Showing 27001 words to 30000 words out of 115235 words

Chapter 10 - Halin Girma Hausa Novel Complete

take amma kuma tana bukatar kiran nasa, tayi missing dinsa da muryar sa gaba daya. Kiran nasa tayi tana tashi tsaye lokacin da ta soma ringing, be daga ba, amma kuma tana katsewa ya biyo kiran a take.

"Assalamu alaikum." Tayi sallama wayar a hannun ta bata saka a kunne ba

"Wa alaykisalam."

Ya amsa sai yayi shiru, itama shirun tayi tana saka abinda zata ce

"Shine baka kirani ba?" Ta samu kanta da fad'a ba tare da tayi tunani ba. Abinda dama yake son ji kenan, tayi missing dinsa in dai har tayi korafi akan rashin kiran, murmushi yayi wanda taji sautin sa ta cikin wayar

"Kinyi kewa ta kenan ko?"

"Um um." Tace da sauri

"Kawai dai na kikkiraka bata shiga, kuma Abba ya bani sako shine kawai dama."

"Ohh, sakon Abba ne yasa kika kira ni ba don kinyi kewa ta ba?"

Shiru tayi dan a zahirin gaskiya ba hakan bane, tana bukatar ji daga gareshi, tana bukatar comforting words dinsa, tana bukatar shi kawai ma in short.

"Ni kuma kinga nayi kewar ki, sosai sosai komai ma da nake anan din yinsa kawai nake ba don naso ba, kiyi hakuri kin kirani, ina wajen da dole na kashe waya, shiyasa har kika jini shiru haka."

"Ok." Tace a ba tare da tasan me zata ce ba

"Ya gida ya kowa da kowa?"

"Alhamdulillah, yasu Ammi? Ka samesu lafiya?"

"Lafiya lou, banje gida ba, yau nake shirin zuwa in sha Allah."

"Ok tam, karka manta ka gaishe ta."

"Ba zan manta ba, zance mata sirikarta na gaishe ta, zan kira sai na bata kuyi magana."

" Um um ba zan iya ba."

" Kunyar ta kike ji? Irin kunyar surkutan nan ko?" Ya kyalkyale da dariya

" Ni dai bance ba."

" Ni kuma nace."

" Uhum."

" Wacece Maryam?"

" Yayata ce da akayi bikin su, nazo gidan ta bata da lafiya zan kwana biyu na dan taimaka mata."

" Owk ayya, ki duba ta, Allah ya bata lafiya."

" Amin zataji."

" Baki fad'a min ba, me Abbanmu yace?"

" Na zata ba zaka tambaya ba ai?"

" Na isa? Ina sane kawai dai."

" Dama cewa yayi, a turo."

" Me!!! Alhamdulillah, Alhamdulillah Alhamdulillah! Kina nufin Abba yace na turo magabatana ayi magana? Kenan Abba ya yarda ya bani ke? Kai mAsha Allah, Alhamdulillah."

" Wannan murnar haka." Tace cikin mamaki

" Ba zaki gane ba, ba zaki gane ba Zahraah, Nagode sosai, Allah ya sakawa da Abba da alkhairi. Nagode nagode, wannan ranar ta shiga cikin ranaku masu matukar muhimmanci a tare dani, Alhamdulillah."

" Allah ya tabbatar mana da alkhairi."

" Amin Zahra nah, Amin Amin. Bari kiga na tashi, banga ta zama ba a yau zanje na same su da maganar, in sha Allah a kwana daya zuwa biyu magabatana zasu zo, ayi komai a gama, Allah yasa Abba ya saka mana lokacin kankani, bansan irin farin cikin da zan ba, Alhamdulillah."

" Uhum." Tace dadi na kamata, a kalla ta samu wani da yake son ta sosai, irin soyayyar da ta rasa tun tana yar kankanuwar ta.

" Zan kiraki anjima, ki kula da kanki."

" In Sha Allah. Ba-bye."

Fadawa tayi saman gadon tana jin farin ciki matsananci

" Ya Allah ka sa ya zama alkhairi a rayuwa ta, Allah ka tabbatar mana da alkhairi."

Ta furta tana jin kamar bata da saurin bakin ciki.

