Showing 78001 words to 81000 words out of 133935 words

Chapter 27 - Mijin Buzuwa Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

261

yanzu na fara daukar wa kaina.
Su mommy kuma da kika gani nan sun zo gidan nan ke nan harsai kin haihu kinyi arbain zasu koma gida.
Ido ta zaro waje tace ina zasu zauna din yace a inda kika gan su and bari kiji idan naji wani rashin mutunci ya fito daga gare ki zan baki mamaki sosai a gidan nan.
Mamaki ne ko rudewa ya kamata a wanan daren na Abdulsamad wanda take gani karfin haline irin nashi daya iya fada mata wanan magana haka babu ko dar a idon shi.
Bai kara kulata ba ya shiga gyaran jikin shi ya barta zaune a gurin cike da mamakin shi fita yayi ya duba ko an rufe gidan ya samu ko ba a rufe ba shi da kansa yaja kofa ya rufe yasa mashi key.
Washegari mommy da wanan yarinyar da suka zo mai suna Aisha bayan sunyi sallah basu kara kwantawa ba suka fito falon gidan suka gyara tas ta saka turaren wuta dana tsunke a ko ina na gidan.
Take gidan ya dauki kamshi da sanyin Ac kitchen suka koma sai da gaban mommy ya fadi ganin yadda kitchen din yake kamar ba mata ke amfani dashi ba.
Nan kuma suka shiga aiki a kitchen din gyara can gyara nan take kitchen din ya koma na macen da tasan kan ta girki suka dora na abinda zasu ci a gidan.
Sai da suka kusa gamawa ne matan dake gidan jin kamshin girki yasa suka fara fitowa daga dakunan kwanan su daya bayan daya.
Suna lekawa kitchen din suna masu ina kwana don tsaron mutuncin su ga maigidan.
Bayan sun gama girki mommy ta zuba masu nasu taba Aisha nasu ta shige masu dashi ciki tabar saura da mutanen dake gidan zasu ci.
Yanyala ce ta shiga dakin Nafisa take kwarmata mata abinda ke faruwa a gidan da fushi Nafisa ta sauko kasa zuwa kitchen din don taga abinda ke wakana mata a gida.
Komai na gidan neat yake yau ya samu gyaran da ya dace daga bakin su ta shiga kitchen din taga yadda suka gyara komai suka jera shi a inda ya dace.
Fita tayi zuwa sama ta samu Abdulsamad ya gama shirin fita tsab ta fado dakin da fushi tana fadin ban san may kuke nufi ba kaida wa yanda kake fadi wai iyayyen ka ne ?
Ya juyo yana fafin kamar ya fa tace don may zasu zo min gida suna min abinda suka ga dama a ciki suna matsayin baki a gare ni.
May sukai maki ya tambaya cikin bata lokacin shi yana sauraren amsa daga bakin ta tace a hasale yanzu ya dace ace sun shiga kitchen sunyi abinda suke so haka ?
Sai da ya dubeta dakyau yace kada ki manta gidan dan su suka zo suna da ikon yin komai da suke so a gidan nan.
Dansu ko dan ta da sauri ya kalleta yace may kike nufi da wanan maganan naki tace dashi gani nayi itama arziki tazo ci kawai a gidan nan do ba itace ta haife ka ba.
Au dama wanan ne tunanen ki ke nan dama raba daya biyu a gida to bari kiji mommy tankar hajiya mu take gare ni don matar mahaifina ne ita ma kamar hajiyan mu don haka nake daukan su daya.
Yanzu ke baki jin kunya baki tashi kin tare su da abin karyawa ba sun tashi sunyiwa kansu har kike fadan akan haka don baki da kunya ?
Tace ba zan yarda da wanan wuce wurin ba irin nata dama na dade da sanin halin ta tun shigowa na cikin ku do haka kayi saurin taka mata burki a hakan.
You're very stupid ya fada da karfi sai data razana yace kada ki fara kice zaki saka masu ido a gidan nan ko bayan fitana ne don zan saba maki sosai kuwa.
Fita yayi daga dakin ya barta cike da mamaki tana ganin wankin hula zai kai ta dare wai itace samad din ta keyi wa abubuwa haka yanzu.
Lalai duniya na shirin juya mata baya idan batayi da gaske ba tin yanzu dakin ta ta koma ta jawo wayan ta cikin tashin hankali take fada wa madam abinda ke faru da ita.
Sai da ta gama sauraron ta tace Nafisa sai kin hada da hakkuri fa yanzu don ni a gani na akwai ida aiki ki ya samu matsala ko kuma don cikin dake jikin ki ne asiri ya daina kama mijin ki yanzu.
Ina cikin wani hali walahi haka na nufin yan uwan samad zasu dawo gare shi suyi yadda suke so gidan nan ke nan wanda ba zan taba yarda ba sai dai duk abinda zai faru sai dai ta faru.
Madam tace Nafisa kibi sannu fa ba kullun ne ya zama dole mutum yayi nasara ga abinda yake so ba kowa kika gani sai yanayi yana hadawa da hakkuri da kuma kissa bawai ga magani kawai muka dogara ba.
Madam ni abin ne yazo min a bazata wallahi tace yanzun dai ki kwantar da hankalin ki mubi komai a sannu.
Tace na ji amma duk da haka zan nuna masu gidana suka zo ba zan bari suyi min abu gaba gadi ba haka tace kiyi a sannu dai na fada maki.

