Showing 123001 words to 126000 words out of 144533 words

Chapter 42 - Dama Ta Book 1 Hausa Novel Complete

son Gaskiya nake miki bawai sha awa da kike zargina akai ba to na goya miki baya ki auri wanda kikeso dan bazan bari ki cutu .
Fandau tace
"ashe son nawa baiyi nisa ba tunda gashi zaka iya hakura dani.

"baki ji ance hakuri yaza ma dole ba ai hakuri yana magani komai Fandau kin min komai arayuwa, ko yaran nan nasa agaba ina gani nasan jinin kine ajikin ki suka fito zai iya ragemin zafin dan haka dole kema nabaki abinda kike so ai awai wata yarinyar da ta dade tana bin bayana yar kono ce zan iya auranta na had'a ta da Hadim inaga su. Ishe ni rayuwa.

Shiru Fandau tayi kwai kode da gaske yake inko haka ne yazanyi

Afili kuma tace "ni kuma meye matsayi na awajen ka.?

"ai ke ta musamman ce matsayin ki awajena yazuce duk ida kike tunani ko cewa kikayi na hakura da Hindu ta kano zan hakura.

Tace "ni bawan nan ba matsayin aurena.?

Nun farawa yayi yana jinjinawa iya takun sa na bugan cikinta yace "bayan sakin da namiki bisa umarni na maida ki agaban Malam shi ya sani najen na nemi yardan ki danaje na tadda kina waya da wancen dan iskan to kinga har yanzu kina matsayin matata saide idan kince na sallame ki zan iya bin umarnin ki dan ni ba abin da nakeso irin nabi zabin ki nasa ki cikin farin ciki kamar yanda kika sani alokacin da muke tare wanda nasan yanzu ma koda bama tare idan naga yaran ki zaki ciga ba dasani.

"waida gaske auren zakayi auren huce haushi kenan.?

Yace "Eh hakane dan Gaskiya da na taba mata 2 nagani bazan iya zama da daya ba."
Ajiyan zuciya ta sauke ta sa Akkam a nono amma sai saiga Nabil yazu bawa wajen ido har Akkam ya tsaki nono tana dubawa yayi bacci zata kwantar dashi saiko ya dauke shi ya meke tare da jan hannun sauran yaran har yajuya tace "da gaske tafiya min da shi zakayi.
"Eh wannan damar kine har yanzu kina da sauran dama ta zama da yaran ki kiyi nazari kafin gobe damar ta kucce miki dan rabuwa da yara ba kara min asara bane kiyin nazari yana gama fadan haka yaza hannun yaran sa suka fita a parlour ko yatarar da su Dr suna kallon ya zuce su ko Habiba da take cewa agaida gida bai kalla ba

Fandau ta sha kuka
Amma tana gayawa Dr da Habiba suka ce plan ne ta zuba basa ido fada suka mata sosai akan ita tabari yagane tana sonsa dan yariga yagano tane kawai
!
Fandau kasa bacci tayi dan kuka ta shayi

*WASHE GARI*

Habiba bata je ko ina baBagana tazo gidan kamar yanda shateema ya mata alkawari suna cikin fira Fandau tace " yawwa ni Bagana jiya ina son na tambayeki bayan tafiyar su YaMainuna sai Shateema yaza kuka tafi abin yabani mamaki wai Yabintu da YaZahra Yakaka naga har da motan su duk dama nasan maza zajen su masu kudine amma harda mota haka.
Dariya bagana tayi tace "yo ai na gasa yazame musu yanzu Yazaina tace itama sai ta tsiya yanzu haka rabin kudin ta yana wayen Shateema ita ma Aisha ta hurawa mijinta wuta ina ga ma yatsiya mata bata koya bane yasa batazo da shiba,

Kawai dan sungan ni da mota kowa gasa yatashi....

Katse ta Fandau tayi da cewa kema kinada mota.?

Bagana tace "ai nina fara yi sun zata Shateema ne ya tsiyamin.

"waya tsiya miki?

