Showing 63001 words to 66000 words out of 144533 words

Chapter 22 - Dama Ta Book 1 Hausa Novel Complete

bata zuwa awu cikin amma zanbar abin arai idan naje gida naga yawa inna

Yau Fandau tun safe take zubar da wani irin ruwa wanda dama tana zubarwa amma na yau yafi na kullum Ahankali take jin ciwo amaranta ga cinyoyin tasun kara mata tauyin da kyar ta ke jan su kafin azahar har ciwo yakaru dan kozama ya gaga reta sai faman yarfa hannun take tana tsaye takasa zama idan tace tafiyan ba iyawan zata yin ba kawai sai ta daure ta sugun na tana yarfa hannun ta rike katakon gado gem tana ta adua
sai dare su Hadim suka shigo dan basu wuni agidan bane amma tunda ta shiga watan haifuwa basa ne sa da kita
Fandau ta gama jigata dan kukan da take ma gagaran ta yayi duk idon ta yafirfito kaman ninta ya canza
Tana jin motsun shigowan ta dago da kanta dukan su da gudu suka karaso inda take cikin kidima suke tambayan ta lfy baye Nabil dayayi saurin rungumo ta jikin sa tabar yazauna cikin jinin kamar ba nabil me tsantsanin jine ba
Hadim gani jine dayawa kamar ba ajikin mutum yafito ba kawai saita kama kuka Fandau tadaga kai ta kali Nabil takamo hannun tadan kamishi wani pepper a hannun sa cikin da shehiyar murya ta fara magana
"wanan mama ta zaka kaiwa idan kaje anguwan gargar kace gidan zannah modu za anu na maka mama ta sunan ta Aisa abata da hannun ta ko kanwata bagana idan Mama tace ta yafemin tonima nayafe muku duk abin da kuka min amma idan bata yafeba nima ban yafeba
Cikin kidima Nabil yafara cewa "bazaki mutu ba kanwata wllh baza ki mutun ba nida hannu na zan dauke kina kaiki wajen mama da ranki da lafiyan ki
Hadim da gata mukai ta asbiti
Ita ma cikin kuka tace "taya zamu kai ta asbiti ka manta haifuwan sirri zatayi ai bawani asbitin ta za akai ta asirin mu yatonu Nabil yace "Hadim kina da hankali kuwa ana maganan rai kina wani maganan tonan asirin yana cikin haka yaga fandau tayi wani irin mika tana salati
Dasauri Nabil ya sake runguman ta cikin kuka yake cewa Wllh baza ki mutu ba Wllh sai kin



*To masoya Fandau yau ne fa* *amma yaza ayin da maganan kaiwa *asbiti ga yasmin yar sa ido dama ta fara gano su*





```B JATTKO```
[3/12, 8:49 AM] Hauwa: *DAMA TA*



*NA*





*BATUL ADAM JATTKO*

29


Bazaki mutu ba
Duk jikin ta rawa yake gem ta kenkeme shi cikin wani karfin da Nabil baisan macce tana da shiba dan idan ance ya kwace bazai iya ba
Gumi ne yake keto mata salati kawai take yi
wani irin ne shine taji yazo mata sake kenkeme Nabil tayi gem
Hadim sai yanzu ta tsorata dan bata taba ganin haifuwa ba azaton ta fitan raine ganin yanda Fandau take yun kuri cikin karfi
Abin ya bata tsoro tace "Nabil idan ta mutu yaza muyi
Tafa de haka tana cikin riki cewa

Shiko Nabil yanda Fandau da danke shi ko halin magana ba shida shi balle yayi yunkurin ta shi
Shikan sa gumi ne yake keto masa duk addua da yazo bakin shi yake tofa mata

Cikin sa a Wani yunkurin tayi da karfi sai gawata sun guceci y'a ta fado dama yau riga da zani tasa zanin dama ya dade da kuncewa sai ciket din ta na ciki
ajiyan zuciya ta sauke ta saki Nabil
Shima jahota yayi jikin sa ganin yanda take sauke ajiyan zuciya ya rungume ta gyam yana sakin ajiyan zuciya bai masan me aka haifa ba
Sai jiyayi Hadim tana tace"kutuma macce macen ma baka me kamar ki kika haifa mana
Nabil
Yace "alhamdulilah alhamdulilah
sai faman shafa kan Fandau yake

yace "yanzu ina ne yake miki ciwo sai a sannan Fandau ta bude ido tace ruwa zan sha da sauri Nabil ya saketa yayi hanyan kitchen yana zuwa ya bude fridge ya dauko roban ruwa ya daga kanta yaba ta kurba daya tayi ta tuno da mejego bata shan ruwan sanyi asanin ta ta zare bakin ta tace na zafi nake so
