Showing 99001 words to 102000 words out of 133935 words
na saka don ban faye sa takalma mai hill ba.
Wani dan yalalon gyale na yafa akaina duk rabin jikina yana bude na fito don ganin wanda ke nema a wajen.
Motar AA na hango can nesa kadan sun faka shi da Yusuf sai naji gaba na ya fadi ras don ban san may ya kawo su ba nasan kuma Yusuf ya fada mai zancen mamud yanzu haka ?
In bashi ba may zai sa su zo gurin mutumin da bani a gabasa zai zo wurina yau kuma ?
Haka na daure fuska na karasa inda motar tasu take aje cikin daure fuskana na isa inda suke sallama nayi masu irin na addinin musulunci.
Tare da fadin sannun ku da zuwa Yusuf ne ya amsa min sallaman nawa don shi sai wani kallo yayi min ya kawar da kan shi gefe daya.
Nima yi nayi kamar ban ganshi ba a wurin khadija ya kuke ya karatu nace Alhamdullahi kune tafe yanzu ashe yanzu ko na shigo hostel din ina cikin makaranta tunda safe.
Aike ko alhudahuda ya kauce maki ga karatu yanzu kin zama ina zaki karatu, ina kika fito karatu .
Dariya mukayi dukan mu dashi nace sunan da na samu ke nan kuma yanzu yace sunan ki ke nan ai bakiga mutumin ki ya dawo bane banji kin tare shi ba.
Nace ai bansan yayi tafiya balle in gaida shi da dawowa yace a a fa kada muyi haka dake nace to an dawo lafiya ya hanya ya mutanen can ?
Saida ya sauke wani irin sayayan ajiyan zuciya yace Lafiya kalau suna gaidaku ya karatu fa nace Alhamdullahi lafiya.
Allah bada sa a nace amin yace ya naga kin ramay haka may ke damuwan ki kuma ko duk karatun ne haka ?
Nace kila dai idon kane ke ma gizo amma ni ban ji na ramay ba Yusuf yace yaganine ya fada halan dan banufen ki bai fada maki kin ramay ba.
Daidai lokacin Mamud din daya fito office ya biyo ta gurina ya faka motar shi gurin idon ni da Yusuf muka bi motar dashi.
Bai fito ba nima banje gurin shi ba don wullakanci baida kyau Yusuf yace wanan mutumin ya zama maye ana maganan shi sai gashi.
Rai bace ya juya yana kallon shi yace waye wanan din kuma ?
Cikin dakiya na bashi amsa da fadin wanda zan aura ne in sha Allahu nan bada dadewa ba cikin wani yanayi yace What da mamaki nace barin kirashi ya gaida yayye na ai.
Ban tsaya jiran abinda zasu fada ba na wuce wurin mamud nace mashi ga yayyena sun zo yazo ya gaida su da saurin shi ya fito daga motar yazo gurin su su gaisa.
Sun dawo daga tafiya ne suka zo su duba ni ya mika masu hannu da kyat AA, ya bashi hannu suka gaisa dashi yana masu yaya hanya .
Yace khadija zan tafi sai eight zan dawo tunda kina da baki yanzu ya juya tafi ya barmu nan dasu.
Shiru gurin yayi na dan lokaci yusuf ne ya kawar da shirun da fadin khadija wai kina nufin da gaske wanan mutumin zaki aura ko may ?
Kana mamaki ne da ba auren shi zan yi ba zan gabatar maku dashi ne a matsayin ku na yayyena a gaban ku.
Yusuf don Allah ciro mata tsarabanta ka bata mu tafi kar mu bata lokacin mu anan nace ai da kun barshi ai ko ganin ka dawo lafiya yafi tsaraban da zaku kawo min .
Don Allah ciro mata mu tafi don banda lokacin magana yanzu ban son damuwa akwai gajiya a tare dani ka sani.
Fita Yusuf yayi ya bude bayan motar ya fito da wani jakka mai daukan ido yana miko min tare da fadin ga tsaraban ki nan aboki na ya kawo maki daga Italy.
Nayi mamakin ganin wanan katon jakkan yadda ya dauko shi ba tare da matar shi ta gani ba godiya nayi bayan ya aje min jakka a gaba na.
Ya koma mota ya tayar suka tafi na ja jakkan zuwa ciki ina mamaki a raina guri na samu na aje can kuryan dakina ina jiran shigowan maryam dakin.
