Showing 60001 words to 63000 words out of 133935 words
baki karya ba.
Bana jin shi do murdan da mara na keyi ina dan cije baki ina jijiga kafa na da matse hannaye na duk yadda na so in daure na kasa sai da na yi ya gani a bakin down hostel din mu ya tsaya da motar shi.
Zaki kara kawar ki ta taimaka maki ne ko in taimaka maki ki fita duk da ciwon da nake ji sai dana harare shi na bude motan na fita ko godiya ban mashi ba.
Ina fita yace turo min kawar ki ta daukan maki magani kai na iya dagawa na shige ciki na samu maryam na girki a dakina din bata da kiuyar girki ita tana gani na tace har kun dawo kaina gyada mata na fada saman katifa nace yana kiranki a waje.
A saka hijab da sauri ta fita daga dakin zuwa wurin shi bata jima ba ta dawo dauke da ledojin nan da ya sayo tace yana maki sannu wai sai kunyi waya yace kici wani abu kafin ki kwanta.
Itace ta zauna ta bude ledan kayan ciyeciye ne a cikin dana sha tarkace dai gasu nan sai dayan ledan dake dauke da pad din mata always kamar mai bude shago dashi ban san ranan da zai kare ba.
Abinci ta debo min na dan ci kadan na kwanta sai barci mai nauyi ya dauke ni a gurin ban kara sanin inda nake ba kuma.
Yana fita ya daga wayan shi six miscall ya gani na Nafisa da sauri ya danna wayan ya kirata yana fadin sorry ina wani abune yasa banga kiran ki ba.
Tace Samad ina kaje wacece akace mi an ganku tare a asibitin doctor Bisi yanzu waka kai asibiti wata macs ce aka gan ku tare tare ta fada cikin tashin hankali.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Bai iya bata amsa ba sai kokatin wuceta da yake yi ya karasa cikin dakin rigar shi ta riko ta baya da mamaki ya juyo yana kallon ta.
Shi da magana take mai wuya ina shi ina tsayawa fada irin haka da mace sau da yawa nafisa takan tunkare shi da irin wanan fita tana kokarin kama mai kaya ko ta sha mai kwala sai dai bai biye mata sai dai ya shige ya kyale ta tayi ta masifanta har ta gaji.
Inda ita kuma a nata ban garen take ganin tafi karfin shi ne, dan bai da yadda zaiyi da ita dole ya zauna da ita take gani yau da ta cakuma rigar shi ta baya tana kokarin kaimai duka ya juyo da sauri yana fadin Nafisa ki na da hankali kuwa ?
Cikin shi tayi tana banda hankali sai ka fada min wacce aka ganka da ita a asibiti dazun hannu yasa ya banbare hannun ta da karfi ya jefar da ita gefen kujera.
Zafin kishi sosai ya rufe mata ido nan ta fara ja mai Allah ya isa ya ci amanan ta ya cuce ta sai taga bayan ko wacece ke son mata katsalandan a rayuwan ta.
Yan uwanta suna tsaye cirko cirko suna kallon ikon Allah sai yare ne ke tashi suna magana rai a bace suna nuna goyon bayan yar uwan su.
Harara ya watsa masu sai suka fara sulalewa daga falon kowa yana barin gurin don yanayin kallon da yayi masu din .
Sama ya hau a hankali inda yake tafiya yana jin sautin kukan Nafisa yana isa inda yake.
Tsaye yake yana balle bottom din rigar shi a hankali sai dai zuciyar shi cike yake da mamakin waya gan shi ya fada ma Nafisa cewa ya ganshi tare da wata mace a asibitin doctor Bisi.Doctor Bisi ne ya fada a ranshi sai kuma yace No it can't be doctor bisi is a man he can do such full to me.
Beside, ma nine na hadasu da doctor bisi din anan don bata san kowa ba a Abuja sai zuwan da yayi da ita ne tasan kan garin.
Bayan wucewan mijin nata ciki ne ta watsa ma yan matan uku da suga rage a falon harara tace a cikin yaren su na buzaye.
Simi simi suka mike suka bar gurin itama mikewa tayi ta bishi ciki su karasa a can sai dai ta samay shi har ya shiga wanka ko.
Zama tayi a bakin gadon cike da masifa tana jiran fitowan shi daga wanka su aza a inda suka tsaya.