Ya juya zai hanyan kitchen Hadim da take ta faman fadan anhafi macce kuma baka amma kuma ta daga yar ta daura ta a cinyar ta na goge bata furka

Tace "Nabil kaga macce ta haifa fa
Yace "good mekyun kenan
Tasake cewa "amma fa tafita kyu zo kagan ta
Yace ina zuwa

Hadim
Zanin Fandau da yake cikin jine Hadim ta jawo ta kwan tar da yar ta nufi lokan gadon fandau inda dama ta tana di almaka shin ta zare duk takawo part din ta ajiye ta dauko ta seta yatsanta kamar yanda aka mata bayan yankan cibiya ta yanke ta daure ta dauko wani zanin a whardrob din Fandau ta nade yar dai dai lokacin Nabil yafito da cup ahannun ya tashi Fandau ya bata
Hadim ta kalle shi ta bata rai tace wai Nabil mehaka ruwan ma sai kai zaka bata
Cikin tsawa tace keee kalle ni idan zaki ware maki ware ki temaki kanki dan mu muna fita adakin nan ba kara shigo miki zamu yiba sai munje mun dawo kafin nan kin gama jegon dan muna zuwa zamu daura daga inda muka tsaya kin haihowa mijina abin da yake so macce ni namiji nake so dan haka baki kubuta ba da namijin kika haifane ma wata kila shi ya hakura mu sallame ki inkinga mun barki to kin haifi namjiji
Amma abin da zan gaya miki ki temaki kanki kicire ragonci ki kasa jikin ki da ruwan dimi dan inda wanan sun kucece yar ta fito ba karamin budewa yayi ba
Inba haka ba kirube Wllh
tana gama fadan haka ta dauki zanin Fandau da yake cikin jini ta daura ajikin ta cire siket din ta ta zauna dabar acikin jinen da kazan tar haifuwan ta na Goggo ga cinyar ta take tayi jagab kamar ita ta haihu ta meke

ta kalle Nabil tace "zomu tafi Mu nunawa yasmin ko
Nabil ya kalle Fandau da kanta yake sunkuye tana zaune cikin jinin har yanzu
yakalli Hadim data rungumi jaririiya tana jiran sufita

Yace"haba yaza mufita mutar ta cikin wannan hali mu temaka mata da koda gyaran wajen ne mana

yamutsa fuska Hadim tayi tace wllh bazan iya ba zuciya ta bakaga yanda yake tashi ba ko wannan tsayuwan karfin hali nake
Gazanin ta dana daura dan yazama sheda awajen yasmin da ma aikatan gidan nan ya dameni da wani irin garni sona ke muje na kunce zuciya ta sai haurowa yake

Nabil yace " toki tsaya ni zan gyara
daukan Fandau yayi yayi hanyan bathroom da ita wani kishine ya kama Hadim cikin tsawa tace "my star a gabana kake daukan wata

Yajuyo ya mata wani irin kallo
yace "meyasa wani lokaci imanin ki bashida yawane idan ban dauke taba kina ga zata iya tafiya ne aga ban idon ki taci wannan a zaban
Itama cikin bacin rai da kishin yanda Fandau tayi wani lif ajikin Mijin ta

Tace"to meye wani a zaba a haihuwar macce macce fa ta haifa
Nabil wani kallo ya mata yace "in fisari kayan ragone kaza ma tayi mana yana fadan haka ya shige da Fandau bathroom ya sauketa abakin bathtub ya hada mata ruwan wanka me dimin ya sata yace "zaki iya yin wankan ko gyada masa kai tayi
Yace yawwa kidin ga kula da kanki dan mu ayau zamu tafi dan su ummi dama basu so Hadim ta haihu a nan ba sai cewa mukayi doctor yace ba ason tayi zaman jirgi cikin zai iya samun matsala dan haka muka musu alkawarin aranan da ta haihu aranan zamu taho dan haka ki kula da kanki kinji abin da tace ai zaki iya rubewa dan ki kula nima ina kaisu zan dawo cikin kwana ukku nan zaki ganni
Bata ce komai ba shikuma har yaje bakin kofa ya sake dawowa yarugume Fandau yace "wllh ko ban zauna da keba kina da mushin manci arayuwa ta daga nan har karshen ta
Kin bani abu biyu arawuwa wanda bazan taba mantawa da shiba
*Budurcinki*
Dakuma
*Y'ata ta fari*