Sai da ta dawo tana shigowa da jakkan tayi arba tana fadin wanan kuma fa khadija ?
Nace bari ke dai maryam wai tsaraba ne duk wanan kike gani su Yusuf ne suka zo min dashi A A ya dawo daga italy tace bakaji batun ba maye a ciki.
Ban bude ba ina jiran ki dawo mu bude ne da sauri ta karasa wurin tare da jawo jakkan ta fara budewa tana ciro kayan dake ciki.
Dogayen riguna ne a ciki har kala bakwai sai turare da su man shafi da jakka handa bag da sauran tarkacen mata a ciki .
Zip din jakkan taja sai ga set din sarka da yan kune da awarwaro suma a ciki da sauri ta karasa fidowa waje.
Sai da na gyara zama na alokaci don mamaki sai ta kara fida wani agogon hannu na mata mai ruwan gold mai daukan ido shima.
Nauyi da kunyan kaina naji maryam ta dago kai tana kallona da mamaki fal a fuskan ta tace khadija kin ga wanan kayan kuwa ?
Nagani maryam nace mata tare da lumshe idanuwana ni kadai nasan abinda nake ji a lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Jikina yayi sanyi sosai da kayan da naga ya sayo min musu kya dagani kasan ai kashe kudi a wurin sarkan maryam ta daga tana fadin.
Wanan kan kizo kiji kudin shi zai kai a kala dubu dari uku fa saurin kallon ta nayi nace kai haba wanan dai kila mafa fashion ne kawai.
Khadija wallahi gold ne haba baki ganin shi ko agogon nan ban debe tsamanin shi ma fashion bane nace a wani dalili zai sayo min kaya haka masu tsada bayan yasan iyayyena talkawane idan naje gida dasu may zan fada masu akan wanan kayan haka ?
Rigunan ta sake tabawa tana daga su tace wallahi ko kayan nan anan zasu kai dari biyu kila koma sufi zaune nakai ina fadin shi wani irin mutum ne da baijin wuyan kashe kudi haka ?
Maryam dariya tayi tace khadija ke nan baki san ko waye shi ba yasa kike fadin haka bafa karamin mutum bane wallahi kudi na shigo mai ta kowani hanya.
Zasu iya sai da fili daya a wuni su samu milayan dari riba bakomai bane wanan a gare su wallahi kwanaki da mijin yaya na zai sai wani fili AA akace sai ya gani ya sa mashi hannu zai iya samun filin.
To mutum da ke samun kudi haka don ya sayo wanan ai kamar ki jefa allura ne a cikin teku gare shi gashi nan muna ganin shi a banza amma mijin yayana yakai wata uku yana neman ganin shi bai samu ganin shi ba.
Da sauri nace shi din tace wallahi Allah khadija wanan AA din kuwa shine don na tambayi anty na nayi mata kwatancen shi tace shine kuwa wallahi ba karamin kudi yake dashi ba ai.
Banda abinki duk wanda kika ga ya auri buzuwa gidan shi har ta zauna haka ai ya mallaki abinda ya mallakane.
Dubi shadda da tasa ranan da gwalagwala a hannun ta da wuya ke ko shaddan nan da zaki ji kudin shi zaki sha mamaki wallahi.
Ido na lunshe na koma na kwanta ina tunane a raina gaskiya ya zama dole in raba dasu kada suzo su batani haka da itin kayan nan in zo gaba abin ya damay ni na saba da saka mai kyau in sha in kuma ci maikyau.
Ranan da banda mai bani irin wanan yaya zanyi ga iyayyena tallakawa ne lis muna neman abinda zamuci a gidan mu.
Muryan maryam ne ya dawo dani daga tunanen da nakeyi tana fadin khadija zaki iya samun fiye ma da hakan gun samari don kyauki ne ya jawo maki haka .
Don ke din baki da maraba da yan buzaye dole ne na miji ya ganki ya rude haka sai dai shi AA nashi sallon son yazo daban da na sauran maza ne.
Yace dake sona yake yi da kike fadin haka kawai dai mutunci ne a tsakanin mu kune dai dake da Yusuf kuke ganin haka din amma ni ba wani abu makamancin so daya taba hada ni dashi.
Balle yanzu nasan da wuya su kara dawowa inda nake don na fada masu mamud zan aura kuma har na gabatar dashi a garesu sun gaisa dashi dazun.
