Showing 105001 words to 108000 words out of 133935 words

Chapter 36 - Mijin Buzuwa Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

278

abinda yace.
Na sake cewa da kai fa nake magana ka kyali ni yace even peck kiss yana lumshe ido kamar zan kai kiss din sai na cije shi a kumatunshi.
Yana shafa wurin yana fadin wassh ko hakan ai na gode zan tunaki watarana na taba haduwa da wata manya yar Niger mai zubin half cas.
Ya bude motar tare da fadin thanks ki kula da kan ki don Allah don kin bar min tarihi nace mugu kawai azzalumi mayaudari da sauri na fita do kada ya kara rufe kofan yana dariya yaja mota tare da min horn ya tafi .
Ko da na shiga hostel na samu har martam ta kwanta ina shugowa tace kun dawo tare da duban time tana fadin ban dauka zaku dade haka ba ai.
Zama nayi jagwal a wurin fuskana kawai zaka kalla kasan ina cikin bacin da sauri ta mike zaune tana fadin wani abu yayi maki ne.
A takaice nace may ye bai mun ba yau maryam AA ya cuci ni ya shammace ni sosai wallahi da sauri naga ta fida ido waje.
Nace ban taba sanin dan iska bane sai yau wai nifa AA ya ruguma maryam har da taba min kai kiji min dan iskan banza.
Ajiyan zuciya naji ta sauke tare da fadin wallahi har kin saka gaba faduwa na fa dauka ko raping dinki yayi wallahi wani irin harara nayi mata nace ya ma isa.
Tace cikin dariya yadda kikai maganan ai dole mutum ya tsorata yayi zaton hakan ne ya faru a tsakanin ku.
Nace may ye marabin wanan da hakan don Allah bada hakan ake farawa ba har aje can daga magana kawai sai naji ya rungumay ni don kawai ya nuna min dan iska yake macuci kawai.
Tace akan kayan dazu ko na kada mata kai nace ashe kin san abinda zai min kika bari nabishi ke nan tace kema kin faye baki wallahi .
Ai gara da kika zabi law don kin iya bakin ki don Allah bani labari nikan in sha dariya don nasan yau ashe yasha zagi a gunki.
Nace ban sani ba cikin hararan ta ina mike tace indai gulma kuka kai shi ke dashi kuna son juna kuna wani noke noke .
May zanyi da wanan dan iskan ni bakiji ba ma wai shi ko matan shi sai yaga dama yake kara waiwayan mace idan yaga dama.
Dariya mai karfi ta kwashe dashi tana fadin ashe akwai aiki kuwa kuma yake sha, awan kara mata fadi dai yayi wallahi.
Toni ina ruwana da rashin kula matan shi ko ya kula ko kada ya kula duk uwar su daya a gun khadija don ba abinda ya shafe ni da hakan na fada mai.
Nan nabarta tana min shakiyanci alwala na dauro ina son yin waka don kada ta zarge ni haka na fito na tayar da sallah na gama na kwanta banci komai ba ranan.
Sai dai ba barci nayi ba don tunane ya hana ni shakat a zuciya na don da zaran na rufe ido abinda ya faru tsakanin mu ne yake zuwa min.
Har dai barci yazo ya dauke ni ranan na makara da sauri na mike ina shiryawa sai ga wayan shi ya shigo min.
Kamar ba zan daga ba kallon da maryam ke min yasa na daga wayan murmushi naji yayi tare da fadin nasan dai kamar yarda banyi barci ba kema hakan bazaki barci ba daren jiya.
Akan may zan hana idona barci nace mai, yace akan dan gidan mommy mana kema kin sani , nace Allah dai ya sauwaka kana ganin kayi wani abun gwanewa kenan, mutumin da ko runguma bai iya ba sai ta hanyar karfi, zai sa na kasa barci na kashe wayan.
Yayi kiran duniya naki daga wayan sai ga text din shi ya shigo min kamar haka.
Saboda kin san kin zuba min dahin ki a jiki daren jiya yasa kika fara garani ko may ?
Niba macijiya bace ai, balle in zuba ma dafi
Na tura mashi, ba a jima ba sai ga amsa shi kamar haka ,
Kin fi macijiya dafi karfa ki manta ke mace ce, mace ko shu,umace ko wace iri ce ita tasan sallon sheri ga da namiji.
