Showing 120001 words to 123000 words out of 133935 words
su dakewa yayi kamar bai ganta ba yaci gaba da hira da abokin shi.
Sai dai hankalin shi yana gurin ta duk abinda yake yi din bayan tafiyan mutumin tun a falo ta fara tambayan shi Fati ta dawo gidan ka ne baka fada min ba.
Yace ta dawo suna nan gida yanzu haka shewa tayi tare da mikewa tsaye tana fadin haukan banza ke nan yadda ta dawo haka zata koma inda ta fito.
Wanan kuma maganan ki ne don dama ai ba wanda ya kore ta ita da kanta taga daman fita yanzu kuma ta dawo tace ashe ko zamu zuba daku mugani a gidan nan.
Ke ban fa son haukan naki na bazan Fati bakuwa ce a gare ki ko yanzu ne na fara zama da ita zaman ki na nan Abuja ita kuma yanzu bayan shekaru ta zabi zama kaduna ita da diyan ta.
Don haka ban son jaye jayen wani matsala kima da zai kawo muna tashin hankali ba gaira ba dalili haka,
Yana fadin haka ya mike ya haura sama ya barta a falon cike da mamaki halin irin na Nafisa da bata iya boye kishin ta .
Satin shi biyu abuja yana hutawa ya kama hanyan zuwa kaduna gida don ya hana kowa yazo daga can yace yana nan tafe.
Nafisa bata yarda cewa iyayyen shi zai tafi gani ba ta shirya wai tare zasu tafi ba yadda ya iya dole a tare da ita yayi tafiyan.
Tunda suka shiga garin ta hana komai a tsakanin shi da Fati din bayan gaisuwa bata yarda komai ya kara hada suba don ko abinci da Fati ta gama sai cewa nafisa tayi abincin yayi mai nauyi ba zai ci ba.
Suna zaune da dare ta na kokarin hana shi shiga wurin Fati da kissa da iyayi wayan hajiya mama ya shigo mashi nasiha tayi mai sosai wanda ya kashe mai jiki inda take mai tuni da cewa ya tuna hakkin ko wace yana a kanshi do haka ya daure yana ba kowa hakkin ta.
Bayan sun gama waya ne da mahafiyar shi bai wani dauki lokaci taga ya mike da sauri take tambayan shi ina zai tafi kuma.
Kai tsaye yace mata gun Fati zan tafi bata iya boye bacin ranta ba ko kadan tace bai isa ba don tare suka zo fati ta bari idan bai zo da ita ba sai ta kwana dashi.
Yace a garin ku haka akeyi wanan dokan hakan wai Nafisa may kika dauke ni kamar wace ta haife ni zaki dinga bani umurni kai tsaye.
Ba sake kula ta ba ya shige sashen Fatin kamar yadda yayi tsamani hakan ya samay ta sunyi barci da yaranta a saman gadon dakin ta tana saye da kayan data wuni dashi a jikin ta tunda suka zo,
Ya dade tsaye a kansu bata san ya shigo dakin ba sai da ya dan bubuga mata kafa ta falka ina zan kwanta yace da ita kai tsaye dan watsake idon ta takeyi daga nauyin barcin da ya fara kama idon ta din.
Sai can tace dakin ka fa yace Nafisa na cikin dakin kin sani mikewa tayi tana gyara ma yaran kwanciya tare da gyara dan wurin da ta bar mashi ya kwanta.
Kallon ta yayi daga inda yake tsaye yana tambayan ta wai dakin su fa da kika dawo da kwanan su nan kamar ba zata bashi amsa ba sai can tace ban san anan zaka kwana ba ai tare muke kwana tunda ba kowa a gidan.
Tsuki yayi yana hawowa gadon ya takure kan shi a guri daya kamar may kyankyamin dakin amma kin san hakan ba daidai bane nasha fada maki haka kwana da yara a daki daya.
Banza tayi dashi ba wai banzan bane ya sani halin ta daine nakasa da kyaluwa haka take kindis da ita ko yaushe fuska ba fara, a.
Tunda ya samu barci ya dauke shi bai falka ba sai karfe hudu da rabi na asuba da bugun kofar nafisa ke masu ya tayar dashi a firgice.
Tambaya yayi yana zura riga a jikin shi tace itace ya bude kofan ya bude da mamakon ta a fuskan shi yana tambaya lafiya take cewa dashi.
