Showing 48001 words to 51000 words out of 133935 words

Chapter 17 - Mijin Buzuwa Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

259

motar kafin ya tafi.
Yaran suka ruga da gudu suka dauki ruwan leda suka sa a plate suka fita dashi waje kamar yadda mama tace dasu ta wuce tabar ni tsaye a gurin.
Dakina na nufa tare da dan hand bag dina dake rike a hannu na rai na babu dadi ko kadan a tare dani ina fadin yaya wanan mutumin zai min haka ya hadani fada da iyayyena su fara zargina.
Anty khadija wai yace a fada maki zai wuce nace ya kice Allah ya kaishi lafiya nace a hasale yaron ya fita da gudu daga dakin zuwa fada mashi.
Daddy ya shigo gida yana fadin ance baby na ta dawo sai kuma yaja ya tsaya yana kallon kayan da mamaki dake zube a tsakar gida.
Mama tace kai nake jira dama kazo ka gani ko zata fada ma inda kaya ya fito haka don wai ita ma bata sani ba tace kuma su sukazo da kayan.
A sanyayye na dago labule dakin na fito ina fadin daddy sannu da dawo wa mun samay ku lafiya ?
Lafiya baby na sai dai wanan kayan kuma fa ina suka fito haka nace wallahi daddy ban san da su ba sai da muka iso na gansu.
Kamar yaya bakin san dasu ba bake kika zo dasu ba sai nayi kasa da kaina ban yi magana ba kuma kayan yake bi da kallo tiryan tiryan yace ikon Allah.
Shiga ciki ki huta zamuyi magana anji yanzu zan tafi inyi sallah ne ya wuce gurin da buta yake yana dauka ni kuma na sake labule na koma ciki jiki a sanyayye.
Na fada saman gadon dakin duk da kuran da yake ciki don ba gyara ake ba a kai akai tunda ba kowa a cikin sa ina zaune kamal kanina ya dawo shiya fara shigo min da kaya yana min sannu da zuwa.
A dadafe na amsa mai ina kallon akwatinan daya shigo min dasu akwatunan da muka sayo a daren jiya ne dashi inba idona ke min gizo ba.
Watau kayan de na yan gidan mu ne kenan ba wasu ya saya wa ba mikewa nayi don in yo alwala ina shiga banda ki sai na samu ai period dina yazo min ba daman inyi sallah ke nan haka na fito jiki a sabule na aje butan.
Sai mama ta aiko da abinci a kawo min ban kali abincin ba nace kaunata ta aje min a nan kawai ina jiran dawowan daddy daga wurin sallah.
Envelop din da driver yaban na tuna dashi na dauko a cikin jakata na bude a hankali kudine a ciki sabbi ful din su anyi rubutu kamar haka a wrafer farko daddy sai na biyun mama.
Na ukun ne bai rubuta komai ba na shiga uku nace tare da yin nadama da haduwa da shi karo na farko a rayuwana don ban san yadda daddy da mama zasu fahince ni ba.
Nayi dana sanin tsaya jiran shi da yace inyi har na tsaya din sam ban kawo komai a raina ba irin haka don ban taba zaton hakan ba dayayi min.
Muryan daddy daya shigo naji ana gaida shi yasa ni kaduwa bai min magana ba har yaci abincin shi ya fita haka na tashi na gyara dakin tsab na fita da na wankewa na wanke a ranan.
Na dawo na sa kamshi a dakin tare da gyara komai a yadda nake bukatan shi a dakin na koma na zauna wayan maryam ne ya shigo tana tambayana yaya muka isa ?
Nace wai kin san abinda mutumin nan yayi mun kuwa maryam nan dai na koro mata labarin abinda ya faru bayan isowar mu gida da driver.
Tace ikon Allah sakayyan da yai maki ke nan ashe kai lallai mutumin nan yaci sunan sa dan Baiwa ne shi din.
Nace ke maryam har kin samu bakin yabashi ko may may kike son in fada ma iyayyena yanzu don Allah wa zance yake gare ni da yai min wanan kyauta haka.
Tace ki fada masu gaskiya taimakon shi kikayi ya saka maki da alheri haka nace ban sin su san ko shi waye tundai Ya Amina .
Dariya tayi tace komai dadewa ai zata sani ne nace amma fa ba yanzu ba koda zata sani din don ban son ta fasara ni da wata manufa.