Kikayi may khadija amma wallahi baki kyauta ma kanki ba wanan wani irin cin fuskane haka kikayi masu lalle kan da wuya su dawo gurin ki kuma sai dai da yake maza ne basu fushi da abinda suke so kai tsaye.
Mun dauki lokaci muna maganan da ita har dai nagaji na kyake ta tanayi ita kadai na bata baya.
Yau da wuri muka dawo dawo daga class bamu dade irin yadda mukan dade acikin makaranta ba maryam ta rigani dawowa har na samu ta gama abinci ko.
Dafa dukan manja yaji atarudu ta hada muna sai naman datayi amfini dashi a ciki danye zaune nake ina cin don ita tace tasha tea da tadawo don maryam bata wasa da cikin ta ko kadan.
Na kusan gama cine wata Ruth Samuel ta shigo dakin tana cewa ina da bako a waje yana jirana maryam ne ta kallo ni bayan Ruth tafita daga dakin tana fadin yanzun haka mamud ne dan kadafin tsiya ya biyo ki.
Nace kada kiga laifin dan bawan Allah a banza don nagane ke son wanda baisan kinayi ba kike yi yasa kike ganin laifin mamud din.
Hijjab dina karami na dauka ina sawa nake maganan na fita waje ban jira may zatace ba kada ta bata min rai.
A zatona mamud din ne yazo amma ina fita sai banga motar shi ba a wurin fitowa Yusuf yayi daga cikin motar da yazo da ita yana min hannu.
Zuwan Yusuf din ya bani mamaki matuka don banyi zaton zasu kara dawowa inda nake ba kuma .
Na iso inda yake tare da sallama yanayin shi kawai ya nuna min bai cikin dadin rai a lokacin yace ya karatu nace Alhamdullahi.
Shirune ya dan biyo baya sai ido daya kura min yace dama nazo ne neman alfarma a gurin ki idan zaki iya yi min .
Da sauri nace in zan iya may zai hana in maka tunda har kataso kazo gare ni a wanan lokacin haka.
Ajiyan zuciya ya sauke yace ina son ki shiga ki shirya yanzu ki fito in kai ki asibiti ki gaida Abdulsamad ne yau kwanan shi biyu kwance bai da lafiya ya dawo da ciwon ciki sosai tunda ya dawo.
Subbahanallahi na fada mace ciwon ciki kuma kodai yaci wani abin ne baku sani ba yace ciki da kai yake fadin yana mai ciwo tun kwana biyu da dawowan shi waje.
Ko ranan da muka zo wurin ki cikin karfin hali nasa shi muka zo ke kuma sai kika bata muna rai da dan banufen ki.
Murmushi nayi nace kuka dai bata ranku ga banza amma ni ban bata maku raiba gaskiya yace kin ko san kishin maza yafi na mata khadija ?
Kishi akan may zaiyi kishi kuma don dan wanan magana kawai yace wallahi ba don nasan Abdul tun farko baida lafiya ba da sai in ce har da maganar dan banufen nan ya sashi ciwo haka.
Sai dai bai karamin magana ba tun wanan lokacin a kan ki yanzu ma ni naga dacewan haka nazo daukan ki muje ki duba shi don Allah.
Nace gaskiya ba zan iya zuwa ba da sauri yace khadija kada muyi haka dake mana na dauka zan iya saki abu kiyi don ni koma badon niba ai yaci kije ki gaida Abdulsamad din tunda akwai mutunci.
Kai na girgiza tare da fadin Allah dai ya bashi lafiya amma ni ba zan tafi ba idan ma naje matar shi ta ganni may kake son in fada mata kuma don komai tamun tana da gaskiyan ta.
Balle ma bazaku hadu ba don ita tana gida bata faye zuwa ba sai sa a mommy ce dai a gurin nashi take jinyan shi.
Ko zan tafi bani kadai zan tafi ba sai inda maryam na fada yace gaskiya ne hakan yana da kyau ai wallahi ni ma kin ga na rude ban ko kawo haka ga raina ba sai yanzu.
Don Allah ki daure kizo muje khadija yin hakan yana da kyau sosai wallahi ciki na koma na fadama maryan zuwan Yusuf din tace muje don Allah ki duba shi gaisuwa ai ladane gare shi so sai.
Mun shirya ba laifi don zakace ba asibiti zamu tafi ba don maryam ne ta saka in shirya haka don kada muje mu hadu da buzuwa a can ta raina muna wayo.
Nace in sha Allahu ma baza mu hadu ba har mu dawo muka fito muka kama hanya ina gaba tare dashi maryam na zaune a baya.
