Showing 90001 words to 93000 words out of 133935 words

Chapter 31 - Mijin Buzuwa Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

266

kuda ya taso ma Nafisa gadan gadan da kyat ta iya saukowa falo hayaniyar su ne ya tayar da su mommy inda mijin duk ya rude saboda bai taba ganin mace tana labour haka ba sai wanan karon don anty fati haihuwan da tayi duk a gida take haihuwan ta bai nan.
Ganin ga haihuwa yazo mata gadan gadan bata ko iya daga kafa yasa mommu tazo da sauri gurin tana fadin ta duka anan shiko duk ya rude sai fafin yake mommy ku kamata mu kaita mota muje asibiti.
Tace bata iya tafiya Iyan bawa ne tace don Allah mazan su fice su barsu zasu kamata zuwa waje su Yanyala ko komai sun kasa iya sai yare suke sun rude .
Da taimakon Iyan bawa da mommy ta samu ta haifi yarta a gurin kukan yarinyar da ya karade falon ya dawo da hankali wa yanda ke waje suna jiran a fito da ita.
Sai da suka gama komai ne suka ce a shigo daga ciki mommy ta kamata zuwa sama dakin ta ta zaunar da ita a ciki tace tayi wanka sai suje asibiti a dubata.
Shine ya shigo dakin yana gaida ita da yima mommy sannu da fama iyan bawa kuma tayiwa yar wanka bayan an yake ci bi.
Ta fito wanka ya kara dawowa dubata tana zaune ta dubar yar ta da tasha kayan sanyi a jikin ta tana barci don ruwan zafin da iyan bawa ta gasa ta dashi .
Da murmushi dauke a fuskan shi yake fadin baki kwanta kin huta ba har anyi sallah fa tace yanzu dai zan kwanta.
Yace ki dan kwanta idan mommy ta dan huta gari yayi haske sai muje asibiti a duba ku tace ai ko bamuje da mommy ba ga Yanyala nan sai mu tafi da ita.
Mommy dai zamu da ita itada tasan kan komai yanyala mai ta sani yanzu ai kinga ranan dauko su danayi suzo su zauna damu ko ?
Tace ko basu zo ba ai haihuwa dai zanyi yau balle ni kadai na sha wahala na ai ba da wani ba yace yanzu zaki fadi haka amma da kike son taimako ai sunan ta kike kira ta taimaka maki.
Fuska ta daure da alaman bata son magana ya mike yana fadin yanzu dai sai ki huta kafin gari ya kara wayewa mu tafi ya fice daga dakin.
Ranta ne taji ya baci bata so su sa mata hannu ga alamarin ta ba sai gashi haihuwan ma a hannu su mommy tayi shi taja tsuki tana jin haushin yan uwan ta da suka kasa taimaka mata a wanan lokacin.
Taja dogon tsuki tana kwanciya tare da tsurawa yar baby ta idanu tana son gano inda tayi kama da uban ta sai dai don kankantan yarinyar bata gane komai ba a gare ta illa yawan kaman da yarinyar keyi da ita na zubin buzaye.
Shiko yana shiga ya fara kiran yan uwa da abokan arziki yana fada masu karuwan da ya samu .
A ban gare na Binta ce ta fara kirana tana sheda min zancen haihuwan wanda yayi masu daidai don a karshen sati ta haihu don haka zasu samu daman shigowa wurin suna.
Bayan mun gama waya da ita ne na shiga tunane a raina maryam na shigowa nake fada mata zancen haihuwan matar A,A din addua tayi ga yarinyar sai cewa tayi saura muje barka ko ?
Da sauri nace wa ai ni nan da kika ganin ba abu kadan zai kaini gidan nan ba sai ya kama dole balle idan bai kira ya fada min ba ko barka ba zan mai ba, .
Dariya ta dinga yi wai ko ina kishine zai sa ba zan tafi ba nace yanzu idan nace zan tafi gidan shi ke ba zaki min fada ba maryam.
In dai ya samu nayi masa a waya ya gode a watse taro lafiya dai indai wanan yar barikin mata nashi ne in ba a watse da tsiya ba da yan uwan shi.
Nan nake bata labarin da binta ta bani na hana ma su mommy dafa abinci a gidan da sauri tace abincin da muka sayo masu ke nan fa khadija ?
