Showing 132001 words to 133935 words out of 133935 words
sama kamar a mafalki a gurin.
Fitowa yaya Amina daga dakine yasa nace ma maryam ta bari idan na huta zan kirata muyi magana, muryan Ya Amina ne naji tana tambayana mota ce ta baku wahala a hanya.
Nace bari ya Amina banji dadin wanan tafiya ba yau don dai kawai na kwallafa son ganin ku ne nayi shi dana koma wallahi.
Gashi ko abinci ban tsaya nayi ba na ranane na rage wa yara don mun shiga gidan su mommy kin san ana buki a gidan nace buki kuma ina suka samu buki ?
Tace a, a kin san ai da gidan su da gidan su Fati matar Abdulsamad kamar Family daya ne kannen ita fati din ke aure ai.
A raina nace no warder ashe shi yasa mutanen nan nan suka zo garin ashe buki suke yi gaskiya naga an shake mota da kaya haka ?
May zakici yanzu in dafa maki ko in shiga aurin mommy in karbo maki abinci don ni naci ko acan tun dazu.
Nace barshi ko tea ne zan sha idan na watsa ma jikina ruwa zan kwanta muna wurin zaune muna hira sai mukaji sallama.
Binta ce da zainab da wasu kawayen su biyu da ban san su ba suna dauke da basket din abinci a hannun su.
Da ihu Binta ta karaso inda nake ta rungumay ni tana fadin wallahi khadija Adamu nafi kowa farin cikin zuwan nan naki ko kema dama kin san da zancen bukin ne wai ?
Nace cikin fara,a wallahi bansan da zancen wani buki ba zuwa nayi duban ya Amina na kawai don nayi kewan ta da yarana.
Aiko wallahi kinzo a sa,a don akwai casu wallahi nace ke har yanzu baki daina maganan wani casu ba can tace ba dole ba mutumiyar fa za aiwa engament jibi .
Da sauri nace wa kenan kuma ta nuna min zainab tana fadin gatanan a gaban ki kuwa wallahi wayo take son muna nidake.
Kallo na mayar ga zainab din dake zaune tana faman taba wayan ta nace wai da gaske ne ko sherin Binta ne kawai dayar yarinyar tace da gaske ne wallahi.
Dan ihu nayi nace amma zainab kin bani mamaki ashe da Allah bai kawo ni ba da saidai inji labari.
Tace a wani yanayi ba haka bane khadija nima ban dauka a yanzu za, ayi abin ba na dauka ko da sauran time ne shiyasa ban fada ma kowa zancen ba.
Ta fada cikin izza da yanga sai yau nake ganin mugun kamar su da yayan nata komai nasu iri dayana sosai sunfi dauka kamanni da mahaifinsu fiye da kowa a gidan.
Nayi murna kwarai sai can na kallo ta nace wai waye wanan lucky guy din da ya iya sace zuciyar wanan yar kwalisan yarinyar haka a lokaci daya.
Binta ne ta bani amsa da fadin ina guy fin nan abokin yayan mu da always Suna tare da yayan mu Abdulsamad mijin buzuwa din nan wanda ake ce Yusuf.
Shine ya sace zuciyar wanan mai zurfin cikin tsiyan da kike gani nima da muke daki daya da ita ban taba sanin wanan labarin ba sai da abin yanuna ya fashe naji.
Kin san matar shi ta rasune a wurin haihuwa shakara biyar da ya wuce shine bai yi wani aure har yanzu ashe rabon zainab ta shiga gidan shi ne ya kashe matar .
Harara zainab din ta aika mata na ki kama kan ki dinan nace amma zainab kinyi dace da mutumin kirki dan arziki daya san mutuncin mutane.
Binta tace kin san shi khadija da kike fadin haka wallahi kin canka daidai kuwa don har yau ban taba jin wani hali nashi na assha ba da aka fadi.
Na dafa zainab din ina fadin yar uwa ina tayaki murna da wanan babban kamu da Allah yayi maki muma Allah ya kaimu ga danshin ki.
Zainab tana murmushi tace baki dai so bane khadija da tuni wani yayi wuf dake wanan zubin naki sai kace wata halfcas dake wani namiji zai ganki ya kau da ido gurine kawai maza basu samu ba.
Kiba da dama yanzu ki gani in bakiga layi a kofan gidan nan ba har ba iyaka na maza a kofan gidan nace ba zasu samu ba yanzu zainab baki ba dai in nan gaba na kammal karatuna na fara aiki ko shi sai kila.
Ya Amina da tunda muka fara magana baita magana ba sai yanzu tace yarinya in tunanen ki ke nan ki canza don baba a jirace yake dake wallahi.
Nace Ya Amina baba ai yafi kowa sanin matsalana karatune burina inga na zama babban lauya wata rana Binta tace wai da mun sha dauri wallahi.
Nace kamar ko kin sani don da na gida zan fara sharia na kada ma kiji wai binta ki rike dakayau a ranki.
Zainab tace kinga mun kama zuba kamar ba gobe ga abincin nan mommy tace mu kawo maki a gurin ta ma muke jin zuwan naki yanzu.
Daga inda Ya Amina take zaune tace wai mommy dai bata gajiya yanzun fa muke maganan abincin nan kamar ta sani sai gashi ta aiko muna dashi.
Mommy ai tafi danan wallahi inji dayar yarinyar ta fada kowa yace wallahi halin mommy ai yayi ne sosai.
Basu jima ba sukai muna sallama akan gobe zamu hadu sai mu kara tatauna abinda za a yi nace dana san da wanan zance ai da tare muka zo da maryam.
