Showing 72001 words to 75000 words out of 133935 words
naga wasu yan mata dake gefen mu sun kura muna ido.
Dole na bude motar na shiga ya tayar da motar muka bar gurin sai da mukai nisa ne naji yace may yasa duka mata wani lokaci halin ku daya ne wai ?
Na bata fuska tare da dan kallon shi nace haba mijin buzuwa da alama yau baka cikin dadin rai kake hango matsalan gidan ka ga kowa.
Kada ka danganta abinda ya hada ka da matar ka dani don bai shafeni ba ko kadan yanzu ma banga abinda nayi da zaka fadi haka ba.
Yace nima ban san dalili kawai dai ina hango hakane gun ko wace mace kamar halinku duk dayane wani lokaci.
Nace baka canka da kyau ba malam ai kaji ance mata suna suka tara .
Ya kalle ni ya girgiza kai yace bazan iya tabbatar da haka ba sai na gwada don naga biyu halin su daya basu damu da damuwan mutum ba kansu kawai suka sani da son abinduniya.
Wow i am impress dama haka ka dauki mata a ranka ashe ?
Yes sai dai ban sani ba ko kamar yadda kika fada inke din ta daban ce don na dan ga alama haka.
Shiru mukayi duka a motar sai can yace cikin langabar da kai please khadija kiyi hakkuri ki fahince ni don yanzu bani da zabi sai wanan tunanen.
But sai dai ban san may yasa ba nake yawan son in kasance a tare dake muna irin wanan tafiya tare da shammatan junar mu.
What na fada cikin mamaki da rashin fahintar maganan shi tare da fadin me ye maanar hakan a gare ka may yasa sai nice zaka ji dadin fada dani ranka yai maka dadi.
Don haka kaje ka dauko ni a lokacin da nake a tsakiyan karatuna don kawai son fitina kace wai kana son muyi ta shammatan juna kana jin dadi.
Murmushi yayi yana fadin bazaki gane ba ne khadija hakane kawai farin ciki na a yanzu a take na daure fuska tare da fadin maidani inda ka dauko ni don Allah.
Haba mana khadija may kike fadi haka ke nan baki bukatan ganin farin ciki na ne komay yanzu fa kika gama fadin mata suna suka tara da bakin nan naki.
Nace da ban dauka farin ciki kaka samu daga yin haka da nake maka ba ai na dauka bacin rai nake sakaka.
Hummm yace sai ya juyo ya kalle ni yace to indai ina da wani matsayi a gare ki yanzu dai ki zauna mu tafi.
Ba yadda na iya haka na koma na zauna tare da kawar da kaina gefe daya yace yanzu na fara sanin ashe suna kuka tara.
Tunda gashi na roki alfarma a gurin ki kin yi min abu biyu ke nan na fahinta a gare ki yanzu zaman mu tare da ke.
Nace wanan bata min lokaci na kawai kake son yi a banza bayan kasan ina da abinyi a gaba na yanzu.
May yasa zan so bata maki lokacin ki haka bayan nafi kowa sanin amfanin abinda kike yi yanzu.
Yanzun dai mubar wanan magana may kadauko ni yi a yanzu ne don Allah na tambaye shi tare da kura mai ido ina son jin amsa na.
Wanan lokacin da wanan yanayin yafi min ko wani lokaci jin dadi a rayuwa na yanzu matukar ina tare da ke khadija.
Kece mace ta farko da nafi jin natsuwa idan ina tare da ita khadija ya juyo ya kalle ni tare da fadin kin san may yasa nace haka ?
Kai na girgiza mai cikin sanyin jiki alaman ban sani ba sai ya fada dai zan sani daga gare shi.
Yayi murmushi ya kalleni yace kin san yadda zakisa zuciyar mutum ya sake ba tare da an rabu cikin bacin rai ba khadija.
Ina jin dadin hakan da kike min ke ta daban ce da sauran matan zan iya yarda a yanzu saboda wasu dalili da na kafa akan ki.
Wani dalili ne haka na tambaya da sauri tare da kallon shi yace baki taba rokona wani abuba khadija alhali nasan kina da bukatan abubuwa da dama tunda kin san ina da halin shi.
Na nuna kaina nace ni in rokeka kuma akan may zan roke ka bayan nasan rabo ne idan rabona ya ratsa a kan ka zaka bani ko ban roka ba.
