Showing 102001 words to 105000 words out of 133935 words
ya tambaye ni mutum ba zai iya fahintar abinda yake fadi ba saini dake kusa nake jin shi nima a hankali na mayar mashi da amsa da cewa next week zamu fara insha Allah.
A yadda muke magana zaka dauka wani magana mai ma,ana mukeyi idon matan nan da suka shigo su uku ya dawo a kan mu suna kallon mu gashi jikina na kusa da nashi kamar dai mata da miji.
Mommy ke fadin yaji sauki sosai yau gashi ma yana cin ayaba har mun ga idon shi ai jiya abin ba dama wallahi.
Basu tsaya ba suka yi ma mommy sallama tare da fatan Allah ya kawo sauki suka fita muma bamu dade ba mukace zamu tafi Yusuf ya taso yana fadin barin je in sauke ku ko ?
Sallama mukai masu muka baro asibitin Yusuf ya fito ya sauke mu tare da yi muna godiya nace ba komai ai Allah dai ya bashi lafiya.
Fitan matan kenan daga daki suna shiga motar su dayan tace nikan yau naga abu wallahi wai waye wanan yarinyar danagani tare da mijin Nafisa.
Dayan tace aini yau imani ya kashe ni anan anya Nafisa batai sakaci ba kuwa ta yaya zata zaune gida ta bada damar wata na mata jinyar mijin ta don tsaban son jiki da sakaci irin nata.
Wanan may ta sani banda karyan arziki da nuna son miji a baki kawai waya ta daga ta kiranta tana labarta mata abinda suka gani.
Bata jira ta gama bayani ba ta kashe wayan tare da fitowa waje a sukwane tana zunduma ashar tare da fadin su Yanyala su biyu ta.
A hanya take fada masu abinda ke faruwa a asibiti da mijin ta da wata sai dai kafin su zo mommy tasha ita da Yusuf da mijun nata uwa uba yarinyar da bata san ko wacece ba .
A fusace ta turo kofan mummy dake zaune tana lazimi ta dago kai tana kallon ta da shigowan ta tace ina yar iskan yarinyar da tazo tana bare ma Ayaba ina karuwan yarinyar ta tafi ?
Wacece ita wa ya bata dama tazo kusa da miji na haka tana magana tana zaran ido ta kalli mummy ta kalli Abdul di dake kwance yana kamllon ta.
Nafisa you're very stupid zaki shigo ma mutane daki ba sallama kizo kina fadin rubish haka wakika ba ajiyan yarinyar da kike tambaya ?
Mommy tace wace yarinya wai take magana ne wani kallon wullakanci tayi ma mommy din tace ko wace yarinya ce ai kun sani ni za a munafunta kuma ?
Dama na sani ai abinda ake kulla min ke nan ba yau ba wallahi anyi kadan aga baya na a gidan nan balle aje a dauko wata karuwa tazo tana bare ma ayaba tana baka a baki.
Subbahanallahi wani munafuki ya fada maki haka mommy barta an bare min ayaban an bani a baki may zakiyi ?
Au ashe ma kasan karuwan ka tazo har ta baka ke nan karuwa kema kin san nafi karfin karuwa don yar kwarai ce ba irin ki ba da tashigo duniya tabar iyayyen ta.
Babangida kubar maganan nan don Allah tunda kai kasan gaskiya tace dole kice haka mommy tunda dake ake hada bakin yin haka.
Samad akan karuwa kake zagi na har kake min gori na baro iyayyena gida nazo nan ni kadai.
Ba karuwa bane yadda na aure ki haka itama zan aure ta in kawo gida ta zauna dani tafiki komai da kike tunanen kina dashi.
Ido ta waro waje kafin tai magana security din asibitin suka shigo suna kokarin jan ta waje suna fadin ba ai masu hayaniya anan kuma ba lokacin zuwa duban marasa lafiya bane yanzu.
Samad aure kake fada min da bakin ka zakayi aure fa kace suka tura ta waje tana masifa tana zagi mommy mamaki ne ya cika ta da jin kalamin da ya furta.
Bayan fitar ta tace Babangida dama kuna tare da khadija ne ko dai ka fada mata hakane don ka bata mata rai.
Mommy bar yar iskan matar nan da bata da hankali zanyi maganin ta nan bada dadewa ba.