Banan ce bata da lafiya basuyi barci ba kallon yarinyar dake sabale a kafadan ta yayi tare da fadin ta miko mashi ita.
Sai da tayi mai wani kallo tace ka karasa fitowa daga dakin mana murmushiin gefen fuska ya sauke kafin ya fito din muryam Fatine take tambayan make damun yarinyar ne ?
Kada ki soma ki taba min ya ta yanzu ranki ya baci a gidan nan tana fadi tare da watsa mata harara da saida taja jikin ta ta koma daga bayan shi.
Karban yarinyar yayi ya nufi falon kasa da ita suna biye a bayan shi dukan su ruwa ya fara ba yarinyar tasha sosai tare da ajiyan zuciya ta lafe a jikin shi.
Dakin da bai koma ba ke nan ya zauna nan falo da yarinyar data koma barci a jikin shi tana sauke ajiyan zuciya .
Juyawa fati tayi ta koma dakin ta don ta san kadan ne daga cikin sherin Nafisa ko ba yarinya a tsakanin su haka take masu idan zai kwana a dakin Fati din tace bata da lafiya karshe a dakin ta zai kwana.
Do haka ta juya abinta taje ta kwanta bata kara ganin shi ba har rana breakfast din da ta hada mai baci ba wani aka kawo masu daga gidan Auta amiyar Nafisa din.
Haka fati tayi ta hadiyan bakin ciki da wanan zuwan nasu ita da ganin miji sai dare idan zai kwanta zai lalabo ya dawo dakin ya kwanta da safe ya fice kuma ranan nafisa tace itace zatai girki .
Dole Fati ta kyaleta tayi yadda ranta ke so tunda har mijin ma ya biye mata ita yanzu burin ta shine ta zauna a cikin yaranta kawai su girma a tare da ita.
Nafisa bata shiga gaida sarakkanta ba balle suga yar jikan tasu data haifa da dan su sau daya ta shiga gaidasu ana gobe zata koma bata ba kowa yar ta ba suma basu taya zasu dauka ba.
Sai kuma abin ya bata mata rai don yadda ta shirya bata samu yi ba sai taji haushin basar da ita da sukayi takoma fadin wai yanzu har kiyayyan da suke mata ya shafi yar ta jikan su.
Haka ya sa AA yaji haushin abinda sukai mata a ranshi har ya kira mommy yana fada mata abinda sukaiwa Nafisa da yar shi baiji dadin hakan ba.
Don ba halin ya kira mahaifiyar shi ya fada mata yasan kwanan wasa yanzu za a jisu da ita idan ta fara mai fada yasa shi kiran mommy.
Mommy tace dashi babangida kasan halin matar ka fa ta make yarta a jikin ta bata ba kowa ba mune zamu karba tai muna wullakanci amma munyi kuskure gaba zamu gyara insha Allahu.
Bayan kwana hudu suka nada suka koma abuja tun da suka kama hanya ta washe ranta da ya rasa gane mata da suke a kadunan.
Yanzu ko kamar ba ita ba sai hira take jan shi a motar tana faman dariya tana kuma wasa da yar dake zaune a cinyar baban ta din.
Tunda ya dawo ta samu kansa da kyau sai dai abinda bata sani ba yanzu asiri bai faye tasiri ya dauki lokaci a jikin shi don maganin tsarin da malam na zaria ya bashi.
Kuma abokin shi Yusuf bai zauna ba akan shi yana tsaye da alamarin shi haka ma mahaifan shi suna tsaye da mashi addua sosai yanzu.
Yau tunda na dawo daga islamiya nake kwance ba wai don banda lafiya ba sai dai ina jin jikina ba dadi ne ko aikin gida da nake taya mama ban iya tayata yi ba.
Barci nayi sosai a ranan can zuwa rana yaro ya shigo yana fadin ana sallama dani a waje mama ta shigo ta tadani tana fadin min wai ina da bako a waje.
Mikewa nayi da kyar don barcin dake idona na ban tsaya gyara fuskana ba na fita daga gidan haka na mamud ne zaune a motar shi da yaran shi biyu.
Na iso inda suke ina gaida shi bayan motan na bude inda yaran suke zauna kafa na suna waje ina gaidasu tare da tambaya su yaya makaranta.
Kafin yaran su bani amsa ya jefo min tambaya yaya naga fuskan ki haka kuma ko baki da lafiya ne ya tambaya ?
