR UWA.. Ki gaishe min dasu mamah.
"insha Allah zataji.. TAUDHAT tabata amsa da ficcewa dana sakar mata Murmushi
Itama Murmushin tasakar mata..

Sanda taji tashin motarsu sannan tanufi dining da kwashe kayan kai. Takai kitchen. Tadawo tagoge wajen. Sannan takoma kitchen d'in tawanke kayan da adanasu a inda ya dace Sannan tanufi bedroom nata tana nazarin qara yin wanka..

ADAMSY da TAUDHAT ko. Kamar yanda suka saba. Idan bataxo da motarta ba.. Toh Idan ya d'auketa atashi motar bamema wani magana
Kasancewar shi d'in miskiline kuma me Aji
Dama Ita kanta tasan ba wani dalilin da zaisa yayi hira da ita imba tana tare da matarsa ba
Kawai zai kulatane da hira ne idan tana tare da NUFAISAT matarsa
Dan tasan shi mata basa gabansa
Kawai matarsa itace agabansa
Wannan dalilin yasa Idan tana tare dashi takan d'auki wayarta tata danne dannanta..
Dama shi yasan kansa ba wata hira da zaiyi da ita. Dan baisan me kuma zasuce ba
Shiyasa kawai yake maida hankalinsa kan tuqinsa dan baya tafiya da masu tsaransa zuwa gidansu
Wannan tsarinsa ne!!!

Ahankali ta kallesa da lankwashe harshenta tace dashi... "Nagode Mijin Qawa
Da Murmushi ya bata amsa da cewa... "Kinfi qarfin hakan. Kuma har yaushe zaki dena godemin Idan nakawoki gida..
Itama da Murmushin tabashi amsa da.. "Ai kaima kullum cikin godemin kake..
Da zaka dena da naji dad'i
"Hidima dani fa kikeyi Kullum.. Idan ban gode miki kullum ba. Me kikesan nayi
"Alamu dai sun nuna ba wanda zai dena godema juna a tsakaninmu....
Kan yabata amsa wayarsa tayi qara.. Koda yaga me kiran nasa. Murmushi yasake da d'auka yana cewa... "Hankalinki ya kwanta my luv. Yanxu na sauke miki qawa..
Murmushi NUFAISAT tayi dai-dai lokacin da take d'aura tawul ajikinta dan shiga wanka tace da shi... "Hankalina kuma bazai qara kwantawa ba. Harsai najika kaje gasu Ammee lafiya kadawo gareni lafiya.
"Fatan alkairi kawai matata
"Na kwana inayi maka Mijina
"Toh kiqara gyaramin kanki da kyau. Dan gajiyar yau.. ta Musamman ce..
"Kace na shirya karb'ar dukkanin tarin gajiyar..
"Abinda nake nufi kenan
"Toh ka kulamin da kanka..
"Naji my luv
Sanda ya ajiye wayar gefansa Sannan ya kalli TAUDHAT da sakar mata Murmushi yace... "Haka kawai kin zauna kina jin sirrina da matata..
Murmushi TAUDHAT tayi da ficce daga motar tana cewa.. "Amin afuwa bansan lefi nayi ba.. Kuma mah banji komai da kuke cewa ba..
Jan motarsa yayi kawai da Murmushi

Ita kuma tad'an cije harshenta da shigewa gidan nasu
Bata tarar da kowa a falan nasu ba. Dan haka saitai jifa da jakarta..
Ta zube akan kujera tafad'a tunani
Ahaka mamah mahaifiyarta taxo tadafata tana cewa... "Niko zanga ranar dazaki dawo daga gidan NUFAISAT ba tare da tunani ba
Murmushin yake tasakarma Maman nata da cewa. "Nima ina fatan naga ranar dazan dawo daga gidanta da farin ciki.
"To Wai meyasa hakan take faruwa dake
"Wallahi mamah San mijinta nakeyi😔
Ina San ADAMSY
Danya tara duk wani abun da mace me aji takesan samu agun Mijin Auranta..
Duk da cewar yanxu kin manyanta.. Amman hakan bai hanaki cewa ADAMSY ya had'u ba
Dan Allah kiyarda mu had'a kai nashiga gidansa matsayin matarsa ta biyu...
Mamah ko kin manta ranar da kika gayamin cewar ya had'u..

"Ban manta ba TAUDHAT.. Kuma yanxu ma zan qara nanata miki..
ADAM ya had'u.. Dan ban tab'a ganin yaro Wanda ya had'e komai na rayuwa irinsa ba
Amman hakan dace da kamata yasa ki soshi aranki ba..
Saboda matarsa Y'AR UWA ta d'aukeki.
Wannan cin AMANA ne
Ina rokwanki daki dena San ADAM.. Dan kwata kwata baku dace da juna ba.
Duk da cewar ke Y'ata ce.
Bazanso kici amanar ADAM da NUFAISAT ba..
Saboda shi nagari ne
Shiba walaqantacce bane
Shi mutum ne me kamun kai
Bai kyautu da had'in kaina kizama mata a garesa ba
Kefa karuwace.. Wacce take karuwanci da manyan y'an iska..
Ko kin manta hakan ne
Shekarunku ashirin da biyar da NUFAISAT.. Amman bata tab'a sanin hakan ba
NUFAISAT bata tab'a sanin kina da wasu mugayan d'abi'u ire iran waƴannan ba.....
Cikin fusata da tsawa TAUDHAT tatashi tare da katse mahaifiyar tata da hannu tana cewa... "Ya isa haka mamah.. Bansan har sai yaushe zaki fara sona ba
Dalilin halin rayuwar da muka shiga nafad'a wannan halin da kike fad'a
Ke wacce irin uwace Mara imani
Kin tambayeni damuwata nagaya miki ita. Mazaisa bazakibi bayana ba
Saikace bake kika haifeni ba..
Sai kace bani kad'ai bace y'arki aduniya..
Ina ganin iyayan da suke bin ra'ayin y'ay'an su. suna jinjina basira irin tasu. Idan sunxo musu da wata shawara. Ko wani abu da suke san aiwatarwa kuma su qarfafa musu gwiwa..
Daga yau idan har zanzo miki da wani batu kuma bazaki bi bayana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login