Showing 81001 words to 84000 words out of 133935 words

Chapter 28 - Mijin Buzuwa Book One Complete Hausa Novel

27 Oct 2025

270

din bai da karfin haka a yanzu.
Suna tafiya yana dafe da kanshi ba tare da ya kalle shi ba Yusuf din yace ba irin ku masu sanyin hali ne ya kamata ya auri irin Nafisa ba.
Sun fi daidai da irisu wa yanda zasu caja junan su a zauna lafiya amma ai dama ita haka suke so su samu wanda suke juyawa son ran su.
Yanzu ai ta fara koya min iya magana ita da wanan yar matsalan khadijan din nasan idan an auna ni za a samu VP dina ya hau wallahi Yusuf damay Nafisa take son inji ne wai ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

Suna shiga gidan su Nafisa ne zaune a falo da yan uwanta sai wata bukuwa da tazo mata a lokacin wace bai san ko wacece ba.
Sun fara gaida shi sai dai ita bata dago kai ta dube su ba ganin su tare da Yusuf da taki jini da tayi don a cewan ta Yusuf ne ke kulla mashi duk wani shawara a gamay da ita.
Shima Yusuf din bai tsaya ta kan su ba ya wuce dakin da su mommy suka sauka dauke da ledan take away da suka sayo masu a hanya.
Nafisa may ne hujjan ki na rufe kitchen da kikayi yau tace saboda gida nane yasa na rufe don ina da ikon yin hakan ko ?
Idan abinci yayi saurin karewa wa zaka tambaya yadda akayi dashi ai naga da kawo abincin sai da ka kirani ai in gani ko ba haka na bane ?
Nafisa lalai wuyan ki ya yi kauri a gidan nan har da zaki iya rufe ma iyayyena wuri kada su dafa abinda zasu ci ko suyi amfani dashi.
Amma ba laifin ki bane laifina ne da na sakar maki wan har kike ganin kin isa kike son wuce gona da iri a gidan nan da rayuwa na.
Baki dafa kin basu ba sun dafa ma kansu kuma kinyi bakin ciki da haka da suke yi ko kin mata nan din gidan dasu ne halal malal suna da iko da komai yadda suke su.
Ai ban sani ba sai yanzu da ka fada a gaban kowa nasan yan uwanka sun fini muhinmanci a gare ka yace da may kike daukan kanki ne.
Tace ai sai su fito mu zuba dasu a gidan bansan ka kawo su nan bane don su kara dani tsawa ya daka mata cikin kiran sunan ta da karfi.
Mikewa tayi da kyat itama tana fadin ban san sun isa da kai ba sai naga muna raba kwana a gidan nan dasu.
Haka kike ce tace an fada din yace bada su zan raba maki kwana ba amma ki sani zan kawo wace ta dace in raba maku kwana gidan nan wace zakuyi daidai da fitsaran ki.
Su wa yan nan iyayye nane yanzu na kawo amma mai zuwa in raba maku kwana tana tafe kwanan nan.
Madam ne dake zaune ta mike tana fadin Nafisa kina da hankali kuwa kin san may kike shirin aikata ma kan ki yanzu ?
Ta figi jakkanta dake aje gefen kujeran da ta zauna tana fadin ni na tafi tunda baki da wayo yace bata san bata da wayo ba yanzu ne zata sani.
Waya ya ciro daga aljihun shi ya fara fadin hello inspector kana jina wasu froriners nake son kazo ka kwashe a gida na yanzu don Allah.
Jin haka duk suka mike tsaye don da a zaune suke gefen guda sun zuba masu ido suna sauraren su madam ce ta fara bashi hakkuri da fadin.
Assha Alhaji ai a bin bai kai haka ba basai ka kira hukuma a cikin zancen iyalin ka ba anan akayi sai a sasanta shi a nan Nafisa kin yi kuskure ki bashi hakkuri ke kuma.
Bani taiwa laifi ba su da ta bari da yunwa tun safe ne za ta ba hakkuri tace ni ban masu komai ba balle in basu hakkuri.
Yace da kyau mommy da suke daki da Yusuf suka ji hayaniya yai yawa a gidan yasa suka fito daga dakin gaba dayan su.
Sun fito daidai lokacin da take fadin batai masu laifi ba bazata basu hakkuri ba mommy tace Nafisa kinyi kuskuren ki ba mijin ki hakkuri mu namu mai sauki ne.