Binta tace Allah sarki ban tambaye ki maryam din ba nace tana can na barta tace gobe ita ma gida zata tunda na wuce na barta.
Har bakin get na rako su suka tafi na dawo ciki a inda na bar ya Amina zaune a nan na samay ta nace wai ina yaran suka tafi ne tace suna can gidan kakannin su zasu kwana masu biyu.
Ban san zaki zo ba aida ban kai su can ba don in samu yadda nake so ne yasa nakai su can inji dadin shiga mutane babu takura.
Wanka na shiga na fito na saka wani dogon riga a jikina na shan iska mai dan karamin hannun yadin rigar baida kauri sosai falo na dawo na samu ya Amina tana kallo.
Zama nayi ina jawo kulan abincin da mommy ta aiko min dashi nayi mamakin ganin abincin haka kamar na wata hamshakiya.
Ban san lokacin da nace wai mommy irin wanan hadin haka wallahi ni har kunyar matar nake ji Allah kuwa.
Dariya Ya Amina tayi min tace ko har kun fara sarakutane da ita ban sani ba nace wa zata bani cikin diyan ta haka dai kawai nake jin nauyin ta yanzu.
Wai ni ina Abdulsamad ne ina zancen ku ya kwana dashi ne tun lokacin ban kara jin labarin ba ko da yake yanzu kin fi zama minna ai.
Tsuki nayi ina zama kasa nace ina ruwa na da wanan miskilin mutum da bai san darajan mutane ba halin su au daya da matar shi shiyasa nasu yazo daya da ita.
A,a wallahi baki ko fahince shi ba khadija Abdulsamad mutum ne wallahi mai mutunci da sanin ya kamata ke dai kice Allah ya hada shi da yar banza mata ne mara mutunci kwanaki fa har gari nan tazo taci ma iyayyen shi da matar shi mutunci.
Don Allah ya Amina abinci zan ci kada ki fada min maganan haushin nan ai ita bata da laifi shine mai lefin don ni wallahi da nice Fati da tasha takaici a wurina.
Don wallahi tsab zan zauna da ita don tun yanzu na karanci iya shegen ta balle fati da suka zauna tare tasan halin ta da komai nata may zata gwada mata.
Ke dan Allah can kin san aure ne da kike wanan haukan haka auren fa akace maki khadija ba wani abu ba ita mace dama ta gaji ganin haka walau mai kyau walau akasin hakan.
Abincina naci gaba daci ban taka mata ba ganin nayi shiru itama taja bakin ta tayi shiru tunda ta fahinci ban son zancen .
Ina gamawa tace min a dakin ta zan kwana tunda ita kadai ne a gidan kuma ba a gyara dakin nawa ba don bata san ina tafe ba.
Nace aiko dakin baiyi wani datti ba dan fes na ganshi har da ban dakin tace duk sati ina shiga ina gyarawa don gudun irin haka duk da haka ki bari sai gobe idan an gyara ki kwana a ciki.
Bayan nagama don naci abincin sosai na kwashe kayan zuwa kitchen daki na koma nayi shirin kwanciya wayana kawai na dauka da hijabin da zanyi sallah da safe na fito xuwa dakin ya Aminan.
Na samu ta shiga wanka haka yasa na kwanta abina don dakin ba bako na bane wayana kunna na bude data sakone ya dinga shigo min daga ciki biyu kawai na duba na farko sokon mamud ne yana tambayana karatu.
Sai kuma karshe da yake ce min ya matsu in gama muyi aure in haifa mai yara masu kama dani yana yawo dasu a mota a gari.
Tsuki naja ina fadin baka da hankali mamud nice zan shiga ma ta uku gida don na rako matan duniya komay ?
Sai sakon maryam tana fadin hostel din ba dadi dana tafi don haka gobe gida zata tunda safe duk da tasan yayan ta basu gari da mijin ta.
Zatai zamane na kadaici koda taje amma yafi mata zama a hostel bani amsa na bata nace niko kinga nazo na samu ana buki anan har da engement din zainab da Yusuf alama murna ta nuno min tace yaushe ne bukin nace mata sturday idan Allah ya kai mu.
Gobe zaki ganni tace kai maryam da gaske tace insha Allah ko naje gida Anty basu kasan suna waje da mijin ta ai gara inzo inda kike muyi hutun tare.
Mukai sallama ina murna har ya Amina ta fito ta samay ni hakana nake fada mata gobe maryam zata zo tace ashe ina da bakuwa gobe a gidan kin ga sai kin min list din abinda take ci a sayo maku kada tazo nan ta takura.
Dariya nayi nace da kin hutar da kanki don maryam suna masu kudi ne kawai amma bata da matsalan komai wallahi komai da kika san muna ci tana son shi.
Allah ya kawo ta lafiya nace amin daga haka had barci ya dauke ni nayi mafalkin ga mutane sun taru ina kuka haka yasa na kasa barci har safe nakai a hakan.
Haka na tashi da safe a cikin damuwa ina tsoron in fadi wani abu mumuna ya faru dani da gari ya karasa wayewa nace da anty zan fita bakin titi in ba da sadaka.
Bata tsaya tambaya na ba na fita zuwa titin in da nayi saa na hadu da wata mata mabukayi tana neman abinda zataci da yaran ta na bata dubu biyu tana min addua na juyo zuwa gida.
Ban yi nisa ba ina karyo kwanan unguwar mu tun daga nesa na gane A A tafe a cikin kayan motsa jiki yana judging shi da su mutum biyu a bayan shi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU