Showing 111001 words to 114000 words out of 133935 words
shirye girka mata wani abu”
“To an hutar da ke”
Ya fada yana jan hancina. Sai nai murmushi.
“Ita ma zan mata magana na ce tai maka maganar karatuna”
“Oh magana kika yi ma Momy tai min magana ko?”
“Aa Wallahi ita tai dan kanta,kawai dai ina son karatun ne kuma kai na ga kamar ba ka so”
“Ba wai so ne bana yi ba, yana ganin kamar karatun a yanzu zai iya zame miki matsala ko wahala”
“Wallahi ba wani Wahala bana jin komai fa kalli”
Na yafa ina daga rigar da ke jikina, sai ya kalli cikin ya kalleni yana murmushi.
“Ai a jikinki ake gani ba, nan gaba na ke miki nuna”
“Idan na ji da wahala nan gaba zan daina”
“Daman ai kin iya raki ai”
“Amman ni ai ina da kokari bana raki a komai ma”
“Ko”
Ya tambaya kamar mai magana da yar shekara uku babu dariya ko murmushi a tare da shi.
“Idan mun koma Abuja zaki fara zuwa islamiyar su da bokon da ke can, amman idan cikin ya kai wani mataki za ki saurara da zuwan har sai kin haihu, sannan ki cigaba”
Ban san lokacin da bar inda na ke zaune ba, na fada jikinsa ya rumgume shi ina murna.
“Da gaske Hamma”
“Ba na ce ki daina ce min Hamma ba?”
Ya fada yana jan lips dina.
“Ni dai amsa min da gaske?”
Ya gyada kai sai na kara rumgume shi saboda murna har da yi masa kiss a gefen fuska, shi kansa abun sai da ya bashi dariya. A ranar sai farincikina ya zame uku, na zuwan Mama da na case din Doc Asim da za ayi ga kuma zancen Karatu da Hamma yai min. Kowa ya ganni a wannan lokacin ya san ina cikin farinciki, har muka yi wanka muka shirya ban daina sake saken yadda zan fara karatun nawa ba.
Bakar a baya na saka shi kuma ya saka wani koren yadi mai kyau mai kamar boyal kuma ba boyal ba, ya saka bakar hula da bakaken takalmi karka so ganin mijina a wannan lokacin yayi kyau sosai fuskarsa har wani annuri take kamar wani ango, ni kaina sai da na kusa shashantar da kaina gurin kallonsa.
“Ashe kai ma kana da kyau”
Ya dube ni da duba irin na wasa da kuma mamaki.
“Oh dacan ba ki taba ganin kyau na ba sai yau? Ko dan ina yawan fada miki cewar kina da kyau?”
“Aa gaskiya yau dai sai naga kamar kana da kyau”
Hannu ya kai ya rikoni ya matse min kunne.
“Na fiki kyau yarinya ni da yan mata ke hari ma, ke ma ba kyau ne ya janyo ki ba, kina ga dan yaro kyakkyawa kika lake min har da addu'ar Allah yasa na so ki, shiyasa na kasa zaune na kasa tsaye sai da na kawo ki gidana”
Ban san lokacin da dariya ta subuce min ba, duk kuwa da irin zafin rikon kunnen da yai min.
“Da zafi sosai da zafi”
Na fada a lokacin da yake jan kunne nawa zuwa gurin motarsa.
“Yau ke za ki bude min motar na shiga”
“Saboda me?”
“Saboda ni ne Sarki”
“Amman ai kai ka saba bude min”
“Lokacin da kina sarauniya ba”
“Yanzu fa”
“Ni ne sarkin”
“Taya?”
“Gashi nan ke ma kin yaba kyau na”
Dariya nai na daka tsalle na cire hular kansa na watsa da gudu gaban motar sai ya biyoni ya gudunsa.
“Ke ba ki da kai ya za ki fara gudu da ciki”
Jin hakan yasa na tsaya sai kawai ya karaso kusa da ni ya karbe hularsa ya sake rike min kunne.
“Na gane ba ki jin magana Babyna”
Haka ya janyo ni har gurin motarsa ya bude min na shiga ya rufe sannan ya zagayo ya shiga mazaunin direba ya tashi motar muka dauki hanyar gidan Momy.
Ina shiga dakin Momy yai kan Mama da gudu na rumgumeta ina murna. Matan da ke tare da ita sai suka saka dariya suna ta kiran wai na cika kurciya, Momy ma dariya take tana fadin haka muke ni da Husna da Siyama kusan halin mu daya Amina ce kawai mai hankali, sai da muka dade a dakin muna fira ni har na manta da Hamma sai gashi ya shigo dakin da kunya ya gaishe su tare da musu fatar an zo lafiya sannan ya fita. Wani abun haushi abun mamaki Mama ta yi ma kowa tsaraba, a gidan sun daga kan Daddy har Momy da Amina Husna da Siyama kai har Hamma sai da ta siyo masa wata dakakkiyar shadda yar Agades amman ban da ni, nikan Nonon Ragumi ne kawai tai min tsaraba da shi. Misalin biyu saura na rana muka fito zuwa inda ake bukatar ganinmu, ni da Hamma a mota daya Mama kusa ta shiga wata mota da yan'uwanta maza suka zo da ita daga can inda suka sauka.
