Showing 93001 words to 96000 words out of 133935 words
ke nan da buzuwa matar shi da Fauziya kanwar shi da su mommy don komai da ake shigowa dashi gidan buzuwa ta hana aba mutanen Abdulsamad sai idan kaje wurinta munafunci zata baka ko matan abokan shi haka bata ba abin sai taga dama.
A daidai lokacin da suka gama rikici da Fauziya da tace sai an raba an basu nasu, ranan ta murje ido tayi ma buzuwa tas a gidan abinda a da suke tsoron mata.
Shigowan mu ne gidan ya dawo da hankalin mutane a gare mu su tambaya ina suka shige haka ne ni da zainab ce da Binta sai maryam muka shigo daga karshe gidan ina tako dadaya duk kan mu kwaliyan mu ba laifi.
Tsaye yake yana magana a cikin fada muka shigo da sallama falon sai da ya so rudewa a lokacin da mukai arba dashi nayi saurin kawar da kai na mommy da na hango zaune na nufi gurin ta har kasa na zube ina gaida mommy ta dafa ni tana fadin khadija kina garin nan nazo na dade a nan ban ganki ba.
Yanzu ma nasan don su Binta ne kika zo gidan nan da bamu gan ki ba na san har mu koma Nafisa dake zaune ta cika ta batse sai huci takeyi tana kokarin son tuno a inda ta san fuska na amma ta kasa ban dade ba muka ce da su zamu koma ko dakin bamu shiga ba.
Binta na fadin ba wani abu a basu mommy shi kuma maigidan ns fadin Fauziya tashi ki hada nasu snack din nan da aka yi da drink's lokacin har mun kai kofan fita daga katon falon nasu ko.
Binta da zainab dake bin mu a baya ne ke fadin ku tsaya don Allah a kawo maku abin buki kutafi dashi na juyo nace da ita.
No ku barshi kawai dama mommy muka zo gaidawa a a yan mata ashe kun samu shigowa bukin ku ma ?
Muryan Yusuf ne dake fitowa daga cikin motar da ta parker a gaban mu yake fadin haka maryam ce ta bashi amsa da fadin wallahi fa.
No ba buki ya kawo mu ba munzo mu gaida mommy ne tsaye Binta tayi tana kallon mu da mamaki tafiya na fara yi zan wuce wurin Binta tace don Allah ku tsaya ku karbi abin buki mana.
Nace a barshi kaya zai muna yawa idan mun tsaya daukan wani abu kuma ke khadija wani kaya ke gare ki banda handa bag da kika rika nace shima ai kaya ne ko.
Khadija ya kira suna na da karfi na juyo tsaya mana ku amshi kayan bukin maryam tace ya Yusuf muna sauri ne mu samu abin hawa kasan unguwar nan naku idan yamma yayi akwai matsalan abin hawa.
You known each other ne dama ?
Zainab ke tambaya cikin mamaki No ya dade da na san su ba irin familier din nan ba dai na fada ina yatsune fuskana.
Barin sauke ku mana Yusuf yace da sauri nacevka barshi kawai zamu karasa ai na fadi ina ci gaba da tafiya na nufar get din zuwa waje.
Da sauri ya shiga babban motar Abdul din yana fadin ku shigo in sauke ku nasu in ki amma Binta na ta kaudi motar yayan sune ai in shiga a kaimu hostel din .
Zainab tace friend ku shiga don Allah bari muje tare a sauke ku sai yaya Yusuf ya dawo damu abubuwa ake fitowa dashi daga cikin gidan wai duk namu .
Mommy ne ta fito waje lokacin da zamu shiga motan tana magana dani tace ga abin buki nan yayan su Binta yace a baku kuje dashi wai angode nace lokacin shima ya fito wajen.
Yusuf ina zaka ne yace zan sauke su khadija ne hostel in dawo barin bi ka mu fita daga can zan tafi gidan MD dayani.
Ga mommy tsaye ta kura muna ido dole na yarda muka shiga motar a tare dashi dasu Zainab da binta ya juyo yana fadin ku kuma ina zaku sukace zamu raka friend din mu ne yaya.
Ba yanzu zamu dawo ba fa ku fita don Allah rike zainab nayi nace a tare zamu fita ke nan don saboda su nazo nan din da kuma mommy.