Nace wa ya sanar mata mara mutuncin mata kawai wai kamar mommy zataiwa rashin mutunci irin haka saboda ta samu guri a wurin shi.
Dariyan mumuke maryam take yi nace wanan dariyan fa haka kamar wace taga an cuci wani ?
Ganin bata da niyar dainawa ne yasa nayi banza da ita har tayi ta gaji ita kadai sai bayan kwana biyu ne Yusuf ya kirani yana fada min wai an masu haihuwa.
Nace nako taya ku murna Allah ya raya yasa dadin musulmi ne aka samu yace amin sai dai baki tambaye ni ko wa ya haihu ba koda yake bazaki rasa ji ba a wan gurin.
Wa yasan na san ku da zai fada min an maku haihuwa ni yanzu nake ji a wurin ka Allah ya dada sa albarka ga abinda aka samu .
Amin yace tare da godiya kamar shi akaiwa haihuwan ya tambaye ni jikin anty na nace da sauki na gode mukayi sallama ya kashe wayan.
Wurin gi nayi da wayan gefe na naci gaba da karatun da nakeyi sai dai ban gane komai ba a cikin karatun yi dai nake yi kawai.
Maryam ta shigo dawowan ta ke ban daga cikin makaranta gaida ita nayi ina fadi kin dawo ta amsa min da eh tana cire kayan jikin tace yanzu naga abin mamaki a waje zan shigo.
May kika gani na tambaya ba tare da na dago na kalle ta ba tace zarah ki na gani yanzu ko kallo na batayi ba ta shige Napep.
Zarah fa kika ce yaushe rabon da nasa ta a idona nima yanzu ina ganin ta watsar da zancen karatu ne tana abinda taga zai fishe ta.
Maryam tace amma gaskiya tayiwa kanta tana ganin wanan rayuwan da ta zaba shi zai fida rayuwan ta watarana.
Ba ace mutum kada yayi yadda yake so ba amma idan zakayi sai kayi yadda ya dace don kada gaba kazo kayi daka sani.
Don maza mayaudara ne idan ka hadu da wanda baida tsoron Allah kin ga kamar wanan mutumin ki din yasan ciwon kan sa sosai haka nima MS yasan mutunci na amma kawai don kazo karatu sai ka biye wa maza suna bata ma lokaci bayan su sun gama gina tasu rayuwan a baya.
Idan da basu tsaya sunyi karatun ba yaushe ne zasu zama haka har su samu kudin da take kwadiyi a wurin su.
Wanan tunanen nake yi kika ga ina son rage hurda da kowa yanzu tace khadija Allah ya raba mu da wanan halin ita fa mace batayi sai da namiji haka namiji bai yi sai da mace.
Abinda yasa nace maki haka don rayuwa ne na taimakawa juna a tsakanin mu dasu to amma idan zakayi kada kayi haramtaciya wanda Allah ya hanna yanzu rayuwan ne yazo da haka.
Sai dai mutum kada ya shagala da ruden duniya ya biyewa shedanun maza sukai shi su baro tun farko a yadda na sanki da mutymin ki dan iska ne na tabbatar tafiyan ku ba zai yi nisa haka ba.
Mu godewa Allah da ya dube mu ya hada mu da natsatsun mutane sai kuma muyi adduan Allah ya kara kauda shedan a tsakanin mu ko wani lokaci.
Nikan har ta bar maganan amma abin ya tsaya min a rai sosai sai nake ganin may ma zai hana in watsar da kowa yanzu har sai na gama karatuna in fara dating.

Yau tunda ya fita office ya rasa gane kan shi sai ta fara aiki yaji bai iya karasawa ya aje, a haka Yusuf ya shigo ya samay shi zaune ya tas files a gaba sai kallo yake yi.
Kallon shi yake tun daga kofa har ya karaso tun bai kai zaune ba yake fadin lafiya dai ko naga yanayin ka ya canza a lokaci daya.
Dan gyara zama yayi yana kama goshin shi yace wallahi haka kawai naji jikina ya mutu yaki fada mai gaskiyan maganan yadda yake jin gaban shi na yawan faduwa haka kawai.
Kallon shi Yusuf yayi yace muje in sauke ka gida ka dan huta kila yawan jigila da baki ne ya jawo maka haka tunda baka saba ba.
