Showing 108001 words to 111000 words out of 133935 words
gaskiya miskilanci shi dai ne ya hana ya nuna mata haka din.
Murmushi mommy tayi tana fadin dana ai ba a haka yanzu matan yanzu sai da so ake saye zuciyar su bawai da kudi ba kawai don ba ko wace mace bace kudi yake gaban ta ba.
Mommy dan nan naki in kiyi duba gare shi bai fa san so ba shi don a yadda ya auri Fati da Nafisa ba wai an tsaya anyi wani soyayya bane dasu.
Auren fati dai kin san komai akai hadine na iyayye tun farko ita kuma Nafisa abu biyu ne nake ganin ya kai su ga aure.
Na farko kin san akwai shi da son fararen mata dogaye sai na biyu ita din batazo mashi abanza ba sai da ta asirce shi.
Wani kallo yayi ma Yusuf din dake magana yana kwane ya harde hannayen shi sama kirjin shi kafafuwan shi a harde yana karkada su a hankali.
Ni kake wa sheri haka Yusuf kuma a gabana Yusuf yace ba sheri bane abinda nagani nake fadi ni baka son khadija ne karya ne maka ?
Ke nan ashe sun dade tare da ita mommy ta tambayi Yusuf din cikin son karin bayani gare shi.
Don ni na dauka zuwan nan na su Binta ne kuka hadu da khadija din har kuka santa yace a,a mommy ba zuwan su bane muka santa don gaskiya dama muna tare da ita.
Ikon Allah a mu kuka boyewa mawa dama amma yaran nan kun iya taku har karshe yanzu ashe kuna tare da yarinyar nan kuna nuna ba komai a tsakanin ku da farko ?
Hakan na da kyau da kuka boye ba laifi bane haka yayi daidai nima zan kama baki na inja ga wanan maganan badon komai zamuyi haka ba sai don matan shi.
Duba yadda Nafisa tazo nan tayi muna yanzu bata san da komai ba ke nan ina ga inta sani din sai idan abu ya kankama a tsakanin su lokacin da wani bai iya komai za a fitar da zancen ga kowa yaji.
Don idan ba haka ba maganar sai yazo yabi ruwa azo ba ayi shi ba sai dai babangida ya kamata ka daina wanan halin naka don ba haka ake neman ba yanzu.
Kamata yayi ka bata lokacin ka ka nuna mata so da kauna ta yadda zata saki jiki dakai har a cin ma abinda ake so.
Mommy sheri Yusuf ne kawai yarinyar nan a yan uwa ta dauke mu har ta gabatar muna da wanda take so ta aura fa.
Tayaya zaice kuma ni na kutsa kaina ga abinda ta riga tayi nisa ga wani gare shi da sauri Yusuf yace.
Wanan magana ba gaskiya bane dakai da mamud din da tace wa yariga wa ta riga sani cikin ku biyun kai ta fara sani kasani ba wancen ta fara haduwa dashi ba kaine ta fara sani.
Yusuf kabar wanan zancen don Allah yarinyar da kaji mommy ma ta fada tana da masu son ta akan may zan tsaya bata lokacin gun ta karamar yarinya ma da ita haka da tara maza ai babu komai sai wulkanci a gurin ta.
Da sauri Yusuf yace ta taba yima wullakanci ne da zaka fadi haka san nan kuma kowa ai da karfin shi yake zuwa ya gwada tashi sa,an akan mace idan tai ruwa rijaya idan batayi ba masai.
Banda wanan lokaci kai ka sani so don Allah kubar wanan zancen na Deedar please zan dai yi hakkuri ina zauna da wa yan nan da Allah ya hadani dasu.
Munyi magana da Abba Fati zata dawo dakin ta karshen watan nan ya kuke son inyi da mata uku yanzu biyun ma yaya na iya dasu balle na kara ma kaina wani wahala can.
Aure ne kawai mafita gare ka a yanzu saboda ta haka ne kawai zai kawo fitar da zargin da ake maka akan Nafisa ta mallake ka don ni nasan matsalan ku da Fati wanda ma kowa ya sani in ba wani aure kara yi aka gani ba, bazaka fita bakin mutane da zargi su a kan ba.
Mommy ban damu da abinda mutane suke cewa a gare ni ba tunda nasan ina tsare kaina ga duk wani abin hani.