Sun yi mamakin jin maganan da na iya fada ma yayan nasu wanda suke matukan tsoro da girmamawa su.
Sun dauka zai yi wani abu sai sukaji yayi shiru bai sake magana ba sai tsawan da ya daka ma Yusuf akan ya tsaya mana su sauka kokarin sauka nike yi zainab tace ki bari gobe zan shigo wurin ki da safe ai.
Ta fice daga motar da sauri ta rufo kofan da mu a ciki yusuf ya kama hanya ya tafi daga gidan ba wanda yayi magana a cikin motar.
Ya Yusuf ka tsaya dan Allah in sauka ko sauraro na bai yi ba sai tukin mota yake a hankali kwance abinshi.
Tsuki na naja daga inda nake zaune muryan shi ne naji yace kibi a hankali fa kada ki bata muna rai a nan sai kace wace aka ce za a sace ta.
Nace ai in ma kunyi niya zaku iya hakan don iya yaudaran ku dariya sosai Yusuf yayi yace munyi kama da mayau dara ke nan khadija.
Kasan ta iya shirme wani lokaci mu sace ki muyi may dake ai ba irin ki zamu sata ba har in muna satan yan mata.
Yusuf yace nikan irin su zan sata don yanzu suna danyun su shar ai kaga daidai sata ke nan nace ai dama nasan zaku iya haka ba sai kun fada ba.
Yace Yusuf ya tsaya a wani guri da ake sai da kaji ya mika mai kudi ya sayo muna da abinsha mai sanyi Yusuf ya fita ya barmu a motan tare dashi.
Naji dadi da maryam ke cikin motar a lokacin ba a barmu mu biyu ba ko kallo gefen da yake ban yi ba maryam ne ta dan zugure ni wai in yi mai magana.
Na kawar da kai kamar ban gane abinda take nufi ba tunane nake ta yadda zan fita motar nasu a lokacin Yusuf ne ya dawo dauke da ledoji a hannun shi ya shigo motan yana aje kayan a gefen shi ya ta da motar muka tafi.
Ban akara ba sai gamu bakin hostel din mu da sauri nayi niyar fita daga motar amma motar tana rufe har lokacin ga sanyin A C motar daya damay ni.
Suna zaune ba wanda yai magana a cikin su har dan wani lokaci can naji Yusuf yace daidai lokacin da nake fadin ka bude mu fita mana.
Shikuma yana fadin gaskiya khadija ba a kyauta maki ba a kyauta maki ba da sauri ya dago kai yana kallon Yusuf din dake magana.
Yusuf fitar masu da tsaraban sunan su su sauka don Allah zaka tsaya wani magana kuma yace ya zama dole mu bata hakkuri don bamu kyauta mata ba.
Da akai mata may kuma ya tambayi Yusuf din cikin tsare shi da ido yace ai kaine mai lafin yaya zaka saka ta saba da kai daga baya kuma kazo ka share ta haka ba dadi wallahi irin haka kaima ka sani.
Please ka fitar masu dashi mu tafi don ina da abinda nafito yi yanzu ba wanan ne a gabana ba zaiyi magana yace fito masu dashi nace please.
Ai da ka barshi zuwa kawai mukayi in gaida mommy da su anty Fauziya da suka zo ya sake fafin don Allah ciro mata mu tafi ya sake maimaitawa.
Fita Yusuf yayi daga motar ya bude bayan motar yana fitar da kayan da aka saka a bayan motar sai da nayi mamakin ganin yawan kayan da aka debo muna mu kadai.
Haka na dake fuska daure na fita daga motan ban koyi masu godiya ba na fice fuuu a motar Yusuf ne ya tsayar dani yana fadin haba yar mama ki sasauta wanan fushin naki ku fahinci juna da mutumin ki.
Dan Allah yaya Yusuf ka daina hadani da wanan mutumin don ba ajina bane shi mutumin da yake under control din mace macen ma yar haure ba jinsin nahiyar mu ba.
To waima may kake son in kula shi aka in kula shi ya bata min lokaci ya hana mutanen arziki zuwa gurina ko may ?
Subbahanalahi ina wanan maganan ya fito haka a bakin ki baki taba tunanen Abdulsamad son ki yake bane ko may ?