Shiko yana fita tun a falo ya fara ganin sauyin da gidan nashi ya samu da zuwan su mommy din ga gida ya koma neat a lokaci daya a falo ya hango su hadiye suna kuskus a cikin yare suna ganin shi suka shiga gaida shi.
Fuska a daure take amsa masu ya wuce part din su mommy din wanda anan fati da take zaune da yaran ta ganin haka yasa ya tuna da abubuwa da dama na rayuwan su a baya a gidan.
Kagin zuwa yanzu da komai ya hargitse mashi haka wanda kan shi yanzu ya dorawa laifin kasancewar haka kamar yadda na fada mai.
Ya samu su mommy sun yi wanka suna karyawa a cikin tsanaki ya shigo da sallama ya gaidasu tare da masu ya gajiyan hanya.
Mommy tace gajiya ai yabi lafiya don mun zama yan gari yanzu ko yace mommy duk ku kukai wanan gyaran haka a gidan nan ?
Tace ba dole ba babangida gida ya koma kamar ba mata a cikin sa kasan mu mun saba mijin mu baya son ganin kazanta ko kadan.
Iya bawa tace mai ni ina mamaki gida da mata haka ace bai samun gyaran da yadace mace ta yi a gidan ta wanan matar taka akwai bakin son jiki ne da ita.
Ciki ai bai hana ka gyara muhalin ka sai dai dama idan gyaran bai damay ka ba can amma yaushe ne mace kirki zata bar gidan ta haka ?
Mommy tace ga abin kari can a kitchen idan ta fito sai ta raba maku ka karya kafin ka fita yace mommy zuba min zanci anan gurin ku don bata fito ba ko ina sauri ne.
Anan ya zauna ya karya tare dasu yana mai jin dadi a ranshi yaushe rabon da ya karya a gidan shi haka cikin dadin rai.
Bayan ya gama yayi masu sallama tare da tambayan ko akwai wani abinda suke bukata a gidan ya sayo masu idan ya fita.
Mommy tace sai kayan kitchen din da taga sun soma lalacewa saboda rashin amfani dasu da ba a yi akai akai yanzu dole a sayo wasu yaje matar shi tai mashi lissafi don gudun su shiga mata hakkin ta.
Bai koma takan Nafisa ba ya fice gidan inda ya samu Sani driver yana jiran shi a waje suka dauki hanyar zuwa office din su.

