Showing 114001 words to 117000 words out of 133935 words
wai ina damun ta tana karatu.
Na fito daga ciki na dora a baya saman kayan ina hararan khadija na iso inda suke tundaga nesa ya watso min harara yi nayi kamar banganshi ba na kawar da kaina ga kallon shi ina gaida su baki daya.
Har muka gama gaisawa da Yusuf yana tambayana karatu da kwana biyu nace lafiya maryam taso ta bar gurin da dabara Yusuf yace ta tsaya ai .
Munzo muyi maku sallama ne zamu tafi umura gobe idan Allah ya kaimu mukayi masu adduan adawo lafiya Allah yasa a karbi ibada.
Daga ida yake zaune baiyi magana ba tun zuwa su yace ashe baki jin magana baki daina saka kaya irin wanan ki fito dasu waje ba ?
Nace wasu kaya kuma ina duban kaina da shigan da nayi yace ai kema kin sani yaya kika fito waje dazun ?
Haba yaushe zaka daina samin ido hakane aiko wanda zan aura yanzu bai isa ya zaba min kayan da zans saka ba a jikina sai idan naje gidan shi.
Murmushi mai kama da yake ya sakar min yana fadin au haka ne fa kuma gaskiya na faye sa ido.
Yusuf yace kajiki da wani magana kuma akwai wanda yafishi sanin ya kamata akan ki ne yanzu dole ya nuna bacin rai ga abinda yake da iko dashi.
Dariya nayi sosai nace sai kace nice buzuwa ko anty Fati wanan dokan yanzu ai sai daddy na yakai can.
A bari a rabu lafiya kin ga tafiya zai yi kada a rabu kuna halin naku kuma kinga zai tafi dake a zuciya kila ba zai maki addua ba idan yaje.
Addua kan kulun ai mahaifa na suna min shi kuma yana tasiri gare ni wanan bakin naki kuwa anya wataran bazai mutu ba khadija ?
Dariya nayi nace yau dai kun tuna mu ke nan aka kawo muna ziyara haka yace bakin ki zuwa gida ki kara gaida shi da jiki ba ai shi baiyi fushi ba gashi yazo.
Dan satan kallon shi nayi naga hankalin shi baya gare mu nan dai mukayi sallama dasu suka tafi.
Da yamma ina kwance sai ga kiran shi ya shigo min a wayana nayi makai dalilin kiran shi sai cewa yayi fito gani bakin hostel din ku kai tsaye kamar yadda ya saba ya katse kiran.
Na shirya na fito shi kadai na sama kamar yadda nayi tsamani bayan na gaidashine yake fadin dawowa nayi don dazu muna barin wurin nan Abba ya kirani.
Yana son mommy ta koma gida kafin in wuce don haka nake son ki rakani musai masu abinda ya dace diban lokaci nayi a wayana bakwai da rabi na dare don haka akwai lokaci.
Ciki na koma na shirya sai da na zauna ya tayar da mota nace kana dai son ka ban wahala kai da sukai ma hidima dakai da matar ka ni may ye nawa a ciki yanzu.
Na dauka yanzu ma ai da shigan dazu zaki fito tunda ban isa in baki umarni ba ban dai ga dama bai don ba mai iko dani a yanzu.
Allah yakaimu in dawo lafiya zanyi maganin wanan fitsaran naki lokaci daya .
Ka fara maganin fitsariyar matar ta gida mai fita rabi tsira wace bata damu da hijjab ba balle gyale kafin kazo kafa min dokan ka .
Sallon yaudara kawai zaka wani gama kalle min jiki kawani ce kai baka son haka na bayan sai da ka kalle ni tsab.
Dama badon akalle ki kika saka ba idan ni kadai zan kalla ba matsala bane a gare ni wasune kawai ban son suga abinda nagani din.
Don kanawa a gare ni zaka hana wasu su kalle ni kada ka mata ni yanzu a kasuwa nake banda hakkin kowa ai kaina amma ga masu hakki baka tsa, , ,
Jinin hannun shi kawai nayi a jikina yana fadin barin fara gwadawa in gani ko tayi min tunda a kasuwa kike kinga idan yayi min basai kin tallata ma wasu mazan ba.