Da sauri nace so so fa kace na girgiza kaina nace a,a dama kace kawai yana amfani dani ne wurin cin ma wani manufa nashi da zan yada da hakan amma ba wanan kalamin naka na so ba.
Sam na sake girgiza kaina karo na biyu tare da fadin wanan wani sallon yaudarane kuma ka dauko yanzu.
Yace to ko ki yarda ko kada ki yarda ni yau na fada maki son ki Abdulsamad keyi har cikin ranshi wallahi bai dai iya fitowa fili na ya fada maki ko ya nuna maki hakan.
Wani irin kallo nayi mashi tare da girgiza kaina na juya na fara tafiya ina jin wani bacin rai a zuciya har na shige ba tare da na dauki komai nasu ba da suka aje muna.
Kwanciya nayi ina tunane a raina maryam da wata suna shigo da kayan daki har suka gama ta debar masu ta basu daga ciki.
Ta dawo ta zauna tana ta faman cicire kayan guda guda tace kai khadija akwai wanda ya samu abinda muka samu kuwa a wurin nan jifa wanan uban kayan da aka loda muna wai duk namu ne mu kadai ina zamu da wanan kayan haka ?
Sai lokacin na dago kaina ina duban kayan data tara a gaban ta na maida kaina saman filo na kwanta magana Yusuf ne ke ta min yawo a zuciyana har wanan lokaci.
Maryam ne naji tace wallahi khadija na yarda da Yusuf daya ce son ki Abdulsamad keyi har cikin ranshi ba karya ya fadi ba don ni na dade da sanin haka tun tuni.
Ina jinta saidai ban yi mata magana ba har ta gama fadin abinda zata nace ke idan nace zan bata lokaci ga wanan mutumin ba zaki min fada ba maryam.
May ke cikin gidan irin su Abdulsamad banda tarin rikici da tashin hankali kulun ni kwadayi bai kai idona ya rufe ga abin hannun shi ba wallahi.
Salama nike nemawa rayuwana ko yaushe ba zan tsaya in yaudari kaina ga abin da nasan yafi karfi na tun yanzu akan matar shine fa ya daina kulani ke ma kin san da hakan.
Tace da sauri Kin san uzurin shine da zaki yanke mai wanan hukucin haka khadaji idan yana son ki ko Allah ya kaddara akwai aure a tsakanin ku matar shi ta isa ta hana ne ko tayi kamar Allah ne.
Sai dai in kece zaki bata kafan da zata hana din ta dauki kanta inda Allah bai kai ta ba kinatsu khadija ki san may son ki da zuciya daya.
Ni na fahinci A,A irin mazan nan ne da furta kalman so ke wahala a bakin su sai dai suyi ta nuna ma mace alama amma basu iya furta mata da baki.
Nace shine kike son in tsaya wahal da kaina gare shi ko may ni koda ya furta bai mun ba don ba zan so shi ba ma ban ra,ayin mijin tace a rayuwa na.
Ban yarda ba wallahi ke ma kina son shi kishine dai ke damun ki ke ma kina ganin kamar ya mutu akan matar shi ya daina kulaki don ta.
Haka zuciyar ki ta fada maki ashe nace mata bata ko fada maki daidai ba ke nan idan tace maki nima ina son shi.
Tace idan baki son shi may yasa yanzu kika rage mashi tsiwa irin da don da dane da yanzu kunyi fada a motan nan yafi a kirga.
Nace amma kin san wulakanci bai da kyau ko saboda haka ne na kyale shi badon komai ba yanzu dai ai kanku ake ji ku karaci gulman ku ku dawo hanya dai.
Indai har kin san kina son shi ya kamata ku daina wanan shirmay tun wuri tun bazuwa bata kara kwace maki shi ba kuma.
Ta kwace shi mana shi ya shafa bani ba nace mata cikin kunan rai tace dukkan ku dai ya shafa khadija bashi daya ba kin dai san so yanzu koda kike kirarin baki taba so ba a rayuwan ki.
Washegari a wurina su Binta da zainab suka wuni don ba shiga school Friday ne yau sai sunday zasu koma kd.
Don haka da yamma muka shiga gari dasu yawo sunyi mamakin sanin garin da nayi don sanin da sukayi min ba mai rigima bace ni.
