Showing 69001 words to 72000 words out of 133935 words

Chapter 24 - Mijin Buzuwa Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

264

abin ka a hannu na zaka dawo kwanan nan.
Ya fice ta bishi da kallo tare da juyawa ta wuce zuwa dakin ta tana mai jin haushin shi.


Kutayani da addua yan uwa


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Yau take son ta gwada abubuwan da aikin boka dan Ondo wanda ya ja mata kunne da gujewa aikata kuskure tace zata tsare in sha Allahu.
Ya shigo bai jima da dawowa ba ya fada wanka Nafisa ta shigo dakon kai tsaye tasamu yana ban dakin gurin wanka nan ta zauna a bakin gadon cike da jiran mijin nata.
Ya fito daga ban dakin ta taso ta karbi duk wani abinda yake ma jikin shi tana mai gama daga goge jiki da shafan mai da saka turare da sauran su.
Shidai ido kawai ya saka ma ta yaga iya gudunta don zuwa yanzu ya fara gano shirin ta sam bai yarda da wanan abinda take mashi ba .
Ya gane sai tana son abu take mashi ladabin shegu a lokacin yake miji da zaran ta samu abinda take so shike nan ta koma ma halinta na I don't care da ta saba dashi.
Zama yayi a bakin gado yana jiran yaji ta inda zata bullo mashi ta dan yi dariya tare da karasowa wurin shi ta zauna itama.
Sai bayan ta zauna ne tace samad a ranshi yace nasan da wanan kan tace wai yaushe ne zamu tafi shopping ga ciki ya fara girma haka ?
Yayi mata kyar da ido sai kuma ya sake guntun murmushi a fuskan shi yace ban san da wanan maganan ba ai.
Ita ko tayine don tana ganin shi ne zai fi saka shi farin ciki har ta samu ta sake da ita ta aiwatar da nufinta gare shi sai kuma taji sabanin hakan a bakin shi.
Sai ta dan tsuke fuska tare da fadin gaskiya ya kamata ace ka shirya wa tafiyan mu zuwa yanzu don kada nazo nayi nauyi da yawa kace ba zan fita ba.
Abdulsamad ya tsura mata ido yana mamakin rigimar Nafisa yanzu bata aje kanta a kusa ba shi kayan bany ko a nan gida Nageria za a samau su ai.
Ya cikin daure fuska kin fi kowa sani komai nake so zan iya odan shi a dan kan kanin lokaci ya iso gare ni ballanta na babu dan da aka haifa a gidan nan da na fita waje na sayo mashi kaya.
Ranta ne taji ya baci don may zaya danganta sauran diyan shi da abinda ke cikin ta a yanzu da ta san tafi karfin kowa ma nashi.
Shikan gado ya hau yana gyara kwanciyan shi don yasan ba tayin abinci zai samu a gurinta ba duk dako yana son saka wani a bakin shi yanzu.
Nafisa kuma bataji dadin haka ba don tana gani idan ta kyale shi bazata samu yadda take son komai ya tafi ba har ya sadu da ita don ta riga ta shafa maganin da boka ya bata tayi amfani dashi.
Tabo shi tayi tana kwantawa a jikin shi da sauri ya juyo gareta yana fadin barni banda lokacin aiwatar da wani abu yau a tsakanin mu.
Tace aiko tunda ni ina da bukatan ka tare dani dole zaka daure ka biya min bukatana haka nan yasan ta da son ya kusance ta akai akai wanda a baya yakan biye mata.
Kara kwanto mashi tayi ya kara daga ta ajikin shi karo na biyu yace ki barni please na fada maki ina bukatan kasancewa ni kadai ne duk iya nacin ta dole ta barshi tafita kamar zatayi hauka take jin kanta a lokacin.
Ta jefeshi da harara ya karkace kai yana mamakin tace ba laifin ka bane tunda kai kana fita waje yanzu kana samun inda ke sauke nauyin ka acan.
Sheri zaki min yau kuma Nafisa tace amma kasan baka kyauta mi ba nima idan kai min haka yau don ina bukace dakai a yanzu yace ki hakkuri nace yau ba zaki samu ba ya gyara kwanciya yana fadin hakan.
A yadda ta rude sai ta bashi tausayi amma bai iya aiwatar da komai a yadda yake jin gabanshi yana faduwa mai.