Bugu nakai ma hannun nashi sosai da yakai ma jikina yana shafawa bai san ina yi ba sai kokarin gwaucewa nake yi ina buge hannun shi.
Fuskan shi a daure bai fasa min abinda yakeyi ba wuri ya samu ya sauka daga titi.
Da karfi nace bude min in fita ina kokarin bude kofar motar a gigice hannun shi naji yana cire min dan gyalen da na yafa saman dogon rigar da nasa.
A take gashin kaina dana tufke daniyar in na samu lokaci inje gurin kitso ya bayana a fili hannu yasa yana wasa da gashin har zuwa inda ya tsaya.
Take naji wani hawayen bakin ciki ya silalo min a fuska na haka bai sa ya daina abinda yake min ba sai ma ji danayi ta rungumay tsam a jikin shi yana sauke wani irin numfashi yana shafa na son ran shi.
Kara sautin kuka na nayi a lokacin sai naji ya sake ni yana fadin are you crying bocouse of dis akasuwa fa kike yanzu.
Hannun shi yakai saman fuskana yana wasa da hawayen dake zubo min din sai kuma naji ya rungumay ni zuwa jikin shi tsam na dan wani lokaci.
Sai da ya gaji don karan kanshi naji ya sake ni ya koma saman kujeran motar ya kwanta yana maida numfashi a hankali.
Kaina na dukar naci gaba da kukan abinda yai min din can kuma naji ya tada mota a hankali ya hau titi ba tare da yayi magana ba .
Kofan bakin wani plaza mai girma ya tsaya ban taba sanin akwai wuri haka a abuja ya bude motar a hankali tare da fadin fito mu shiga ki zaba masu abinda ya dace dasu kuma ki share wanan hawayen kada ace satoki nayi.
Sai lokacin na dago kaina na dubi wurin nace ka sani har kullun Allah ba zai taba baka sa a akaina ba mayaudari kawai.
Dariya naji yayi yana bude motar yace banda wanda Allah ya bani yanzu a kanki kuma koko kina nufin karfin ki ne ya kwace ki a kaina .
Kuma ki daina kira da mayaudari don da yardan ki muka fito nan ki sani banda niyar aikata komay yanzu a gare ki amma ki aje a ran ki time will soon come .
Ko yanzu ke kikaja in maki haka da wanan bakin naki da bai taba mutuwa don ki san irin abinda zaki fada ma mutum.
Fita yayi ya zaya ya bude min gefen da nake zaune na sauko motar a hankali na fito don girman jeep din nasa.
Mun fara tafiya naji ya rada min a kunne anya kuwa ke ma ba buzuwan bace deedar wanan irin gashi da jiki mai dadin tabawa haka fa ?
Hararan shi nayi idon shin kyam a kaina ya sake fadin nayi haka don ki san har gobe nafi wani banzan dake zuwa wurin ki komai.
Banyi magana ba don mun kawo bakin shagon haka muka shiga a jera da juna sayaya nai wa mommy har da gaiya don har yaran ta na zabawa abu.
Ya kalli kayan mai makon inji yayi korafin sunyi yawa sai ji nayi yace kina ganin wanan kayan sunyi ke nan idan kuma kin sai wa yaran mommy ita kadai su sauran yaran anty amarya fa ?
Dole na koma na kara zaba muryan shi ne naji a bayana yana fadin ki zaba ma su ummi da su hajiyan mu kayan suma.
Sosai ya kashe kudi bayan na mommy dana su iyan bawa gana su hajiya mama dana zaba masu super masu kyau su ma.
Mun kai ya biya ko dar nanga yayi ba da akai mashi list din kayan aka saka ga wani katon buhu zuwa inda motar shi take tsaya nayi ban shiga ba sai da ya zauna ya leko yana fadin shigo mana mu tafi.
Nace dashi katafi kawai zan bi taxis in koma ni da sauri naga ya bude kofan motan ban san lokacin da na bude na shiga ba muka bar wurin.
Sai da mukayi nisa naji yace kina zaton abinda ya faru zai kara faruwa a tsakanin mu ne yanzu idan haka kike tunane kinyi kuskure.
Don ni ko matana dake gida sai naga dama nake waiwayan mace do ba haka nake ba kowani lokaci.