Ko da muka isa gurin biyu daidai, wani katon gurine mai kamar ma'aikata, yan'uwan Mama maza da Hamma suka shiga gurin da aka tana da domin sallah, ni kuma da Mama da wata yar'uwarta da ake kira da Mama Lattu muka shiga wani dan fili mai kamar dakin karatu mukai na mu sallah.
Ba mu zauna a dakin ba sai uku daidai domin bayan gama sallah sai da aka jira isowar wasu daga cikin wadanda za a zauna da su. Maza da mata ne da yawa a dakin za su kai su goma a dakin, sai wasu kujeru da aka jera can dabam wadanda aka nuna mata aka ce mu zauna, duk irin kusancina da Hamma na kasancewar mijina hana shi shiga akai a gurin, da kuma yan'uwan Mama sai aka hana su shiga, wai da mu kawai suke son su fara magana.
Inda Doc Asim yake zaune da dabam da inda muke zaune, sai kallona yake kamar be tana ganina ba, na kalleni ya kalli Mama wata kila mamakin rayuwarta ya kashe shi ko kuma mamakin kawo kararsa yake oho, sai dai a yanayin da ya ganmu daga ni da har Mama ya sam yanzu ba kamar da ba ce domin ta canja zane. Da turanci suka fara magana kamin dayan ya fara yi da hausa yadda ni da Mama za mu fahimta.
“Doc Asim ka san wannan?”
Sai ya kalleni ya gyada kai.
“Eh na santa”
“A ina ka santa?”
“Ta yi zaman jinya asibiti tare da mahaifiyarta a lokacin da ta siyar min da kodar mahaifiyarta”
“Ke kin sanshi?”
“Eh shine likitan da ya cire kodar mahaifiyata ba tare da sanina ba ko saninta”
Daga haka suka fara karanto masa abunda ake kara akansa da kuma zarginsa da ake.
“Wannan yarinyar fa karya take ita ta siyar da kodar mahaifiyarta, kuma ta kai karata a gurin police ba ta ci nasara ba suka koreta shine yanzu take kokarin ganin ta bata min suna, wasu ne suke sakata saboda aci min zarafi”
Sai da suka tambayeni sannan na bayyana komai yadda ya faru ciki har da kulleni da akai gurin police, da suka tambayi ko ina da shaidu akan hakan sai na ce shukura ce ta san komai yadda ya faru.
“Fine na yarda a nemo shukura za ta fadi gaskiya ai, and zan kawo takardar da ta saka hannu akai za ku ga komai”
Yana fadar hakan na raya a zuciyata cewar akwai abunda yake kokarin shiryawa, wata kila ita ma zai siyeta kamar yadda yai ma polisawan da suka kama ni.
“Za mu cigaba da bincike, za mu gone gaskiyar lamarin idan har ba shi da laifi za mu hukuntashi, kuma zamu mika shi kotu domin ta hanke masa hukunci daidai da abunda ya aikata, ba zamu yarda wani likita ya bata mana aiki ko suna ba, ko kuma ya taka daya daga cikin dokikinmu, idan kuma ke muka samu da laifi yin masa kazafi za mu hukunta ki babu ruwanmu da kasancewar jikan Sarkin Agadaz babu ruwanmu da kudin kakanki ko babanki za mu hukunta kuma mi mika ki kotu domin a yanke miki hukuncin daidai da abunda kika aikata”
“Na yarda”
Ina fadar hakan Doc Asim ya maida hankalina a gurina, wata kila yana mamakin yadda nake da karfin hali ne wata kila kuma yana mamakin jin alakata da wani babban mutum nw kamar sarkin Agadaz da kuma zancen kudi da sukai ko da be san waye shi ba yana ji ya san ba karamin mutum, a take yanayinsa ya canja ya koma kamar ba shi ba rama yai ko lalacewa ba, yana nan yadda yake amman hankalinsa ne a tashe, domin ya san waennan likitocin ba kamar police ba ne da zai iya siye su ba. Ninkaina a yadda na gansu na san za su adalci ko da yake abun ba a fuska ba ne, da a fuska ne da Doc Asim ba zai min haka ba.
