Showing 117001 words to 120000 words out of 133935 words

Chapter 40 - Mijin Buzuwa Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

274

kuma ya koma biya , ?
Mu da mukazo aikin lada zaka saka muna da wanan irin alherin haka mai yawa gaskiya hakan bai muna dadi ba gaba baka son inzo zama da diya ta ke nan in Allah yayi abin.
Murmushi yayi yace ko baku zo nan ba mommy zan iya maku fiye da hakan don haka wanan ba komai bane Abba yace a tura ku gida yau kafin in wuce.
Nasan ya kiraki ya fada maki komai ai don haka idan da sauran wani abin sai ku fada min a sayo maku kafin ku wuce na kuma gode kwarai da kokarin ku a kaina.
Sai dai ayi hakkuri da yanayi matar gidan don Nafisa sai hakkuri nima dai kun ga shinakeyi.
Ka dauki kudin nan ko ka rage dawainiyar yayi yawa haka abin ya zama kamar biya mu kayi ke nan ya mike yana murmushi yana fadin ba komai iyan bawa ai yima kaine.
Na shirya driver da zai sauke ku idan kun gama sai aimin waya zan dan leka office don tafiyan mu sai dare zamuyi shi akwai dan sauran lokaci zuwa yanzu.
Godiya sosai sukai mai ya fita nan dai mommy suka fara shirin tafiya don ba a ketare maganan Abba a gidan.
Yana fitowa bai koma ciki ba ya nufi hanyar fita daga gidan muryan Nafisa yaji a bayan shi tana fadin dama nasan abinda ya zaunar da su ke nan a gidan nan tun bayan suna basu tafi ba kamar yadda kowa ya wuce.
Suwa ke nan kike nufi wanda kasai wa kaya bada sani ba yanzu Allah ya tona ma asiri na gani do baku so in gani ba.
Wai nafisa kina da hankali kuwa iyayyen nawa ma bakin ciki kike dasu akan nayi masu alheri tace ai ba su kadai suka wahala a gidan ba har dasu Yanyala sun wahala .
Don may ba zaka saya masu tare ba ka ware naka kadai watau sune ka sani ke nan kai ya girgiza cikin kunan rai yace ba laifin ki bane sai kawai yaga ta sha mai gaba ta inda zai wuce ta.
Hayaniyar su ne ya fito dasu mommy waje ganin su mommy ba sa ta fasa ci mai mutunci ba mommy ce ta hana shi magana.
Duk ta hade dasu mommy tana zagi tare da fadin tayi ma kowa nashi iyaka da gidan tun da ba zuwan arziki suke yi ba jifa samun wuri a gurin wanan matar ita ha gida taf da yan uwanta kullun sai kara yawan su takeyi a gidan.
Kowa yazo da sunan ganin ta sai ya nemi wuri ya zauna ba maganan zuwa gida kuma gare su an shafe ke nan.
Haka ya fita gidan ranshi bace ranan su mommy sun ga fitsara a gurin Nafisa inda tayi ta aiban ta su suna ji suna gani ba abinda zasu iya yi tana gani taci gaban su.
Ranan haka dai ya wuni cikin bacin rai halin Nafisa ya jutayin irin zaman da suke na rashin jin dadi a gare shi kuma bai jin zai iya rabuwa da ita ko kadan.
Bayan su mommy sun gama shiri suka kirashi yace gashi nan zuwa ya samay su a shirye don haka basu bata lokaci ba suka fito da kayan su Yusuf suka loda a mota sukai sallama dasu suka tafi suna kara bashi hakkuri.
Da yamma ya fito cikin shirin shi ya samay ta a dakin ta tana zaune tana waya ganin shi bai sa ta katse wayan ba sai data gama yake fadin su zasu tafi.
Wani sabon lalura ta kirkiro mashi aladole kudin da take hasashen ya kashe ma iyayyen nashi sai ya kashe mata su bayan ya riga da ya sallamay ta da safe ta lissafa mai abinda take so ya bata.
Nafisa wai may zakiyi da kudin da kike karba ne haka ya tambaye ta wani kallo tayi mashi tace idan zaka bani ka bani ba sai ka tsaya ka tambaye ni ba kuma ina sin idan ka dawo zan tafi gida inyi gyaran gidan mu na can.
