Showing 84001 words to 87000 words out of 133935 words

Chapter 29 - Mijin Buzuwa Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

271

zancen nan kuma can su karata shi da ita tunda shi ba tsayayyen namiji bane ko yaushe.
Namiji ne mana khadija ai shiyasa na kiraki don ki sheda mai cikin wanan wasan da kuke yi don ya farga ga abinda yake yi din.
Ni tsoro na shine kada su mommy daya dauko gidan shi su fahinci susucewar shi a kan wanan shuumar matar tashi sugane gazawan shi a gaban kowa.
Shiya sani mana tunda shi ke ji a jikin shi ba wani ba yayi saurin fadin a a khadija ba haka zamu yi ba daurewa zakiyi mu fitar dashi daga wanan kangin don Allah.
Ni haba yaya Yusuf ni may zan mai kuma shiya sani don Allah khadija dakata ki saurare ni don Allah nace ina jin ka ai.
Zaki iya hakkuri ki daure ki kirashi a waya ki fada mai magana daya wanda zai shi ya natsu ya dawo cikin hankalin shi yanzu don ke ce kawai mafitar da nake dashi bayan Allah.
Ni kuma why sai nice mafita akan haka yace saboda ban taba ganin wani ko wata dake fada mai magana yadda kike fada ba azauna lafiya kuma yai amfani da abin da kika da mai a zauna lafiya.
Dan jin nayi ina tunane yace kada ki karaya khadija don nasan zaki iya ki taimaka muna please wanan taimako ne indan kin yarda.
Yaya Yusuf wanan ya zama na karshe da zan ma wani alfarma akan wanan mutumin don gaskiya baida niyar canza halin shi nake gani .
Khadija ba laifin shi bane shu,umar mace ya hadu da ita take juya shi yadda take so nace har da halin shi a haka.
Kin yarda zaki taimaka muna ke nan nace naji zan gwada don Allah don kai amma da ba haka ba babu abinda zai kara damuna da rayuwan shi.
Nagode kwarai da hakan da zaki min don wanan ne kadai hope din da nake dashi yanzu akan wanan matar tashi.
Ina aje wayan maryam dake zaune ta kura min ido tana sauraren maganan da muke yi din tace kai wasu maza suna haduwa da shu,uman mata wallahi.
Koda yake ba abin mamaki bane ga wanda yasan mazajen da ke auren irin yan yaren buzaye zai san mazan ne a kasa matan suna sama.
Sai abinda sukace komai su mamaye na miji yazama nasu su raba shi kuma da kowa nasa sai su da yan uwan su zasu dinga bushasha da shi da dukiyan shi.
Sai dai kima sam basu son auren mazan yaren su don irin bakar wahalan da suke sha wurin su amma namu mazajen su ke kwadayin matan buzaye saboda bakar jaraban da suka iya.
Yanzu dai kira shi muji yadda zaku kwashe a tsakanin ku don nasan akwai drama nace ni wanan daure ni suke son yi maryam.
Ban san may yasa suke cewa wai sai nice zan iya masu haka ba bayan yana da kanne mata da yan uwa da zasu iya.
Su iya may khadija ai abin sai da hikima ke fa ba yar uwan su bace kin ga yadda kuke moved dashi kamar saurayi da budurwa ne.
Ke komai zaki iya fada mashi a zauna lafiya wani dan uwa idan yafa da sai inda karfin shi ya kare ke ko sai ki fada mai a wasa bai dauki abin da zafi ba.
Wayan ta na karba ta hanyan yi mata karya wayana ba kudi a ciki tace ai bai san layi na ba don haka ba lale bane ya dauki kiran .
Bari dai mu gwada mu gani idan bai dauka kiran har ya kusa karewa ya daga tare da fadin hello nace dole zama da yan haure ya kowa ma wani akidar banza.
Wake magana please ya tambaya nace wata buzuwa ce ko kana son kari su zama biyu a gidan ka murmushi yayi yace khadija nace ba ita bace.
Kina zaton muryan ki nan zai bace min ne nace marya na yana kama da na buzaye ne ?
Yace ai kamar ma ta baci baki ganin zubin ku daya dasu sai dai yaren da baki ji nasu kai malam ni kiran ka nayi naji ko mommy ta koma ne?
Don nasan ba lale bane buzuwan gidan ka ta barsu su dade a gidan yace idan kina son sani kije gidan ki duba mana.