Zancen malaman ta ne ya fado mata a rai da kyat ta yaki zuciyar ta ta dan sasauta zafin da take ji nashi koda ya fito anan ya samay ta zaune cikin masifa bai kula ta ba ya fara gyaran jikin shi kamar yadda ya saba yi idan ya fito daga wanka.
Kallo daya yayi mata fuska a daure ya kawar da kan shi gare ta ta mike ta tako gare shi tace samad ka daina ganin laifina.
Ni kadai ce macen da ta dace kai a duniya da ina da iko ko macen kudi ba zan bari ta sauka a akan ka ba balle macen mutum.
Ta hade wani miyaun fitina da yazo mata a makoshi tare da fadin nasha alwashin duk macen da tayi gigin shiga gonar ka sai naga bayan ta a duniyan nan.
Kallonta yake da mamakin abinda ta fada yaga kuma gaskiyar maganan nata har cikin kwayan idon ta da gaskiya take maganan.
Kuma ko wacece wanan macen sai na tono ta a garin nan na nuna mata ruwa ba sa, an kwando bane.
Juyawa tayi ta fita daga dakin a fusace bayan taja wani uban tsuki tare da rufo kofan da karfi, binta yayi da kallo bayan ta fita ya girgiza kan shi ya tabe bakin shi gami da daga kafadan shi yace mahaukaciyar banza kawai.
Karasa shirin shi yayi ya fara gyara gadon shi don yana bukatan ya huta don ya gaji yau sosai ga maganan Nafisa da ke ci mashi rai kishi kamar wace bata da hankali.
Gadon ya hau ya kwanta bayan ya gama gyara yana sauke ajiyan zuciya a hankali may Nafisa take nufi da kalamin ta na sai taga bayan khadija.
Yasan zata iya abinda ta fada mashi a yanzu karfa ya ja ma yarinyar mutane matsala a rayuwan ta don bai san abinda Nafisa zata aikata mata ba.
Tunane yayi kada ya sare Nafisa ta samu daman da zats yi mai abinda taga dama a rayuwan shi don haka zuciyar shi ta bashi shawaran gwada Sa,an shi akan khadija ko zai yi nasara akai.
Bai koma ta kanta ba yadda ya saba binta yana bata hakkuri har sai yaga ta hakkura yake samun saida a ranshi wanan karon sai yaji ba zai iya tunkaranta ya bata hakuri ba akan kuskuren da take tuhumar shi da aikawa ba.
Kamar yadda Nafisa itama a dakin ta take zaune abin duniya duk ya damay ta ji take tankar tayi hauka don bacin rai wai yau samad din tane yakai wata mace asibiti ba ita ba.
Wai wacece wanan da samad har ya iya tunkara da sunan so may take dashi may take tunkaho dashi a duniya wanda ake cewa tafi ta komai.
Zubur ta mike ta fara zagaya dakin duk da dan cikin ta dake mata motsi a lokacin bai sa ta damu ta tuna da yadda take kaunar cikin nan ba.
Kishi ne zalla a rayuwan ta kawai so take tasan wacece wanan yarinyar don tasan ta inda zata iya fito mata da shirin ta.
Tana yi nata kallon lokaci don tasan dole yazo gare ta idan ta yi mai irin wanan boren nata sai dai a yan watanin nan tana ganin abubuwa suna son sauya mata sallo ga aikin ta.
Shiko Abdul a dakin shi yana kwance barci yaki zuwa mai a lokacin tunane kala kala yayi shi a wurin Yusuf ya kirashi yana tambayan shi ko yaji yaya jikin nawa don ya kira wayana yana a kashe.
Yace ban kirata ba don likita yace zatayi barci sosai a idan maganin ya fara mata aiki a jiki wata kila ta samu barci ne ta kashe wayan.
Nan yake labarta mashi yadda suka kwashe da Nafisa da ya dawo gida hankalin Yusuf ya tashi yace sai nake zaton doctor ne ya fada mata tunda kace baku hadu da kowa ba a gurin.
Yace idan shine ya fada mata kuwa yayi kuskure don cikin shi tayi don zan can za wani likita ke nan yanzu.
Yusuf yace baka tunanen kada Nafisa ta gano a inda khadija take tayi mata wani abin yace haka ma ba zai faru ba zanyi tunane mafita akan hakan.