Bagana "tace wata rana Shateema ya kaini gida da yamma yace aiki yamasa yawa na hau napep na koma nace to shine dana gashi wayan tacewa Mama zanje na hau napep shine Shiddams yana wajen ya dinga tsoka nana da wai kamar ni big girl acikin napep shine yasa aka kaini gida washe gari kawai sai ga motoci kuda 2 masu tsada wai nawane daga Shiddams shine fa kowacce ta tashi amma ai masu isa su hau irin nawa ba wai dan ma boye dayan nayi gudun magana.

Fandau tace" Haba sai kibani dayan yar uwa.

Habiba dariya tayi tace" yanzu ke har kina matar Shiddams ai kinfi karfin mota daya sonawa nake cemiki za kisha mamaki duk sanda kika zama cikekiyar macce agidan Shiddams kyutan gidan da mota da kujeran makka wllh ba wani abu bane jin Shid kike baki san waye shi ma wllh shugaban kasa saide ya nuna masa mulki baki ga yanda Hadim ta ke bajinta a kawayen ta da yan uwan ta mota kuwa ita take canja wa kannen ta duk wanda ya fito sabo su suke fara hawa acikin meduguri.

"Bagana tace "rabu da ita Aunty B kuma tana son daman ta ya kufce mata ko dan jiyan nan saida yarura min pic din yarinyar da tamutu akansa amma yaki amsa mata amma yanzu yace zaije ayi maganan auran ta zaiyi wai sunata Hindu yar kano ce.... Fandau ta katse ta "na shiga ukku kinji Aunty da ma nace muka kamar da gaske fa yake kuka ce min plan ne kinji ko har yana fada.

Bagana tace" da gaske ne mana ga pic dinta tanuna musu wata gayiran budurwa

Ita ma Habiba shiru tayi tana son gaskan tawa tace " inaga fa da gaskene.
Bagana tace "da gaskene.

Fandau tace "yanzu yazan yi kar fa yayi auren yace baya sona shiyasa yace daganan zuwa gobe ne *dama ta* idan nayi wasa ya kufcemin shikenan shikenan aunty wata kilama yatafi kanon.

"Bazai tafi ba kibari Abban Nol yazo zai samo miki mafita kinji.

Shiru Fandau tayi gaban ta yana faduwa

Ganin tabar zancen yasa Habiba tace Allah Bagana ayi magana Gaskiya wanan *Issetan* taki nayiwa *Haris* kamu kinsan da FUJJI muka ce sai naga yanzu FUJJI tanawani mahaukacin girma kiga har taso wuce ummuna a tsawo tafi karfin mu...
Fandau mekewa tayi ta shige d'aki tana shiga ta fara safada marwa yanzu yazanyi idan narasa mijina wazan so kamar sa da saurin ta wawuri wayar take ta danna dialing no nashi

Alokacin Nabil suna kan hanyan gidan Dr din zai kai Akkam yasha kona ce zai barshi dan Fandau ta hada shi ta Mama Mama tanuna masa b'acin rai sosai yabata hakuri yace zai mai dashi
Yau ma kamar jiya shiga irin daya sukayi saide yau farin rigane bakin wado fulan ba b'aki ne sai tambarin Chelsea club din su ajikin fulan da rigan har agogo medauke da tambar ne a hannun su har Akkaam suna baya FUJJI tanata zuba masa surutu su ma su Maaf runa gwarancin su yana biye musu ahaka yaji wayan sana family yayi ringing dole ya dauka duk da basuna amma sallaman da yadoki kunne sane yasa yayi saurin mekewa da ga dan kishingid'an da yayi muryar sa yana kwaruwa yace "eh a am Mata ya akayi nasan Akkam kike mema ko?
"a a har da kai dan Allah kana ina?

"da gaske mata harda ni kike son gani?

"Eh amma idan kazo ka kirani a waje bana son Aunty tasan kazo zan fito.

"to ai gamu ma ina hango gidan kifito.

