Showing 123001 words to 126000 words out of 133935 words
ne sai ko masinjan office din nashi.
Muryan da yaji yana mashi sallama ne yasa ya dago a lokacin wani hamshakin Alhaji ne ya shigo office din tare da wata mata a bayan shi.
Yana ganin su ya kara daure fuskan shi tare da amsa masu sallaman su wuri suka samu suka zauna tare da fara gaida shi hakan yasa ya aje aikin da yake a lokacin yana fuskatar su.
Bayan sun gama gaisawa ne mutumin ya fara magana da cewa yau ma gamu mun dawo gare ka bayan wahalan da mukasha kafin mu iso gare ka.
Cikin daga hannu ya dakatar da mutumin ga maganan da ya fara yace Alhaji na fada ma wanan business din ba zai yuyu ba tun farko.
Ba haka muke sake fili ga mutanen da basu san darahan shi ba suna gina abinda suka ga dama a cikin gari.
Mutumin yace ba zancen gina wancen company a yanzu gare mu ni buri na kawai a yanzu shi ne in mallaki filin nan isan yana a matsayin nawa ne.
Zan baka ko nawa kake bukata muddin zaka yarda ka saka min hannu in malaki daga milayan daya har zuwa hamsin zan baka idan kana so don wallahi ina , , , , ,
Table di gaban shi ya buga tare da mikewa tsaye yace na fada maka tun farko ba haka nake aikina ba kada kayi tsamanin da cin hanci ire iren ku na dogara.
Ina da abinda zanyi a wuni daya million dari ya shigo min a accout dina ba tare da nasha wani wahala ba nafison in ci halan dina da na tsaya amsan cin hancin ire iren mutane irin ku.
Matar ne ra katse shi da cewa ba wai cin hanci muka kawo maka ba kanina ka sani gogi bai ki kari ba balle mutum mai lalura da jama, a irin ki ko yaushe.
Ina son ki sani wani gogin ne ke son kari wani ko an zuba mai wani ruwan aman shi yake yi don ba wurin zaman shi yazo ba.
Don haka na roke ki ku fita min office yanzu ina da abubuwan yi a gabana da yawa da zanyi kada ku bata min lokaci.
Matar zatai magana don ranta ya gama baci a lokacin mutumin ya daga mata hannu yace barshi mu tafi Allah ya bashi hakkuri bata mai rai da muka.
Ya mike yana fadin mun barka lafiya sai dai ka sanin haka ba zai sani fushi dakai ba don abinda nake so nake nema a gare ka.
Kuma ka sani ni ma ba irin mutanen ne da kake zargin suna sayen filin gwanati su gina abinda bai dace ba dashi nima kamar yadda zuciyar ka yake fari a kan kasan ka haka nawa zuciyar yake fes ga komai.
Do haka mun barka lafiya matar tace bai kamata kana saurin yanke hukunci haka ba akan abinda bakai bincike akan shi ba.
Binsu yayi da kallo har suka fice a office din nashi wani iri tsuki yaja tare da dafe kan shi da hannu shi daya yana fadin wai may mutane yanzu suke daukan kan su ne ?
Yana jan tsuki tare da bude file din gaban shi yana gyara zaman shi da kyau Yusuf ne ya turo kofan ya shigo da sallama ciki.
Tun daga nesa yake kallon yanayi abokin nashi yace may kuma akayi naga yanzu yanzu ka sauya gaba daya mana ?
Bai yi magana ba sai duban files din yaci gaba dayi wuri Yusuf din ya samu ya zauna yana fuskanta abokin nashi tare da kara maimaita tambayan shi gare shi.
Yace wanan mutumin mai bakin nacin tsiya akan sai ta mallaki filin da yake so mu bashi ne ya sake zuwa yanzu tare da wata mace dake son karanto min hauka.
Wai har ni zasuce zasu iya ba daga million daya zuwa dari don dun mai dani mubukaci ban san ciwon kaina ba ko may ?
No ba haka bane wasu ne ke bata wasu ga alumma shiyasa suke daukan haka ga kowa idan da sun san ko kai waye da ba zai tunkare ka da wanan zancen ba.
Kai din ne ka faye boyon kurwa ga jamma, a kaki fitar da kan ka fili mutane sunan kokai waye may zai hana irin mutanen bazasu dinga tunkaran ka da suna baka ci hanci ba ko yaushe.