Don shi muka zo gidan nan kuma da bakin shi yasa muzo ba wai haka kawai muka kwaso kafan mu zuwa nan ba tunda mun san baki son wani nashi ya rabe shi yasa kowa ya sallama maki shi yanzu.
Shigowan inspector din da wasu polisawa uku ne ya ruda Nafisa da da ta dauki abin da burgan maza yake mata sun gaisa ya nuna su Yanyala da su hadiye yace gasu nan .
Yar uwar su na aure suka zo suka tare min a gida ban san dalilin su nayin haka ba sai ku tambaye su hankalin kowa a falon ya tashi ya juya gurin su mommy ya fara basu hakkuri.
Mommy tace mu bakai muna komai ba don wurin ka mukazo dama ba wurin wani ba macen police din ne ta fara ingiza keyan su hadiye gaba.
Samad kayi hakkuri don Allah ba sai ka wulakanta min yan uwa ba don ni suka zo gidan nan sai ka hada dani duka kace a kwashe mu.
Bissimila yace idan haka yafi maki yan uwa na daine dole na a yanzu gidan nan na kuma gwada maki haka kina iya binsu ga hanya nan a bude ya juya gurin police din yace ku tafi dasu duka.
Samad ni zakai wa haka ni zaka fada a kwashe mu a tafi damu babu ko nauyin haka a bakin ka kake fada.
Ke uwata ce ko may ko ajeni kika yi a gidan mara mutunci kawai ya juya zai fara tafiya da sauri tasha gaban shi tana fadin kuskure ne nasan nayi ba daidai ba don Allah kayi hakkuri.
Madam tace tun farko da haka kikayi da abin baikai haka ba ya nuna su mommy yace su zaki ba hakkuri bani ba ai.
Mommy kiyi hakkuri kisa baki a maganan nan don Allah mommy tace naji zan bashi hakkuri amma haka ya zama ishara a gare ki gaba.
Nan Abdul din ya dage sai idan ta basu hakkuri zai jaye maganan tace cikin dukawa mommy kuyi hakkuri nayi kuskure don Allah.
Iyan bawa tace amma ke kan anyi mutumiyar banza a nan yanzu baki ji kunya ba don Allah ga yan uwan ki ko ina a gidan baki bakin ciki da cin su ba sai mu da mukazo zama daku na dan lokaci.
Dan mune fa mai dukiyan da kike kadagi dashi din har kike ganin kowa ba kowa bane a gurin shi sai ke da yan uwan ki keda iko komai dashi.
Nan suka kaita fada mata abinda suke so a cikin nasiha tace ayi hakkuri zata gyara yusuf ne ya sallami yan sanda suka wuce.
Ranan dai anyi ta ba dadi a gidan tayi nadama tayi bakin ciki abinda Abdulsamad din yayi mata a gaban kowa ya nuna bata da wani power a gare shi yanzu ga madam ma tayi fushi da ita ta tafi tana fadin ta bashe su a idon duniya.
Ta kula wanan ta kwance wancan haka na ta wuni da sake sake a ranta a kan sai ta rama abinda yayi mata akan su mommy din da suka zo gidan don ganin bayan ta.
Ita sam bata dauka don dan su da taimakon ta suka zo ba har yanzu don idon ta ya rufe da son bata kaunar taga wani wanda ba nata ba ya rabe shi saboda tsananin kishi da take dashi irin na buzaye.
Ta kira madam ta bata hakkuri har suka shirya take anan kuma suka fara sabon shirin da zasu aiwatar a kan kowa ma daga bangaren shi.
Shiko a bangare shi ranan daki ya shige bai son yawan hayaniya da kowa don haka ya ke be kan shi a daki ba abinda yake sai tunanen hanyar da zai samu mafita ga alamarin Nafisa.
Saboda yasan ba canza halin ta zatayi ba kwanto kawai tayi a yanzu tana nazarin ta idan zata biyo mashi ne.
Allah ya gani yana son ya kara aure kamar yadda Yusuf yasha fada mai shine kawai mafita gare shi akan Nafisa to amma wa zai aure din da zasuyi daidai da Nafisa a zauna lafiya.
Khadija ina khadija karama ne sosai ga Nafisa da halinta ba zai dauko yar mutane ya jefa a matsala ba ya cuta mata don yanzu yana jin yarinyar a wani bangare na rayuwan shi .