Tace" ok.
Mayafin ta tazara ta cilla ta wundo dayake su Aunty B suna parlour ciki tafita kamar me zuwa babban parlour amma sai tafi ta kofar baya ta dauki mayafin ta tafita tana fita ko ta hango motacin nasu tsayawa tayi dan bata san wada yake ciki ga gashi duk b'akin glass ne motan tsakiyan taga yatsaya daidai gunta kofan yabude yace "kishigo ciki ko ba musu ta shiga kofan yakoma
Shiru ne yabiyo baya
Can yace "to yanzu afara bawa Daudana abin cinsa dan nasan ma shine dalilin ne man nawa ko.?

Tace" wai dama da gaske kake auren zakayi?

"ba kyason nayi ne ai dama saida na nemi sha awaran ki kuma na baki damar ki idan kince ba kyason bazan yiba amma bazan iya zama da Hadim kadai ba sai kisa momin mafita.?

Cikin masifa tace "To wai ne cemaka nayi bazan koma ba ko duk kora da hali kake son yimin.

yace "da gaske kike zaki koma dani wllh inde zaki koma har abadan bani ba kara aure ke da Hadim kun isheni ita ma tayi nadaman abinda tayi baki ga yanda take kuka ba jiya muka shiya har ta koma gidan ta nabar ta dan Allah Fatina da gaske ne.

"da gaskene Nabil bani da wani zabi sai kai duk da baka cancan ci nasoka amma ba yanda zanyi umarni zuciya tane kai......
Bai san sanda ya rungumota ba yana mata godiya har da kwallan sa.
Yace "nami ki alkawarin zama dake amana duk wannan zargin da kike min na nayaudare ki ko ban miki adanciba ba ki bani dama nan da 1week bazaki fada ba, acikin sati 1 tal zaki gane irin matsayin ki awajena,
kuma kicire wani Hindu aranki ni ba wata hindu dana taba sani na sauke pic din tane kawai a media kinriga kinrufe zuciya ta da tarin sonki.
ya dago yabawa driver umarni da yajuya kan motan zuwa gargar
tace "amma ya tsaya na sauka dan Aunty bata sani ba nafito kuma itan Yaya yasani wllh zai min fada....
"Waye kuma yaya?

"Abban Nol.
"ai dama na gama gane plan dinsu shiyasa wancan dan iskan na neme shi narasa akarin nan amma zan dawo kansu sun cutar damu.

"mesu kayi na cuta mu kuma dan sun temakeni.

"Ni awajena ba temako bane raba ma aurata tsawon watanni 10 fa har jinya nayi badan demako Malam ba da yanzu sun miki asaran san talelen miji, har kina cewa sun temake ki
ai wllh sai sun gane basu da wayo baga shi na shawo kan abina ba ai sun san ni me sa ane.

Dariya tayi tace "kaji yaban kai wai san talele,
Nide sauke ni.

"ai ba inda zan sauke ki sai gaman Sayinna dan shine yace naje na nemi yar danki kuma na samu ayau agidan ki zaki kwana.
"dan Allah kar kasa naji kunya awajen mutanen da sukamin karam ci kaga yanda Dr yabar aikin sa da karatun yaran su yazo suka zauna dani.

"kar kiji komai matar Shiddams kike yarinya sai kinga dama ma zasu ganki balle kiji kunyar su,
ai zuwa da sukayi na muna firci ne ba.

Daganan ya kawar da zancen ta cewa bari nakira Hanif yaje yashare mana gidan muna Shagari yaciro wayan yana bada umarni a share gidan.