Munsha yawo sosai rana sai dare muka dawo hostel dasu bamu dade da dawowa ba wayan Binta yai kara ta dauko da sauri tana dubawa take fadin nashiga uku yayane fa ke kirana zainab.
Zainab tace dauka mana kiji may yake kiran mu nasan dai sunga dare yayi ne bamu dawo ba suke neman mu ta dauka tana fadin hello yaya A,A yace kuna ina ne har wanan lokacin hankali mutane ya tashi.
Tace gamu nan wurin khadija tun dazu ita ce zata rako mu mu dawo yanzu yace tana da motane tace a a yaya karatu fa take yi ina zata samu mota kuma ?
Yace ganinan zuwa in dauke ku yanzu ku jirani in zo yace ya kashe wayan kallon ta mukayi nace yanzu ba zai bari ku kwana nan ba ke nan ?
Tace tunda kika ga yakiramu ai haka yake nufi damu nace bari yazo ni zan fita nagan shi da sauri tace ke baki san halin shi bane bari kawai yazo din mu tafi gobe sai mu dawo muyi sallama ba shike nan ba.
Zainab tace ni nafi sakewa a nan wallahi amma can gidan duk a tukure muke wallahi shegiyar matar nan tashi bata bari mutum ya wala a gidan.
Dariya nayi mata sosai da take fadin haka ba a jima ba sai gashi ya kirats yana fadin su fito nace barin je in gashi tace bari dai mu tafi ban son fadan nan nasa wallahi.
Maryam tace ku bari ta fita ta gan shi mana ai zai yarda ku kwana nan idan ta roke shi baku san ko waye bane yaya AA kawai.
Mikewa nayi na fita batare da na kula da kayan dake jikina ba a lokacin yana zaune a cikin motar shi ya fitar da kafa daya waje yana shakan iskan dake kadawa a lokacin .
Na iso gurin sallama nayi mai ya dago kai da sauri yayi min wani irin kallo ya kawar da kan shi kuma kallon da ada in yayi min nasan na bata mashi rai ke nan.
Sai dai yau ban san may yake nufi da hakan ba da yayi min shi nace don Allah ka barsu su kwana guna tunda gobe ne kawai haduwan zasu koma gida jibi.
Ya sake kallo na a karo na biyu yace su ke son kwana nan din sukace maki nace suke son hakan bani ba yace to shike nan indai zaki basu kulawan da ya dace may zai hana nace mai sai yadago ya dube nayi saurin kawar da kaina gefe daya nima.
Nace na gode na juya zan tafi naji yace khadija nayi saurin juyowa sai naga ya kada kai kawai sai kuma yace may yasa kika fito waje haka da wanan kayan ?
Don Allah ki bar fitowa haka na roke ki please kallon kayan dake jikin nawa nayi sai lokacin na ga kayan don na cire abayan da na dora sama da muka dawo daki.
Ki kula daga yau ban son ganin mace a waje haka gara idan mace tana cikin gidan ta zata iya amfani dashi haka ko ga mijin ta.
Kai na rausaya cikin wani irin jan aji da ban san nayi ba nace ga matar da bata da miji fa itama sai a hanatayin yadda take so ko may.
Yayi tsuki yace na dai fada maki ban so ki kula daga yau kada in sake ganin ki haka a waje daga yau.
Jikina ne yayi sanyi na kasa yin wani magana kuma ya kawar da kan shi gefe bai sake magana ba sai ya mayar da kafan shi daya dake waje tare da jan kofar motar yana fadin ni na tafi sai da safen ku.
Kin dai ji abinda nace dake ki kiyaye duk abinda nace dake ban so ban so ne ya rufe motar yai mata key gurin nake tsaye kamar wace aka kafe har ya bace ma gani na naja kafata na koma ciki.
Ina shiga na samay su har sun shirya suna jiran shigowa na dakin nace dasu yadda na gansu a takure yace ku fito bai yarda ba wai.
Zainab tace ai dama na sani don kada kice mun hana ki ne do ba mu son kwana din amma ninasan ba zai yarda ba ta fada a sanyaye.
Tare da fadin tashi muje Binta binta din taja wani tsuki tana shirin mikewa nace ya tafi fa tace don Allah ki bari nace wallahi ya tafi tun dazu na tsaya magana ne a waje.
Wai da gaske