Don haka ba zai cuta mata ba ta wanan hanya na hada aure a tsakanin su wani abu yazo ya samu yar mutane a hannun shi.
Ga mahaifin ta ko yaushe sukai waya yana mashi godiya akan kyautatawan da yake ba yarsu wace kamar kauna take a gareshi.
To amma kuma ga shakuwan da sukayi taya zai iya rabuwa da khadija a yanzu nan tunanen irin rayuwan da suke yi da khadija din ya fado mashi a rai abinda ya sa shi dan murmushi ke nan kadan ya gyara kwaciya yana lumshe idanuwan shi.
Wayan shi ne ya yi tsuwa alaman kira na shigo mai ya dan juya ya daga wayan Queen of matsala ya gani da sauri ya daga kiran nawa.
Tambayan shi nayi lafiya kake kuwa yau ?
May kika gani ya bani amsa dashi sai na rasa abinda zan fada mashi karya na samu kaina da yi nace kawai dai sai nake tunanen hakan .
Fada min kewa na kikayi ko may kika kirani a cikin wanan daren haka baki san ina da mata bane ni Family man ne idan kika hadani fada da mata na fa ?
Wayan na kashe ina ci gaba da tunanen mafalkin da nayi dashi a yanzu daga dan barci ya dauke ni sai wanan mafalkin yazo min gaba daya na saka waya na a off na gyara kwanciya cike da zullumi ina tunanen mafalkin.
Can dai barci ya dauke ni na manta da zancen mafalkin koda na tashi naci gaba da alamura na shima kuma bai kira ba don haka na kara share shi.
Nafisa ko hankalinta bai kwanta ba gida Niger ta kira mai mata aike a can da kukan ta wiwi matar tace may ke faruwa Nafisa ko sakin ki mijin ki yayi ?
Tace bai sake ni ba serah sai dai gaba daya ya canza min yanzu nan dai ta koro mata bayanin abinda ke faruwa cikin kuka.
Serah tace share hawayen ki Nafy murde dan iska zamuyi ya koma sai yadda kika ce a gidan ki bai isa ba wallahi yanzu dai ki daure kibi yan iska yan da suke so daga yau zan shiga in fita zaki gannin nan da kwana uku kedai turo min da kudi kiga aiki da cikawa.
Tace serah har kin kwantar min da hankali na wallahi don yanzu ni damuwa na bai wuce cikin nan dake jikina ba don cewa ake wai idan mace nada ciki ko jinin haihuwa wai komai nata baici.
Serah ta katse ta da fadin da ke nan wanan zancen yanzu may ye kudi baiyi Nafy ina nan shigowa nan da kwana uku kada kiji komai.
Bayan sun gama wayan ta zauna ta zabga ta gumi ta rasa ta ina zata fara da shi zata fara ko da iyayyen ko wanan mugun abokin nasa da ta tsana.
Zaman gidan yanzu haka ake yin shi ba ruwan wani da wani sai gaisuwa a tsakanin su dasu mommy kowa na harkan gaban shi.
Shiko yana tsananin basu mommy girma da kulawan da ya dace a gidan wanda hakan keyi wa Nafisa ciwo matuka ta rasa yadda zatayi dasu a gidan.
Kunci cikin zuciyar ta ba a maganan shi har yakai bata iya boyewa hakan yasa ma ta daina yawan saukowa kasa inda zata gan su ko wani abinda sukeyi shiko sam bai kula da halin da ta jefa kanta a ciki ba yanzu.
Kamar yadda serah tayi alkawari haka ya faru tazo da kule kule da sihiri kala kala tun a ranan suka fara aiwatar da komai kamar yadda suke so ya tafi.
Nafisa sai gani take har aiki ya fara ci saboda yarda da tayi da maganin don irin labarin da Serah ta bata yadda ta shiga kungurumin dajin kasan su wurin samo mata wanan asirin mai amfani da ci da sauri ga wanda akaiwa.
Haka kawai yake ji kwana biyu yana jin haushin kowa a gidan inbanda Nafisa da yanzu yake jin wani irin so da kaunar ta yana shigan shi.
Mommy dake da kaifin basira ta fahinci abubuwa suna sauyawa a gidan don haka ta fara tuntubar Iyan bawa akan abinda da ta fara hangowa ga dan nasu don tun zuwan Serah mommy tasha jinin jikin ta da ita don tsarin ta da zubin ta yafi kama dana yan duniya ta irin mutanen su.