Barci nake a dakina tun dawowana class wayan shi ne ya tayar dani daga barcin da nakeyi nayi mamakin kirana a wanan lokacin da yayi.
Bayan na karba mun gaisa ne yake tambayana idan maryam tana nan don Allah zai aiko Sani driver shi mu taimaka mu sayo mai abin girki a gidan shi.
Da sauri nace mai kaga malam bafa zaman ka nake a garin nan ba da zaka dora min nauyi irin haka a kaina ina matar ka kaje ka tura ta ta sayo ma mana .
Don Allah kiyi hakkuri ku taimaka min for today only naji nace na kalli maryam dake barci nace yanzu yau friady muna hutawan mu ya dauko wahala ya dora muna kuma.
Ban sake komawa barci ba motsina ya tayar da maryam nan nake fada mata abinda ya bukata da mu tace to may ye a hakan khadija ?
Ai taimako ne kin san matar shi ba wani wayewan kaine da ita ba kuma kin san gata da ciki baki yanzu nace wanan ai ba excuse bane.
Son dorawa mutane wahala kawai yake yi don kada a zauna lafiya muna zaune kalau zai dauko wahalan gidan shi ya dora muna.
Kin san may khadija nace aa cikin kada kaina tace walahi sai nake ganin wanan Abduldin yana bukatan taimako a rayuwan shi.
Bai samu macen da ta dace da irin halin shi bane har yanzu yasa komai yanzu yake bukatan taimakon ki ban san yaya zaiyi ba ranan da zaku rabu dashi tunda kince ba soyayya bane a tsakanin ku.
Nace ai ke kin fi kowa sanin hakan shiya san yadda zaiyi don ni bashi ne a gabana ba karatuna ne ya damay ni inga na kammala Allah yaban sa,a in samu aiki da wuri.
Duk da haka khadija akwai matsala ranan rabuwan ku kan inda ran mu zamu sha kallo nace in babu sai abaku labari ai.
Tace labarin taimako ya juye ya zama soyayya haushi maganan ta yabani ban samu bata amsa ba naso ta biye min kada muje ko ina ya karata can da halin shi shiya sani.
Karfe uku bayan an fito sallah jumma,a sai ga malam sani driver yazo daukan mu nan yaban kudin yace wai zamuyi waya dashi.
Muna hanya ya bugo min yana fada min duk wani abinda muka sani ana amfani dashi a fannin girki har nama da kaji da sauran su mu sayo mommy ne ke bukata a gidan.
Kai dama duk wanan abin ba a saya a gidan ka may kuke ci a gidan silly girl ya fada ya kashe wayan shi naja tsuki.
Mun shiga kasuwa maryam tayi kaca kaca da kudin komai mun hada sai yamma lis muka baro cikin kasuwan inda ya fara sauke mu a hostel ya wuce bayan hilux din su acike muka bashi sauran kudin shi ya kai mashi canji.
Wanka nayi tea kawai nasha da nai sallah muka samu wuri muka kwanta don gajiyan da muka debo a kasuwan bamai taimaka wa wani a cikin mu duk a aikin sa kai da mukayi.
Barci yana batun dauka na wayan shi ya shigo min jin murya na yasa yace har kin fara barci ne ko may ?
Nace ba dole ba yau an samu wahalan da ba namu ba lada ba zunubi sai tarin gajiya khadija ke wace irin yarinya ne wai da ba tsoron fadin magana a bakin ki ?
Yanzu dai ba wanan ba don may kuka ba sani ragowan kudin da ya rage yakawo min kuma ya fada min komai baku sayo wa kan ku ba ku.
Saboda ba hakkin mu bane yasa muka bashi yakai ma kudin ka don Allah barni na huta malam gara da kai kana da madafa.
Murmushi naji yayi yace ina dashi tunda ina da matar da zan runguma inji sanyi ke ko sai dai ki kama filon ki ko ?
Kaidai ka sani nace mai sai da safe yace ba zaki tsaya nayi maku godiya ba zaki kashe min waya ?nace ai ba don ka gode muna muka taimaka maka ba na kashe wayan gaba daya.