Dole ya bata daga cikin kudin da zaiyi amfani dashi don kawai su rabu lafiya da ita.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Tun bayan rabuwan mu dashi ban kara jin labatjn su ba haka yasa nasan sun tafi ke nan tun tafiyan su kuma ban sake ji daga gare su ba bakuma labarin mamud.
Duk da son mamud da nake a zuciya na yanzu na fara fitar dashi a raina don na fahinci ba wani son gaskiya yake min ba .
A cikin haka muka gama exam din mu na wanan zangon kaduna ya kamata in tafi amma don gudun haduwa da mommy a can yasa na kekeshe kasa nace ma Ya Amina ba zan tafi can ba gida nake son yin hutu dole ta kyale ni don tasan tunda nace haka ba zan zo ba.
Tunda na dawo gida in ba islamiya ba ban fita ko ina don haka ba kowa ne yasan ina garin ba yau satina biyu da zuwa gida na shirya zuwa gidan anty mu dake aure a falamingo easthe.
Tare da karamin kanina muka fito daga gida mun zo bakin titi inda zamu tare Napep din da zai kai mu unguwar nasu mun dan tsaya a gurin na hango wata mota daga can gefe tafe.
Zuwa mai shi yayi roud ya dawo inda muke tsaye da kanina a hankali yazo inda muke tsaye ya tsaya ban daga kai na kalle shi ba wata taxis tazo tana tambayan inda zamu.
Sai lokacin na cikin motar yace wai ba khadija bace wanan a hankali na dago ina kallon shi mamud ne ya kara yin fresh dashi har bakin shi na sheki.
Ya samu wuri ya parka motar shi da kyau ya fito daga cikin motar zuwa inda muke tsaye tare da fadin hajiya khadija ke nan ashe kin shigo garin namu.
Nadan yi murmushi nace mamud manya ashe kuna kasan na dauka baka kasan murmushi yayi yana fadin i am sorry wallahi na bar Abuja ban samu leka wuri ki ba sai yanzu gashi mun hadu.
Mun gaisa duk da ban wani sake mai fuska ba sai kame kamay yakeyi yace ya labari nace kai za a tambaya kai dana ga sauyi a tare da kai.
Yace sauyi gare ni ko a gare ki jifa yadda kika koma dan kwana biyun nan danayi ban ganki ba kin koma wata danya dake kamar wata diyan larabawa wai ma ko kina karatu kuwa ?
Dariya nayi nace kai mamud bari bani dariya haka akan titi muke fa yace haka fa ina zaku naga kamar mota kuke jira nan.
Filamingo easthe zamu na fada kai tsaye yace muje in sauke ku nace ka barshi kawai zamu samu taxi anan yanzu .
A a khadija kada muyi dake please ai ko ba siyasa akwai daga hannu ko dariya nayi nace ashe dai hausa ya zauna a bakin ka haka ?
Yana dariya muka taka zuwa bakin motar shi ya bude min gaba na shiga ya bude baya mansur ya shiga ya zagayo ya shiga mazaunin driver ya fara tuki.
Mun dau hanya yace van san yaya zan fara maki bayani ba ma sai dai da farko na gode da kika fahince ni har baki nuna min komai ba haka.
May kake son in nuna maka gudu da kayi daga wuri na ko may yace wallahi khadija ba laifi na bane ba naki bane.
Laifin waye na tambaye shi cikin kallon fuskan shi yace ba zaki gane bane khadija amma tunda kina gari zanzo har gida in maki bayanin komai.
Nace kasan gidan mu ne yace zandai sani yanzu daga bakin ki idan kin bani dama can kuma yace gaskiya khadija kin kara wani itin kyau da girma a lokaci daya.
Nace kai mamud wanda ke karatun wahala kake fadan haka gareshi dan kallo na yayi yace kin ko ga yadda kika koma kuwa ?
Ina dariya na kalle shi nace yaya na koma kuma ya dan bugi sitiyarin motar da hannun shi yace I don't know how to say.
Amma ai kema kin san kin sake gaba daya wallahi nace dama ance ku Nufawa mayu ne to kurwa na kur kada ku cinye ni.
Dariya yayi sosai yace amma kin kusa gama karatun naki ko yanzu dariya abin na mamud ke bani don na gane nufin shi sarai.
Katse shi nayi da fadin ina madam din ka ya fadada murmushin shi yace yaya akayi ki san ina da aure yanzu ?