Kai dai ka sani da kayan sherin ka in ma dafi ne kai kazubawa kan ka bani ba ya karanta yana dariya bai san shigowar Nafisa ba dakin.
Sai jin muryan tana tambayan shi kaidawa ke waya haka kake dariya ?
Dakewa yayi duk da kaduwan dayayi cikin ranshi amma a fili cewa yayi da ita nida Yusuf ne don yasan ba karatun boko ta iya ba balle ta amsa ta karanta.
Ba don ta yarda ba ta kyaleshi kawai tana zargin shi a cikin ranta don yanzu ya fara bata tsoro gaba daya don ya daina sayin ta da yake yi a da can baya.
Daga haka ya sauka kasa yana yana kiran yaran aikin gidan shi ya shigo mashi da buhun da ya dawo dasu jiya.
Ya sa akai masu dakin da su mommy suke tare dasu iyan bawa a gidan daidai lokacin Nafisa ta sauko kasa tana fadin Sabel wanan kayan haka daga ina kuma ?
Yaro gidan dan yaren su na buzaye yace maigida yace ya dauka yakai dakin dabakin shi suke ciki tabi buhun kayan da kallo nan ta so sanin abinda ke ciki.
Don haka tabu shi a baya wai taje da sunan gaida mommy yau da kwana yana zaune saman kujeran dakin suna hira da iyan bawa ta shigo tana gaidasu idon ta akan buhun dake gaban shi nan ya fahinci buhun ta biyo a lokacin don ganin may ke ciki.
Idon ta ya gano mata atamfan da ya fara fitarwa kasa yana son fitar da sauran sai gata ta daure fuska tamau idan da dane da ya shiga hankalin shi ga yadda ya ga ta daure fuskanta.
Sai ci gaba da fitar da kayan yake yana bin sunaye su yadda na rubuta ajikin ko wani ledan kayan yana ajewa gaban mommy bai fara bayani ba ta juya ta bar dakin a fusace cikin bacin rai.
Sai bayan fitan ta daga dakin ya fara yiwa mommy bayanin kayan tare da dora ma ko wani kudi a saman kayan yace suyi dinki sai Allah ya dawo dashi lafiya zai shigo yayi masu ban gajiya.
Kallon shi mommy tayi da kyau bayan ta gama sauraro shi tace wanan hidimar yayi yawa haka babangida don haka kabar kudin nan abin kuma ya koma biya , ?
Mu da mukazo aikin lada zaka saka muna da wanan irin alherin haka mai yawa gaskiya hakan bai muna dadi ba gaba baka son inzo zama da diya ta ke nan in Allah yayi abin.
Murmushi yayi yace ko baku zo nan ba mommy zan iya maku fiye da hakan don haka wanan ba komai bane Abba yace a tura ku gida yau kafin in wuce.
Nasan ya kiraki ya fada maki komai ai don haka idan da sauran wani abin sai ku fada min a sayo maku kafin ku wuce na kuma gode kwarai da kokarin ku a kaina.
Sai dai ayi hakkuri da yanayi matar gidan don Nafisa sai hakkuri nima dai kun ga shinakeyi.
Ka dauki kudin nan ko ka rage dawainiyar yayi yawa haka abin ya zama kamar biya mu kayi ke nan ya mike yana murmushi yana fadin ba komai iyan bawa ai yima kaine.
Na shirya driver da zai sauke ku idan kun gama sai aimin waya zan dan leka office don tafiyan mu sai dare zamuyi shi akwai dan sauran lokaci zuwa yanzu.
Godiya sosai sukai mai ya fita nan dai mommy suka fara shirin tafiya don ba a ketare maganan Abba a gidan.
Yana fitowa bai koma ciki ba ya nufi hanyar fita daga gidan muryan Nafisa yaji a bayan shi tana fadin dama nasan abinda ya zaunar da su ke nan a gidan nan tun bayan suna basu tafi ba kamar yadda kowa ya wuce.
Suwa ke nan kike nufi wanda kasai wa kaya bada sani ba yanzu Allah ya tona ma asiri na gani do baku so in gani ba.
Wai nafisa kina da hankali kuwa iyayyen nawa ma bakin ciki kike dasu akan nayi masu alheri tace ai ba su kadai suka wahala a gidan ba har dasu Yanyala sun wahala .