Lamarin Nafisa ne sai hakkuri kabar biye mata kuna sai da hali haka haka ba tarbiyan ka bane wallahi.
Bai iya mata magana ba don ranshi a bace yake da abinda nafisa tazo tayi masu yanzu sai mommy tace wai ma a ina taji wanan abin ?
Har take aibanta yarinyar mutane haka khadija ne take kira da karuwa wanan bata da tarbiya wallahi.
Har ta kare bai mata magana ba tace Allah ya kyauta taja bakin ta tayi shiru zuciyar tab da sake sake a cikin shi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Kwance nake saman katifan dakina ina karanta handout dina maryam zaune a bakin katifan tana gyara kumbar kafan ta.
Waka take wanda take damuna dashi sai ya hanani yin karatun tunanen mamud nakeyi wanda ya kai sati biyu yanzu bai lekoni ba kuma banji daga gareshi ba har wanan lokaci.
Hijjab dina dake gefe na dauka na rufe jikina dashi tace sanyi kike ji ko may da zaki rufe jiki haka nace sanyi nake ji wallahi.
Na kara jawo handout inci gaba da karatu tace wai ni ko dazun sai naji kina waya ina son in fito in tambaya wakiraki ko mutumin naki ne naga ya dade bai zo ba kuma banji yana kiranki ba.
Maryam kin damay ni fa karatu nake kuma kin gani a, a wani karatu yanzu inga kina tunane ke kika ga wanan din na gyara kwanciya ina bata baya.
Sai da ta gama abinda takeyi tace don Allah tace muje mini market mu sayo kayan miya nace ban zuwa tare da lumshe idona.
Fada min a jiki naji tayi tana dariya tare da sake ihu daidai kunnuwa na a zabure na mike na biyo bayan ta da gudu zuwa waje.
Dagani sai dan body hook da nake sakawa a ciki in dora abaya kaina ba dan kwali gashina dana daure ya fado min a baya don duk zuben filani na gajeshi wurin kakannin mahaifan daddy na.
A daidai lokacin nz hango motar su tana fakin a daidai inda suke tsayawa da mota idan sunzo guri na ban dauka su bane sai da na duba da kyau don gurin na kowa da kowane masu zuwa wurin yan matan su.
Itama maryam din ta gansu da sauri ta dawo inda nake tsaye tana fadin su yaya Yusuf ne can ko ?
Ba yadda zanyi don sun gama gani na gashi ko dan kwali babu akaina da sauri na koma ciki ita ce ta tafi wurin su tana gaidasu.
Yusuf ne ya tambaye ta gudun may muke haka kamar yara tace wallahi khadija ce ta biyo ni da gudu wai ina damun ta tana karatu.
Na fito daga ciki na dora a baya saman kayan ina hararan khadija na iso inda suke tundaga nesa ya watso min harara yi nayi kamar banganshi ba na kawar da kaina ga kallon shi ina gaida su baki daya.
Har muka gama gaisawa da Yusuf yana tambayana karatu da kwana biyu nace lafiya maryam taso ta bar gurin da dabara Yusuf yace ta tsaya ai .
Munzo muyi maku sallama ne zamu tafi umura gobe idan Allah ya kaimu mukayi masu adduan adawo lafiya Allah yasa a karbi ibada.
Daga ida yake zaune baiyi magana ba tun zuwa su yace ashe baki jin magana baki daina saka kaya irin wanan ki fito dasu waje ba ?
Nace wasu kaya kuma ina duban kaina da shigan da nayi yace ai kema kin sani yaya kika fito waje dazun ?
Haba yaushe zaka daina samin ido hakane aiko wanda zan aura yanzu bai isa ya zaba min kayan da zans saka ba a jikina sai idan naje gidan shi.
Murmushi mai kama da yake ya sakar min yana fadin au haka ne fa kuma gaskiya na faye sa ido.
Yusuf yace kajiki da wani magana kuma akwai wanda yafishi sanin ya kamata akan ki ne yanzu dole ya nuna bacin rai ga abinda yake da iko dashi.
Dariya nayi sosai nace sai kace nice buzuwa ko anty Fati wanan dokan yanzu ai sai daddy na yakai can.
A bari a rabu lafiya kin ga tafiya zai yi kada a rabu kuna halin naku kuma kinga zai tafi dake a zuciya kila ba zai maki addua ba idan yaje.