Nace tambayan ka ai nayi suna lafiya yace lafiyan su kalau wallahi daidai lokacin muka shigo Filamingo din da kwatance har muka iso kofan su antyn nawa.
Godiya nayi mashi ina bude kofan motar yace khadija na juyo ina kallon shi cikin jan aji yace wani time zaki koma gida inzo in dauke ku ?
No ka barshi kawai mun gode da hakan sai anjima nafita daga motar Mansur kanina ya kira yasa hannu a aljihun shi ya ciro kudi ya ba yaron ya tafi bayan yayi min horn.
Gidan Ya Hauwa muka shiga da sallama na bude labule falon su da danta babba na fara cin karo zai fito yana ganin mu ya saki ihu yana fadin ga mommy khadi .
Murmushi nayi ina kamo shi nace Lawal kaine ka girma haka ina yan uwan ka yace suna ciki jin ihun yaron yasa Ya Hauwa ta fito daga kitchen din su tana fadin sai yau kika ga daman zuwa gidan mu ?
Haba dai ya hauwa kema kin san ba halina bane haka na dawo da gajiyan karatu ne wanan karon na dan tsaya in huta.
Mansur ne ya gaida ita tace a a mansur tare kuke tafe da antyn naka ashe nace ai kin san mutumi nane shi nan dai muka zauna a falon shi wanda ke bukatan gyara ba halin yin hakan gare su don yanayi.
Ranan ni na girka masu abincin rana a gidan yaran suna ta murnan kasancewa tare da mu bayan na gama na gyara mata gida don haka take ba gwanan gyara bace ita amma idan ka ganta a waje sai ka dauka ko agidan ta haka take da tsabta.
Ranan sai magariba muka koma koma gida na samu daddy yana fadan rashin dawowan mu da wuri gida.
Muna shiga ya mayar da fadan da yake wa mama akan mu may yasa na bari nakai wanan lokacin ban dawo gida ba idan na fita kada in kara kai dare haka bamu dawo gida ba .
Kaina yana sunkuye a kasa na amsa da toh daddy daga haka ya fita daga gidan rai bace buta na dauka naje na kewaya na dawo na daura alwala don har an sallamay sallah a lokacin.
Sai da na idar da sallah na gaida mama da gida da take dakin ta zaune saman sallaya tana jan tasbaha.
Tace khadija may yasa kuka kai wanan lokacin a waje haka kika bari har magariba yayi maku a waje haka baki san fita a wanan lokacin baida kyau ba.
Mama kuyi hakkuri ba zan kara kai haka ba tsayawa nayi gyara ma ya hauwa gida shine yasa mukai wanan lokacin a can .
Tsuki tayi tana kawar da kanta tare da fadin ita ke nan malalaciya bata iya gyaran gida kullun sai dai ai mata ina amfanin a ganta a waje fes amma a gidan ta baya kalluwa.
Ban san inda ta dauko wanan hakin nata ba nidai nasan na koyar daku abinda ya dace koda kun kama dakin ku zaku iya kulawa dayi amma sai dai kayya bata dauki wanan tarbiyan dana baku ba ita.
Wanka nashiga don inji dadin kwaciya saboda yau na aikatu a gidan yar uwar tawa bayan na fito na tayar da sallah isha,i mama ta turu yaro wai idan na gama inje in debi abinci nace a koshe nake munci abinci gidan ya hauwa kafin mu dawo gida.
Wani yaro ne ya shigo yana sallama da bazan iya sheda muryan yaron ba yana fadin wai ana sallama da khadija a waje.
Da mamaki daga cikin dakin da nake, nake tambayan yaron ko waye yace shima zai wuce ne ya aiko shi don haka bai san ko waye ba.
Jekace dashi tayi barci yaron ya fita can sai gashi ya dawo yana fadi cikin daga murya wai yace kiyi hakkuri kizo minti biyu .
Na fito daga dakin ina fadin bana ce kace dashi nayi barci bane yaron yace na fada mashi yace indawo in fada maki haka.
Zan sake magana mama tace da yaron ya tafi ganin nan zuwa tace kije giga kowaye kin san damay yazo gurin ki wulakamci bai da kyau ina fada maku.
Hijjab na dauko na aza saman rigar dake jikina na fita tun daga nisa na gane motar mamud ta dazun da ya dauke mu dashi.
