Showing 87001 words to 90000 words out of 133935 words
san babu wanda yasan wanan abin don ko Yusuf baida labarin abinda ya faru can sai ga wanan tsohon na bashi labari tiryan tiryan.
Bayan ya kare mai wanan bayanin ya dago ya kalli Abdul din wanda kanshi ke kasa yana tunane yace sai kuma maganan da ya shafi iyalin ka yanzu.
Malam ya danyi shiru na wani lokaci ya sunkuyar da kan shi kasa kamar mai nazarin wani abu yana kada kafan shi jefe jefi yace.
Yace gaskiya nayi istihara a kan ka sai dai abinda zan fada ma ba lale bane ka yarda zaka iya zuwa wurin wani yai maka ko kai kayi da kan ka don zaka iya istihara ba abu bane mai wuya idan mutum yasa kansa yi.
Yusuf ne yace malam ba matsala ai zaka iya muna bayanin abinda ke nan yanzu don musan abinda ke nan.
Malam yayi baiyananen murmushi ya na gyara zama yace bani hankalin ka nan ka saurare ni da sauri suka dago suna sauraren bayanin shi.
Yace abinda nagani a satin farko shine kana tsare a karshin wata mace fara doguwa sai kayi kamar zaka kubce daga sherin ta sai ta sake sabon shiri a kan ka ta kara daure ka.
Sai dai dana sake yi naga wata yarinya fara itama a cikin rayuwan ka ban sani ba ko kasan da ita ko baka sani ba tana nan dai yar matashiya ce haka da ita.
Sai dai ina ganin itace kamar warakan matsalan ka watarana amma dai ban sani ba Allah masani.
Sai wanda nayi a karshen nan ya nuna min cewa zaka kara aure wanda haduwan ka da yarinya alheri ne sosai sai dai akwai matsala daga wurin wanan matar taka .
Zaka kara aure nan bada dadewa ba zai zams maka alheri dan yarinyar mai biyaya gare ka ta kawo karshen komai a gare ka don arzikin ku yazo daya da ita sosai.
Duk zauren akai shiru ana sauraren tsohon sai Abdulsamad wanda ke shatan zufa daga goshi shi.
Malam yaci gaba da fadin sai kayi da gaske ka zama namiji zaka samu mafita don yanzun haka matar da zaka aure ban debe tsamanin ba ayau ko gobe zaku iya haduwa da ita.
Yace wanan ke nan bansan abinda yasa yaran yanzu kuke sakaci da ibada ba bayan kuna da sanin da Allah ya baku wanda idan mutum ya rike yanayin sa ba wani shedanin da zai iya tunkarasa.
Ya dauko wani abu yace amshi rika nan ya mika hannu da sauri yana karban abinda yake miko mashi din yace yau nake son kayi amfani da wanan abin idan ka isa gida.
Zaka shaye shi duka sai ka rage kadan ka wanke fuska da hannayen ka kamar dai yadda kake alwala zakayi dashi sai ka kwanta insha Allahu zaka kubta daga sherin su da yardan Allah.
Yace har in kayi yadda nace kayi da yardan Allah ba wani sihirin da zai shige ka koda kuwa sun hada da jinnu da sauran su don kamar ka dafe wani kafa na jikin ka ne da wanan tsarin Allah ya tsare ya kare yace dasu.
Yusuf ne ya ce da tsohon malam batun yarinyar da kace fa tana nan kusa tsohon yayi murmushi yace gaskiya tana nan kusa damu a yadda nagani yanzu.
Kuma ina sa ran haduwan ku ko yau ko gobe idan Allah ya kaimu sai dai mu bar ma Allah sanin shi.
Gaban Abdulsamad din ne ya fadi a ranshi yana tunanen don yana tunane wacece wanan yarinyar da zai hadu da ita yaji har yana so ta.
Godiya sukai ma malamin suka kawo kudi suka bashi kai ya kada masu yace ba wanan a tsakanin mu aikai jika nane bazan karbi ko kwandala a gare ka ba.
Sukai mashi godiya suka mike zasu tafi sai tsohon yace akwai tafiyan da zai taso maja gashi na gani a gabana kayi kokari kayi wanan tafiyan don zaka samu alheri mai yawa a cikin shi.
Ya kara godiya suka fita sai da suka sauke kawu salihu suka kama hanyar kaduna a lokacin yamma yayi sosai.