Good girl tafiya zatai dadi a tare dake kuwa tunda kin san haka she nayi saurin fadin ashe kai marowaci ne ke nan ga mata ?
Ya dan lumshe ido yace ko daya wallahi na dai fi son inyi abinda ba sai an roke ni bane sai dai ina haduwa da matan da basu da hakkuri ne khadija.
Ban san lokacin da baki na ya bude ba nace kana nufin har da anty Fati haka take yaushe ma ta samu gurin roko a wurin ka kai ?
Ya na tukin shi hankali kwance ya murmusa yace kin ga yanzu ma kin fada da bakin ki yaushe na kula ta balle ta samu tambaya na ?
Haka kowa ke gani khadija shiyasa manya sukace tsakanin miji da mata sai Allah wanan abin na bar wa kaina sani kawai.
Daga ya mayar da kanshi ga titi yana ta tuki a hankali tare da shakan isakan dake kadawa a lokacin may hade da kamshi kasa wanda ke nuna dama na son sauka a lokacin.
Ba wani guri mukaje ba sai yawata garin da mukayi kawai ya dawo dani hostel ya aje ba tare da na tsaya ba na shige kai tsaye yaja motar shi ya tafi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Mommy wayayir mace mai haba haba da jamma irin matan nan ne masu fara,a a fuskan su kuma ita har cikin zuciyar ta haka take da kowa sai dai bata daukan raini.
Abin ta bai rufe mata ido ba tana da ilimi na boko wadattace don duk matan na Abban su Abdulsamad suna da ilimin su ya aure su in ka debe ummi wace iyakarta secondary kadai tayi har hajiya mama mahaifiyar Abdulsamad a gidan shi ta hada karatun ta na NCE wanda dama koyarwa take koda ya aure ta.
Ita anty amarya ma da aikin ta ya auro ta wanda yanzu ta daina duk ya hana matan nasa aiki ya tsaya ga bukatun su kuma.
Mommy ne zaune tare da Abban yana karyawa hajiya mama wadda yaranta ke kira da hajiyan mu ko hajiya mama ta shigo falon.
Akan maganan tafiyan mommy da Abdul din ya bugo yana mata tuni a daren jiya don sun fara tatauna maganan sai Abban bai bada goyon baya akan haka ba.
Yanzu shine ta shigo ayita akaare idan zai yarda shigowan mama yayi daidai da shigowan hajiya ummi da anty Amarya data kira kaffinta shigo.
Sun sami wurin sun zauna tare da fuskantar shi yasa yasan da magana sukazo mai ummi ce ta fara maganan amma sai anty amarya ta dan saka larin kishi a ciki tace ni naga ai ba sai taje ba ya mayar da matar shi mana zaifi sauki.
Ummi da wanan kkaron bata goyi bayan maganan anty amaryan ba tace a a Sadiya tunda har kika ji wanan yaron ya bukaci hakan ai sai mu gode ma Allah da har wanan tunanen yazo mashi a rai.
Ko ba komai ya kamata ace sanin halin ita Nafisa ya kamata wani daga cikin mu yaje ya zauna kamar yadda ya bukata din don ace mai daki shiyasan ida ruwa ke yoyo a dakin.
Nidai kunsan ba lafiya ke gareni ba ba zan iya zuwa ba ita dai suwaiba din ya dace ta tafi don ita dai zainab din ya dace taje ta zauna dasu ta saka ido tunda da iyan bawa zasuyi tafiyan.
Murmushi Abban yayi yace ke nan dai kun gama magana kuna goyon bayan dan ku ko ummi tace ba hakana bane Alhaji.
Ganin dai dacewan hakan mukayi yasa muka goya baya ga maganan shi da kan shi babangidan ya fara tuntubana da wanan zancen da yazo na bashi goyon baya akan haka.
Sai anty amarya ta kalle ta ta rausaya da kanta gefe daya bata kara magana ba har lokacin da Abba ya gama ja ma mommy kunne akan zaman da zatayi a gidan dan nasu.
Suka bar mommy dashi a falon kowa ya kama gaban shi tun wanan ranan mommy ta fara shirin tafiya Abuja gidan Abdulsamad wanda suke kira da babangida kasancewa sunan mahaifin maigidan su ke gare shi.
Abdulsamad bai fada ma Nafisa zuwan mommy ba gidan sai cin karen su ba babbaka suke ita da yan uwanta a gidan banza ta fadi masu kasa gasasa dama haka aladansu yake yar su ta auri mai arziki dangi su kwaso a taru aci arzikin ta.
Mommy bata boye ma Anty Fati zancen tafiyan ta ba inda ta kirata ta fada mata da bakin ta tare da cewa zatayi iya kokarin ta taga ta shirya tsakanin ta da mijin ta kafin ta bar Abuja din.
Allah ya kiyaye hanya Fati tai mata tare da cewa mommy amma fa sai kin hada da hakkuri don kun san Nafisa bata kaunar taga kowa ya rabi yaya Abdulsamad.
Abinda yakai ni shi zanyi idan tayi ba daidai ba dole ne in fada mata gaskiya koda kuwa bata so dariya tayi don sanin halin Nafisa da tayi kamar yunwar cikin ta.
Tsaye yake tsakar falon inda yake umartan masu aikin da ya shigo dasu da su gyara part din Fati yana masu kwatance yadda yake son gyaran.
Nafisa da ke barci a dakin ta Yanyala ta shiga mata da maganar cewa may ke faruwa ne taga ana gyaran dayan part din da tace na uwar gidan ta ne.
Kamar ba cikine a jikin ta ba ta diro saman gadon ta fito inda masu aikin su nan ta hausu da fada wayasa su aiki a gidan ta ba a fada mata ba.
Daga bayan ta ya bata amsa yana saukowa daga sama yace nine nan maigidan na basu aiki suyi in biya su wani irin kallo mai kama da kai asuwa ta aika mashi.
Bai tsaya kulata ba sai kokarin shiga dakin da yake yi tasha gaban shi da sauri ta tsare shi may kake nufi ne samad da wanan gyaran da akeyi ?
Yace abinda kika gani Nafisa shi nake nufi don gida nawa ne ba naki ba kamar yadda kika fadi yanzu.
Nan hankalin ta ya tashi sai ta fara surutu ita may yake nufi da ita da zai mata haka yace don yaga zata haihu zai dawo da fati da yaranta gidan shi.
Tace nasan dama kule kulen da ake shiryama ke nan kake yawan zuwa kaduna akai akai yanzu dama ba so na yan uwanka keyi dani ba .
Shi dai bai mata magana ba don mazan dake gidan suna aiki ya fita batunta basu raba hali a gaban su ba.
Hankali tashe ta kira madam tana fada mata abinda ke faruwa madam tace kika sani ko watace zai dauko ya saka a dakin ba Fati ba ?
Nan hankalin ta ya kara tashi sosai tace Nafisa dam wanan tunanen baizo min ba sai da kika tunatar dani haka yanzu.
Madam tace to zauna nan kina fada akan fati wata tazo ta shige dakin kina gani saboda sakaci irin naki in zaki mike ki mike tun yaushe muka gama da wata fati can.
Wacce hudi daya mukai mata muka fitar da ita a gidan har diyan ta sai tarihin su yanzu har kike tunanen ita zai mayar dakin ta.
Ke kasar ku fa zaki koma aiki kaifi sai Niger nan kusa kafin ma mu dawo aiki ya kankama ko mu huta da ko wacece ma ke son muna kutse haka cikin ruwan sanyi.
Nafisa tace madam kin san ba zuwan ba kuma ba kudin nake jiwa ba don zan iya saida da duk wani kaddara da nake da akan wanan aikin tunda yanzu na rasa gane kan shi.
Matsala daya ne shine mutumin nawa yanzu kin san matsi yake min tun wanan tafiyan da mukayi ondo ya kara burge min a gidan nan baya sake min har yanzu ga kuma lalurar cikin nan dake jikina yanzu.
Madam tace ke dai kawai tawa ki nemi kudi in ma bai barki ba sai ni inje maki manene amfanin zaman mu tare da ba zan iya maki komai ba.
Ai kawai ki daina damun kan ki mu za a gwadawa hanyar boka ko malam kuma ko latsandan ne gaba da lahira indai ana zuwa zamuje shi.
Sai lokacin Nafisa tayi ajiyan zuciya taji dadi a ranta tana ganin aduniya bata da kamar su madam dake tsaye a kan ta yanzu.
Tace uwar dakina Allah dai yaja muna nisan kwana tare ni nasan banda kamar ki a duniyan nan yanzu.
Da wanan shawaran hankalin Nafisa ya kwanta nan ta shiga buga waya gida Niger ko an samu wani bakon boka ko malami mai tashe a kasan.