Don may ba zaka saya masu tare ba ka ware naka kadai watau sune ka sani ke nan kai ya girgiza cikin kunan rai yace ba laifin ki bane sai kawai yaga ta sha mai gaba ta inda zai wuce ta.
Hayaniyar su ne ya fito dasu mommy waje ganin su mommy ba sa ta fasa ci mai mutunci ba mommy ce ta hana shi magana.
Duk ta hade dasu mommy tana zagi tare da fadin tayi ma kowa nashi iyaka da gidan tun da ba zuwan arziki suke yi ba jifa samun wuri a gurin wanan matar ita ha gida taf da yan uwanta kullun sai kara yawan su takeyi a gidan.
Kowa yazo da sunan ganin ta sai ya nemi wuri ya zauna ba maganan zuwa gida kuma gare su an shafe ke nan.
Haka ya fita gidan ranshi bace ranan su mommy sun ga fitsara a gurin Nafisa inda tayi ta aiban ta su suna ji suna gani ba abinda zasu iya yi tana gani taci gaban su.
Ranan haka dai ya wuni cikin bacin rai halin Nafisa ya jutayin irin zaman da suke na rashin jin dadi a gare shi kuma bai jin zai iya rabuwa da ita ko kadan.
Bayan su mommy sun gama shiri suka kirashi yace gashi nan zuwa ya samay su a shirye don haka basu bata lokaci ba suka fito da kayan su Yusuf suka loda a mota sukai sallama dasu suka tafi suna kara bashi hakkuri.
Da yamma ya fito cikin shirin shi ya samay ta a dakin ta tana zaune tana waya ganin shi bai sa ta katse wayan ba sai data gama yake fadin su zasu tafi.
Wani sabon lalura ta kirkiro mashi aladole kudin da take hasashen ya kashe ma iyayyen nashi sai ya kashe mata su bayan ya riga da ya sallamay ta da safe ta lissafa mai abinda take so ya bata.
Nafisa wai may zakiyi da kudin da kike karba ne haka ya tambaye ta wani kallo tayi mashi tace idan zaka bani ka bani ba sai ka tsaya ka tambaye ni ba kuma ina sin idan ka dawo zan tafi gida inyi gyaran gidan mu na can.
Dole ya bata daga cikin kudin da zaiyi amfani dashi don kawai su rabu lafiya da ita.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

Tunda muka muka bar asibitin shiru nayi ban iya magana ba sai su ke dan hira jefi jefi a motan ajiyan zuciya na sauke ina fadin yanzu baku ganin kamar yawan ciwon kan nan wani abune ?
Da sauri Yusuf ya juyo yana fadin wani abu kamar yaya sai nayi shiru kuma yace tambayan ki nake yi mana kin yi shiru kuma.
Nace akwai ciyon kai irin wanan da yake na shihiri ne in kunyi diba ga irin matar nan nashi zai yuyu wani aike tayi mai wanda bai zauna a jikin shi ba sai ya iya haifar mai da hakan.
Idan ba kasan da irin shi ba ba kowa ne yake gane hakan ba zaka mutum na fama da ciwon kai mai tsanani ayi ta magani kamar ba a yi.
Nima gani nayi a makwabtar mu haka ya faru koma dai ba shi bane ya kamata ku hada da na gargajiya tunda likitoci sun ce basu ga komai ba su .
Shiru yayi na wani lokaci ba tare da yayi magana ba abubuwa da dama yake tunane a ranshi sai can yace maganan ki na da kamar gaskiya khadija.
Don dai a yadda yake rike kai yana kugi zakace zai iya mutuwa ne a lokacin kuma kan sai cikin dare kawai yake damun shi .
Nace abinda ya ban mamaki ke nan nima ace ciwon kai kamar na sihiri sai dare kawai yake tashi cikin ne ma wani lokaci yake dan tashi da safe ko idan ya ci wani abu.
Allah ya sauwaka nace maryam dashi suka amsa da amin lokaci daya maryam tace gashi har ya ci ayaba ya zauna mashi ciki lafiya abin ya ban mamaki ai.
Nidai har muka shiga hostel ban yi magana ba sai dai ido da sauraren su da nake yi kawai.
Kwance nake tun bayan dawowan mu da nayi sallah magariba da ishai na kwanta nan iya cin komai ba na kwanta zuciya na cike da damuwa.