Mommy tace babangida kada kace haka idan kasan kana son yarinyar nan kada ka bari wani yazo ya kwace ta daga gare ka.
Shawaran da zanbaka shine ba,a kin shawara idan na kwarai ne ka gwada a gani ko hakan ne mafita a gare mu kaga sai a wuce wurin a manta da komai sai fatan samun zuri, a masu albarka.
Murmushi Yusuf yayi Allah yakawo lahadi don litinin yai niss inji maza ranan nasan ni za,a kira da munafuki yafi a kirga gun Nafisa.
Yanzun dai maganan mommy ne mubar wanan zancen a yadda yake a rufe sai munga komai ya kan kama za a ji.
Mommy kaifin basira irin na khadija yasa nake mashi kwadayin ta a gidan shi don khadija yarinya ce mai tunane wallahi.
Mommy ta tashi taje yin alwala lokacin ne Yusuf ke fada mashi gobe yana son ya je zaria da safe akan ciwon shi yaga malamin nan na gurin kawu salisu.
Yace kana ganin zuwan ka wurin shi yana da wani alaka da ciwo nane ko may ko wani abin ne zai kaika wurin shi.
Sai da ya mike tsaye don zuwa sallah ya bashi amsa da cewa akan ciwon ka nake son zuwa can don yanzu wanan shawaran yazo min .
Bai mai magana ba sai mikewan da yayi shima don zuwa yin sallah magariba data gabato a lokacin.
Da dare yana kwance na kira shi muka gaisa na ba maryam ita ma tayi mashi yaya jiki yace da sauki ya gode muka kashe wayan.
Maryam ne tace ni har yanzu sai nake ganin kamar jikin nashi da sauki a yadda naji muryan shi a yanzu nace haka nima nake tsammani danaji.
Daga haka ban kara cewa da ita komai ba ina kwance rigingine ta dauko waya tasa muna kira,a shine naji hankalina yana kwantawa a hankali naji damuwan da nake ciki wanda ban san dalilin shi ya fita a raina har barci ya dauke ni daga hakan.
Washegari na tashi wasai dani wanka nayi na shirya na kama hanya zuwa cikin makaranta don ina da test a ranan gashi banyi wani karatu ba isashe.
Ban fito ba sai yamma lis na fito daga cikin makarantan alokacin yunwa ne ya addabe sosai a sukwane na shigo dakin ina wurgar da handbag dina ina cire hijjab din dake kaina a lokacin.
Maryam kuma bata dawo ba nake gani alokacin don haka na fara kokarin hada jeloup din taliya don ina ganin shine mafi saukin dahuwa a gare ni a wanan lokacin.
Agurguje nake aikin daidai lokacin da na kusan gamawa ne wayana kira ya shigo min sai da na duba abincin sama sama na dauki wayan.
Ban tsaya duba mai kiran nawa ba naji murya shi yana fadin yau ba akira anji jikin nawa ba dan banufen naki ya dauke maki hankali ko ?
Murmushi nayi a baiyane ta yadda har yaji a cikin wayan mommy bata nan ne daka bugo min waya ?
Kina tsoron taji ina waya dake ne a gaban ta komay ?
Ina da kunya da girmama na gaba shiyasa amma ba don tsoro ko wani abuba kawai don kawaici ga manya ne .
Gata zaune tana jin ki ko in bata wayan ku gaisa ne kana fara shi wanan ma ai fadi ne kawai nasan mommy tafita yasa ka kirani kamar yadda nake da kunya kai ma nasan zakaji kunyan waya a gaban ta ai.
Muryan mommy ne take fadin khadija kun koma lafiya jiya ya karatun Allah ya tsare ya kare ban iya cewa komai ba sai daburcewan da nayi a lokacin.
Hello khadija ba kya jine ina magana kin yi shiru nan ma ban iya magana ba shiru nayi mata a lokacin sai naji tayi murmushi.
Wayan na kashe sai da na gama girkin sai kuma cin abincin ya gagare ni duk da yunwar da nake ji din da farko .
Waya na dauko na tura mashi text kamar haka baka kyauta min ba ya zakai min haka ka san girman mommy a idona kuwa ai sai kasa ta zargi wani abu a zuciyar ta a gare mu.
Na gama na tura mai maryam ta shigo dakin tana fadin wai yau na gaji wallahi zama tayi tana kallon yanayin da ta samay a ciki.