Itade Fandau shiru tayi dan tasan abin kunyar tariga ta sake afkashi

Ya katse mata tunani da cewa yanzu wadanan yaran duk ka yaran kine kina yar misisiyar nan wllh abin yana bani mamaki wai yawan nan duka naki ne duk girman gadona fa jiya muda su da my one wllh amatse muka kwana agadon mu 6.
Wani kululu kishi ne yatsaya mata ta hade rai ta juya kanta
"sai asanan yagane ahe zata iya kishin Hadim dinma yafara basar wa yana wani janta dawasa har suka karasa gargar dakyar Fandau ta fito tana jan mayafin ta tana rufe fuskan ta dayake da safene Nabil yana tambayan almajiran ina Malam suka ce yakoma ciki Fandau zata shige cikin gidan bangaran su yayi saurin kama hannun ta da ALLAH yatemaka ba kowa awajen
Yace "sai mun fara shiga wajen Malam tukun.
tace "ai nasan yanzu Baa yana bacci tunda antashi akaratu sai anjima.
Ina bai saya bata amsa ba kuma bai saki hanun nata ba yaran suna binsu abaya suka shiga har parlour Malam zaunar da ita yayi ya yace mari kiga ai taso sa zanyi ta dauka wasane dan idan Malam yana baccin hantsi ko matan sa basa tayinsa ai sai gashi ya haye sama ba ta gaskan tashi ba saida taji yana knorking din kofa ba ajima ba ko sai gashi sun sauko tare dariya malam ayi yace lalle da shirin ka kazo.
Fandau ta sauko akan kujeran tazube k'asa jikinta na rawa kanta a k'asa dan ita duk duniya ba wada yake mata gwar jini irin Baban ta tana mugun tsoron shi dan koda bata zuwa koda ai gaishe shi sai taga yana wajen zatayi sanda ta shiga satan apple dan abincin tane shima Malam yana son apple dan haka awai ranan asirin ta yatonu aka ganta aka gaya masa yakirata yace kullum tana zuwa tana dauka idan tana so amma ita da sunan gaida Baban sai tayi wata ma bata ganshi ba
Bayan sun gaisa malam yace ta tashi tashiga ciki anjima za akira taro.

Yauma taron aka kira na gaggawa dan yau harda baban Hadim dayayin ta da mamar ta da iyayen Nabil kamar na wancen karon da BilAL da Dr da farko dan gidan Malam ne yabude taro da addua a malam yace "Jaji kaine mahaifin Halima matar Muhammad ko?
Baban Hadim yasun kuyar da kai yace "Sanyina nine wllh da baka kira ba ma yau mukace zamuzo mubada Hakuri akan abinda yafaru wllh ban san komai ba sai jiya.
Malam yace "Masha Allah tunda kaji abinda yafaru wanda ba Halima kad'a ba duk kansu masu nefine shiyasa zamu taru mu gyara abin tunda duk na gidane

Yanzu ta kanka zan fara Habubakar kasan tun alokacin da kace Fatima bata da idda nace maka tana da shi kace kasani kayine dan yayi hankali to tun adaren nasa shi yamai da auren anzu haka matar sace saide sakin da yamata yasa igiyar auren yazama saura 2 dan tun alokacin dan ka bukaci nabaka daman kane amma banso kayi wasa da saki ba Malam ya musu nasiya sosai.
Baban Nabil yace "hakane duk abinda mukayi na cewa auran Fatima da BilAL shirine dama Nabil ya dago kai ya zaggawa BilAL da Dr harara BilAL yayi murmushi

Malam yace "Halima matso kusa Hadim ta matso dama Nabil da Fandau suna kusa dashi Malam yace "yawwa Halima kamar yanda Fatima take y'ata haka kema kike ina son kuyin zama na amana atsakanin ku zaki karbi amana ko?
Hadim jitayi mutumin yamata mugun kwarjini wanda ta sha gaisawa da shugaban nin kasa she daban daban bata tabajin wani ya mata wanan kwar jinin ba gaban ta yana baduwa ta gyada kai alaman eh
"malam yace "bude baki zakiyin kimin magana zaku zauna lafiya.

Hadim bakin ta yana rawa tace "eh insha Allah.

Malam yace "to Alhamdulilah
Fatima ga yayaki Halima karnaji wani matsala yata so tawajen ki kiyi koyi da hali irin na Aisa kinu namin ke jinanin tane zakiyi.?
cikin in ina Fandau tace "Eh Baa
"to Masha Allah,
Muhammad ga matan ka kazama adali a tsakanin su.