Murmushi ya sake a fuskan shi yace dole ne sai na fito na nuna ma duniya ko ni waye san nan zasu sani kana ganin ko a gidana da matsalar Nafisa kawai bai isheni ba yanzu.
Ni ba wanan ba ma gida nake son ka sama mun mai dakuna da yawa inda zan sai wa yan uwata su koma nagaji da zaman da suke min a gida na wallahi.
Mutum da gidan shi baida halin ya huta yaji dadin gidan nashi sai a hana shi shaka wanan abin yana damun raina sosai wallahi.
Ya zakayi abinne sai hakkuri tunda yan uwar matakar ce kaga ko don yar uwasu zasu zo gidan da son ka ko ba da son ka ba.
Iska ya furzo daga bakin shi tare da ci gaba da aikin shi yayin da Yusuf yake dan tunane a zaune a gaban shi.
Can ya dago kai yace ina ganin fa hutun su khadija ya kare don haka nake ganin tana garin nan duk yadda akayi yanzu ta dawo school din.
Ummm nima abinda nake tunane ke nan do hutun su ya kare ai ita ba zata iya neman mutane a ida take ba tana jira a nemay ta ko ?
A, a kaiko yaya zata nemay ka kafa san halin mata da jan ajin su ko yaushe aji kawai take ja muna ita ma a matsayin ta na mace.
Ashe ko zata tsunke idan nine ya fadi ba tare da ya dago kanshi ba ya kalli Yusuf din dariya Yusuf yayi yace idan bata tsunke ba kai ai zaka tsuke din.
Nayi mamaki da tunda muka dawo ka daina maganan khadijan amma acan kusan kullun kana min zancen ta har ina jin dadin ta shiga ranka yanzu ashe abin ba haka yake ba a gurin ka ban sani ba ?
Au so kake banda aikin yi sai na ta yanzu kai ni fa tunda yanzu muna lafiya da Nafisa wani batun karama kaina wahala ya kawu min a zuciya.
Ban gane may kake nufi ba yace Yusuf amma dai kaga aiki nakeyi ko yana mikewa yake fadin nagani barin baka wuri ka taba aikin ka.
Har ya mike yake fadin ina son ka turawa Fati kudin da ta bukata na bukin da suke dashi don jiya take fada min bukin ya gabato.
Kallon shi Yusuf yayi yace baka fada min nawa zan tura mata ba and kuma ina ganin ya dace ka tura ma da wanda zasuyi suturan fita bukin dashi.
Katura mata biyar dakomai da komai don saboda laluran yara idan zai ishesu dariya Yusuf yayi yace indai fati ne ko bai isa ba baka jin korafin ta akai shiya nake ganin zubin su daya da khadija wallahi a wani gu.
Baiyi magana ba sai murmushin da yayi a baiyane tare da fadin yar matsala wai ita a dole fushi take ba a kulata ba.
Mata idan suka samu guri sai so wuce limit din su akai ni dake da mata biyu wata mace zata tsaya jawa rai a waje yanzu ?
Fita Yusuf yayi yana mashi dariya tare da fadin ni dai nasan yanzu akwai nadi a lauje muje zuwa dai a hakan .
Kwance nake a dakina ina so in huta don yau a gajiye nake ga test ga pratical da muka fita da rana maryam ce ta shigo dakin tana fadin malama tashi zakiyi fa mu fita.
Don har kayan miya nake son mu sayo kin ce kuma kina son kayan make-up ke ma da sauran abubuwan bukatan ki.
Wani kallo nayi mata nace cabdi jam a yanzu yadda nake din nan don Allah ki tafi ki dawo yau na gaji wallahi sosai maryam.
Ke ma kin san dole zaki tashi mu tafi don yau kadai kike free kara kwantawa nayi na fita batun ta tana ta shirin ta har na fara barci sai naji takai min doka a baya.
A zabure na mike tana fadin don Allah tashi muje khadija kada ki bata muna lokaci mana nace maryam ba zaki barni in huta ba don Allah wallahi na gaji ne yau.
Matsa min tayi dole na mike na fara shiri ba don naso ba dogon riga na saka kaman kullun don sune kayana ko atamfa zan dinka nafi inyi dogon riga dashi yanzu nafi sakewa a cikin shi.