Addua kan kulun ai mahaifa na suna min shi kuma yana tasiri gare ni wanan bakin naki kuwa anya wataran bazai mutu ba khadija ?
Dariya nayi nace yau dai kun tuna mu ke nan aka kawo muna ziyara haka yace bakin ki zuwa gida ki kara gaida shi da jiki ba ai shi baiyi fushi ba gashi yazo.
Dan satan kallon shi nayi naga hankalin shi baya gare mu nan dai mukayi sallama dasu suka tafi.
Da yamma ina kwance sai ga kiran shi ya shigo min a wayana nayi makai dalilin kiran shi sai cewa yayi fito gani bakin hostel din ku kai tsaye kamar yadda ya saba ya katse kiran.
Na shirya na fito shi kadai na sama kamar yadda nayi tsamani bayan na gaidashine yake fadin dawowa nayi don dazu muna barin wurin nan Abba ya kirani.
Yana son mommy ta koma gida kafin in wuce don haka nake son ki rakani musai masu abinda ya dace diban lokaci nayi a wayana bakwai da rabi na dare don haka akwai lokaci.
Ciki na koma na shirya sai da na zauna ya tayar da mota nace kana dai son ka ban wahala kai da sukai ma hidima dakai da matar ka ni may ye nawa a ciki yanzu.
Na dauka yanzu ma ai da shigan dazu zaki fito tunda ban isa in baki umarni ba ban dai ga dama bai don ba mai iko dani a yanzu.
Allah yakaimu in dawo lafiya zanyi maganin wanan fitsaran naki lokaci daya .
Ka fara maganin fitsariyar matar ta gida mai fita rabi tsira wace bata damu da hijjab ba balle gyale kafin kazo kafa min dokan ka .
Sallon yaudara kawai zaka wani gama kalle min jiki kawani ce kai baka son haka na bayan sai da ka kalle ni tsab.
Dama badon akalle ki kika saka ba idan ni kadai zan kalla ba matsala bane a gare ni wasune kawai ban son suga abinda nagani din.
Don kanawa a gare ni zaka hana wasu su kalle ni kada ka mata ni yanzu a kasuwa nake banda hakkin kowa ai kaina amma ga masu hakki baka tsa, , ,
Jinin hannun shi kawai nayi a jikina yana fadin barin fara gwadawa in gani ko tayi min tunda a kasuwa kike kinga idan yayi min basai kin tallata ma wasu mazan ba.
Bugu nakai ma hannun nashi sosai da yakai ma jikina yana shafawa bai san ina yi ba sai kokarin gwaucewa nake yi ina buge hannun shi.
Fuskan shi a daure bai fasa min abinda yakeyi ba wuri ya samu ya sauka daga titi.
Da karfi nace bude min in fita ina kokarin bude kofar motar a gigice hannun shi naji yana cire min dan gyalen da na yafa saman dogon rigar da nasa.
A take gashin kaina dana tufke daniyar in na samu lokaci inje gurin kitso ya bayana a fili hannu yasa yana wasa da gashin har zuwa inda ya tsaya.
Take naji wani hawayen bakin ciki ya silalo min a fuska na haka bai sa ya daina abinda yake min ba sai ma ji danayi ta rungumay tsam a jikin shi yana sauke wani irin numfashi yana shafa na son ran shi.
Kara sautin kuka na nayi a lokacin sai naji ya sake ni yana fadin are you crying bocouse of dis akasuwa fa kike yanzu.
Hannun shi yakai saman fuskana yana wasa da hawayen dake zubo min din sai kuma naji ya rungumay ni zuwa jikin shi tsam na dan wani lokaci.
Sai da ya gaji don karan kanshi naji ya sake ni ya koma saman kujeran motar ya kwanta yana maida numfashi a hankali.
Kaina na dukar naci gaba da kukan abinda yai min din can kuma naji ya tada mota a hankali ya hau titi ba tare da yayi magana ba .
Kofan bakin wani plaza mai girma ya tsaya ban taba sanin akwai wuri haka a abuja ya bude motar a hankali tare da fadin fito mu shiga ki zaba masu abinda ya dace dasu kuma ki share wanan hawayen kada ace satoki nayi.
Sai lokacin na dago kaina na dubi wurin nace ka sani har kullun Allah ba zai taba baka sa a akaina ba mayaudari kawai.