Yusuf ya kawar da shirun da motar yayi a lokacin yace nasan zaiyi mamakin ganin ku yau saidai don Allah ki tuna a wani hali yake yanzu.
Nan dai ma banyi magana ba sai murmushin da na danyi kawai yace maryam khadija ta fada maki abinda tayi muna ranan ko ?
Wallahi ta fada min bata kyauta ba ai nayi mata magana kasan tayi nisa yanzu ga son dan banufen nan bata jin kira sai ta kai.
Da sauri yace ehyehh tayi nisa fa kikace har ya shiga gidane bamu sani ba komay ?
Amma khadija idan kin muna haka baki kyauta muna ba wallahi yaya zaki yi da abokina kuma idan kika fitar da wanan mamud din ?
Nace Allah kadai yasan wa zan aura yanzu da kuke wanan magana niko mamud din ina shakku a gare shi ne don ban faye son mutum mai mata ba a rayuwana .
Murmusgi Yusuf yayi yana kada kanshi yace yanzu dai kikai magana dama nayi zaton don ki musguna na munane kikai hakan.
Nace a a wallahi ni gaskiya na na fada maku har cikin raina bandai son mai mata ne a rayuwana yasa nike shakkan shi.
Tsaya yayi ya sayo kayan dubiya asibiti ya dawo ya shiga motar muka tafi dan jefi jefi yake dan jan mu da magana har muka kai inda zamu.
Motar ta shiga cikin Turkeys hospital ya samu wuri ya faka muka fito zuwa cikin dakin da aka kwantar dashi wurin tsit yake baka cewa akwai mutane saboda natsuwan da wurin ke dashi.
Da sallama muka shiga dakin yana gaba muna bayan shi biye har zuwa cikin dakin yana kwance rai,rai ya doran hannun shi daya saman goshin mommy tana zaune gefe saman kujera tana duban wayan hannun ta.
Sallaman mu yasa ta dago kan ta tana amsa muna tare da zuba muna idanu don bata sheda ko suwaye tafe don maryam ce ke bin Yusuf din.
Sannun ku da zuwa tace muka amsa da sannu mommy muna gaida ita sai can tace khadija kune tafe kun san baida lafiya ne ashe , ?
Yusuf ya karba da fadin wallahi sunji mommy yanzu na gansu shigowa nan din na karaso dasu ya mai jiki nace da mommy .
Mai jiki gashi nan yaji sauki yau ai mun ga hankalin shi jiya kan da muka zo abin ai ba dama wallahi.
Maida hannkali na nayi inda yake kwance yana saye da wandon three quarter fari sai yar riga irin na shan iskan maza din nan mara hannu amma rigar na da kauri blue colour.
Ya jikin nace a cikin wani irin murya mai taushi da sanyin jiki tare da dan kura mai manyan idanuwa na a hankali ya sauke hannun shi saman kan shi yace da sauki.
Shirune ya biyo dakin na dan wani lokaci Yusuf ne ya karaso zuwa bakin gadon suna magana dashi wanda ba lalai ne mu jisu ba.
Ledan da muka shigo dashi ya mika wa mommy yana fadin mu muka zo dashi tace kai khadija ina laifin zuwan da kukayi ke da ke makaranta kikaje yin wani dawainiya kuma haka ?
Tana nuna mashi daga inda yake kwance tare da fadin kako gane ta yarinyar nan ne kawar su Binta da suka kwana wurin ta kawar matan officer na layin mu.
Murmushi yayi mata kawai ba tare da yace komai ba muna nan tsaye jin yace yace Deedar akwai ayaba ki bare min in ci kai na gyada mai ba tare da nasan ko akwaishi ba.
Na bude ledan ina ciro ayaba daga ciki na fara barewa na miko mai tashi yayi zaine ya dan jingina jikin shi da filo ina mika mai a hankali yana karba dakin yayi tsit a lokacin.
Kofan aka turo wasu mata ne suka shigo dakin hamshakai dasu idon su caraf a kaina a yadda nake tsaye wurin kan shi ina bare mai ayaban ina bashi yana ci ko mommy ido ta zuba muna tana kallon mu sai take gani kamar da can musan junane ko kuma namu daine yazo daya bata sani ba.
Shigowan matan ya dauke mata hankali ga barin kallon mu ta maida hankalin ta gare su suna gaisawa dasu.
Kun fara jerabawa ne ko da saura