Showing 78001 words to 81000 words out of 144533 words
kuka meya sameshi Inna tadan zamoshi tasake kallon fukansa
tace" Modu lfy usman ne yayi saurin cewa Inna lfy lau sai alkairi akwai albishir sai Munje gida tukun
Haka suka karasa gidan
Inna direct inda su Hadim suke akayin da ita tana shiga habiba tameka mata jariri Inna tace"meye dan waye
habiba tace"inna kibude kigani mana Inna tabude tace"aiwanan Modu ne jaririn sa karde kucemin Halima ta haifu dasauri zahra ta meka mata dayan ma idon Inna kamar yafado take kallon yara takasa cewa komai kawai sai Halima Halima take kira Hadim ta sunkurar da kai wai ita irin kunyan nan
Inna ta Kalli Nabil tace" modu dole kayi kuka sai itama kawai ta fashe da kukan ta zauna kujera tahada yaran tana daga hannun tana godewa Allah tace" kubani abukar a waya nagaya masa."
Dariya sukayi sukace ai kowa yaji dama kune dakuke hanya bakuji ba sai dare sosai kowa yawatse ina tana shiga toilet tace karo da kayan jini a baho tace"aikin banza duk wanan taron kawayen naki ko kayan jinin ba asamu mai wankewa ba yau naji rashin hankalin irinna afuno yo ko hannu zaka sa awanke ai kawanke balle dagawa ka jefawa injin yawanke haka tazuba kayan a engine tas tagama tukun ta fito tana fadan da Hadim tace" basu shiga nan din bane basu gani ba nikuma dazun idan natashi sai indin gajin jiri shine nabari namanta."
Inna tace"dama yaushe zaki iya shiyasa fa dawatan haifuwan yakama nace bazan zauna ba zanzo kuke cewa wani karna zo
Shiko Nabil daga rakiyan abokai dakin Fandau yafada amma Baccci take yasameta dakani nagaji yane dakuma ramukon Baccci dan shi bcc inkaci bashin sa sai kabiya tsayawa yayin yazuba mata ido kunburin na fuskan ta yananan ajiyan zuciya ya sauke afili yace"yar albarka kenan yafito
Yayi saman karshi inda su Kamal suke suma suna shirin kwanciya yasamesu dan haka suna kara gaisawa yafita
Daya dakin na gefen su har ya kwanta kuma ya tashin ya canja security yayi part din Fandau har yanzu Baccci take dan haka yakwata agefenta yarungumo ta
Da asuba yatashi yayi alwala yafita masallacin gefen gidan sa wanda su basufi 4 suke sallahn asuba saboda karancin musulmai a wajen hakan ma 2 sai sunyin tafiya sosai amma idan na ranane akwai wanda suke zuwa awani anguwan suyin jam i yau de yasan su Kamal sunzu
Tare ko suka fita
Da daren yayi Hadim saida tarena kanta dan Fujjirat kuka saita sha nono idan aka bada madara bata so gaba ruwan nonon twins sunzuge idan Inna tace''hakan ma bata hadim harda kukan ta dan wani irin ja fujjirat take wai zata zuko ruwa ana cikin haka sai dayan yatashi shima kukan neman abincin yake ga doc Muktar agaban Inna yace kada a kuskura abawa jaririn nan madara kowane irine idan ba nono ba har zuwa wata 6 sannan adaura su kan madaran da yadace tasan idan tace zata basu madara Inna bazata bari ba daya nonon Inna tafita tasa jaririn aiko da karfi yaja saida tasaki kara inna tace" ai dama yanzu sai kin daure dama tsosan namiji yafi zafi kekuma naga alama kinada tsoron tsosa Hadim cikin yarfa hannu tace"inna to ayaye fujjirat mana."