Sai da ya ga komai ya kankama yadda yake so ya bar gidan bayan ya sallami mutanen da sukai mashi aiki duk da yawan samari yan uwan Nafisa a gidan ba wanda zaiyi bugun gaba dashi yayi mashi aiki alhalin biyansu yake duk wata dasunan aiki suke mai a gida.
Bayan kwana biyu su mommy sun gama shirin su tsab ya tura Yusuf ya dauko su zuwa garin Abujan mommy a gutin hajiya mama ta bar yaran ta tazo ita kadai sai iyan Bawa da suka zo tare da wata yar mai masu shara budurwa don taimaka masu da wani abin.
Mommy sunyi waya da Ya Amina tana sallaman ta tace zata gidan Abdulsamad wanda matar shi watan haihuwan ta ya kama zasu dan kwana biyu acan .
Ya Amina sai sulbul da baka tayi tace mommy ashe zaku hadu da Khadija na ke nan mummy tace banda abinki khadija dake makaranta ina zan ganta ni ?
Sai dai idan sawa zanyi a dauko min ita ko akaini in gano maki lafiyan ta idan na samu lokaci dariya kawai ta Amina tayi don ta san gidan su Abdulsamad basu san komai ba a tsakanin mu dashi.
Tafiyan rana sukayi don haka sai da yamma lis suka shigo garin Abuja din direct gidan shi suka nufa yana gida a lokacin don yana dakon zuwan su.
Nafisa wace ke falo tana shan iska ga yan uwanta a kewaye da ita kowa na shaanin gaban shi sai sallaman su mommy da su iyan bawa suka ji .
Gaban tane ya fadi da ganin su mommy din gidan don bata taba zaton zuwan su ba don a wautan Nafisa ta gama da kowa nashi yanzu babu mai marmarin zuwa inda yake.
Zuwan su mommy ba karamin faduwan gaba yasa ta ba sai take ganin ai zancen auren da take zato ko dawowan Fati gidan gaskiya ne.
Shiya fito daga daki bayan sunyi waya da Yusuf ya sheda mai sun iso ya fito da yar fara, a a fuskan shi yayin da ko kallo su mommy basu ishi Nafisa da yan uwanta dake falon ba .
Shi da kanshiyayi masu iso dakin da zasu sauka din bayan dun gaisa sun mashi yaya gida ya fito tare da Yusuf da ya shigo da kayan su ciki da taimakon wani saurayi.
Falon ya dawo inda suka samu Nafisa da yan uwanta sun juye harshe cikin yaren su na buzanci suna maganan zuwan su.
Fuska a daure ya kalle ta yace Nafisa baki san mommy bane da gwago na iyan bawa da baki tare su da zuwa ba ?
Tace a yatsune na san su mana ba matar mahaifin ka bane ita yace OK cikin wani irin kallo har ya fara tafiya sai ya juyo yace tunda kin san ta kin san kuma matar mahaifina ne baki iya taron su ba nima haka ban son in fita yanzu in dawo in samu wa yan nan yan uwan naki a gidan nan yanzu.
Yana fadar haka ya juya ya fara tafiya tace wallahi baka isa ba don zuwan su zakace yan uwana su bar maka gidan ka yanzu yace zaki san na isa idan yan sanda dun shigo sun fitar min dasu.
Idan akwai abin da yan Niger sukaki jini shine dan kakin Nigeria don basu yi masu da wasa idan sun farmake su.
Nan Yanyala ta fara magana tace haba Allaji ai bin baikai can ba daga dan wanan magana har zaikai ka kira muna polizawa kawai dai jira muke su huta mu mika masu gaisuwan mu.
Ya fice zuwa nemo ma su mommy abinda zasu ci a gidan don yasan ba zasu iya taba cin abincin da suka dafa ba.
Bai dauki lokaci ba ya dawo dauke da ledoji iri na restaurant dauke abinci dasu ruwa a ciki ya bayar aka shigo masu dashi har dakin.
Mommy ta idar da sallah sai ga yaron shi isyaka yana shigo da kayan ciki tare da gaba tar masu da abincin.
Sunka ce har da dawai niya zuwa sayo abinci kuma nan dai iyan bawa ta kasa hakkuri tace zainabu may kika fahinta ga wanan zaman ?
Murmushi mommy tayi tace ke dai iyan bawa ai ayi