Batai kasa a gwiwa ba ta sanar da mahaifiyar shi hasashen ta amma tace kada ta bari kowa ya fahinci abinda ta fada mata ta dai taimaka mashi da addua.
Hajiya mama tayiwa mommy godiya bayan sun gama tataunawa akan zancen sukai wa juna sallama aka aje wayan.
Sosai hankalin hajiya mama ya tashi da maganan mommy haka yasa ta kira yayan ta da suke uwa daya uba daya a zaria tana neman shawaran shi.
Yace ta bari zai ga wani malamin shi a nan cikin garin zaria da zancen don rayuwar Abdulsamad da wanan matar tashi yana bukatan addua sosai.
Haka suka bar zancen akan zai kira ta taji duk yadda sukayi da malamin nashi idan ya dawo daga wurin shi.

Ban san mun shaku da shi ba sai wanan karon ga jerabawa ya na gaba to muna ga zancen zuci dake damuna haka ya dan sani rama kadan.
Karshe nabawa kaina shawaran abinda ka fisheni na watsar da komai na rugumi karatu na gadangadan ina yi tare da share zancen su gaba daya a raina.
Ranan muna zaune da Maryam a dakin ta tsifar kaina na ke da ya kitso ya tsufa min zan je in wanke kai na wayana yayi tsuwa na duba Yusuf ne a kan layin.
Nayi mamaki kwarai da ganin kiran shi a wanan lokacin na dauka da sallama tare da gaida shi ya amsa yana fadin kanwa ta ina kika shige haka ?
Kai yaya Yusuf ina nan inda nafi karfi mana na bashi amsa yace ko dai mutumin nawa ya boye muna ke ne ban sani ba ?
Wa ke nan kake magana nima na tambayeshi yace abokina mana kuma ogana a wurin aiki nace wai mijin buzuwa kake magana ?
Dariya ya kyalkyale dashi yace kai khadija baki da dama wallahi har yanzu dai mijin buzuwa aiko zaku kwasa dashi idan ya jiki.
Nace ina ruwa na dashi balle balle ya jini .
Yace ke ko keda ruwa dashi khadija yar mama amma dai baki da kirki Abdul din ne zaki ce yau ina ruwan ki dashi da bakin ki kike fadin haka .
Tsuki naja na tabe baki kamar yana gani na a lokacin nace ni na fita batun shi yanzu banda lokacin shi.
Yace subbahanallahi may yai zafi haka ne a tsakanin ku kuma keda mutumin naki khadija ?
Mutumi na ko naka yaya na kai nifa ko wancan lokacin da nake kula shi albarkacin ku ya samu a gare ni har na biye mashi amma ba don shi ba.
Kai haba yar mama bai dace ki fadi haka ba tsakanin ki dashi yanzu ai kunyi nisa sosai bai kamata aji wanan maganan ba a bakin ki.
Taimako fa kikace zakiyi sai da abu ya kusa kai karshe zaki ce ba ruwan ki dashi yanzu ai ko kece mai ruwa har da tsaki akan shi yanzu.
Mu dai bar wanan zancen nace dashi da sauri yace akan may zamu bari idan na tambaye ki zaki fada min gaskiya ?
Nace akan may ke nan yace akan mutumin naki mana nace idan na sani may zai sa na boye maka kuma ?
Yace Yaushe rabon da yazo gurin ki ko kuyi waya dashi when last kukayi koda waya ne please kada ki boye min komai just feel free with me khadija?
Dan jin nayi sai can nace gaskiya mun kwana biyu dashi don ba zan iya tuna zuwan shi gurina ba na karshe ko wayan shi a yanzu.
Yace abinda nake son ji ke nan daga bakin ki sai dai zan ari bakin aboki na inci mashi albasa Abdulsamad yayi tafiya two weeks ago amma dai yanzu ya dawo.
Sai dai ko a yanzu da bukata nazo maki a kan shi don gaba daya khadija ba zan boye maki ba Abdulsamad ya canza ga komai cikin yan kwana kin nan.
Gashi matar shi na shirin haihuwa watan ta ya tsaya tun last month sai dai har yanzu bata haihu ba yana gida ko wani lokaci tunda ya dawo like da ita.
Katse shi nayi da fadin ni may ye nawa a cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login