Mun fito maikon mu tsaye kusa sai da ta jamu zuwa ciki gari a shagon da take ganin zamu samu kaya da sauki a gurin.
Raina na bata ina fadin ni ban iya wahalan ki wallahi shiyasa nace kizo ke daya don ban iya wanan wahala saboda son banza zaki jawo mu zuwa nan.
Dariya take min tace kin dai riga da kin fito yanzu sai yadda nayi dake kuma ai shagon babbane so sai kaya iri iri ne a cikin sa .
Binta nake a baya kamar dole banko iya magana don gajiyan da nake ji din ta sai wanan ta dauki wancan.
Wani set din kaya make-up na gani mai kyau na mika hannu zan dauka naga hannun wata mace ta mika itama zata dauka.
Duk tare da ita muka dauka a lokaci guda na juyo ina kallon ta Nafisa ce a baya na ta ke daukan set din ita ma nace cikin wani irin murya sake don na rigaki dauka.
Nawa gare ki da zaki biya wanan make up din halan ta na shirin bangajeni ta dauka na riga ta rike kit diin nace don Allah ban wuri malama.
Baki isa ba mara kunyar banza nace marasa kunya din ke wacece da zan dauki abu kice wai na bar maki kamshin turaren shine naji a hancina yana fadin may ke faruwa ne Nafisa ke da waye kuma ?
Yana tsaye bayan ta rungumay da yarsu a kafadan shi tana barci tace dashi cikin zafin rai wanan mara kunyar mana tana ganin ina da raayi abu kuma zata sa wani kazamin hannun ta ta dauka.
Bar mata mana tunda ta riga ta daukan wanan ba sai a kawo maki wani ba tunda baza su rashi ba anan din .
Haba malam yaya zan ce ina son abu sai kace wai in bar mata ita wacece da zan bar mata murmushi nayi nace au shagon dama na gidan ku ne ashe.
Maryam ne ta iso take tambaya ganin shi kuma sai duk ta daburce tana gaida shi tare da gaida nafisa wace ke ta kunduma ashar a bakin ta.
Nace da maryam muje ko ban tsaya kulataba na raba su na wuce maryam ta biyo ni baya duk a tsure take bamu tsaya magana ba muka mika kayan wurin biya suma a lokacin suka iso gurin biyan kudi yace hada kudin da nasu ka cire a katina lokacin nafisa ta iso ta samay shi tace dani.
Karya kike yarinya zanyi magananin ki a garin nan dani kike wasa wallahi nace kafin kiyi magani na ni zan fara yin naki a garin nan na watsa masu harara har mijin nata naja hannun maryam muka tafi.
Bayan mun fito muna saman titi da maryam muna jiran abin hawa sai ga su sun fito daga cikin shagon suma suka shiga wata hadadiyar motar su a gaban mu ta leko glass din motar tana fadin matsiyaciya ko mota ashe baku da.
Tsawa mukaji ya daga mata tare da fadin wai manene haka nafisa ya ja motar da karfi suka bar gurin tsuki naja gami da harara na raka su dashi.
Maryam tace yau naji takacin barin mota na a gida wallahi da dashi muke wanan matar bata isa tayi muna haka ba.
Nace au ke kin damune da maganan ta ita uban wa ya bata motar gidan su badai da namijin nata take barazana ba.
Matar nan lallai bata da hankali khadija jifa yadda take abu kamar wata yar bariki can nace guri ta samu tayi abinta amma ni bata isa ta fada mi in kyale ta ba.
A can kuma cikin motar su fadi Nafisa keyi wai ni ina ma nasan wanan fuskan ne na mance ida nasan wanan yarinyar wallahi ?
Bai mata magana ba sai tukin motan shi yake yi shi kadai yasan abinda yake ji a ranshi a lokacin wai a haka zai hada wa yan nan yan zafin rai guri guda.
Tace wai ashe ba yarinyar nan bace kuwa sai kuma tacce ba ita bace don waccan bata waye haka ba koma waye taci bashi wallahi in dai nice zamu hadu wata rana ai zata raina kan ta.