Dukanmu da farinciki muka dawo a mota na ke labartawa Hamma yadda akai yana ta kara kin kwarin guiwar cewar za su yi adalci domin gurin ba gurina na wasa ba, kuma ya san wasu daga cikin ko dab ganin abun ya fito ta bangaren Mai Martaba dole su kwatanta adalci domin ya nuna musu hakkin yarsa yake son a bi masa, abu na biyu kuma ba za su so wani likitan mai zaman kansa ya bata musu suna ba.
A gidan Momy na wuni ni da Mama domin bayan Hamma ya aje ni sai ya shiga gari, muka wuni muna ta maganar likitan har ake dauko zancen wasu likitocin masu taimakon da gaske da kuma wasu masu halin Asim sai dai su ba su kai shi ba ba domin na shi ya yi yawa ba kowane mai imani ne zai aikata haka ba. Daga bisani Mama ta dauko min labarin yayan Ammy da wasu yayan yayyunta ke so, wai magana har ta yi nisa ta kai gurin Mai Martaba ana zancen yin baiko. Na jidadin sosai jin cewar yaran Ammy ne duk dai Mama bata rike sunansu ba, amman ina ayyana cewar Humaira ce da Anty Zee, sosai na so ganin fuskar Mama Fulani da Maryam dan na san ba zata jidadi ba, saboda ba son shiri da Ammy take ba, kuma babu wanda zai so y'ar kishiyarsa ta samu jiki ta sa bata samu ba, balle Mama Fulani dake ta falako a cikin gida da nuna isa. Lallai Allah mai yadda ya so, kuma sai ya bawa Ammy surukai a cikin jikokin Mai Martaba yayan masu arziki wanda nasan Mama Fulani ce zata fi kaunar hakan.
Sai da dare muka koma gida, bayan Mai Martaba ya sake Kiran mama ya fada mata cewar an saka wani ranar Assabar mai zuwa wato nan da kwana biyu kenan. Kamar yadda ya saba yau ma sai da siya mana dan abun tabawa a baki sannan ya muka isa gida yana rike da hannuna kamar ba zai sake ki ba.
*** *** ***
Gaba daya al'amarin duniya ya koma mata sabo kuma ya zo mata ta inda bata zata ba, bayan daukakar da Allah yai ma Ataa akansu ya daukakata fiye da su sai kuma Allah ya kawo ma yaya Ammy miji daga cikin zuri'ar da tai kwadayin yayanta su samu, har magana ta fara karfi ga nata yayan babu wanda ya taya ban da Kamal shi ma Kamal din ma tun da akai fada da shi akan Ataa be sake kula Maryam ba. Balle Rukaiya ita ko zancen ba a ayi yadda kasan ta kasa kashi haka take, ga shi ba kyau ne babu ba amman babu mai gani ya taya kamar wanin abun amai. A yadda take so ita bata ki an hade su da auren Muhseen da za ayi ba, ita ta wanke su gaba daya ta huta ya zamana baby ce kawai ta rage mata.
Fitowa tai daga kitchen ta nufo inda Maryam take zaune tana lasar waya ta fara mata masifa kamar mai jin haushinta.
“Ai dole ku rasa mijin aure, ina can ina aiki kina nan kina lasa waya, idan safiya ta waye dakinku kawai kuka iya gyara kamar ku? Ace ba za ku iya aikin komai ba? Idan ma kun yi auren ai ba duka namiji ne zai dauki haka ba, dan ba ko wane namiji na kamar Aliyu ba da zai yarda da hali irin na Rahma wanda yai kama da halinku, su yayan Ammy haka suke? Indai auna nan ai su suke mata komai ku gyara ko'ina girki ne kawai nata shi ma wata rana su suke yi, gashi nan ai Allah ya basu maza a cikin waenda nai muku burin samu saboda ku ba ku san ku yi tausayina ko idan ina abu ku rika min ba, duki ki ga yarinyar Ataa haka ta zo tana aiki a gidan tai nan ta yi a can gurin Ammy duk akan mahaifiyarta kuma da Allah ya tashi bata gashi nan har Muhseen da Aliyu sai da sukai fada akanta, kuma yanzu gashi nan Aliyu take aure, mai taimakon uwa ai baya faduwa amman ku kullum kuna kan waya sa kan gado sai ka rantse kujera sai idan na gama ku taso zuwa dinning room dan ba ku da kunya”
Maryam ta kalleta cikin jin haushin fadan na ta ta ce.
“Oh Mama yau kuma duk wannan fadan a kan mu? Kamar dai kin gaji da ganinmu”
“To wace uwa ce zata so yayanta kamar ku su zauna a gida suna jera tsawo da ita? Yanzu idan an wanke Zainab da Humaira ai kubkadai kuka rage domin na ji Abbah ku na zancen har da Batula zai aurar tunda tana da mijinta amman ku ko mai sallama babu, balle mai zancen aure ko a wayar nan da ake haduwa da maza ku ban ku, ace kuma tausayina da yanzu kuma Allah ya tauyasa muku ya baku inda za ku huta ku jidadi”
“Mama kin san aikin nan fa ba mu saba ba, taya jiki irin nawa zai iya aikin wahala dan girman Allah? Kara dai a nema wata nai aikin”
“Wallahi ba zan dauko wata mai aikin ba, wato n dauko wacce Aliyu ya aure yanzu kuma na dauko wacce ubanki zai aure ko? To ba za a koma ba”
Mama Fulani na rufe bakinta Rukaiya na shigo cikin falon makkale da waya a kunnenta baki har kunne tana wasa da keys din motar hannunta, zaunawa tai kusa da Mama Fulani a lokacin da ta sauke wayar ta rumgume Mama Fulani tana murna kamar wacce akai ma albishir.
“Mama ke dai wani ne na hadu da shi, ya hadu Mama ga motarsa yar yayi”
“A'ina?”
Mama Fulani ta tambaya baki a sake Maryam kuma ta tashi zaune tana jin kamar ita ce.
“A gidan mai shi ya biya min kudin mai aka cika min motata tam, sannan ya karbi number wayata yanzu haka ina isowa yana kira wai na ji na isa lafiya, yana ta tambayar gidanmu”
“Wow Allah yasa mijin ne yanzu nan Mama take ta fada sai ka ce mu muka dorawa kan mu bakin jini”
Cewar Mama. Rukaiya ta kyalkyale da dariya tana kara rumgume Mama Fulani da ke murmushi cikin jindadi.
AG cera ya zo domin ya temaki garkuwan jiki da kuma lafiyar jiki. Sinadari ne wanda ze magance matsaloli da dama wadanda suke hana garkuwan jiki aiki yadda ya kamata ko kuma yake rusa garkuwan jikin ita kanta.
Cututtukan zamani daban daban sun sa mutane gaba kuma magance su yana da wahala; irin ciwon Sugar, hawan jini, ciwon sanyin kashi, ciwon gabobi da sauran su. Haka ma cutukka irin wadanda suka shafi fatar jikin wadanda sun hada da kyasfi, pimples, takurewar fata, rakainuwar fata da kuma haske da kyallin fata duka ana shan AG cera kuma yana temakawa wajen magance illolin nan. Mutane masu fama da rashin karfin jiki wajen kwanciya da iyali da kuma mata masu fama da yawan ciwon mara lokacin al'ada ta karshen wata suma baa bar su a baya ba. A takaice dai AG Cera yana temakawa wajen magance cuttukka daban daban wadan ke damun mutum. Domin karin bayani ku tuntuni mu a wannan number +60167474649 ko kuma ku ziyarci shafin mu http://agnutritioninternational.com.
[11/1, 10:39 AM] Khadeejah🥰: Kwance nake saman katifan dakina ina karanta handout dina maryam zaune a bakin katifan tana gyara kumbar kafan ta.
Waka take wanda take damuna dashi sai ya hanani yin karatun tunanen mamud nakeyi wanda ya kai sati biyu yanzu bai lekoni ba kuma banji daga gareshi ba har wanan lokaci.
Hijjab dina dake gefe na dauka na rufe jikina dashi tace sanyi kike ji ko may da zaki rufe jiki haka nace sanyi nake ji wallahi.
Na kara jawo handout inci gaba da karatu tace wai ni ko dazun sai naji kina waya ina son in fito in tambaya wakiraki ko mutumin naki ne naga ya dade bai zo ba kuma banji yana kiranki ba.
Maryam kin damay ni fa karatu nake kuma kin gani a, a wani karatu yanzu inga kina tunane ke kika ga wanan din na gyara kwanciya ina bata baya.
Sai da ta gama abinda takeyi tace don Allah tace muje mini market mu sayo kayan miya nace ban zuwa tare da lumshe idona.
Fada min a jiki naji tayi tana dariya tare da sake ihu daidai kunnuwa na a zabure na mike na biyo bayan ta da gudu zuwa waje.
Dagani sai dan body hook da nake sakawa a ciki in dora abaya kaina ba dan kwali gashina dana daure ya fado min a baya don duk zuben filani na gajeshi wurin kakannin mahaifan daddy na.
A daidai lokacin nz hango motar su tana fakin a daidai inda suke tsayawa da mota idan sunzo guri na ban dauka su bane sai da na duba da kyau don gurin na kowa da kowane masu zuwa wurin yan matan su.
Itama maryam din ta gansu da sauri ta dawo inda nake tsaye tana fadin su yaya Yusuf ne can ko ?
Ba yadda zanyi don sun gama gani na gashi ko dan kwali babu akaina da sauri na koma ciki ita ce ta tafi wurin su tana gaidasu.
Yusuf ne ya tambaye ta gudun may muke haka kamar yara tace wallahi khadija ce ta biyo ni da gudu