Sai dai nayi mamakin ganin yadda kika narke min a jiki kaman dama jira kike in taba ki haka ya nuna min ke nan dama a jirace kike da hakan ya faru.
Ban san lokacin da nace mai mugu mayaudari kawai macuci ba wanda ya taba min haka a duniyan nan sai kai kai kasan wani mace ta narke ma ajiki dan, , , ,
Hannu yakai zai kara kamoni na gwace da zafin nama yayi murmushi yace gobe idan halin ki ne ki kara cika min baki haka.
Ba sai ka kara ganina ba zakace in cika ma baki kaji dadin yaudaran da ka sabayi wa mata a kaina.
Zaki bar Nigeria ne ko mutuwa zakiyi don wanan ne kadai abinda zai hana in ganki in kara kallon wanan suran da kike kasawa a kasuwa in riga kowa kwashewa.
Haushi bai barni na sake magana dashi ba sai juya mashi baya danayi kawai shima bai sake magana ba sai da muka kusa tsayawa naji yace
Wallahi shiyasa kike kara burge ni da wanan halin naki na dan juyo na harare shi yace yes i mean it da wata ce sai tayi nata sayayyan amma ke naga ko tsinke baki dauka a shagon ba naan kuma dole kin ga abinda zuciyar ki ke so a ciki .
Kinga ke nan kin nuna min abin mutum baya gaban ki idan bai baki ba yana da kyau hakan keep on da wanan hali.
Sai dai ai na biyaki ladan ki ko ina ganin ba sai an rubuta maki wani lada ba ko bani wanan lafiyan fresh body din da kika yin kin more ai ke ma.
Ya tsaya da motar na bude najita a rufe na juyo na kalle shi nace bude min in fita hug me for d last time tunda kin ce baza mu sake haduwa irin haka ba.
Malam ka bude min mota in fita ni ba yar iska bace ka sani wallahi ban sani ba zan dai sani nan gaba in Allah ya yarda ban fahinci abinda yake nufi ba bai kuma bude min motar ba yana jiran wai abinda yace.
Na sake cewa da kai fa nake magana ka kyali ni yace even peck kiss yana lumshe ido kamar zan kai kiss din sai na cije shi a kumatunshi.
Yana shafa wurin yana fadin wassh ko hakan ai na gode zan tunaki watarana na taba haduwa da wata manya yar Niger mai zubin half cas.
Ya bude motar tare da fadin thanks ki kula da kan ki don Allah don kin bar min tarihi nace mugu kawai azzalumi mayaudari da sauri na fita do kada ya kara rufe kofan yana dariya yaja mota tare da min horn ya tafi .
Ko da na shiga hostel na samu har martam ta kwanta ina shugowa tace kun dawo tare da duban time tana fadin ban dauka zaku dade haka ba ai.
Zama nayi jagwal a wurin fuskana kawai zaka kalla kasan ina cikin bacin da sauri ta mike zaune tana fadin wani abu yayi maki ne.
A takaice nace may ye bai mun ba yau maryam AA ya cuci ni ya shammace ni sosai wallahi da sauri naga ta fida ido waje.
Nace ban taba sanin dan iska bane sai yau wai nifa AA ya ruguma maryam har da taba min kai kiji min dan iskan banza.
Ajiyan zuciya naji ta sauke tare da fadin wallahi har kin saka gaba faduwa na fa dauka ko raping dinki yayi wallahi wani irin harara nayi mata nace ya ma isa.
Tace cikin dariya yadda kikai maganan ai dole mutum ya tsorata yayi zaton hakan ne ya faru a tsakanin ku.
Nace may ye marabin wanan da hakan don Allah bada hakan ake farawa ba har aje can daga magana kawai sai naji ya rungumay ni don kawai ya nuna min dan iska yake macuci kawai.
Tace akan kayan dazu ko na kada mata kai nace ashe kin san abinda zai min kika bari nabishi ke nan tace kema kin faye baki wallahi .
Ai gara da kika zabi law don kin iya bakin ki don Allah bani labari nikan in sha dariya don nasan yau ashe yasha zagi a gunki.
Nace ban sani ba cikin hararan ta ina mike tace indai gulma kuka kai shi ke dashi kuna son juna kuna wani noke noke .
May zanyi da wanan dan iskan ni bakiji ba ma wai shi ko matan shi sai yaga dama yake kara waiwayan mace idan yaga dama.