Ban tashi ba ne da zanje yace ya kike nace ina nan yarda ka sanin a baya ke ba a maganar girma da arziki dake ne ?
Nace banson don ba gaisuwa na kira ka muyi ba ko tambayana yaya ni yace ai kogi ba ki dadi ba ko nace .
Wani kogin ke nan dai wani ko wani ruwa ne ya shige shi in ba nasa bane amansa yake yi don haka ba gaisuwan ka nake nema ba.
Yace becareful nace a nan ko sai kaga mutum har mutum amma a gidan shi sai ka rena mai wayo idan kaga abinda yake yi.
Ta yaya bakin haure har zasu shigo su samu mutum a gidan shi in ba samun wuri ba suce sai abinda suke so zasu mai ni wallahi na dade da raina aya don tsakuwar ta.
Yau hausa kike ji ke nan nace daurowa ne hakan adai ji tsoron Allah kada mutum ya zauna mace ta mayar dashi saniyar tatsan ta .
Ba mai ci sai ita da yan uwan ta kadai yace kina son wani abu ke nan nayi saurin fadin haram wallahi adai ci lafiya.
Ga yan ketare nan suna taya ka ci idan ka wawuro su kuma sai su cafke ranan na zuwa da zan maka irin ku kotu masu ba bakin haure makafa suyi yadda suke so da dukiyar kasan mu.
Yace magana kike ji ke nan dai nace ba wani magana sai fadin gaskiyan da na saba kulun idan naga anyi ba daidai ba.
Ya Abdul ace mutum baiwa kansa adalci kulun sai abinda mace ta dora shi a kai yake bi yace wai may kike nufine don na rasa gane ida maganar ki ya doso har yanzu.
Mafalki nayi naga ka susuce kazama bawan mata sai goyon su kake yi a bayan ka ka manta da kowa na naka sai masu jajayen kunne kasa a gaba.
Murmushi yayi yace ki fito fili kice kin yi kewa na kawai kin tsaya kina dora wa wani laifi kuma ko na kulata ba mata na na kula ba na kula matar wani ne ?
Mata wai mata matar namu duka dai inji manya mata kan tana kaduna ka barota can wanan ai ta bugi ne .
Khadija you are very stupid matar nawa kike aiban tawa a gaba na nace ko a idon ka sai na fada don gaskiya ake fadi.
Namiji kamar mace baida say a gidan shi sai na mace macen ma abin kyamatar mu gaskiya ka gyara halin ka sai anjima nayi saurin kashe wayan batare da najira amsan da zai fada min ba.
Wanan yarinyar ta ci uban rainin wayo wallahi yace Yusuf da ke zaune gefen shi yana murmushi yace khadija ce halan ?
Wa kasan zai min wanan idan ba ita ba ban san mayeatsalar ta da Nafisa ba ko da yake su mata haka suke dama ko Nafisan da tasan da zancen khadijan Allah kadai yasan iya boren da zatai min.
Kana zuwa gurin ta ke nan har yanzu ya danja tsuki yana fadin wallahi na dade ban ganta ba tunkan naje Lesvegan rabo da na ji daga gare ta.
Yusuf yace ai gashi yau ta kiraka ita yace ta kirani taci min mutunci ba sai nayi maganin yarinyar nan wallahi ta raina ni da yawa I don't know why take min abinda taga dama haka ?
Kun fi kusa ai bani shiga tsakanin ku yanzu ai wani kallo yaiwa Yusuf din yace tunda ka gama hadawa ba ai ka fadi haka yanzu ?
Au ni ma hada ke nan ashe wa ya manna min wanan chewing gun din idan ba kai ba ina zaune kalau abina.
Amma ai tayi muna rana ba kadan ba kasan da hakan dai ?
Tsuki yaja yace ban san ya nakoma ba wallahi yar karamar yarinya ta shige min na kasa yin komai akan hakan ?
Kun dai shige ma junan ku yanzun ne kuma kake neman maraba da ita ko why zaka so ka rabu da khadija bayan kasan tana da amfani a gare ka ?
Amfani fa kace Yusuf yana kallon shi da idon shi da ya kafa mashi sai da Yusuf ya rausaya kai yace kafini sanin haka malam.
Kada ka bari shedan ya rudeka kaiwa kan ka hasara zukekiyar yarinya kamar khadija may kake fadi ne wai Yusuf ?