May ya faru tace tana kallon fuska na cikin damuwa ga yadda ta ganni din sake tambayana tayi tana maida hankalin ta gare ni.
Ga abinci can ki diba ina kika tsaya har yamma haka lis wallahi mugun malamin nan namu ya tsaida mu haka yau test din yayi wuta sosai tamike tana fadin har kin ci ne ke tana kallo na.
Kaina girgiza mata tace kin ci wani abin ke nan ko naga ko karyawan kirki baki tsaya kinyi ba kika fita yau.
Wallahi da yunwa na dawo sai da na gama kuma naji ban son cin komai ki sha wanu abu mai ruwa kila yunwa ne yai maki yawa ya hanaki cin abincin.
Ta debo ta fara ci tayi nisa ga ci nake cewa da ita kin san may wanan mutumin yai min yau maryam.
Da sauri ta dago kanta tana fadin wani mutumi mamud ko wa nace wani mamud kuma AA fa don ya maidani karamar yarinya wai a gaban mommy zai kirani yai waya dani.
Maimakon inga damuwa itama a fuskan ta sai naga sabanin hakan a fuskanta dariya ta soma tana fadin lalai wanan dan barki ne .
Ya daure tamau yanzu a gurin mommy ta gama sanin komai a tsakanin ku ke nan ?
Komai kamar yaya ya dai daure ni wallahi tace ai maganin ki ke nan tunda bakya jin shawara ai gara da ya fito maki tanan.
Haushin ta naji sosai a rai na don rashin nuna jin haushin hakan dayayi min da ta nuna rashin damuwan ta akaina.
Bayan ta gama ta mike lokacin nayo alwala zanyi sallah itama ta shiga bayin ta dauro alwala muka gabatar da sallah mu.
Zaune nake bayan na idar da sallah ban bar wurin ba sai da nayi isha,i na mike ina nade sallaya maryam ta mike ta dauki heater tare da dauko cup ta hada min shayi mai kauri saida ta gama ta miko min.
Kamar ba zan karba sai dai na mika hannu ko ba komai nasan shan tea din zai taimaka min ga yunwa da ke ciki na.
Tunda na kwanta ban sake bi ta kan komai ba har barci ya dauke ni a haka yadda nake cikin dare na falka na ga ta rufe min kofa itama tana kwance a kusa dani ranan a dakina ta kwana.
Zaune take a falon madam datai ma tsuke tunda safe ta isa gidan madam din a yadda ta ganta sai take tambayan ta ko lafiya haka da safe.
Madam gaskiya yanzu samad ya rikice min tunda na haihu din nan na rasa gane kan shi gaba daya.
Jiya fa a gaban wanan kishiyar uwar tashi yake fada min wai aure zai kara saboda kawai nace sai ya fada min wace yarinya ne tazo gaida shi har take bare mai ayyaba tana bashi ?
Ke a ina kika ji wanan labarin ne wai waya fada maki ne shiya daure min kai tace kai tsaye su hajiya karima ne da suka je gaida shi.
Baki ga irin wullakancin da security din asibitin nan sukai min bane suka fitar dani waje yana kallo baiyi magana ba.
Haba Nafisa kullun ina fada maki magani fa bai ci sai da siyasa da kissa da kisisina da kutungwila na mata.
Ya zama dole yanzu ki bishi a sannu ko banza kin zubar da jinin haihuwa a gidan ki kiga komai da kikayi na asiri yanzu ya karye.
Ai ba karamin hikima bane aka samo na haihuwa asibiti da mata ke yi yanzu bature ya taimaka ma mata da ya fito da wanan hikimar haka na haihuwa asibiti.
Kinga ko da za a dawo da mace gidan ta an wanke komai a asibiti kinga wanan uwar tafiyan na haihuwa yafi komai karya asiri ga mutane ba matan ba ba mazan ba.
Shiyasa iyayyen mu na da basu wasa dashi a gida zakiga da sauri ake fitar dashi gida asamu gefe a binne shi amma mu matan yanzu sakacin mu yayi yawa ga komai wallahi.
Yanzu ya zama dole gare ki ki lalaba shi ki kara sabon shiri sosai a kanshi dan kada yazo ya bijire maki nan gaba.
Zancen kuma aure ni nasan ba dagaske yakeyi ba don ba abinda kika rasa da ake so gun mace yana kuma son ki tsakani da Allah.