Sukai sallama bayan sun gama tataunawa ga maganan ya kashe wayan yana gyara kwanciyar shi a hankali.
Bai dade da gama wayan ba yaji an turo kofan an shigo dakin yasan ita ce don ita kadai ce mai shigo mashi daki.
Ta karo gaban gadon ciki da mamakin ganin shi a kwance da tayi cikin rashin damuwa da ita har ta iso a gadon ta zauna tana fadin nasan ba barci kakeyi ba.
Ya dago ido ya dan kalle ta yace banyi barci ba kuma hutu nake so a yanzu ta gyara zama tana kallon shi tace samad cikin sanyayar murya.
Wai may na rage ka dashi a duniya may ye wanda ban maka har kake kokarin hadani da wata mace a duniya bayan kasan irin son da nake maka ba na wasa bane.
Ta kamo hannun shi tana fadin gaba daya ka canza min a yan watannin nan ko dan ka gani da ciki ne ka dauko yimin hakan.
Ka hana mu kwanciyar hankali gaba daya a gidan nan sai faman takura min kake yi ko yaushe.
Sai ga hawayen da yaki zubu mata a daki yazubo mata a lokacin tace ko wacece sai na kashe ta a garin nan idan na gane ta.
Cike da jin haushinta yace ashe ko ke ma za a kashe ki ke nan kinga matsalar ki ko meyasa ne har kullun ke baki tunane a rayuwan ki sai bakin kishi .
Ni ina kokarin ganin ko yaushe inga lafiyan ki ke ko sai wani banzan kishi ke a gaban ki ban tsamaci haka daga gare ki ba na dauka kece mutum ta farko da zata shedi rayuwana a idon jamma,a.
Yarinyace na kadai ta zan dawo gida in dubaki dole na dauke ta na kai asibiti doctor Bisi ya dubata ashe yariyar bata da lafiya shine ya taimaka mata.
A rashin wayo na Nafisa sai cewa tayi ashe wanan likitan munafuki ne shine ta kirani yana fada min wai yaga ka kawo amaryan ka asibitin shi yanzu.
Kawai may yake nufi don ya hada mu fada yayi min wanan maganan ko may yace da yake ke baki da tunane sai ki biyewa zancen shi ko ?
Ace kulun mutum ba zai saka ma zuciyar shi salama ba koda yaushe sai bakin kishi ke baki hangen nesa akan ki fa duk yan uwana suke fushi dani.
Hakan bai maki dadi ba sai kin tayar min da hankali kuuma har na tunzura na aikata abinda ban tashi yi ba.
Tace da sauri don Allah samad kayi hakuri sherin shedan ne wallahi dana doctor Bisi sai da ta san yadda ta bashi hakkuri har ya hakura suka koma dai dai suka sulhunta kan su.
Bai fita ba sai washegari bayan ya gama abinda yakeyi ya fice a gidan kiran Auta tayi ta fada mata ta koma kusfa ta fada ma malamin ta ya duba mata idan akwai matsala.
Sai da ya duba wasu file ya dan huta tare da kiran layina maryam ce ta dauki wayan tana fada mashi ina bandaki amma naji sauki.
Bai kai ga magana ba tace gani nan ma na fito tana mika min wayan tayi tana fadin yaya Abdulsamad ne a layin.
Karba nayi tare da kara wayan a kunne nace hello cikin murya kasa kasa yace yaya jikin naki nace da sauki baki je class ba ke nan nace sai anjima zan shiga.
Kin karya ko nace yanzu zan karya dai to idan kin karya kisha maganin ki zan shigo idan na rage aiki zuwa yamma in dubaki.
Nagode na tsunci kaina da fadi Allah ya sauwaka ya fadi yana kashe wayan maryam tana gefe tana sauraren mu bayan ya kashe wayan na zauna saman katifa tare da kaiwa kwance.
Tashi kisha tea din kada yayi sanyi gashinan na hada maki yamutsa fuska nayi nace miko min in sha bakinane bana jin dadin shi har yanzu.
Daure dai kisha ko kadan ne sai kisha maganin ki gashi ta mike tana dauko min ledan maganin dake aje a gafen kayana.
Tea din nasha tare da hade magani na koma na dan kwanta wayan daddy ne ya sake shigo min yana tambaya na ko lafiya jiya tanemi wayana yaji ta a kashe.