Inna tace" a a bayan zuba sai tacika shekara tukun kafin nan adage da koya mata cin abinci amma yanzu lokaci daya idan akacire ta zata sha wahala ana haka dayan ma yatashi shima da kuka Hadim tace"wayyyo nashiga ukku
Inna tace" karki damu nazo da garin kunun kanwa zan miki kisha yana gudano daruwan nono haka Hadim suka kwana ana kwantar da daya daya zai tashi bakin nonon ta yayi jajajir kamar ataba jini yafita sai faman gyangyadi take azaune ai koya nonon yazame abakin su zasu sawani uban kuka har asuba Inna ta tashi tayin sallah ita kuma Hadim Allah yasota awanan karon tana rashin sallah sai abin yazo mata adaidai har pants dinta tacire ta jefar a toilet dan Inna tasake gaskanta ta haka inna da ta shiga alwala tagani tadauka tawanke tana cewa Allah sarki ai wanan jaraban tsosan yaran ma zaisa ta taman ta garashin bacci
Hadim tana zaune ido yamata hulu hulu kowa yaganta sai yatausaya mata ba medauka ba ita ta haifu ba dan yanda tayin kaya kayan Nabil ma daya shigo saida yayi mugun tausaya mata daya tambayeta meyasame ta tafashe da kuka tace "kai bakaje kana Baccin kaba nina kasa yara sai kuka suke min sorry dama reno akwai wahala Allah zai baki lada
Fandau tana kulada jikinta yanda yakamata dan tanada wayo sosai ruwan zafi sosai take shiga kamar nawancen karan amma awancen nafari tafi jin zafi kodan wannan din bawani girmane dayaran ba
Washe garima haka Hadim tasha azaba har yafi najiya itan kaganta har tafara rama sosai
Aranan sukayin shirin tafiya dan yan gida sun matsu suga wanan twins dan wasu ma harcewa suke zasuzo shine Inna tace to atafi dama ita tace ta gaji saita huta
Nabil da zasu tafi yana ta kallon saman fandau amma bai shiga ba yasan idan yashiga zata masa kuka jiya de yabata waya yace "zaina kiranta dashi amma kafin yabata saidaya settings din wayan number sane kadaya zai shiga
A meduguri fadin murnan da family din nan sukayin bata lokacine misaltashi kowa yagani yace kamar kara katsaga da ubansu Iya ko kishiyar ummi haka tace har zafin irin na Nabil ne dan yanda suke wusulniya shima haka yayi yasha faduwa amannun mutane idan yabank'are shiyasa kakar sa tasamasa shitta
Kwana 3 Nabil yace zainafi Hadim tace "haba katsaya mana suna jibi ne yace "tafiyan nefa yakama dole sai naje" wane abune da bazai yuwu kayishi online ba kace dole sai kaje ko uzurin can din yafi kanunawa Duniya murnar kyutan da ALLAH yamaka."
Ai kyutan da ALLAH yamin basai nanunawa Duniya ba wanan tsakanina dashine dan bawani ne yasa yabani ba nema bani nasa yabani ba,
Ana miki maganan meeting ne gameda companyn mu kina wani zance
"Amma ai general manager yana nan basufiye neman kaba."
"Waine meyasa kikafiye son jan zancene bayan hakan bazai sana fasa ba."
" zuba masa idon Hadim tayi meyake damun Nabil ne yanzu badama tayi masa kyara ko shawara bazai dauka ba wanda da kome tace daidaine awajen sa nunfasawa tayi tace tom "amma da Sani zakutafi ko?
"yayi me?
"yatawo dawanan yarinyar munyin da doctor agadys ta samo alluran sai kusame ta kawai amata yazo da ita ."
"A a Sani nabashi aikin company nan yakusa kammaluwa amma naga anfara mun wasa da al amuran shine nacirin ahannun Sandan da Bunu nabawa Grema da Sani jiya naje har an sa suna sunan yayi fujjirat Muhammad akasa baro baro
"amma kai kace susa natan ko?
"Yees ninace."
Hadim batasan dalili ba kawai sai taji ba dadi ai kwara yabari asunan sa nada dayake sawa *shidmas*
Kasa hakuri tayin tace kawai sai kasa sunanta bayan da sunan ka kake amfa ni dashi kumama ga maza nan sai asa na macce bayan na gaba ma bakasan abinda zamu samu ba ni kacireni sawun mata masu haifuwa ne."