Ba mai magana a cikin su kowa da abinda zuciyar shi ke saka mashi a lokacin don shi da farko bai yarda wai nafisa tana mashi sihiri bane.
Ya dauka so ne kawai yake mata na tsakani da Allah mutane ke ganin wai sihirce shi tayi baida ta cewa akan ta sai abinda taga dama takeyi.
Amma yanzu sai gashi dan tsohon nan ya jefo zancen ta a cikin maganan shi shi bawai ya yarda bane to amma kuma abinda ya daure mashi kai shine zancen tafiyan da yayi tsohon ya sani.
Zai gwada abinda yace don ba a kin ta maya koma maye zai gwada maganin ya gani zai kuma bi a hankali yaga maganan tsohon ko gaskiya ne.
Muryan Yusuf ne yaji yana fadin wallahi na dauka khadija ce tsohon nan ya gani a tasbahan shi ashe ma watace.
Sai dai wallahi naso ka auri khadija ashe abin ba haka bane muna namu Allah na nasa ne.
A tunanen ka ke nan kai ni ban kawo komai ba har yanzu don ba wata mace a gaba na yanzun haka abinda ya damay ni ya damay ni.
Koda suka isa dare yayi don haka suka bari sai da safe idan zasu wuce su shiga su gaisa da su hajiya mama.
Barci nake bayan na gama mata komai sai na koma in huta can cikin barcin naji muryan Y Amina a kaina tana fadin khadija don Allah tashi ki shiga gidan su mommy ki karbo min lemun tsami.
Na dago idona cike da barci nace haba ya Amina nifa ban son shiga gidan nan har in koma tunda ba dadewa zanyi ba.
Khadija magani zan hada dashi don Allah daure ki shiga ki karbo min dole na daure na mike ta fita daga dakin ta koma falo ta zauna.
Na fito sai take cewa dani wurin hajiya mama zaki karbo min don mommy bata nan tana Abuja gidan Abdulsamad takai wata can an dauka matar shi zata haihu a lokacin suka tafi gashi har yanzu bata haihu ba.
A raina nace ai nafiki sani na fita ina ce mata sai na dawo a gidan sunyi mamakin ganina don basu san da zuwa na ba .
Sai da nabi kowa na gidan na gaida su na nufi dakin hajiya mama nan falon ta na samay ta na zube kasa ina gaida ita take cewa hadija yaushe a garin ?
Nace jiya da safe na shigo nazo duba Ya Amina ce da jiki tace ayyah ai amina taji jiki wallahi haka take cikin ta ita.
Nayi murmushi nace tace in karbo mata lemun tsami a gurin ki ne tace to barin in tashi in duba maki ko akwai saura.
Sallaman su ne ya katse muna magana ta amsawa tare da fadin yaushe kuka shigo garin nan kuma ba labari don da gani anan kuka kwana.
Hajiya jiya muka shigo munje zaria ne gurin kawu salihu sai dare yai muna a can kafin mu dawo cikin fadada murmushi tace toh daga wurin yaya din kuke ashe.
Wuri suka samu suka zauna suka fara gaisawa dasu kaina na duke a kasa na somay da gani du sai bayan sun gama gaisawa ne hajiya ta tuno dani tace Aff.
Kinga khadija na manta dake wallahi zuwan wa yan nan na bazata da sukai muna da sauri suka kallo ni kowan su na mamakin ganina a dakin mahaifiyar tasu.
Mikewa tayi tana fadin khadija ga yayan ku nan wanda ya taba rage maki hanya kwanaki ashe suna hanya suma da kin sani ai dasu kika biyo koda yake kin ce ke shigan safe kikayi.
Ina wuni nace dasu cikin jin kunya ban ko saurari amsar su ba na kawar da kaina gefe ina wasa da yan yatsun hannu na.
Fita tayi zuwa wurin fridge din ta dake waje fitan ta naji muryan Yusuf yana fadin khadija yaushe kika zo garin nan ne ?
Nace don Allah malam ban saku ba ku bari in rabu lafiya da hajiya don kunyar ta nake ji sosai na fada ma wanan aljanna ce wallahi.
Inba ba wanda ya saba dashi ba ba zai dauka shi yayi maganan ba alokacin ban basu amsa ba don na hango hajiya tafe da bakar leda a hannun ta.