Jin fitan ta a fusace bayan ta gama mashi mita ta fice daga dakin ya girgiza kanshi ya gyara kwanciyan shi sai barci acikin barcin ne yayi mafalkin mara dadi da Nafisa wanda ya tayar mashi da hankali.
Tunda ya falka bai koma barci ba tunanen mafalkin da yayi ne ya tsaya mashi a rai mikewa yayi ya dauro alwala ya gabatar da sallah tare da samun sauki alamura a gare shi kamar yadda mahaifan shi ke koyar dashi ko wani lokaci.
Washe gari ta tashi gaban ta yana fitar da wani irin kaikayi dake damun ta sam bata kawo cewa aikin boka da ta sakane ya jawo mata hakan ba.
Tunda ya watsa ruwa ya fito yana shiri zuciyar shi cike da tunanen abubuwan da suke faruwa dashi ya yanzu din.
Sai da ya biya dakin ta ya dubata kamar yadda yayi mafalkin a haka ya samay ta tana ta faman da soshe soshe don kaikayin dake damun ta.
Yace may ke damuwan ki haka ne kike wanan soshe soshen haka cikin bacin rai tace dama ai haka kake so dani tunda na bukace ka kashere ni.
Banga dalilin da zaka daukoni karabo ni da kasata ba kazo yanzu kana nuna min gazawanka a kaina inda take shiga banan take fita baya ya ciki da irin kalaman da take fada mai.
Hannu ya daga mata tare da fadin ya isheki haka na kada kine me ki fada min maganan banza an fada maki ni banda abinyi ne sai na kwanciya da mace kullun , ?
Kallon shi take da mamaki don bata dauka zai fada mata wanan magana haka ba yace kinje kinyi biye biyen ki kin dauko wa kanki cuta kiike son aza min.
Kuka ta saka mai tan
, aza mai kururuwa bai kulata ba ya fice daga gidan kai tsaye kukan ta ne ya jawo hankalin yan uwanta gare ta suka shigo dakin.
Har yaje office bai iya tsinana komai ba da yamma koda ya dawo ya samay ta a hargitse ya dawo har ya dade ta bishi dakin shi ta samu ya fito wanka yana daure da dan karamin tawul a jikin shi.
Tunda ta shigo mai daki ya dago ido ya kalleta ya kawar da kan shi gefe daya yaci gaba da abinda yake yi din tazo gaban shi tace.
Allah kuwa sai ka fada min abinda yasa ka tsiro yimin wullakanci haka ko dan kaga ina dauke da ciki ne a jikina yanzu yasa har kake guda na.
Ya jefeta da wani muggun harara har sai da taji tsoro ta dan ja bays kadan yace look Nafisa idan dan dai kina son mu zauna lafiya dake sai kin aje kanki a matsayin da na dauko ki a gidan nan na mata.
Macen kwarai itace wace ta san damuwar mijin ta da cin shi da shan shi da gyara mai makwacin sa da sauran su.
Amma duk ke baki san yin wanan ba sai dai kici arziki ki wadatar da yan uwan ki ba tare dani kin dubi nawa da komai daya shafe ni ba.
Don haka kodai ki gyara halin ki ko kuma in karo wata a gidan nan ku zauna tare wacce zata dinga kyautata min.
Ya na kaiwa nan yaja dogon tsukiy ya dauki key din motar shi ya fice dakin ya barta tsaye tana kurma ihun bakin ciki.
Wanan halin da Nafisa keyi wani lokaci kamar zautata sai daga baya kuma idan ta samu abinda take wa haukan ta dawo ta gyagije kamar ba ita ba.
Iyanzu ya fahince ta idan tana bukatan abu bai mata shi ba babu sauran zaman lafiya a gidan tsakanin ta dashi shiyasa da zaran ta bijiro da bukatatun ta yake saurin biya mata akan lokacin.
Wanda ita kuma take ganin aikin bokayen tane da mahaukacin son da yake mata yasa yake biya mata bukatanta a haukace kamar ba gobe.
Wanda tayi believing da baka da malamai ta ne aikin su yake ci a gareshi da kuma kyau da zati wanda take gani dashi take rudan shi ba zai taba samun mace kamar ta a cikin matan hausawan Nigeria ba sai dai kalan matan mu na nan.
Burin mazan Nigeria ne su malki mace mai kyau koda bata da hali na gari adai ce matar shi ta gwada wa tsara ne a gari.
Bata san Nigeria akwai wanan akwai kuma la,akari da ilimi tare da wayen mace da tarbiya ga mazan da suka san kan su.