Mamakin abinda ya kawo shi nake yi da wanda ya nuna mashi gidan namu yazo yana ganina ya fito daga motar zuwa guri na.
Bayan mun gaisa ne yace kin yi mamakin hani na yanzu ko nace kwarai kuwa yace to kibar mamaki don abin jiya na dawo maki dashi.
Da sauri nace meke nan sai da yayi murmyshi yace khadija ke nan So mana da kaunar ki khadija don tun dazun dana ganki na kasa natsuwa tundazu na kasa control din kaina akan ki abin ya dawo min sabo yanzu a raina.
Mamud ke nan abinda ya wuce ai ya riga da ya tafi don ni kuma sai naji yanzu sam baka kwanta min ba a raina.
Da sauri yace saboda may khadija nace halinka bai mun a yanzu don ba zan kara yarda ka sa min miki a zuciya ba.
Kasan ina son ka da farko mamud sai da ka bari na gama yarda dakai ka gudu ka barni babu bayanin komai daga gare ka Allah ya taimake ni, ni ba mai sa abu ga zuciyana bane .
Khadija ba haka na bane wallahi don koda muke tare dake already ina da mata karawa nake son yi sai kuma naje ma iyayyena da maganan ki amma sukaki banin goyon bayan haka don basu son in auri wace ba yaren mu ba.
Kin ga kuma bazanki maganan iyayye na ba sai naji kunyan komawa gare ki in maki bayanin halin da nake ciki .
Katse shi nayi da fadin basu sona yanzu may kadawo yi wuri na kuma yace ina da daman yanzu in zabi wace nake so tunda ina da yaren mu mutum biyu .
Kai na girgiza tare da fadin mamud kasan tun farko ban kika ba kai da kanka ka guje ni yanzun kuma baka da bakin cewa ka dawo gare ni.
Ko banza na farko ba zan shiga inda ba a sona ba sai na biyu yanzu ni mai zai kaini wurin mai mata biyu in ba daukan magana ba.
Dariya yayi a lokacin tare da fadin khadija ke nan watau kin mayar da laifin a gare ni ni daya to naji na dauka kuma ki kwantar da hankalin ki ba a gida daya zan ajeki dasu ba.
Don haka ai min hakkuri muci gaba kamar yadda muke da don son ki yana son ya min illa a rayuwana.
Mamud gaskiya sai dai kayi hakkuri don ba zan iya ba yanzu gidan ka yafi karfi na da sauri yace what ?
Nace yes I mean it don bazan dauki wanan risk din ba da hankali na ina ji ina gani.
Shiru yadan yi na dan wani lokaci kafin ya dago kai yace is ok naji amma zaki yarda ina kawo maki ziyara lokaci lokaci don ban sani ba koda rabo na ciki.
Dadai kayi hakkurin kamar yadda nace dakai zafi kyau don ban son ka dinga wahal da kan ka yace ke kika dauke shi a wahala.
Ni abinda nake so ne na damu dashi don haka ban hakkura ba ki sani nace wanan kuma matsalar kace ni dai na fada ma gaskiya.
Bai dade ba mukayi sallama ya tafi na shigo gida alwala nayi na gabatar da shafa,i da wuturi na samu wuri na kwanta.
Amma ranan sai barci ya gagari idona saboda tunanen dayayi min yawa a lokacin a raina nace ohh ni khadija haka rayuwa zai kasance kuma sai masu mata ne ke zuwa ne mana ni ban san ko may yakawo haka ba gare ni.
Gashi ni kuma banda sha,awan auren namiji mai mata don ban son yawan fitina daga anayi a gidajen masu mata nasan da laifi nane kin kula samari amma yanzu ban san dalilin rashin samun su ba, da haka har barci ya dauke ni ban sani ba.

Matafiya umurah sun sauka lafiya don haka yan uwa da abokan arziki suke shigowa gaida shi gidan shi wanda ba wasu mutane ke zuwa ba don sanin hslin matar gidan da sukayi sai wa yan da ya zama ma dole sai sun zo ke zuwa gaida shi.
Bata san cewa Fati ta koma dakin ta ba sai a bakin wani abokin shi da yazo yana mashi sherin yaushe zai leka can kaduna yaji ance fati na gidan shi yanzu.
Wani kallon mamaki ta aikawa AA din sai da yasha jinin jikin shi don yasan akwai rikici babba yau a tsakanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login