Miko min tayi tana zama tana fadin ki gaida min ita da jiki in na samu lokaci zan kara shigowa in duba ta.
Nace to mama an gode na mike da sauri ina barin dakin naji tace yaushe ne zaki koma Abuja ke.
Nace gobe zan koma mama tace ku yaushe ne zaku koma tana tambayan su suka amsa mata da yau insha Allahu.
Ai na dauka sai goben zaku tafi sai ku rage mata hanya nidai na wuce na barsu nan ina sauri in fice gabana na faduwa da ganin su.
Har nayi nisa naji muryan Yusuf a bayana yana fadin yar gidan mama gani fa na biyo bayan ki.
Tsayawa nayi ina jiran karasowan shi inda nake ya iso yana fadin surprise to see you dama ashe kema zaki shigo kaduna baki fada muna ba ?
Yaya tace bata da lafiya nazo duba ta yace gaskiya naji dadi da na ganki nan nace namay fa baka san ina zuwa nan bane dama ?
Yace na sani amma banyi tunanen zuwan ki nan a wanan lokacin bane sai abin ya ban mamaki matuka.
Nace zai shige sai mun hadu idan mun koma yace shike nan amma da wata mota kika zo ne nace motar haya mana ina wucewa nake bashi amsa.
Naba da baya naji yana fadin zamu biyo mu gaida yayar tamu nace basai kun zo ba an gode na shige gidan ya tsaya yana kallon gidan da na shiga.
Abdul ya fito ya samay shi waje yake fadin dama kasan zata zo garin nan ne ita ma ko ta san da zuwan mu ne ta biyo mu.
Murmushi yayi mai yace haka dai Allah ya tsara abinsa nima yanzu na ganta wallahi.
Ina shiga nace dana sani wallahi da ban shiga gidan nan ba yanzu wallahi ina mika mata ledan nake maganan tace saboda may?
Nace wai fa mutanen nan nagani a gida da sauri tace suwa nace su Yusuf da Abdulsamad mana tayi murmushi ta fara bude ledan tace a haka da yawa aiko na gode.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Ido Ya Amina ta bini dashi kaawai na shige daki iya yanzu haushin su su duka nake ji shiru shiru basu zo ba yasa na saki jiki na koma normal life dina a gidan.
Kwana hudu nayi a kaduna na juya na dawo Abuja ban tsaya na sallami kowa ba don dama banda gidan su mommy ban shiga ko ina ba .
Tafiyan marance nayi don ban da kaya a tare dani ba zansha wahalan zuwa hostel ba daga inda na sauka.
Maryam ta tare ni da murna tana fadin wallahi har hankalina ya tashi da naga yau ma har dare baki dawo ba nace na tsaya ne inga yadda jikin nata ya kara sauki.
Ban mata hiran haduwan mu dasu ba itama din bata tambaye ni ba don batayi tsamanin zamu hadu dasu ba a can.
Suna gaisawa da Abba shine Nafisa ta kira shi tana fadin bata jin dadin jikin ta yau tun da ta tashi yace subbahanallahi yanzu zamu taso.
Sun iso sun samu taje asibiti ance haihuwa da sauran lokaci suka dawo gida duk wanan abin su mommy dake gidan basu san wainar da ake toyawa ba a gidan.
Don dama sai taga dama take gaida su da kwana bayan nan zasu wuni basu ganta ba a gidan.
Ga A,A sun ga sauyi a gare shi sosai tun bayan zuwan wanan matar a gidan komai da yake masu na kulawa ya rage a yanzu wani lokaci har fita yake bai gasa dasu ba.
Ya dawo duk da yadda yake ji ya rage jin shi yau direct gurin su mommy ya fara zuwa ya gaisa dasu sukai mai sannu da zuwa tare da tambayan shi mutanen gida.
Ya amsa da suna lafiya suna gaida su ya fito ya nufi part din su kwance ya samu Nafisa tana barci ya dan dade a tsaye kanta yana dubata ya juya zai fita ta falka.
Shima juyowa yayi yana fadin kin tashi tare da zama a kusa da ita yana tambayan ta jikin ta tana wani yamutse fuska take fadin da sauki.
Taje asibiti an dubata ance ba haihuwa bane da sauran lokaci Allah ya sauwaka yayi mata ya mike zai fita tace samad yanzu ya dace katafi kai zaman ka ka kyale ni.