Shi ya sauke shi gidan shi don haka ba a san dawowan shi gidan ba babu kowa a falon sai tv dake aiki don haka ya wuce kai tsaye sama inda dakunan barcin su yake.
Tun yana hawa yake jin hayaniya na tashi a saman sai ya dauka yan barka ne har saman suka hau a step din karshe ya fahinci dariyan wani abu suke sai yaji yana son zuwa ya duba baby shi kafin ya kwanta.
Haba Nafisa kina bani mamaki namiji kamar mijin ki zai gagare ki kin kasa juya shi yadda kike so a hannnun ki.
Itako Nafisa sai tace ba na kasa juya shi bane dama vikin nan dake jikina ne ya hanani aiwatar da sauran aiki na amma yanzu tunda na haihu lafiya may za a fasa sai in dora a inda na tsaya kawai.
Sai na kama shi na mayar dashi marayan dole sai abinda nace kamar mahaifiyar shi zan koma duk wa yan nan dagin kala dake ganin dun samu kan shi har zasu zo gidan shi suyi yadda ran su ke so ba za su ga kafan sake gigin zuwa ba kuma.
Don kafin su wuce sai na samu sherin da na kula masu gidan nan sun tafi ta baibai ai ni kowa yaci tuwo dani ya san miya kawai yasha.
Da baya baya ya koma dakin shi ya koma ya bude a hankali ya shiga ya kwanta bai taba yarda Nafisa zata iya fadin magana ba haka duk da yasan halin ta amma bai dauka takai haka ba.
Sai zuwa can ta raka madam ko may ta shigo dauka dakin taji shi a bude ta sa kai ta shiga kwance ta hango shi rigingine ya na tunane.
Da sauri ta karasa wurin shi tana fadin lafiya kadawo a wanan lokaci yace ban jin dadin jikina ne na dawo in huta.
Tace tun dazu ka dawo ke nan yace shigowa na ke nan kika shigo sai ta sauke ajiyan zuciya yana lura da ita.
Zata zauna yace ki barni in huta please ko zan samu barci jikin nawa ya sake haka yasa ta mike ta fita daga dakin yabita da kallon mamaki yana fadin Allah ya kara kare shi daga kaidin ta.
Ranan yayi tunane iri iri a ranshi barcin da yake son yi gaba daya ji yayi ya fice mashi a idon shi.
Shiryawa yayi ya fice daga gidan ya rasa inda zai nufa yaji sanyi sai tunane na yazo mashi a da in yana cikin wanan yanayin guri na yake zuwa muka shi rikici dashi har yaji ya manta da komai a ranshi.
Sai da yakusa kaiwa ne tunane yazo mai a rai yaushe rabon da yazo guri na ya dubani yanzu zai iya kai wata hudu fa tun cikin wancan hutu kafin muje gida.
Gaskiya dole ya hakkura da zuwa sai kuma wata zuciya yace mai ya tafi kawai yasan abinda zai fada min uzurin rashin zuwan shi din.
Waya ya dauka bayan ya iso ya kira ni ina ganin wayan shi gaba na sai da ya fadi nayi saurin kashe wa ya sake kira ba kashe don yasan naga kiran nashi kai ya girgiza ya kara danna kiran na sake kashewa.
Tsaki yaja ya kira Yusuf yace kace ma wanan yarinyar ta dauki wayana na kirata ta kashe min waya Yusuf yace wata yarinya ke nan.
Kai tsaye yace khadija a takaice Yusuf yace ko tana class ne yanzu bata don yanzu sun rufe ya kashe wayan nashi.
Yusuf din ne ya kirani shima ban dauka ba har kiran ya katse ban daga ba karshe ma da naga zasu damay ni sai na kashe wayan gaba daya.
Kiran shi tayi ya fada mai abinda ke faruwa yace bata dauki wayan nawa ba sai dai barin kira kawar ta maryam in ji.
Maryam din ya kira yana tambayan ta ni ko ina ciki ne tace mai eh ina nan bari ta duba dakina ta gani sai zuwa can sai gata tace na duba bata dakin ashe tayi mai karya.
Yace mata ya gode ya tayar da motar shi ya wuce badon ya yarda ba do yadda yaga maryam din ta da farko ranta a bace ta dai kare ni ne kawai kada ya dauki wani abu.