Nace daga barci na tashi yanzu ba tare dana kalle shi ba hannu na mika wa yar karamar yarinya dake saye a cikin uniform din shekk lemo sai yarinyar ta noke taki zuwa.
Tambayar ta nayi yaya sunan ta yace sadika dayan kuma nasir ina taba kafar yarinyar nace zakici biscut ta daga min kai nace to sai kinzo wurina sai ta kara makewa.
Ina zuwa nace dashi cikina koma na hado masu kayan kwalama na yara wanda na dawo dashi muna ci da kanne na nafito rike da leda a hannuna namikawa yaran.
Da sauri suka karba nan dai muka taba dan hira yace zai maida yaran gida daga islamiya ya dauko su mukai sallama ya tafi.
Bayan sun isa ma sai da ya kirani muka taba hira ya kashe wayan tare da fadin zai zo amsa gudane wurina nace na hutar dakai kada ka wahal da kan ka.
Yace to zamuyi waya nace sai najika aiki gida na taya mama ta koma folo tana kallo sai dana gama zuwa dare na shiga daki na samu wayan mamud har six miscall ya kira ban dauka ba.
Kiran layin shi nayi aka dauka ban tsaya sauraren ba nace ina waje ne ina aiki banga kiran ka ba.
Ban karasa magana na ba naji muryan mace tana fadin ke wacece da zaki kira lamban mijina kin san ko waye mamud kuwa ?
To bari kiji daga yau kada ki sake shiga harkan mijina in ba haka ba zan sa ayi maganin ki a garin nan shiru nayi ina sauraren ta sai da ta gama nace.
Ke kuma wacecd a guri mamud din bari ki ji ki sani ba don ki ke kadai akayi shi ba daga yau ki gyara kalamin ki inzaki magana akan shi ki dinga cewa mijin mu.
Ina fadin haka ban tsaya jin haukanta ba na kashe wayan ina dariya nace banza mahaukaciya ni mijin ki bai a gaba na yanzu da kin ga tsiya wallahi.
Bai kirani ba nima ban kirashi ba sai bayan kwana biyu sai gashi ya aiko kirana wai ace mamud ne mace ace ban samun fitowa aiki nake yi.
Mamace ta samin baki dole na fita naci karo da dan aiken ya dawo wai yace don Allah inyi hakkuri minti biyu kawai zanyi.
Tare muka koma da dan sakon na samay shi zaune a cikin motar shi yana duban wayan shi karasowa na ya fito yana washe baki.
Fuska na a daure na gaida shi magana yake na kyale shi sai ko umm ko ummumm nake bashi amsa dashi kaina a kasa ina dakilan wayana.
Muryan shi naji yana fadin yau gimbiya may ya faru ne naga an fito min haka a daure nace wani abu ka gani halan ?
Yadan motsa kafan shi kadan yana murmushi tare da harde hannayen shi guri daya yace ko gimbiyar tawa mulki take jine haka ?
Sai da nayi mashi wani irin kallo shekeke nace mulki ai mulki yana gidan ka don ko wayan ka sai an baka izinin dauka kake dauka ko zuwa gurina yanzu waya sani ko santan hanya kayi kada matan ka su gani.
A cikin rashin kuzariya dago kai yana kallona yace wanan wani irin magana ne haka khadija kikeyi kai tsaye ba tare da tunane ba.
Nace irin wamda matar ka tayi min jiya daga kiran wayan ka ta dauka tana zagina a wayan ta daukar min waya fa kikace nace ka duba nan ga kirana a wayana kana gani katuna ina kaje jiya a daidai wanan lokacin ?
Look mamud na fada ma soyayya dakai a yanzu akwai matsala ka nace akan sai munyi gashi tin ba a je ko ina ba an fara kirana ana zagina daga gidan ka har da yimin iyaka dakai.
Ya kai duban shi gare ni tare da sake dan murmushi yace mai shi tayi nasara gare ki ke nan tunda gashi har kin karaya zaki bar mata ni.
Haka muka kasance dashi muna musayan maganan karshe dai yaban hakkuri nace ya wuce amma ya daina zuwa wurina.
Yace ba da sanin shi ba amaryan shi ce ta dauka daya shiga wanka kuma da ya fito bata nuna mashi akwai wani matsala ba.