Saida yakare mata kallo yace "baki ji ance ko dukane karbi nafari ba ai duk wani da dazan samu bayan uwata yake dan hakama jiya nasiyi file zan gina mata company nata na kanta akudinta da kungiya ta bata dan jiya ankawo min korafin duk girman meduguri bamuda company man abinci atake na bada umarnin memo inda yadace yayi kuma muje dan har ansiyi filin yanzu za afara aikin( *Fujjirat groundnut oil* )
Ai Hadim ido ta zaro dole ta batar da Fandau karma watarana tane mi tada mata hankalidole tayin abinda yaran nan zasu zama permanent
Awajen ta
Tanacikin wannan tunanin sanda tajin fujjirat tana tamata kwaranci wai tana mata bye kafin tabude baki har Nabil yafita parlor gagida acike ba daman magana ga tanason taji towane shawara yayanke akan yariyar nan ita kam ayanzu tanaganin alluran mantau yayiwa Fandau kadan ga ita bata san bin malamai ba yazatayi tana jitana gani Nabil yayi sallama dasu ummi yafita,
Yara sunci sunan bilal da kuma Habubakar baban nabil dan haka suna kiran su bilal da maaruf suma ansha shagalin suna
*YAU FANDAU A KASAN SAUDIA*
Amma ita kira take ita bata gane ba saita ganta ak'aba
Nabil yace"a a sai kin samu tsarki dan kiji dadin ibadan ki muzauna a Riyadh kawai kafin kisamu tsarki
Ai ko ko awanan zaman Nabil yana rage zafi da Fandau ga yana kula da magugun ta yakar bomata awajen mama Kafin yabar garin
Ba inda yake fita kullum suna makale da juna koda zaije gaida sarkin Saudiya zuwan bazata yayi musu saboda yan jarida shikuma yanason zuwa da Fandau tare sukaje Fandau de jinta take kamar aduniyar mafarki bai san dalili ba idan abokan sa na larabawa suka zo aidashi faya shayin nuna fandau amasayin matar sa sukuma basa ganewa tunda tana cikin shijab d nikaf wani wani company yakaita na gyaran jikin ta mata sun yiwa Fandau aiki sosai fadin yanza Fandau takoma bata lokacine sosai sunfito mata da colour chocolate dinta sunada kwana 10 a Riyadh Fandau ta samu tsarki lokacin tanada kwana 18 da haifuwa ai ranan Nabil bai hakura ba dayake dama amatse yake saida yahana ta saket
Washe gari dasafe bayan sungama break yaja kujeran sa gaban ta yace"Fatima
Saida Fandau taji wani yar ajikinta" dama kasan sunana?
Murmushi yayi yace"bansan sunanki ba zanmiki passport din fitawani kasan."
Ai sunan ki narike shitun sanda kika furta minshi Fatima amma anakiran ki Fandau kokin manta ranan acikin shid hotel lokacin kina me allon ki
Dariya tayi tace "yanzu ma aini me allo ce wazai ki karatun allo yafi zama akwakwalwa."
Yace "Fatima shigowan ki rayuwata kin shigomin da abubuwa dayawa cikin na alkairi kinbani farin ciki maran misaltuwa arayuwa wanda bawani nunfashina dazai wuce batare da yawuce da tunanin kiba kowane irin bacin rai yasamemi ke nake sawa arai naji kin yayemin
saide wani babban matsala idan natuna rabuwa zamuyin dan koyau Hadim tasa kafar ta cikin London zaman ki yakare agidana wanda nikuma shine babban tashin hankalina."
Fandau tace" kana sona ne?
Zuba mata ido yayi yace "ai wani son baki bazai iya furtashi ba idanu da ganganjiki kawai kenunawa."
Tace" kenan baka sona ko?
Batarai yayi yace" karki kara tambaya na batun so
Yanzu abinda yake gaban muyafishi mushin manci
Kuka tasa tace ai dama nasani bazaka taba sonaba shine Sani yace" wai zakasoni
"audama munafircin da kuke kulawa kenan keda Sanin ko
Tace" shikenan za amin alluran ko?