Har dai dare banji daddy yayi min magana ba haka yasa na dan sake jiki naji shigowan daddy gidan sai na sha jini jikina a daki ban fito yadda na saba muyi hira ba dashi.
Ina nan kwance wayana yayi kara na dauka kamar yadda na rubuta a sunan shi dan Baiwa shi ya baiyana a wayan.
Kamar ba zan dauka ba dai na daga maimakon inyi magana sai na kama kuka nace may yasa zakai min haka don Allah ?
May kake son in fada ma iyayyena yanzu a kan kayan nan yace daddy na gida nace yana nan yace dama shina ke son magana dashi na kira ki yanzu.
Da sauri nace may zaka fada ma daddy din yace gaisawa nake son muyi dasu in masu bayanin kayan ba shike nan ba.
Yasir na kira nace ya kaiwa daddy waya ana magana dashi ban san yadda sukayi ba a wayan har mama naji suna gaisawa da ita.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Washe gari muka shirya zuwa beji duba wani kakan mu dake zaune acan kanin mahaifin maman mu ni da ya Amina da yaran su.
Bayan Nkwa bamu iya wani gaisuwan kirki ba sai habalu da sauran kananin kalma irin na gwarawa da muka rike a bakin mu.
Tsohon yaji dadin ganin mu yana ta murna da zuwan mu gidan duba su anan muka wuni tare da su sai yamma muke son mu dawo mu biya maikunkele gidan iyayyen mama din.
Tsohon bagwaren yana waje zaune da bakon shi muka fito zamu wuce muna masu sallama bakon nashi ne yayi yare sai naga tsoho yayi dariya tare da fadin yaki nan amarya na.
Nazo na duka a gaban shi yace bako na ne ke son ganin ki sai na gaida dattijo ya mika min hannu alaman in bashi nawa hannun.
Ban ki ba nayi kamar yadda yace min sai da ya kalli tafin hannu na da kyau yayi murmushi yace Allahu akabar akwai tarin alheri ga wanan hannun naki sosai zan ba kaka ku wani abu ya baki gobe ba mai wuya bane abin inda zaku tsaya na awa daya zan iya hada maki ko anan ma.
Don tsari juyawa nayi na kalli ya Amina tace ai zamu iya tsayawa mu karba nan saman tabarman muka zauna ya bude jakkar shi ya ciro wani dan farin abu a wani kwanko yayi ta abinda zaiyi a abin sai ya miko min hannu na mika mashi nawa.
Ya fara murza min abin a tsakiyar tafin hannu na har saida abin ya bace bat a hannu na ya dan dade rike da hannu na yana min tofi har kaina sai daya dafa yayi min yadda yayi a hannun ya sake ni dama tsamin jikin shi duk ya isheni sosai.
Ya Amina ma tace aiwa yaranta da ita ba irin wanda yayi min yayi mata ba zamu tafi na bude jakka na fido dubu daya na bashi ya girgiza kai.
Yace idan ina da dari biyu in bashi kawai yaci goro dashi na duba naga wani sabon dari biyo na dauko na bashi nayi mai godiya muka tafi.
Muna cikin mota ya Amina tace na rasa may sa tun kina karama idan mun fita ke kawai mutane ke taimakawa wanan karo na biyu ke nan da haka ya faru dake.
Nace su suka san abinda idon su ke gani a kaina wanda mu bamu gani hakan dariya tayi tace kila ya hango maki buzuwan ku ne .
Kai ya Amina may yasa kuke fadar haka ne karfa maganan nan yakai kunnen su mommy da yan gidan su fa.
Tace indan ya kama suji ai ji zasuyi khadija lokacin jin su ne baiyi ba kawai amma duk wanda yaji mamaki zai yi wallahi.
Sai dare muka isa gida don mun bata lokaci a maikunkele wurin yan uwa da abokan aarziki ko da muka dawo wanka kawai nayi na samu wuri na kwanta abina.
Da safe muka tashi da labarin haihuwan antyn mu Anty Hauwa dake aure a pilamigo easther wanka mukayi muka nufi gidan ta acan muka wuni sai four muka baro gidan ta.
Koda muka dawo gida mama tana dora girkin dare sakwara zatai muna da miyan egushi tubewa nayi na fara taya mama aikin dakan sakwara don doyan ya dahu ko.