Tana takama don tana da kyau da diri wa zata nunawa kyau da fari anan kai dake dani a gida tana ganin kyauta zai rude kane take wani far da idanuwan ta haka.
Murmushi ya danyi cikin kunan rai tare da fadin ki san abinda zaki fadawa mutane don baki san ko ita din waye ba a garin nan kizo ki jawo wa kanki matsala wata rana.
Maryam ke ta zuba a mota nace please maryam ki rabani da maganar wanan matar mara mutunci wallahi sai na gwada mata ita karamar yar iska ne daga yau .
Ni fa laifin ki nake gani da kika bata wanan daman take ganin ita wata tsiyace da kin jaye hankalin mijin ta ai da zata gane bata da wayo.
Nace cikin mata wani iri kallo wani mijin kike magana badai wanan mijin da baida ta cewa ba a gaban matar shi kike nufin in sace zuciyar shi in kai ina idan na sace ga mai iko da zuciyar shi kina gani.
Jifa yadda yau ya nuna bai sanmu ba a gaban ta kwata kwata wallahi saboda tsoron mace da yakeyi.
Ta kada kai tana fadin wallahi ba tsoro bane mutunta matar shi ce kawai yayi kuma ko wani namiji ne ma haka zai yi ai a gaban kowa.
Don dai kawai a zauna lafiya amma da gidan shi kike yai haka shine zakice wani abu kyale ta nayi don ina ganin don ba ita akaiwa hakan ba yasa take fadin hakan.
Har muka isa hostel din ba wanda yayi magana da dan uwa wanka nashiga na fito da alwalana na tayar da sallah ina gamawa na kwanta tare da bata baya .
Muryan ta naji tana fadin bazaki ci komai ba ke na kike nufi zaki kwanta yanzu banjin cin komai murmushi tayi tare da fadin .
Ai ba haka ya kamata ki bullo mata ba da fushi da abinci don ita ko shi basu ma san kina yi ba ai yanzu wallahi khadija lokaci yayi da zaki falka daga barcin da kike yi.
Kamar yaya na katse ta tare da juyowa ina fuskantan ta nace may kike son in yi mata tace wallahi ki cusa kanki ga A A shine mafita a gareki.
Kaina girgiza nace haba maryam wanan zubar da ajin kike son inyi komay kuma ni nasha fada maki ban ra, ayin wanan A A din sam.
Tace ko baki son shi ki girgiza buzuwan nan don Allah tasan shayi ma ruwa ne ba ita kadai bace mace a duniya har duniya ta kare akwai mata kyawawa a duniya.
Nasan wallahi kyau ki da zatin ki kadai ya ishe ta ballw uwa uba karatu da kike dashi wanda nasan ko bokon primary ita batayi ba kila acan .
Dama na farko da zaki fara nuna mata kai tsaye shine gorin motar da taimaki kona kwana gudane kice mashi mota kike so anan zamu gane idan yana son ki sai muci gaba da aiwatar da shirin mu akanta sannu a hankali.
Kallon ta nayi wani iri nace mota fa kika ce maryam ina zankai mota tace baki zaiyi kai tsaye akace maki balle ki damu.
Fada mai hakan kawai zakiyi don mu gani kina da tasiri a gurin shi ko baki dashi ajiyan zuciya na sauke tare da fadin zan gwada in gani to.
Har na kwanta kuma na juyo nace mata maryam idan ya bani motar fa ai na kashe kaina a gurin iyayyena wallahi.
Kyautan mota wasa ne khadija ai ba baki zaiyi ba kai tsaye anan kin ga zamu san abin yi kuma nace to shike nan tunda haka kika ce tare da juya mata baya.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Wanan magana ya tsaya min a rai sai dai gaskiya ban aminta da maganar maryam ba don ba zan iya bude baki na in roki namiji koda kwandala ba balle har mota.
Ina zan kai mota idan ya bani a gida ince dasu ina nasamo mota kana wa yaban motan akan wani dalili zai min kyautar mota haka inma har zai bani din.
Gaskiya maganar ta bai karbu ba a wuri na sam zandai gwada mata nima ba kyale bace zan mata abinda sai tarena kanta da kanta anan na aje maganan azuciyata.
Sai dai ban fada ma maryam abinda na yanke a zuciyana ba nabar abin a raina don ita maryam ba abinda ya damay ta wanan nake