Bakin cikin da yake ciki yaji ya karu mashi kai tsaye gidan Yusuf ya nufa yana aje mota ya fada ciki yana huci tare da fadin ni za a kawo wa iskan ci don ta samu na zubar da ajina ina kulata take daukan kanta wata mace can.
Kaida waye kuma Yusuf dake zaune yana kallon shi yake fadin haka cikin kafa mashi idanun shi yana so ji ko shidawa ke fada.
Sai cewa yayi duk haka suke dama irin daya mata basu da banbanci wurin karamin kwakwalwa wallahi ko wace taga kana kokari sata a inuwa sai tayi kokari kai ka rana kai.
Wai may ke faruwa ne haka duk ka hargitsa kan ka haka yace Nida wanan yarinyar ne mana khadija don kawai yau na tuna da ita naje gurin ta shine har zata nemi ta wullakanra ni.
Kai mutumi na cool down don Allah ka fa san khadija yarinya ce mai kaifin basira da aiki da hankalin ta kamar ba karamar yarinya ba.
Ke nan ka goyi bayan wulakantani da nakai kaina tayi min ke nan ko may ?
Dole in goyi bayan ta don itama mutun ce kamar kowa don may zata yarda ka bata mata lokacin ta a banza bayan ta gama fahintar ka ba don Allah kake tare da ita ba.
Ba don Allah ba fa kace Yusuf
Kwarai kuwa don hakane tunane ta a yanzu tsakani da Allah yau rabon ka da zuwa wurin yarinyar nan zaka iya tunawa ?
Waye khadija da zan ta binta koda da yaushe don banda aikin yi ko may ko yaushe zan kama hanya gurin wata can daba matana ba ko wata nawa ?
Yusuf yace ba wanan ba yanzu in tambaye ka may kaje yi gurin ta har tayi ma haka ?
Wani kallo yayu mashi yace May naje yi kacs da ban kan lekata ne idan na tashi ko yanzu abinda ke kaini gurin ta ne ya kai ni ba wani abu .
Kai mutumina kafito fili muyi magana kan yarinyar nan ni dai ba bako ka bane ko na khadija ka sani watau kaje ka ganta ka sata wani abin sai aka samu akasin hakan kake ganin laifinta don taki.
Yace ko gani ta nayi ta ki daukan wayan mu na tura akira ta kuma wai ni zatace ace wa bata nan may ta dauki kanta ?
Yace ita ce daidai da kai wallahi wace daga kai har Nafisa zakuyiwa ta tsaya ta kwatar wa kanta yan ci a gurin ku ba Fati bane ya dace tayi kishi da nafisa sai khadija ta dace da wanan.
Kai duk mata a yau din nan daya na dauke su a guri na don may zanje gurin ta na debo baci rai a gida nazo gurin ta don inji sauki sai ita ta zuba min nata dafin.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

Yan uwa da abokan arziki ba laifi sun zo mashi karan suna sai dai taron ba wani dadi don mai jego ta tsare komai na gidan ta hana mutane suyi yadda suke so.
Ganin haka ne tu sha biyu suka buga min waya suna tafe gurina don basu ga amfanin zama gidan da suke yi ba gara kawai su fita suga gari.
Da waya har suka iso gidan da muke zama inda ake kira da up k na mata inda a nan nima nake da dakin na da aka kama min tun zuwa na Abuja.
Ranan nayi mayan baki don karshen ta dole suka samu gaba wai mu zamu nuna masu gari shigan dai guda ne don ko yau wani abaya baki mai kyau ne ke saman lace din da nasa.
Shigan yayi min kyau matuka don ya mayar dani kamar wata yar bukuwar haure dani munje wuse market mun dan leka gura re sai yamma lis muka bar SAHAD zuwa inda gidan yayan nasu yake inda suka zo suna.
Don nace dasu ni ban sani ba can ko sai faman tambayan su ake don wata ta bar yar ta karama na barci a gidan ta biyo mu yarinyar ta tashi tana kuka sosai don haka ake tambayan ina suka je.
Har shi kanshi maigidan da kukan yarinyar ya damay su yake tambaya akace mai suna gurina bai tsaya mamaki ba ya fara fadin may suka je yi wurin yarinyar dake makaranta.
Mun shigo suna falo an gama rikici

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login