A gidan shi ya iso da kayan akai ta shiga dasu ciki shi kanshi yayi mamakin yawan kayan da muka sayo din ya kira Nafisa kafin ta sauko ya kira mommy da kanshi kan tazo idan akwai abinda babu sai a sayo gobe.
Nafisa na zuwa mommy tana fitowa tare dashi yake tambayan ta ta duba ta gani ranta a bace tace komai yayi sai mommy tace komai an sayo sayayya haka kamar na mace.
Nafisa da ta juya zata tafine ta juyo da sauri ta kara kura ma kayan ido tana kallo kayan da bata kalla ba da farko saboda idon ta ya rufe da masifa a lokacin.
Maganan mommy ne ya tsaya mata a rai da tace sayayya kamar mace tayi komai an saya yadda ya kamata ta kira hadiye da yanyala wai su kawar da kayan wurin tana daure fuska gata mai gida.
A daki ta samay shi zaune lokacin muna waya tace gurin ka nazo ya aje wayan da na kashe yana kallon ta ta samu guri ta zauna da kyat.
Tausayi ta yaji ya dirka mai a zuciya tace may kake nufi da baka shawarce ni ba ka sayo wanan kayan haka sai da kasayo abinka zaka kirani.
Yace saboda baki damu da asaya din bane yasa na sa a sayo min tace wace yar iska ce ta sayo ma cikin kura mashi ido da son jin amsa daga gare shi.
Wanan ba matsalsn ki ba ne ke dai kiji da kanki ya fada mata yana kokarin mikewa tsaye samad mai kake nufi dani ne wai ?
Da akayi may kuma yanzu tace ban fa gane inda ka dosa ba gaskiya da irin wanan halin naka yace saboda baki son gaskiya ne yasa na canza nima.
Kana nufi nice mai laifi yanzu aike ma kin sani idan kina son mu shirya dake to ki canzs ke ma yaushe rabon da na karya a gida na in ba yau ba da mommy tazo.
Dama nasan abinda ya kawo su ke nan ai hadin fada a tsakanin mu in bashi ba may zai sa su kwaso kafan su suzo nan wai sai na haihu.
Yace saboda ina dan su kuma ni na bukaci haka a gare su tunda ke baki san komai ba sai bakin yawo da lalaci kawai da kashin kudi.
Nice mai kashin kudi murushi yai mata yace ko yanzu ma nasan amsan kudin ne ya kawo ki ai ba wani abu ba tunda baki damu da damuwa na ba.
Kaine dai ai naga kamar kana gudana yanzu nan dai suka shirya ranan ace tsakani miji da mata sai Allah suka manta da komai a ransu.
Washe gari mommy ta sake hada masu break fast mai rai da lafiya tasa Aisha ta gyara dining din aka jera kkmai a yadda ya dace ta aikawa su hadiye da nasu.
Tare suka sauko suka karya a tare sai hadiyan abincin take ba kunya ko wani nauyi a tare da ita bayan sun gama ya fita zuwa wurin aiki.
Sai lokacin Nafisa ta kalle gefen dakin da su mommy ke ciki ta kira hadiya ta rufe mata kofan kitchen da store din gidan gaba daya.
Da rana mommy ta turo Aisha ta gyara mata kitchen din sai ta samu gurin a rufe ta koma ta fada ma mommy.
Mamaki ne ya kama mommy ta kira hajiya mama tana fada mata abinda Nafisa tayi masu ita kuma mama ta kirashi inda take shiga ba nan take fita ba tace maza ya dawo dasu gida tunda yasan gidan shu ba a hannun shi yake ba ya dauke su.
Hakkuri ya fara bata yace zai dauki mata hakan tace ya yake son yi idan Abban su ya samu wanan baki labarin dama abinda yake ma gudu ke nan ya hana su zuwa tu farko.
Hakkuri ya dinga bata har ta saurara mai tace tana jiran taji matakin da ya dauka a gidan idan ba haka ba zata fada ma Abban su abinda ke faruwa kada yaji a gurin wasu.
Yusuf yana zaune yana sauraren su yana kashe waya ya dago idon shi da suka kade sukai ja yace wai may Nafisa take nufi da nine ?
Guri ta samu take wanan abin mana Yusuf ya bashi amsa yace in bashi ba rashin mutuncin nata har yakai ga su mommy kuma yanzu.
Mommy ne zata rufewa dakin girki bata girka ta basu ba basu damu ba suna yi kowa kuma yaci har zata rufe kada suci su kwana da yunwa komay ?
Tasan yadda Abba yake ji da iyalin shi kana zaton da ba mommy bace in anty amarya ce Abban zata kira da kan shi ta fada mai kasan ko yau ba zata kwana gidan ka ba.
Wallahi idan zaka kara aure ka kara shine kawai mafita ga wanan shu,umar mace da ka dauko wai mata bazata taba ganin darajan ka ba idan ba ta bude ido tagan ka da wata mace ba a gidan.
Idan tana zama ta zauna in bata zama kuma ta kara gaba dama ba akirata ba kutse ne da sa kai irin su ta kallamay kada dadin baki da komai ta aure ka.
Kai yace tare da bugun tabur din gaban shi ya mike cikin fushi Yusuf yace ina zaka kuma yanzu ?
Gida yace cikin wani irin murya kamar mau zazzabi shima mikewa yayi ya bishi a baya tare suka fita daga office din shiya jasu don Abdul

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login