Zancen kuma ita yar iskan yarinyar dake dmson maki kutse a gidan ki ta dauke maki hankalin mijin ki tambaya zamu muji da gaskiya ne hakane ?
Idan da gaske ne sai mu san ta inda zamu fito da zancen nata ga wanan irin arziki da ya taso ma mijin ki haka ina zamu bari muba wata daman da zata shigo ciki muna kallo.
Yar iska bamu san ko wace iri bace ita tazo tafimu iyawa dashi babu yadda zamuyi ko wacece zata shigo maki kin san itama ta shirya.
Don kishi da buzuwa ba wasa bane duk matan nahiyar nan namu sun sani shiyasa suke tsoron ku buzaye don cire ice har sayen shi komai tsufan shi ba wasa bane gare ku.
Madam duk da haka ya zama dole gare ni in tashi tsaye in hana gaba da bayan shi motsi a gare shi ko mace ba zai iya daga ido ya kalla da sunan tausayi ba balle so.
Yanzu dai duk ba wanan ba sai fa kin kwantar da hankalin ki ko ta siyasa zaki iya gano gaskiyar maganan gare shi idan kin kwanta amma.
Tace a sanyaye naji zan gwada yin abinda kika ce min din tai mata godiya tare da sallama ta nufi gida tana ba kanta hakkuri.
A ranan ya samu sallama bayan dawowan Yusuf da bayanin abinda ya girgiza shi daga malam don yace a lemon da ta tare shi dashi yasha batare da yayi bissimillah ba.
Yayi arziki akwai tsari sosai na Allah a jikin shi da ba karamin wahala zaiyi ba don ba maganin alheri akabata tabashi ba.
Ya iso gida zuciyar shi ba dadi wanka ya shiga don ya tsabtace jikin shi don baijin zai iyacin abinci ga yadda yake jin kanshi a lokacin.
Yana zaune bakin gado ta shigo dakin ta saba diyar ta a kafada tana rangaji tana zuwa ta azamai yarinyar saman jikin shi itama ta samu wuri ta zauna a gefen shi.
Yadda taga bai sake fuskan shi ba yasata fadin har yanzu abinda ya faru ne kake ma fushi haka ko jikin naka ne har yanzu.
Kallon ta yayi yace may ya faru kamar bai fahince ta ba tace akan maganan nan na asibiti da ya faru raina ne ya baci a lokacin nayi haka ba tare da nayi tunanen komai ba.
Wanan matsalan ki ne sai dai ki sani duk abinda zaki karbo daga yau da sunan malakana a gidan nan kada ki sake karbo wanda zai cuta min haka don ki sani nasan abinda kika zuba min a lemon da kika bani ranan.
Kuma shiya haifa min wanan ciwon danayi ban hanaki yin abinda kike ganin shine mafita a gare ki ba don dama haka yawancin mata kuke da wanan shigeshigen din sai dai ki sani ba zaki taba mallakana ke kaidai ba domin ni din mijin mace hudu.
Yana fadin haka ya mika mata yar tare da mikewa ya bar mata dakin nan ya barta cike da mamaki tana wasi wasin ko dai wani ya fada mai a gidan.
To ina ma wani ya ganni nida na zuba a cikin dakina amma yaya akayi wanan maganan ya koma kunnen shi haka.
Watau ke nan abinda ta zuba mai ne ya jawo mashi haka ba maganin kwarai aka bata ba kena cutar ta akayi akan maganin da ta kashe makuden kudi akan shk a bazan zai tafi ba zaiyi aiki akan shi ba tunda had ya gane may ake ciki.
Ko dai shima yana irin nata ne har yaje wani ya fada mai abinda tayi mai tace kai wanda ke kwance haka ba lafiya ina zai iya zuwa ?
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Na farka cike fa far'a da kuma farincikin zuwan da Mama za tai, ban taba tabbatar da na yi missing dinta sosai na sai da na farka da kewarta. Hamma ya shirya mana abun karyawa ni kuma na gyara gidan a wauta taa na zata gidan zata fara sauka sannan ta wuce gidan Momy. Bayan na gama komai muka zauna muna karyawa sai ga Momy ta kira Hamma a waya tana labarta masa cewar Mama ta zo tana gurinta.
“Laa ba nan za ta sauka ba?”
“Shikenan sai ta sauka nan saboda ga ta ita mai ya ko?”
“Amman na dauka nan zata sauka, har ina shirye