Kissing din lips dinta yayi yace "ke ta musamman ce

Ita ko Hadim Nabil yana gaya mata wannan maganan tayi tsororo a tsaya ta bisa da kallo tana mai maita
_idan fisari kayan ragone kaza ma tayi mana_
Idan ta fashince shi gatse ya mata ne ko gori yanzu ni Hadim har nayi saken da Nabil zai gaya min wannan maganan kuma yasa hannun sa agaba na yadauki macce wanda ni bai taba dauka naba koda bani da lafiya sai yace nayi girma
Me hakan ke nufi
Kwaban zuciyar ta tayin da cewa tausayin ta yaji ganin ta wahala ita ma kan ta lokacin da Fandau take cikin nakudan ta tausa ya mata balle Nabil sarkin tausayi
Kukan baby ne yadawo da ita haiyacin ta tayi saurin kijjigata
Alokacin Nabil yafito ko kallon inda jaririiya da Hadim bai yiba yafara gyara wajen
Hadim cikin mamaki take binsa da kallo yau *shidmas* guda da sa hannu cikin jine yana aiki tukuru tas ya goge wajen yashiga yafita yana cikin wanke kayan jinen ne yaju ya yakalli Fandau da take ta faman gasa jikin ta da towel sai da ya gama wanke komai na kayan da ta haifu mabiya kuwa dakyar yasa mu yayi fishing din sa

Ya karasa inda take
yace "wankan ya isa haka kodan kin wahalu fa ba keba ai koni sai nayi wankan sati ina ga wannan matsa da akamin Duk jikina ciwo yakeyi a tare suka fito

yasa mu Hadim tacika fam
Sai faman jijiga jaririiya take
abakin gado fandau da zauna shikuma yayi hanyan kitchen
Tace ina kuma zaka sake Komawa

Bai kalle taba yace" zan hada mata tea me kaurine
Aiko Hadim tasake cika cikin fusata tace wai me kake nufine

Ko juyowa bai yiba ya wuce kitchen
Bayan yaka wowa Fandau tea din yabata karba tayi ta fara sha

Yaka rasa wajen Hadim da bakomai cikin idon ta sai tsabar bala i
Yasan idan bai yin lallami ba sauki dafa ta yayi yace maman baby girl ya akayi ne muga yartaki kinwani kan kame ta dan rowa

Bata rai Hadim tayi
Tace"Nabil kasan me kayi kuwa
Cikin salon sa na yaudara yace "menayi?
Tace"baka ma san me kayi ba a gabana fa kake tattalin wata macce
Yace ba tattalin ta nayi ba kinsan ance dan tuwon gobe ake wanne tukunya

Duk magan ganun su cikin kunne Fandau dan bawani nesa suke ba

hima kansa yana fadan haka yaji wani iri azuciyar sa yace Allah yasa bata ji ba amma yana juyawa ya ga idon ta da hankalin ta duk akan su da gani yanayin kallon da
Take musu taji komai

Hadim tace "aisai kai karbi yar karike yasa hannun yakarbi yar ita kuma Hadim jagaf jagaf da jine ajiki ta fara ta fiya wanda baisa nima zaice haifuwan gaske yi
Dariya yakama Nabil daya tuno lokacin da hadim ta zage ta na ta shafa kazan tan haiwuwa ajikin ta
Ga zanin Fandau
Daga nan suka fito
Hadim tana takawa Ahankali sai wani cicci je baki take
Aiko kamar yanda suka zata a man falon ko suka samu
Yasmin tana kallo
Ai tana hango su dagudu tayi inda suke aunty karde haifuwa kikayi ne ina tan take tayi kan ai tama manta dawani tsoron Nabil da suke yi wanda ko waje yaje tofa basa zama awajen dan shi ko kamal wanda yabiyo bayan sa soron sa yake
Kai har yayinsa mata su zainab wada suke uba daya suna tsoron sa dan Iya uwar gida maman su zainab cewa take kar karaga musu ai kaine babba tunda kaine namiji amma sai ga yasmin taca muko ya baby ha hannun sa tana tace "memuka samu mugani meka mata yayi
Yajuyo yana yiwa hadim sannu harda riketa kamar wanda ita tayi nakudan

Yasmin tace lahhhhh anty kin haifi me kama da Kala wllh suna kama da kala
Hadim sake kallon jaririya ta tana murmushi dan mata so yariyar tayi baki ma amma taji dadi da aka dan ganta tada Kala Kala kanwar Nabil ce uba daya ita ma yar gakin iYa ce
Wow amma fa hancin ta irin na yashid dakum.. ...