Haba Nafisa jiyane fa nayi tafiyan nan kwana daya nayi a can kawai shine kike fadin na tafi na kyale ki haka ?
Nasan wurin wanan yar iskan matar taka fati kaje ka fake ga wai aiki ne zai kai ka can barin fada maka wallahi baka isa kace zaka wullakantani ba ka dawo da Fati a gidan ba.
Kallon mamaki yake mata yace idan baki yarda Fati ta dawo ba ai zaki yarda wata ta shigo gidan nan ta zauna ko ya fadi a hasale.
Ke baki damuwa da abinda ke gaban ki sai bakin kishi kawai dake cin ki haka har zaki ce wai saboda fati naje kaduna.
Idan ma naje gurin ta ai ba laifi bane don fati matanane kowa yasan ina da hakki a kansu yana fadin haka ya juya ya fice daga dakin.
Bin shi tayi da kallo mamakin shine ya rufe lokaci guda a lokaci daya ya juye mata haka har yana da corrage din bude baki yana fada mata magana son ranshi.
Amma sai ta basar da zance da fadin kila gajiya ne a tare dashi ita kuma ta tare shi da zancen Fati da bai kaunan ayi mashi.
Washe gari na idar da sallah ina zaune wayan Binta Abdulrahim kaunan Abdul samad ya shigo ga wayana.
Na daga in fadin B,A ya kike tace wallahi khadija Adamu baki da kirki yanzu kizo kd ko neman mutane bakya yi in ba mama da ra fada muna yanzu muna maganan ki ba wai kin zo kin shigo har gida mu baki ne may mu ba
Dariya nayi nace Binta Abdulrahim ke nan ni da na shigo gidan ko amsan abu kuma ban dade ba wanan miskilin yayan naku mai jin kai ya shigo na fita.
Ashe kwana biyu kika yi kawai nace hudu dai don jiya na dawo Abuja da dare tace baki da kirki naji nace da ita.
Zamu shigo Abuja idan matar yayan mu ta haihu zan nemay ki ai idan mun shigo kin san mommy na garin gurin shi ai.
Nace Ya Amina ta fada min da nazo kd ai tace kin san yanzu mun dan fara samun kan shi yana dan kula mutane sai dai ba can ba.
Nace da san nu zai kula ku ai watarana tace ai shi nace ma hajiyan mu da ta tayar da hankali kin san shegiyar matace buzuwan nan.
Don su mommy sun je gidan kawai sai ta kule kitchen wai ba zasuyi mata girki a gida ba ki san muguwa wai da yunwa zata hore su kuma ?
Don kawai su bar mata gida tunda bata kaunar ta bude ido taga yan uwan shi sun rabe shi ko kadan nace wanan yayan naku kamar soko yake ai mutum ya zauna haka mace tana juya shi.
Khadija kin fa san buzayen nan yadda suke wurin mallake maza ai ke da gani kin san ba banza tabar shi ba idan munzo dai ai zamu sha kallo don nasan sai an kwasa da ita.
Nace idan haka ne may zai kawo ku kuma ba sai ku zauna gida abinku ba tunda ba dole bane sai anzo din tace kindan haihuwar ta ke nan na farko a gidan shekara shidda da aure sai yanzu ta samu ciki dashi ana ta cin duniya.
Wani abu da ban sani bane na ji ya tsaya min arai nace ku kuka sani ni dai idan kin samu lokaci don Allah ki shiga ki duba min jikin yar uwata don in san halin da take ciki.
Tace insha Allahu zan shiga in duba maki ita nace halan ina Z,A take ko ta fita ne tace gata zaune tana jin mu wai fushi take da ke .
Dariya nayi nace su zainab manya fushi akan may idan batai hankali ba sai na hada ta da buzuwa matar yayan ku ta latsa min ita da kyau.
Tace ai kawar ki ce gaku kuma zaune a gari guda waya sani ma ko kun kulane da ita dariya ne ya kamani sai naji wayan ya mutu nasan kudin ta sun kare ne.
Ita Binta bata jin ta kiraka ta dade kuna hira har sai kudin ta sun kare zata kyale mutum sai kuma tunanen buzuwa ya fado min a rai .
Tsuki naja ina fadin lalle wanan takai shu,uma nan nake ba maryam labari muka zauna nan muka rage mata zunubin ta wurin cin naman ta.
Bayan kwana hudu da dawo wan shi cikin dare ana ruwan sama sosai na