Daddy iam sick yace may ke damun ki khadija murmushi nayi nace naji sauki ai period time dinane yake damu na amma kin je asibiti yace ?
Naje daddy wanan mutumin ya kaini asibiti jiya yace good zan buga inyi mashi godiya don kwana biyu bai kirani ba yace nace bai kasan ne daddy ya kara da Allah ya sawaka ki kula da kanki ki abinda kika je yi khadija insha Allahu daddy na gode ka gaida mama.
Madam ranan a gidan Nafisa ta wuni sun kule a dakinta suna jiran kiran Auta daga zaria suji abinda malam zai fada masu.
Madam ta kawar da shirun da cewa wai shi wanan mijin naki wani irin mutum ne da baijin magani haka sai anyi kamar an samu kanshi sai abu ya zo daga baya ya can baki daya.
Tace shike damu na madam dubi irin kudin da nake zubawa akan bawan Allah nan sai naga nasara daga baya sai komai ya lalace.
Komai zan iya yi akan Samad din in dsi zan samu ya kawar da ido akan ko wace mace a dunuyan nan.
Madam tace idan shiya kawar da idon shi a kan mata su matan kina tsamani zasu kawar da ido su ne akan shi dole suma dole da tasu shirin da suke don suga sun kamo shi.
Don shegen kyau da daukan hankalina da wanan mijin naki ga abinda mata keso a tare dashi kudi da kyawo da hali.
Hankalin Nafisa ne ya tashi sosai da maganan madam tace wallahi da ina da hali da boye shi zan dinga yi a gida.
Dariya madam tayi tace idan kika boye shi kuce may ke da yan uwan ki Nafisa karki matanta shine hannu da kafar ku kaf zurian ku.
Yanzun dai zan tafi Ondo ance akwai wani boka acan may aiki kamar yanka yuka wata kawatace ta gano hakan.
Nikan ina can na dan samu karfin jikina shiryawa nayi zan leka cikin makaranta don kada a wuce ni da karatu da nazo yi.
Daddy ya kira Abdul yana mashi godiyan kaini asibitin dayayi yace ba komai insha Allahu zai kula dani kamar yadda zai kula da kaunar shi.
Bayan ya gama abinda yake ya kira Yusuf don su leka wurina kafin yaje gida Yusuf din yabar abinda yakeyi yazo suka tafi.
Sun samu na dawo ke nan ya kirani a waya na fito na samay su a waje lokacin da na karaso wurin su na samu suna magana suna kallon laptop din dake a saman kafan Abdul din nasan wani abu suke duba a ciki.
Karasowana suka bar abinda sukeyi din tare da maida hankalin su a gareni Yusuf ke fadin lalai jiki yayi sauki kauna na sai dai har kin dan fada kadan wallahi.
Murmushi nayi na dan jingina jikina ga motar su nace naji sauki sosai yusuf yace barin in dan je can inga shagon yan makaranta indawo ina son duba wani abu a gurin.
Nasan yayi haka ne don ya bamu wuri mu gana dashi wuce wanshi yace dan gyara zama yana fadin abin ya daina zuba ke nan ko ?
Harara na aika mai tare da fadin ban sani ba sai ka fito ka duba ai tunda kana son sani ne sai yau naga dariyan shi yace kin dai ji abinda likita ya fada saukin abin ai.
Banji ba kuma bana son naji tunda ba kai ke da lalurar ba au yanzu tunda kinji sauki kina da bakin magana ashe jiya fa nan kike ta murdemurde ina tausaya maki.
Kawar da kainayi gefe guda ban bashi amsa ba na share shi yace na tambaye ki jiya ciwo ya hana ki ban amsa na.
Nace may ka tambaye ni jiya din yace kwana nawa kike dauka kina off shiru nayi tare da bashi ba a raina ina fadin wai shi baisan ina matukar jin kunyanshi bane da yasan abin dake damu na.
Gashi kuma ya tsare ni da tambaya irin haka da zai sani jin kunya da nauyin shi ai wanan kamar kamar yar iska ya dauke ni.
Niko gidan mu in badon ciwon mara ba har zanyi in gama basu sani ba ji nayi yace may nene abin jin kuya kibani amsa na kawai don ya kama ne in sani.
Nace don Allah yaya Abdul ka daina wanan zancen naji yace na daina tunda baki son zancen yanzu.
Badai kina shan maganin ki ba akai akai nace ina sha