Ya Amina data fito dakin ta tsaya tana kallon yadda nake dakan sakwaran ta kwashe da dariya tace ashe kin iya idan nace muyi sai kice bakya son ci.
Sallaman da muka jiyo a kofan shigowa gidan mu ya hana ni bata amsa naci gaba da dakan sakwarana.
Anty Amina ce ta dan leka raga mai sallaman sukai kicibis da Yusuf a tsaye yana gyara rigar shi da ya dan takure ga zaman mota.
Kamar daga sama ta san shi a gidan su mommy shine dai bai santa ba tace cikin mamaki Yusuf kune tafe haka da yamman nan ?
Yayi mamakin sanin shi da tayi haka shi bai santa ba sai dai ya gane muna da kama da ita sosai sai dai tsayin da nafita da kuma hasken fata don ni daddy na fadin gidan mu na debo sosai ina da zubin fulanin su na ka,aje ne.
Ta juya tana fadin barin sanar da Khadija gata can yau sakwara take daka muna a gidan yayi dariya ta wuce ciki ina ganin ta shigo tana dariya ina rike da tabarya mama na duke tana saka wanda na daka a leda tace khadija ga ki da baki fa a kofan gida.
Da sauri nace da ita su waye ya Amina tace wa kike tsamani zai zo maki yanzu banda su Yusuf da abokin shi nace kai haba dai ya Amina may zai kawo su nan in ba gulma ba.
Tace to gulman ko ya kawo su gasu can a waje dai nace wai da gaske tace ina wasan haka dake ne dama tabarya na aje ina fadin yau na shiga uku.
May suka zo yi yanzu kuma don Allah tace kyaji idan kin fita ai ni wallahi sai naci masu mutunci don may kuma zasu biyo ni har gida haka ?
Harara mama ta watsa min tace idan zaki natsu ki natsu kije ki gan su falo ya Amina ta shiga ta fara gyara wurin inda zasu zauna ko kafin in fita na samay su da daddy suna gaisawa a waje na juyo na dawo ciki abina.
Har ciki daddy ya shigo dasu ina labe a dakin mu ina kallon su sai da suka shiga sun dade ciki da daddy da ya Amina kafin ta fito ta kwala min kira ban fito ba ta samay ni a dakin tana dariya.
Ya Amina may wanan mutumin ke nufi da nine wai for god sake may ya kawo su har gidan mu ne don bata min suna.
Kallona tayi da mamaki tace zuwa gidan ku shine barnan suna khadija ai gara da suka zo zai fi hankali mama ya kwanta.
Ni kan na shige su wallahi tace don Allah ki natsu kije ku gaisa sunce hanya ne ya biyo dasu nan suka ratso su gan mu.
Ina shiga na samu har da abinci aka aje masuz sai hira Yusuf keyi da daddyn mu shiko sarkin miskilanci ido kawai ya zuba ma kofan shigowa falo.
Da sallama nashiga tare da samun wuri gefe na zube gwaiwa na a kasa ina gaida su Yusuf ne ya amsa min shiko ido kawai ya zuba min kamar yadda na samay shi zaune.
Daddy ya fita falon yana cewa dasu yana zuwa ya fita daga falon bayan fitan daddy ban daga a yadda nake na dago ina kallon su nace may ya kawo ku may kuka zo yi gidan mu ?
Baiyi magana ba sai bude kula abincin yayi yana kallon sakwaran tare da fadin ke kika yi wanan abincin wai ?
Yaya akayi suka san haka nake tambaya kaina a zuciyana Yusuf ma budan abincin yake yana faadin yar mama ashe kin iya girki ne haka ?
Yayana may kuka zo yi nan yace gashi kinga munayi kawai dai mun yi marmarin cin girkin gidan ku ne mukazo muci dan harara na aika masu.
Abdulsamad din ne yace kina ganin zaki iya kashe min waya don kada na kiraki da sauri nace ni ba kashe ma waya nayi ba.
May yasa baki kuna wayan naki ya tambaya cikin kura min idanuwan shi dake ban tsoro yanzu nace wayar ce bata da lafiya.
Baiyi magana ba ya fara cin abincin ba ko kunya hankali a kwace nace baku da kunya ne zaku ci a binci a gidan mu ku wai wasu irin mutane wai ?