Yau ma kamar jiya tashigo mai tana bukatan su kasance tare amma fir yaki amincewa ya biya mata bukatan ta kamar jiya haka ta wahala da wanan dan banzan kaikayin na gaba da tadamay ta.
Yanzu kan ya gama sakankancewa a ranshi mafalkin shi gaskiya ne inda ya ganta dauke da wani mugun abu tana goga ma gabanta.
Washe gari har ya shirya bata tashi ba daga barci tana ramuwar barcin da bata samu tayi ba a daren shiya tsaya ya tayar da ita cike da tsanar halin ta na rashin son yin ibada.
Idonta da sauran magagin barci bai gama watsakewa ba tace har ka shirya fita ke nan yace idan ma ban fita ba wani abin zaki min ne tunda ba abin kari zaki hada min ba.
Cikin bacin rai ga maganan shi tace ba muyi wanan alkawarin da kai ba na cewa nice zan dafa ma abincin da zakaci na dauko masu dafa ma kace basu iya ba don haka banda matsala ga wanan.
Yace yana daukan jakar Laptop din shi tare da sabawa a kafadan shi Nafisa zakiyi nadaman wanan maganan da kike fada min don ya zama dole idan baki canza ba in dauko wace zata bani kulawan da nake so a gidana.
Maganan shi Ya bata mamaki kwarai don bata zaton zai iya fadin wanan magana a gabanta ba kai tsaye sai gashi yau yana fada mata da bakin shi wai zai dauko mai kula dashi a gidan.
Wai ina kudin da take narkawa malaman ta yake shiga ne haka gashi ta dalilin bin bokaye da malamai dasa gaba yanzu ta daina kai kudin da suke kaiwa gida duk wata ana amfani dashi.
Ya bata mamaki kwarai ta samu ta danne zuciyar ta don ta san yanzu akwai sauyi a tare dashi ta dago ta kalleshi yana shirin fita daga dakin.
Fuskan shi a daure yake har lokacin gabata ne ya kara faduwa sosai dole sai ta hada da kissa da kisisinan mata yanzu.
Tace kayi hakkuri don naga yanzu magana kadan sai ka dauki zafi dani haka yace ai kece zan bawa hakkuri keda ban san na dauko ki kawai ne gidana don ki ji dadi ba.
Ta sada kai kasa tace ba laifina bane ka sani don ba girki zan iya yi yadda kake so ba bai sake yin magana ba yaci gaba da shirin shi bayan ya gama ne ya dago ya kalle ta yana fadin ki tashi ki sallah don lokaci ya gama kure maki ko.
Ya fice daga dakin bayan ya gama fadin haka bishin shi tayi da kallo har ya bacd ma ganin ta sai lokacin ta saukar da ajiyan zuciya.
Tace lalai da sake ya zama dole ta canza halin ta idan ba haka ba wankin hula zai iya kai ta dare wanan wani irin mutum ne da magani bai saurin kamashi.
Shin shi ba kamar sauran mazaje yake bane da take jin mata na hiran yadda suke samun kan maza je nasu suke juyasu ne ?
Yazama dole duk wani abu da zatayi taga ta samu ya sauko kamar yadda malam yace ta bi komai a sannu kada alamarin ya juye mata gashi ko taga abubuwa na shirin juyewa da ita.
Wai shin ko da gaskiya ne asiri baya kama mutum idan mace nada ciki ko ta haihu dole ne ta jirkinta har ta haihu ta bishi a yadda yake so ta nuna mashi ta kwanta yanzu.
Alaadan shine idan ya fita office zai mata kira uku ko sama da haka amma sai take ganin sabanin haka yanzu tun yana mata kira daya har yakai yau ya bai kirata ba ki daya.
Haka yasa ta fara zargin dama dalili yake nema da ita ai sunsha yin fiye da haka dashi amma bai sa ya daina kulata ba sai wanan kawai zai dauka da zafi haka.
Har tayi wanka ta fito falo wurin yan uwanta da ta samu suna shayen shayin su bata daina tunanen halin da take ciki da mijin ta ba.
Gaida ita suka farayi ciki harshen buzaci tana karba masu da kyat yanayin ta ya nuna ba ta cikin dadin rai.
Yar dattijuwa daga cikin su ne tace yau ba zaki fita bake nan ta amsa tare da yamutse fuska tana fadin ba inda zanje yau suko sunfi sin tana fita a gidan don sun fi sake jiki suyi yadda ransu ke so idan bata gidan.