Yace"bar wannan nifa mafita nake nema kin kasa nusuwa kigani nufina
Yanzu me mafita bazan iya rabuwa dake ba sannan bazan iya kai kaina gaban malam amatsayin wada ya dauke masa yar ba dama badan malam bane baban ki dasai nace zain iya yin hakan amma yanzu kinsan bazai yiwuba in keta idon mama innuna nine nayi mata wanan aikin ba
kinga kebazaki iya zuwa gida dasunan kin batane kika fito ba dasai nace" kije daga baya sai nakoma na aureki yara kuma kibarwa Hadim kawai allah yabaki wani
Fandau tanisa tace" hakan bazai yuwuba dan agidan ansan guguwa nayi har nabar musu wasika kaga banida bakin cewa ansaceni ko mama baza ta yarda ba."
Yace "Shine aina cemiki alluran shine mafita."
Tace "danme baza ka kai kanka wajen baban ba ba ALLAH mamuna masa lefiba kuma munemi yafiyar sa yakuma yafemana ni ina macce banji tsoron zuwa dakai amatsayin nayi aure bada sanin iyayena ba sai kai namiji da yakamata kakaramin karfin guiwa zaka ce bazakayi rai abace take maganan."
Shiko bayason bacin ranta dan haka jawota yayi ya rungume yace "za ayin abudaya yanzu kitashi ki shiya kar murasa jirin yanzu zamu shiga cikin makka jin haka tasakin ranta
Fandau da taganta adakin ALLAH tameka kukanta sosai wajen kwanan ta ukku can tatare Nabil yayi yayin taki binsa gidan sa wanda shine masaukin su idan sunzo sarkin Saudiya ne yabashi
Yau sunsha pic da Fandau acikin k'aba tayi mugun kyu Nabil ko dama mekyu ne sukan su larabawan sai kallon su suke dan sun burgesu sai daukan su hoto ake tako ina dan kowa yana soyaga yadauki picture din ficece Nabil
Suna kwance cikin bathtub rabin jikin su ajicin kunfa amma Nabil duka hankalin sa yana wajen kallon labarun da akeyi Fandau tafaki idon sa tadauki su pic ahakan ta tashi cikin dabara tafito
Azuciyar ta tana cewa wannan shine *DAMATA* nafara sa muguwar kuka
Da sauri ta bude whassapp dinshi dan whsp shiya fiye mata saukin taturawa Hadim pic dinsun wada sukayin ak'aba dawan da sukayi acikin wani kayataccen waje sunyi kissing din juna da nayanzu nacikin bathtub sai da ta tabbarar yashiga sanyan tayin delete dinsu ta ajiyen wayan ta zauna akan mirror ta fara makeup
Hadim da jaraban chatting tana kan online yashigo tasauri tayi murmushi tace my star ansamu wani abun cin dariya kenan wanan pic rututu haka tana shiga ko hotona suna budewa idonta yaci karo da wannan bakin ganin wada inda gayi mata akayin ko mutum zai hadiyi Qur ani bazata yar daba mijin yadauki wanan yariyar yajen saudia kuma yashiga cikin cikin bathtub daya shida ita kwance ai dawanan mugun ganin kwara mutuwanta wani irin razanenen kara tasa tare da jifa da wayan tana cewa Nabil Nabil tana nuna wayan ai da gudu yan matan tasuke parlor suka shigo lfy suka ce ganin tana nuna wayan yasa amma bata cikin haiyacin ta yasa sunzata nabil mutum yayi duk suka gigice Jidda koji take nunfa shin ta kamar zai dauke da saurin Ashuwa ta dauko wayan tana dubawa tagani tasauke ajiyan zuciya tamekawa sauran suka gani sai asannan ahankali su yakwanta dan tunanin mutuwa ne kawai zai cefa mutum cikin wananan hali amma sunyi mugun tausayawa hadim dan taciwo ace anturo maka hoto miji da karuwa sunbatu Hadim tafara tana jifa da duk abin da tasamu wllh kasheki zanyi idan na kasheki na kashe banza wato kun hadani da renon yaran ku kukuna cin dunya fujjirat tana haka ta fara kuka ta zowajen ta ai wani irin cille Hadim tayin ta ita wan ko shakka babu yarinyar ko bata suma ba zata samu karaya gadon ta hau ta dauki maaruf da yake bacci shima zatayin cinlin dashi da sauri suka kar bi yaron dama BilAL yana parlour