Dariya mai karfi ta kwashe dashi tana fadin ashe akwai aiki kuwa kuma yake sha, awan kara mata fadi dai yayi wallahi.
Toni ina ruwana da rashin kula matan shi ko ya kula ko kada ya kula duk uwar su daya a gun khadija don ba abinda ya shafe ni da hakan na fada mai.
Nan nabarta tana min shakiyanci alwala na dauro ina son yin waka don kada ta zarge ni haka na fito na tayar da sallah na gama na kwanta banci komai ba ranan.
Sai dai ba barci nayi ba don tunane ya hana ni shakat a zuciya na don da zaran na rufe ido abinda ya faru tsakanin mu ne yake zuwa min.
Har dai barci yazo ya dauke ni ranan na makara da sauri na mike ina shiryawa sai ga wayan shi ya shigo min.
Kamar ba zan daga ba kallon da maryam ke min yasa na daga wayan murmushi naji yayi tare da fadin nasan dai kamar yarda banyi barci ba kema hakan bazaki barci ba daren jiya.
Akan may zan hana idona barci nace mai, yace akan dan gidan mommy mana kema kin sani , nace Allah dai ya sauwaka kana ganin kayi wani abun gwanewa kenan, mutumin da ko runguma bai iya ba sai ta hanyar karfi, zai sa na kasa barci na kashe wayan.
Yayi kiran duniya naki daga wayan sai ga text din shi ya shigo min kamar haka.
Saboda kin san kin zuba min dahin ki a jiki daren jiya yasa kika fara garani ko may ?
Niba macijiya bace ai, balle in zuba ma dafi
Na tura mashi, ba a jima ba sai ga amsa shi kamar haka ,
Kin fi macijiya dafi karfa ki manta ke mace ce, mace ko shu,umace ko wace iri ce ita tasan sallon sheri ga da namiji.
Kai dai ka sani da kayan sherin ka in ma dafi ne kai kazubawa kan ka bani ba ya karanta yana dariya bai san shigowar Nafisa ba dakin.
Sai jin muryan tana tambayan shi kaidawa ke waya haka kake dariya ?
Dakewa yayi duk da kaduwan dayayi cikin ranshi amma a fili cewa yayi da ita nida Yusuf ne don yasan ba karatun boko ta iya ba balle ta amsa ta karanta.
Ba don ta yarda ba ta kyaleshi kawai tana zargin shi a cikin ranta don yanzu ya fara bata tsoro gaba daya don ya daina sayin ta da yake yi a da can baya.
Daga haka ya sauka kasa yana yana kiran yaran aikin gidan shi ya shigo mashi da buhun da ya dawo dasu jiya.
Ya sa akai masu dakin da su mommy suke tare dasu iyan bawa a gidan daidai lokacin Nafisa ta sauko kasa tana fadin Sabel wanan kayan haka daga ina kuma ?
Yaro gidan dan yaren su na buzaye yace maigida yace ya dauka yakai dakin dabakin shi suke ciki tabi buhun kayan da kallo nan ta so sanin abinda ke ciki.
Don haka tabu shi a baya wai taje da sunan gaida mommy yau da kwana yana zaune saman kujeran dakin suna hira da iyan bawa ta shigo tana gaidasu idon ta akan buhun dake gaban shi nan ya fahinci buhun ta biyo a lokacin don ganin may ke ciki.
Idon ta ya gano mata atamfan da ya fara fitarwa kasa yana son fitar da sauran sai gata ta daure fuska tamau idan da dane da ya shiga hankalin shi ga yadda ya ga ta daure fuskanta.
Sai ci gaba da fitar da kayan yake yana bin sunaye su yadda na rubuta ajikin ko wani ledan kayan yana ajewa gaban mommy bai fara bayani ba ta juya ta bar dakin a fusace cikin bacin rai.
Sai bayan fitan ta daga dakin ya fara yiwa mommy bayanin kayan tare da dora ma ko wani kudi a saman kayan yace suyi dinki sai Allah ya dawo dashi lafiya zai shigo yayi masu ban gajiya.
Kallon shi mommy tayi da kyau bayan ta gama sauraro shi tace wanan hidimar yayi yawa haka babangida don haka kabar kudin nan abin