Dariya naji yayi yana bude motar yace banda wanda Allah ya bani yanzu a kanki kuma koko kina nufin karfin ki ne ya kwace ki a kaina .
Kuma ki daina kira da mayaudari don da yardan ki muka fito nan ki sani banda niyar aikata komay yanzu a gare ki amma ki aje a ran ki time will soon come .
Ko yanzu ke kikaja in maki haka da wanan bakin naki da bai taba mutuwa don ki san irin abinda zaki fada ma mutum.
Fita yayi ya zaya ya bude min gefen da nake zaune na sauko motar a hankali na fito don girman jeep din nasa.
Mun fara tafiya naji ya rada min a kunne anya kuwa ke ma ba buzuwan bace deedar wanan irin gashi da jiki mai dadin tabawa haka fa ?
Hararan shi nayi idon shin kyam a kaina ya sake fadin nayi haka don ki san har gobe nafi wani banzan dake zuwa wurin ki komai.
Banyi magana ba don mun kawo bakin shagon haka muka shiga a jera da juna sayaya nai wa mommy har da gaiya don har yaran ta na zabawa abu.
Ya kalli kayan mai makon inji yayi korafin sunyi yawa sai ji nayi yace kina ganin wanan kayan sunyi ke nan idan kuma kin sai wa yaran mommy ita kadai su sauran yaran anty amarya fa ?
Dole na koma na kara zaba muryan shi ne naji a bayana yana fadin ki zaba ma su ummi da su hajiyan mu kayan suma.
Sosai ya kashe kudi bayan na mommy dana su iyan bawa gana su hajiya mama dana zaba masu super masu kyau su ma.
Mun kai ya biya ko dar nanga yayi ba da akai mashi list din kayan aka saka ga wani katon buhu zuwa inda motar shi take tsaya nayi ban shiga ba sai da ya zauna ya leko yana fadin shigo mana mu tafi.
Nace dashi katafi kawai zan bi taxis in koma ni da sauri naga ya bude kofan motan ban san lokacin da na bude na shiga ba muka bar wurin.
Sai da mukayi nisa naji yace kina zaton abinda ya faru zai kara faruwa a tsakanin mu ne yanzu idan haka kike tunane kinyi kuskure.
Don ni ko matana dake gida sai naga dama nake waiwayan mace do ba haka nake ba kowani lokaci.
Sai dai nayi mamakin ganin yadda kika narke min a jiki kaman dama jira kike in taba ki haka ya nuna min ke nan dama a jirace kike da hakan ya faru.
Ban san lokacin da nace mai mugu mayaudari kawai macuci ba wanda ya taba min haka a duniyan nan sai kai kai kasan wani mace ta narke ma ajiki dan, , , ,
Hannu yakai zai kara kamoni na gwace da zafin nama yayi murmushi yace gobe idan halin ki ne ki kara cika min baki haka.
Ba sai ka kara ganina ba zakace in cika ma baki kaji dadin yaudaran da ka sabayi wa mata a kaina.
Zaki bar Nigeria ne ko mutuwa zakiyi don wanan ne kadai abinda zai hana in ganki in kara kallon wanan suran da kike kasawa a kasuwa in riga kowa kwashewa.
Haushi bai barni na sake magana dashi ba sai juya mashi baya danayi kawai shima bai sake magana ba sai da muka kusa tsayawa naji yace
Wallahi shiyasa kike kara burge ni da wanan halin naki na dan juyo na harare shi yace yes i mean it da wata ce sai tayi nata sayayyan amma ke naga ko tsinke baki dauka a shagon ba naan kuma dole kin ga abinda zuciyar ki ke so a ciki .
Kinga ke nan kin nuna min abin mutum baya gaban ki idan bai baki ba yana da kyau hakan keep on da wanan hali.
Sai dai ai na biyaki ladan ki ko ina ganin ba sai an rubuta maki wani lada ba ko bani wanan lafiyan fresh body din da kika yin kin more ai ke ma.
Ya tsaya da motar na bude najita a rufe na juyo na kalle shi nace bude min in fita hug me for d last time tunda kin ce baza mu sake haduwa irin haka ba.
Malam ka bude min mota in fita ni ba yar iska bace ka sani wallahi ban sani ba zan dai sani nan gaba in Allah ya yarda ban fahinci abinda yake nufi ba bai kuma bude min motar ba yana jiran wai