Da yasmin da fanta gana suka rike ta su Jidda suka fita da yaran da gudu amma ganin yanda take fusgewa ta na dukan su sunsan yasmin sun san bazasu iya rike taba da tafara dukan su kawai sai suka saketa suka fita da gudu kafin ta karasa suka rufe kofan suna jinta tana cewa kukawo yaran nan Wllh ta kansu zanfara afin uwar su da uban
*Tofa masoya kuyin hakurin yanda kuke *samun posting bayan da kuke soba Ahankali komai zai daidaita*
*B JATTKO*
[3/12, 8:49 AM] Hauwa: *DAMATA*
*NA*
*BATUL ADAM JATTKO*
*Wanan page nakine*
*AUNTY SIS*
*Allah yaraya mana*
*IBRAHIM KHALEEL*
*MRS OMAR*
*AUNTY MEJIDDA MUSA*
*MMN FARIDA*
*MIE MIE MIE MIE*
*Ina mugun tare daku tare kuma da soyayar ku kuda duk kan masoya mabiyan DAMATA*
*35*
dagowan da zatayi ido 4sukayin da Nabil da yajima yana kallon ta cike da zargi damashin kullum acikin dar dar yake idan Fandau da daukin wayan sa to yanzu mayana saneda yanda tafita da wayan cikin tsand'a shine yayi yabiyeto amma shi tunanin dama idan tadaukin wayan karta kira malam ko Mama yana fitowa yaga tana tura abu jikin ta harrawa yake karasowa wajen yayin
Yasa hannu ya dauki wayan yabude dama wayan a setting yake inde bashi bane yayi amfani dashi to sai yanuna masa abunda akayin da kuma fuskan wanda yayi amfani yana shiga yanuna masa komai ido yazaro cikin tsoro yake bin bayanan wayan tabbas Hadim ta turawa
Meyasa yariyar takasance hakane danme tafito cikin mata masu miyagun hali masu tona tsirrin aure
Dagowa yayi yakalle ta dum gaban ta yafadi dan bata daba ganin sa cikin wanin yanayin ba idon yayi ja kaman nisa sun janza kamar wani zaki take ganin kallon da yake binta dashi kadai idan kaduba kasan ransa amugun bace yake
Cikin mugun tsoro ta jada baya
Tace" abban Fuj lfy?
Kasayi mata magana yayi yana sauke wani nunfashi dan idan yace zai furta wani abu tabbas yasan zai fadi kalman da yasan daga baya bazai mar dadi ba idan ransa ya bace haka yake tunyana yaro dan ko agida ansani idan kuma yace duka zaiyi yasan bazai kyalita ba saiyaga tadena nunfashin akwai ranan da ogan sune ya bata masa rai daya dankeshi sai dakyar aka samu nunfashin sa yadawo daidai
Dan haka wajen whadrrop yayi yabufa ya bude yasa kayan sa yafice
Tana binsa da kallo yana fita ta sauke ajiyan zuciya tome aka masa nide nasan nagoge lefin danayi wata kila shida matar sane taga sako daga kafada tayi taci gaba da makeup dinta
Sunyin jugum jigum a parlorn ga Fujjirat da take ta kwala musu kuka tana ta shafa goshinta inda ya fashe yana fitar da jini
Suna cikin haka Allah yakawo hanef yace"ku kuma lfy kunsa yarinya gaba tana kuka haka ina uwar ta sai asanan yaga suma ahe hawaye suke yace "ba tambayar kuna keba dan uban ku".
Gana ce tamasa bayani yace"bani wayan nagani." yasmin tameka masa
Dayagani ransa yayi mugun bace
Yaza ace Nabil yayi haka atake ya kira Nabil
Lokacin Nabil yafito kenan ransa abace bai sanma ta ina zaifara ba yanaganin kiran Hanif ya daga
Haba Yashid meyasa zakamana haka acikin yara yanzu dawani ido zaka kallemu kai da yaka mata kamana fada....
"dakata yimin bayani meyafaru?
Hanif yamasa bayanin komai
Nabil ransane yasake bace Hadim zata kahemasa yara akan abinda bai kai yakawo ba ina duk sonda take musu
"yanzu kai aina kake?
"Ina gidan."
"ina nufin kana gaban yaran da abin yafaru akaban sune?
"Hanif yace"eh