Dan zumudi yace "insha Allah nagode Malam.
Malam yace "Yawwa sai batun yara Halima na miki jajen abin da yafaru dake na rashi mahaifa to hakan baya nufin bakida yara kina dasu ko a musulumce yaran nan kina da hakki na sharan da su tunda suna da gadon ki kema kina da nasu koda ace yanzu zai yuwu ace zaki haifu dawani wanda ba baban su ba to ba aure tsakanin su,
a yanzu ace kanin ki da kuka sha nono daya yace yana son Hajara to ba aure tsakanin su nono ya hada shi kuma da ma atsakanin d'a da uwa nono aka ambata yaran yanzu zasu gajeki zaki gajesu,
ita ma haka tana da hakki tana mahaifiya agare su wanda ita tafiki hakki a kan su,
dan haka inason na raba muku yaran dake da yar uwar ki amma kezaki fara zama dan haka kizabi 2 wanda kika bari sune na yar uwar ki
Hadim gaban tane yake faduwa yanzu shikenan Fandau taza ma matar Nabil yanzu shikenan yaran nan kowa yasan na Fandau ne to ma kita wane irin zama zatayi da kishiya kawai sai ta fashe da kuka

Sukuma mutanen wajen tunanin su karam cinda Malam yayi ne yasa ta kuka saida tayi kukanta me isarta

Cikin tashewa murya tace ina neman almarma a hadamin da Fujjirat sai abani ko BilAL ko Maaruf.

Malam yace "amma naso ace yan biyun kika zaba sabo da bai kamata araba suba amma yanzu ma ki hada kirike su duka na baki,
Ita yar uwar ki tarike Daudan ta tunda ALLAH zai bata wani tunda tana da lafiya Allah yabata masu albarka kema Allah ya raya miki yabaki ikon tar biyar tar dasu sai kuma ab.......
Fandau wani irin kuka tasa wanda ta katse Malam

Cikin kukan ta fara magana Baa dan Allah ga Akkam din ahada mata dashi dan Allah abani Fujjirat wlllh ita nake so dan Allah Aunty kiji tausayina kar kiraba ni da FUJJI wllh duk burina akanta yake.

Dak wajen kowa yayi shiru
Sai Nabil yace "Malam dan Allah aduba lamarin nan wllh ba ayiwa Fatima adalci ba ita Hadim ta dauki yan biyun ta barwa Fatima Fujjirat da Akkaram din.

Shiru Malam yayi Can yace "to Halima zaki iya barin Fujjirat din ne kinji abinda yar uwar ki tace ta baki harda Dauda.

Hadim da gaba daya haushin Nabil da Fandau ya kamata a gaban din bin mutane Nabil zai nuna yafi son ra ayin Fandau kwafa tayi aranta
Afili kuma tace "Baa nima wllh FUJJI nake so koda zan bar mata dukka yaran ne.
Wani irin kuka Fandau tasake fashiwa dashi dan tasan anga ma bawa Hadim zabinta.

Nabil yace "da zakice zaki bar mata da nakine ai nata ne dan haka wanda ta keso shi za abata.....

Itama Hadim kukan tasa cikin kukan tafara magana" yanzu ni za kayiwa gorin akan yaran toni bana soma dan dun daga yanzu an faramin gori.......
Shiru tayi da dililin wani wutan mari da yaziyar ci fuskanta.......

*to masoya waya mari Hadim Hadim zatayi Fandau almarman da tanema ta bar mata*
*B JATTKO*
[3/12, 8:50 AM] Hauwa: *DAMA TA*


*NA*


*BATUL ADAM JATTKO*

WATA DAGACIKIN MASOYA TAMIN ABIN *AL SHERI* NA GODE ALLAH YASAKA DA ALKAIRI YABAR KAUNA


Wanan shafin nakine *UMMU MARMYA*


🌈Kainuwa writers Asso🤝🏻

*47*

Baban Hadim yasake d'aga hannu zai zaf ga mata wani marin Malam ya dakatar dashi da cewa "Jaji agabana ake nuna min Halima yar kace.
Baban Hadim sunkuyar da kai yayi kamar mene man gafara yace "Sayinna Allah ya fuci zuciyar ka tuba nake.

Malam ya tumfasa yace" Muhammad Nabil kace ban yiwa matar ka adalci ba ko?
Shiru Nabil yayi dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login