Nace wanan kai ta shafa ni dai na gama magana kuma.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Hutun mu yana karewa na fara shirin komawa makaranta bayan na kara sati daya a sama agida ina tare da iyayyena da yan uwa na.
Duk da ba so daukan kaya nake yi ba hakan bai hana mama ta dan tanadar min irin abubuwan da uwayen mu mata suke tanadarwa yaro idan zai koma karanta.
Inda mahaifina ya bani kudin da zanyi sayayya na raba kudi biyu na mayar mai da rabi nace ina da kayan abinci da ban ci ba a daki na.
Bayan na shirya ina shirin zuwa Abdulsalam garage da kayana inda zan shiga motar zuwa abuja na fito a cikin shiri na yan uwana suna a bayana zasuyi min rakiya bakin titi.
Gaban daddy da mama nazo na durkusa har kasa ina fadin daddy zan tafi ya dago kai ya kalle ni tare da fadin khadija kin fito ke nan.
Yace do Allah khadija ki kula da kanki kamar yadda kika saba a baya ki maida hankali ga karatun ki kinga lokaci na tafiya yanzu.
Kaina na kasa nace in sha Allahu daddy na gode mama tace banda kai kai inda Allah bai kaika ba kawar da kanki ga komai sai kiga komai yazo maki a cikin sauki nace na gode mama na mike tsaye jiki a sanyaye.
Ban dade ba na samu mota naba kanne na kudi su raba daga cikin wanda daddy ya bani in rika din muka tafi tare da kanina dake bin min.
Na isa Abuja da wuri inda na samu maryam ta rigani dawowa lokacin ranan mun jima tare muna hira ko barci bamuyi da wuri ba dan shaukin juna da mukeyi duk da muna waya kusan kullun da ita.
Dayake muna da abinci ga kuma wanda maryanm ta karo don haka ban damu da nashiga gari in sayo komai ba don akwai shi a dakin.
Mun samu sabbi fuska a gidan namu don an dauki sabbin dalibai yanzu wasu sun tafi kuma koda zan dawo ban bari mamud ya sani ba .
Idan ya tambayeni yaushe zaki koma nakan ce dashi ba yanzu ba idan na tashi zan sanar da kai lokacin da ya samu labarin na koma school ranshi ya baci sosai dani.
Kirana yayi ga waya yana fada wai ya fahinci gaba daya yanzu ban damu dashi ba don may zan koma school ban sanar dashi ba saida yazo gidan mu ya samu labarin na tafi.
Nace dashi na fada maka tun farko kada ka wahal da kanka gare ni don ba auren ka zanyi ba na riga na rufe babin nan ko a raina.
Satina biyu da dawowa sai ga mamud din ya kawo min ziyara gaskiya banji dadin zuwan shi ba don na gane yana son da karfi da yaji ya shiga raina again.
Yadan jima a guri na muna hira dashi wanda hiran duk a kan zaman mu dashi ne anan maryam da wata Aisha da yanzu muke tare da ita suka samay mu.
Da zasu tafi ya basu alheri sukayi mai godiya yace ma maryam ta taya shi kanfen a guri na dariya tayi tace ban maka wanan alkawarin ba don abaya ka gujemu ba wani dalilin komai.
Haba maryam banyi zaton jin haka a gare ki ba yace tace gaskiya na fada don yanzu tace karatun tane a gaban ta doon kaga muna gab da gamawa ba wasa a gare mu.
Kaya masu yawa yazo min dashi irin na bukatan yan makaranta na nuna mashi hakan da yake yi ba daidai bane yace yace bai son irin kalamin nan da nake mashi.
Bayan tafiyan shi ne muka bude kayan da yazo min dasu muna kallo Aisha tace amma ni kan sai naga kun dace dashi very handsome dashi wallahi.
Nace Aisha ba handsome bane abin damuwa abinda ke cikin gidan mamud din ne ai maryam tace da ita ai khadija haka take samun handsome guys don baki ga AA bane har kike ganin mamud a matsayin handsome a gare ta.
Nafitar da zancen wani mamud da AA a raina karatuna kawai nake fuskanta a yanzu da ya dau zafi gare mu banda lokacin kowa a tare dani ban kuma shiga gari ko yaushe ina cikin makaranta ko hostel din mu.
Zaune yake a office din shi yana aiki a wani file aka turo kofan office din nashi aka shigo baidago ya kalli wanda ya shigo din ba don yasan daga Yusuf