Kiran kawun shine ya katse masu magana da mamaki a fuskan shi ya furta kawu habu yau lafiya kawu ya kirani haka ?
Ya dauka suka fara gaisawa da kawun nashi wan mahaifiyar shi cikin kunya da nauyin kawun nashi yake amsa mai gaisuwan.
Don ya manta yaushe rabon shi daya kira shi ya gaida shi a matsayin shi na wan mahaifiyar shi da take ji dashi a cikin yan uwanta.
Bayan sun gama gaisawa ne kawun nasa yace dama na kiraka ne idan da hali ina son ka shigo kaduna a cikin wanan satin .
Da mamaki ya tambayi kawun nasa yace kawu lafiya ko yace a, a lafiya kalau sai alheri akwai abinda nake son kayi ne idan kazo amma fa idan ba takura.
Haba kawu ba komai in sha Allahu satin nan zan shigo ranan jumma, a asabar zan karaso zaria in gan ka kawun nashi yace nagode Allah yayi maku albarka ya kara tsare muna ku.
Ya amsa da amin kawu na gode ya aje wayan yana mamakin maganan da kawun nashi ke dashi akan shi Yusuf dake gefen shi ne ya tambaye shi ko lafiya.
Yana mai da kan shi bayan kujeran da yake zaune sama yake fadin wallahi ban san abinda yasa yake nema na ba a yanzu.
Zamu tafi karshen satin nan don haka sai ka shirya muna tafiyan yadda ya kama sai dai ban so tafiya yanzu ba a yadda Nafisa take haka haihuwa yau ko gobe.
Zamu iya zuwa muyi kwana daya idan hakane sai mu juyo idan ka gama ganawa da kawun.
Yace hakan za ayi Allah ya kaimu lafiya gaba daya har ya manta da zancen wata khadija ko don mantuwan da yake fama dashi a yanzu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Tunda mukai waya da Ya Amina tace min bata da lafiya sosai sai naji hankalina bai kwanta min ba ina bukatan zuwa kaduna weekend in dubata.
Kwatsam aka wayi gari inace wa maryam kaduna zan tafi yau in duba jikin Ya Amina da bata da lafiya tace shine baki fada min zaki tafi ba muje tare .
Nace kada ki damu watarana mu tafi tunda muna tare ai har bakin titi ta rako ni na shiga mota ta koma ita.
Da wuri na isa don sammakon da nayi na samu jikin nata da sauki sosai na fahinci ciki ne ta samu ashe yana bata matsala dama haka take ciki da wahala ita.
Gidan da bai samun gyara saboda laulayin da takeyi yasa gidan yayi datti da yawa sai da nayi wa gidan tas na yi wanka na kwanta don in huta.


Tunda ya fara shiri Nafisa take tsaye a kansa tana fada dashi akan may zaiyi tafiya yanzu bayan yasan halin da take ciki zata iya haihuwa ko yau ko gobe.
Ya dago yana ce mata tafiyan ya kama shi ne dole don haka na fada maki gobe zan dawo insha Allahu may nene kuma na fada yanzu.
Tace yanzun dai baka damu dani bane ban san may kake yawan zuwa yi gida ba akai akai haka ?
Au ke da kike zuwa gida wani abu kike zuwa yi a can tace zaka hada kaina da kaine nifa kasan ba nan iyayyena suke ba ya zama dole in rika duba su a kai akai.
Da kyat ya samu ta barshi zai tafi koshi don yace aikin shine zai sa ya tafi yasa Nafisan ta daga mai kafa.
Da suka isa kaduna zaria suka wuce kai tsaye don ganawa da kawun nashi dake neman shi ida sukai saa sun samu kawon a gida wanda ya nuna jin dadin shi da amsa mai kiran da yake mai din.
Bayan gaisuwa sun natsu ne kasun ke fadin ba wani abune yasa na kiraka ba sai yar wata magana da ta taso daga mahaifiyar ka a gamay da kai.
Zama ya gyara don ya saurari may mahaufiyar nashi hajiya mama tazo ma kawun nashi dashi duk sunyi tsit suna sauraron kawun.
Yace tazo nan ta samay hankali a tashe take fada min abinda ke faruwa dakai na rayuwa musanman da kai da iyalin ka.
Dama yasan maganan ba zai wuce wanan ba ai yace cikin karfin hali kawu wani abin tace nayi kuma yanzu ?
Yace eh to tace bata ce ba kasan dai tsakanin da da mahaifi akwai wani kulawa da damuwa na musanman shiyasa tazo min akai ya kamata a taimaka ma da addua da wani taimako.
Shine na kwantar mata da hankali nace zan yi wani abu akai don kasan naka sai naka a yadda naga damuwa a tare da mahaifiyar taka.
Yasa bayan mun rabu naje wurin wanj malami tsohone aminin mahaifin mu tun yana raye nakai mashi wanan matsalar taka.
To Alhamdullahi ya karbi maganan namu sosai da muhinmanci ida ya ce in bashi sati hudu zaiyi istihara sai a san abinda za a yi bayan satin hudun dana koma sai yace dani yana bukatsn ganin ka sai kazo da kanka zakuyi magana dashi.
Wanan ne yasa na kiraka don kazo ku samu ganawa dashi kaji may zai fada maka sai musan mafita ga zancen.
Zama Abdulsamad din ya gyara acikin ranshi yana fafin ikon Allah ita kuma mama tanan ta bullo min kuma yanzu bayan tasan ban son irin abubuwan nan tun farko.
Amma a fili cewa yayi to kawu ba matsala amma dai sai dai ina fata aikin shi ba na kaucewa Allah bane dai ?
Murmushi kawun nashi yayi yace haram haram kana ganin munyi kama da masu kaucewa alamarin Allah ne ya kamata ka shedi mahaifiyar ka kasan halin ta.
Yanzu haka ma bata san komai ba tukun a wanan zance nafi son muyi magana ta maza da maza kafin ta samu labarin komai.
Yace hakan na dakyau kawu don nima ban isa can gurin su ba tukun nan muka fara zuwa yanzu sai mun koma zan isa gidan.
Tashi sukayi zuwa gidan tsoho malam illu don su gana dashi sun samu yana ganawa da wani babban mutum don haka suka zau a motar su suna jiran fitowan mutumin.
Bayan mutumin ya fito ne kawun nashi ya ce su taso su shiga daga ciki suka fito daga motar zuwa ciki amma sai Yusuf yace zai jira shi a waje.
Ya juyo yana fadin haba haba Yusuf ya zakace haka kuma mushiga don Allah zai fi akwai abin da baka sani bane nawa.
Kawun yace mu shiga mana ai ba komai bane wanan mushiga daga ciki kawai mugan shi.
Cikin suka shiga tsohon yana kishingide saman farin buzu irin na dabbobi da malaman da ke zama a sama.
Yana ganin su ya dan dago daga kwanciyan manya da yayi nan suka zube don girmamawa suka fara gaida tsohon yace salihu kune tafe yanzu ?
Yace eh baba yaron da kace yazo ne dan wurin ita kanwar tawa hafsat yazo yau daga can abuja inda yake aiki don amsa kiran da kai mashi din.
Tsohon ya daga kai yana kallon su Abdul din yana jijiga kai yace Allahu Akbar yanzu wanan jikan mahaifi ku ne Allah ya jikan malam shaibu suka amsa da amin .
Ya dauko wani tasbaha ya rike a hannun shi ya dan murza ya mikawa Abdul din baya ya ce shine wanan din ko kawu salihu yace shine baba.
Yace canki daya a nan yana mika mashi tasbahan dake a hannun shi Abdulsamad din ya mika ya zabi dayan dan tasbahan tsohon ta girgiza kai yana murmushi.
Ya dago kai yace Abdul yake ko yace eh Abdulsamad yake sunnan kakan shi yaci na wurin mahaifin shi yace to kamar yadda na fada ma zanyi istihara akan jikan nawa Allah ya bani iko nayi.
Sai dai naga abubuwa da dama da suke faruwa da jikan nawa wanda da farko zan iya cewa akwai sakaci aciki alamarin jikan nawa.
Abdulsamad yaya akayi kabar gida haka kana dan musulmai jikan malamai kamar mu kabar abubuwa suka cabe haka a lokaci daya gare ka.
Zama Abdul din ya gyara yana sauraron shi maganar da ta fara zuwa bakin tsohon shi ne na fitar da yayi zuwa kasan waje satin da ya wuce zuwa wasan da suke yi acan na milloners in world.
Zufa ne ya tartso mashi a goshi yadda tsohon ke bashi labarin abinda ya faru acan har ya fadi a wasan ya dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login