Hararan ta Nabil yayi tayi gum da bakin ta

Tabi bayan su suka haye sama
Toilet hadim ta wuce ta tayi saurin yin jifa da zanin duk jikin ta karni yake wani irin amai ne taji yana taso mata wanka tayi yafi so 5 turare kam bawan da ba ta fesa ba tafito daure da towel bata ga Nabil ba dan tasan yaje daya dakin wanka ne yanda jikin sa ya baci
Yasmin ce da waya ahannu sai kolotun ihu ta ke takira wannan idan tafa da ko amsa bata sayawa ji zata kashe takira wani
Hadim ce tazo ta zauna abakin gadon yasimin tace"aunty kin ganki uwa ras kaman bake kika haifu ba
Amma ANTY tare kuka haifu da yashid ko yanda naga duk jikin sa jine har yafiki baci

Gaban hadim ne yafadi ras tace ban gane kamar bani na haifuba
Yasmin tace "wllh anty fuskan ki tayau kamar baki sha wahalan nakuda ba sai tafiyan ki da ya canza kawai anty

Hadim tace"yasmin kinada yawan shirme a maganan ki mekomin wayata naki ra Habiba da su faridan Amjad
Suzo suga baby dan yanzu zamu wuce
Kita shi ki hada mana kayan mu

Yasmin tace "yawwa anty ina siyayyan kayan baby da mukayi kinga kamar nida yashid munsan macce zaki haifa muka dinga iban kayan baby girl keko kikayi ta jidan na baby boy
Wai ina suke ma wllh akwai wani mekyu dama na nace idan macce ce shi za afara sa mata
Hadim tace "inaga fa anwuce da shi 9ja dan kayan da muka bari anan ba yawa duk mun aika anty yanzu wazai mata wanka Hadim tace "bana jin za ayima ta wanka anan sai munje gida dan awai wasu abubuwan da ake yiwa diya macce a wankan fari a al adan muna shuwa
Yasmin tace "shuwa iyayen....
Keee bani man zaitun da auduga na goge mata jiki dashi tana maganan tana kiran wayan Habiba babbar amini yar ta
Aiko habiba cikin ihu itama da murna ta kaye waya kawayenta zallah nanan London take kira dan su zo suka baby kafin suta fi tana ganin kitan yangida amma bata dau ka
Tafijin kawayen baye idan ta tuna kyutan da kungiya su tayi akan abin da a ka Haifa baki yaki rufuwa
Nabil kwance cikin
Bathtub yayi shiru nunani yakeyi wai dama haka nakuda da haihu yake da azaba Lalle annabi yayi gaskiya da yace abi uwa uwa uwa ummattii
Akwai wani hassari da akayin agaban sa ankayi ta mutuwa da raunuka manya harda wanda kafansa ya fille yabar gan gan jikin sa amma mai ga yashiga halin da Fandau tashiga ba
Anya yayiwa uwar Fandau a dalci da yara bata da yarta gashi ita ma Fandau din zai rabata da yar ta
Yar fa nima tawa yar ta girma a mata haka
Tsaki yayi afili yace aine y'ata tafi karfin haka yata
Wllh ina ma wani zai ganta tana yawo a kafa balle ya yaudareta kofilin wasa zan shiga aisai na hada ta da body gard sannan baza tayi Rayuwar Nigeria ba
Da wannan karfin guiwan yafara gasa jikin sa da yake masa ciwo baye kafadun sa inda nan Fandau tafi matsewa

Sun samu rakiyan dinben mutane wada yafi na da zuwa airport doctor Muktar ko kin zuwa yayi dan yaji mugun haushi da wai Hadim haifuwan gida tayi kuma bayan hakama yayi yayi subari aduba lafiyan ta amma sunki shiya fijiye mata ma karuwa dan yar da girman ta
Haka agidan ma Hadim kin yarda tayi kowa ya bata wanka sai fada suke da mamar ta sai tace ita zata iya ai ita ba yarinyar bace ummin Nabil ma tasa baki tace Hadim kibari a koya miki abubuwan kinga haifuwan farine
Ai ita kanta ummi ce mata tayi ita fa bame kanin siraicin ta dan bakyu wani yaga siraicin wani

_Niko nace keko kika gama ganin na Fandau_ _a he kinsan da haka_

Haka suka rabu da ita ga hade haden na shuwa ba kadan ba amma haka suka bata ta shiga dashi idan na tsugun none zata zuba tana gani zai gama hayakin sa yagama idan na wanka ne ko wanke wajen tayi floshing dinsu
da wayan ta ma take shiga tayi zaman ta tana chatting dinta da kawayen ta akan baby

Nabil ya sake sunkurar da kai a gaban Maman Fandau yace"yauwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login