Matar tace yanzu ya kamata ace kin fara natsuwa guri daya saboda cikin ki da ya fara girma don kina bukatan hutu.
Ta dan lumshe ido tare da jan tsoki ta dafe kan ta tace wani irin hutu Yanyala, ni da abubuwa suke son rikewa a gidan nan yanzu.
A lokaci daya suka zaro ido tare da mayar da hankalinsu gare ta suna sauraren ta tace ya zama dole dukkan ku ku gyara a gidan nan.
Yace mun bata mashi gida bamu gyara ba ai mai girkin da na dauko ku da sunan masu aiki a gidan saboda haka nake son kowa ta dan fara aikin ta.
Yanyala ta fidda idanuwa waje tana mamaki tace garin yaya har kika bari haka ya faru a tsakanin ku tace wallahi ke ma shedace ina iya kokarina don ganin haka bai faru ba amma hakan bai samu a gare ni.
Yanyala tace gaskiya ya kamata ki fara tura kaya gida tun yanzu ko za a watse dai kin riga da kin debi rabin ki ko ke.
Dama bazan Nigeria ai basu da tabbas ba kowane ke kamuwa yadda ake so ba don haka muke daukan su kamar wurin cin kasuwa a gare mu.
Don ko da kasuwa zata watse dan koli yakasa ya kwashe rabon shi nan dai sukai ta shawaran abinda zasu yi akan sauyin da ta ke gani ga mijin nata yanzu.

Idan da sabo na saba izuwa yanzu haka kawai zai zo ya dauke ni a mota sai dai mu zagaya gari ya dawo dani ya aje ya wuce makaranta.
Yau ma da yai kwana biyu bai zo inda nake ba komai na tafiya a guri na normal sai dai zan iya cewa haduwa na dasu ya bude min wani sabon babi na rayuwane.
Duk da nake yarinya kuma mace ban yarda na fara hurda dasu ba sai da na karanci rayuwan su nagane zama dasu ba yana nufin jefa ni a gurbataciyar rayuwa bane.
Yauma ina daki kwance ni kadai ina nazarin wani littafi don sabon da nayi da yawan karatu sai dai ance sabo turken wawa ne don har na dan fara shiga damuwan rashin ji daga gare shi kwana biyu.
Waya na da yai ringing na juya ina kallon mai kirana a lokacin ganin sunan shi a screen din wayan yasa na dan sake murmushi sai da naja mai aji na dauki wayan.
Da sallama na fara magana ya amsa min yace kina hostel ko kina cikin makaranta ne nace ina hostel yanzu fito ina waje yace ya kashe wayan shi.
Na shirya cikin wani dogon riga mai dan hannu shara shara riga yana dan matse kadan daga saman shi kasan shi a bude.
Kai tsaye daga inda yake zaune a motar yana sana,an shi na hango shi cikin motar ya mayar da hankalin shi sosai ga abinda yake yi.
Tun da ya dago kai ya hangoni tafe ya daina abinda yake yi ya tsura min idanuwan shi masu kashe min jiki da zuciya haka ya sake min su tankar wanda ya samu tv har na iso gare shi.
Daga waje na gaida shi kamar wanda baiji ni ba yayi sai bude min motar yayi da alaman in shiga kai na daga na kalle shi carab muka hada ido dashi.
Nan nace dashi karatu nake fa yallabai ka kirani yanzu yace shiga mu tafi na sani ai.
Tambayan shi nayi da ina zamu tafi tare da kashe shi da idanuwana dasu ke rikitashi idan ya kalla.
Sayar dake zanyi yace murmushi nayi nace ai dako kayi babban kamu yau galleliyar yarinya kamata ba karamin kudi zaka samu ba ko.
Nace yanzu ya kamata ace kana wurin aiki ka ko gida kana hutawa dan murmushi ya sauke tare da fadin.
Bazan iya zama gida ba ne yanzu.
To ka koma office yanzu mana tunda lokacin aiki bai kare ba don nima karatu nake yi yace don Allah ki shigo mu tafi kona fito na daukeki in sa a mota.
Nayi saurin nuna kaina nace ka dauke ni sai kace wata yar tsana ko matar ka can da zaka dauke ni.
Don Allah shigo mu tafi kin sa mutane suna kallon mu na dan juya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login