Washe gari tunda safe da na tashi ina shiri jikina ba karfi a tare dani sai tunane nake na yadda na ganshi kwance jiya yana jin jiki sosai wai a haka yaji sauki ke nan.
Waya na nadauko ba tare da na tsaya tunane ko yana barci a wanan lokacin ba na dana mai kira wayan ya shiga yana ta ringing ba a daga ba.
Sai kusan zai katse aka daga wayan muryan shi da alaman barci a tare dashi yace hello Deedar ya kike nace ina kwana ya amsa da lafiya nace ya jikin yace jiki da sauki nagode.
Sai nayi shiru yace hello dayaji shirun yai yawa nace kaji sauki sosai ko yace mm a ji sauki Deedar ya kuka koma jiya nace lafiya a sanyaye.
Can nace nagode Allah saka da alheri yace namay fa nace na tsaraban da ka kawo min ranan nagode kwarai Allah saka da alheri tsaraba haka da yawa.
Yace ba komai nagode sai an jima na kashe wayan ajiyan zuciya na sauke ina aje wayan cikin hand bag dina tare da lumshe idona.
Haka na shiga makaranta jiki ba karfi duk yinin ranan haka nayi shi a sukurkuce dani yau ma kamar jiya na dawo ban dade ba a cikin makaranta na dawo.

Yusuf tunda ya aje mu hankalin shi ya koma kan maganan mu kawu salisu ya kira yana fada mai matsalan Abdulsamad din.
Kawu yace zai je a ga malam yayi mashi bayani komai kai tsaye asibiti ya nufo inda ya samu Nafisa na fada da security a bakin get.
Nan ya tsaya rai bace yake masu magana abin mamaki sai ta maida fadan wurin shi tana fadin sune ai munafukan da suka ja a wullakanta ta din sun dauko karuwa sun kawo ma samad har cikin asibiti tazo tana iskanci.
Da mamaki yace karuwa may ya hada AA da karuwa kuma tace in ba karuwa bane may zai sa tazo tana bashi ayaba a baki ?
Kai ya girgiza yana mamakin inda maganan ya fito mata yayiwa security din magana akan su kyalesu su wuce basai sun tura ta ba.
Ciki ya shiga fuskan su kawai da ya kalla yasan akwai damuwa a tare dasu yace mommy ya akayi har Nafisa tazo nan da fitina haka ?
Yusuf Nafisa tana fada ne bisa ka,ida zuwa tayi nan tana hauka nasan kawayen ta ne da suka zo dazun suka fada mata don dun samu yana cin ayaban da suka shigo.
Ya girgiza kai yana murmushi yace mun dai auna arziki bata samu su khadija a nan ba da ba karamin tashin hankali zasu yi ba don ko ita khadija ba baya ba da alama wurin fitina.
Khadija ce kaidai zata yi daidai da gidan Abdulsamad a halin yanzu mommy don itace kadai nake ganin zata iya da Nafisa a yanzu.
Shi babangidan yace yana son ta ne ko ya nuna wani alama na ra,ayin tane da dai zanyi hakan gaskiya da yayi dace da kamilan mace a gidan shi don ni yarinyar tanayi min wallahi.
Don akwaita da natsuwa da girmama na gaban ta ga ilimi addini da na boko ta samu a tare da ita kaga kowa ma zaiyi kwadayin wanan mace a gidan shi ai.
Tun farko ina ma yaran gidan mu kwadayin ta sai dai kasan yaron yanzu ba ai masa haka gara inshi yagani da kanshi yace yana yi shine za a zauna lafiya.
Duk da nasan khadija tana da masoya ko anan kaduna din amma haka bai hanani jin wani nawa ya so ta ba.
Amma kai da kake fadin haka akwai wani abu makamancin so ne a tsaka su dama kodai dacewan haka kaima ka hango yasa kai magana ?
Mommy gaskiya ba zan boye maki ba akwai sai dai dan nakine miskilanci da ji da kai da izza yahana shi tsaya su fuskanji juna shi da ita kin san kuma ba a son mutum da haka.
Shi yana ganin idan yaje mata da zancen so kamar ya zubar da kiman shi a gare ta ita kuma khadijan kallon yan uwa take muna a yadda na fahinta ni.
Sai dai dukkan su suna boye feeling din su ga juna ne amma indan so akwai so

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login