Ruwan abincin gidan ku zaki muna ya fada nace ni naci na gidan ku ne to yace wayasan iyaka wallahi ban taba shan ko ruwan gidan ku ba ni.
Yusuf yace saboda may yar mama yana kai lomar sakwara a bakin shi kunya su nake ji ban iya shan ko ruwa a gidan don nauyi.
Ashe ko kin cuci kan ki don ni dai a sani na gidan mu bako bai shiga ba a tare shi da abin sha ko na ci ba daddy ya kwala min kira daga cikin gida na mike na fita da sauri ya daga kai ya bini baya na da kallo.
Saurin kawar da kanshi yayi yana cin abincin da yaji dasin dan danon shi har cikin ranshi ina fita naga baba da leda ya sawo drinks.
Yace in kai wa baki a falo a tire na saka nakai na dire masu a gaban su nace gashi kun sa baba kashin kudi bai shirya ba.
Murmushi magana na yadan yi sun ci abincin sosai suka wanke hannu na fita da kayan bayan sun gama ne suka ce inyi masu iso su gaida mama zasu tafi.
Fita nayi na kira ya Amina ina fada masu abinda suka ce man ita ta fada ma mama zasu shigo su gaida da ta nan mama ta gyagyara suka a kofan daki aka shimfida masu tabarma suka zauna.
Bayan fitar sune na samay su a waje har sun shiga mota ina isowa Yusuf ya miko min waya kallon wayan nayi ina tambayan shi ta may yace ogana yace a baki tunda naki ta lalace kiyi maneji da wanan kafin ki dawo Abuja a sai maki wani.
Amma don Allah kada ki kara kashe muna waya mu kira bamu samay ki ba ran mu baya dadi rashin jin ki da bama yi a koda yaushe.
Kai na girgiza tare da fadin kubar wayan ku ni wayata lafiya take kashewa nayi kawai don, , ,
Ban karasa ba naji yace don kada kiji muryan mu ko may khadija nace kawai abubuwa ne sukai min yawa a nan bata waya nakeyi ba.
Yaushe zaki dawo school don hutu ya kara nake gani nace sai anyi sunar yayan mu data haihu zan dawo uffer week may zaki zauna yi har uffer week Abdulsamad ya tambaya.
Ba a gida nake ba tare da iyayyena na bashi amsa da hakan yace ranan tuesday zan turo a dauke ki yana fadin haka ya rufo kofan motar Yusuf yayi min sallama tare da kara mika min wayan suka tafi.
Azato sun tafi ne sai ga yara suna shigo da drinks da wasu abubuwa a kwali wai i ji su ina daki ina kallon wayan daya ba babban wayace mai tsada fara kwal da ita.
Ya Amina ne ta shigo dakin tana kallo na tare da fadin wai shi baya gajiya da wanan daiwaniyar da yake haka ne kuma kin ce ba soyayya kuke dashi ba.
Wayan da ya bani ne na miko mata ta karba tana fadin ta maye wanan kuma nace shiya bani do kawai nace tawa ta samu matsala ne yasa basu samu na .
Abin nayi ne ashe yanzu a ka fara wasan da ba ansan maci tuwo ba sai miya ta kare nace ba wani wasan da aka fara indai nice da na koma zan kakabe shi in huta da zancen su gaba daya.
Tace ai wanan da alama kin samu kaska baya kakabuwa wasan dadi don ko ya fiki dabara yanzu gashi ya gama daure ki a gurin daddy da mama ko.
No way to exscape daga tarkon shi a kwai game da na sani kan nan gaba din ba karamin aiki kika banbaro muna ba yarinya.
Kai ke ya Amina ke kekara ma abin wuta wallahi ni may zanyi da mijin da wata ke juyawa a gidan shi kina so in shiga nima in koma yar bi ce kamar fati ?
Ke zaki tsayane ki zauna kamar ita a wirin shi ta kai zaune tana fadin da farko ina tsoron abinda ke shirin faruwa tsakanin ku da shi.
Amma yanzu zuwa na gida da daddy ya wayar min dakai sai hankali na ya kwanta da zance nake ganin kece haske da zai yaye duhun da Abdulsamad din ya shiga.
Ya Amina ki bar wanan magana kimun fatan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login