***Da karfin sa da kwarin guiwar sa ya isa masarautar su, wannan karon shigar da yasan Bubu yafi so yayi, shigar Manyan kaya da rawani, yayi masifar kyau ya fito a basaraken sa na ainihi, duk wanda yaci karo dasu sai sun kalle shi sun sake kallon sa, kai tsaye bangaren Aji ya nufa, domin wanchan karon be samu ganin Hajjan sa ba, shiyasa ya fara tachan dan tasan sai tayi korafi. Tana ganin shi kuwa ta hau murna, ta rasa in da zata sakashi, mace ce me jin mulki sosai domin mulkin a jinin ta yake dan har tafi Aji, amma kuma a duk abinda ya hada da muhammad bata hada shi da komai da kowa, da kanta take masa komai duk abinda yake so kuma shi take so ko da kuwa kowa ba zai goyi bayan sa ba.
Sai da ya gama mata shagwabar sa son ransa sannan ya gabatar mata maganar auren da yake so aje a nemar masa, murna a wajen ta kamar ta dauke shi ta goye haka taji, karshe ta dinga tsokanar sa da sauran idan amaryar tazo ya manta da ita, da tsohuwar zuma dai ake magani. Da haka ya wuce fada in da yasan zai samu Bubu wanda tuni labari ya riga ya kai masa, ya shirya yana dakon karasowar Muhammad din. Ganin sa ya saka Bubun farin ciki, musamman da ya ganshi cikin shiga irin ta gidan sarauta!

***Abba na zaune ya gama karatun alkur'ani me girma Maman ta shigo, ta zauna a gefen sa yayi kamar be ganta ba

"Dr wai fushin ne har yanzu? Be kamata ace abu irin wannan ya bata maka rai ba, yara hakuri ake dasu."

Daga mata hannu yayi

"Bana son maganar nan, idan har ba zaki iya tankwara yarki ba, kuma ba zaki nuna mata dai-dai ba, shikenan, abinda kuke so kuka zaba zanyi muku."

"Allah ya huci zuciyar ka, da anyi auren ma.in sha Allah zaka sauko, musamman idan kaga zaman nasu lafiya lou."

"Allah ya taimaka." Yace yana kokarin mikewa

"Dama magana nazo muyi, gida zanje."

"Allah ya tsare hanya, ya kiyaya" yace kawai cikjn halin ko in kula

"Kwana uku zuwa sati nake son yi."

"Duk yadda kika ga yayi miki." Ya karasa ficewa. Kwafa tayi ta mike tana jin haushin sa. Ko me zaiyi ba zata hana Zeenat abinda take so ba, an wuce zamanin auren dole. Zai gaji dan kansa ya sakko.
1/12/22, 08:56 - Buhainat: Halin Girma
    12

*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* 

I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb

***Kai tsaye ya wuce zuwa chan gaban Bubun, fadawa na aika masa da kikari, kirarin da yake jin sa har cikin kansa, sai dai baya taba bari yayi tasiri a gareshi, hasalima yi yake tamkar be san me suke cewa ba. Dukawa yayi kamar yadda yake a al'adah ya gaida Bubun, ya amsa masa da ka ba tare da yace komai ba, a irin wannan zaman Bubun baya magana sai ta kama, sanin haka ne yasa Muhammad din ya koma daga bangaren dama ya zauna kafin sauran yan fadar su shiga kawo masa gaisuwa. Amsawa yayi duk a jimlace, ya hakimce a gefe yana sauraron zaman yake wakana. Kasancewar zaman na gab da tashi ne yazo, shiyasa yayi tunanin ba za'a wani ja lokaci ba, sai yaga an dauki lokaci ana maimaita abinda aka fad'a a baya, ya sani sarai hakan tsarin bubu ne, kila kafin ya iso ya shirya hakan saboda shi, murmushi yayi yana satar kallon Bubun da shi din ma shi yake kallo. A karon farko yaji tausayin mahaifin nasa ya kamashi, yadda yake kokarin ganin ya damka mulkin a hannun sa bayan shi kuma bashi da ra'ayin hakan, amma kuma be tursasa masa ba, ya cigaba da bin sa a hankali zuwa lokacin da yake ganin ya dace.
Be san ta yaya zai fahimtar dashi ba, amma yana da dalilin sa babba da ya saka shi tsayawa akan bakan sa, akwai babban kalubale a gabansa idan har ya amince da muradin Bubun , amma ta yaya zai iya gujewa hakan? Bayan babu wanda yasan dalilin sa?
Yana jin sanda zaman ya kare, ya sauke ajiyar zuciya me nauyi ya daga idon sa sama yana kallon tsaruwar fad'ar, komai na ciki me tsada ne da kawa, haka duk wani abu da yake ciki me muhimmanci ne ga masarautar.
Tunanin Bashir ne ya fado masa, da ganin da yayi masa da fitsararriyar yarinyar nan, Bashir yana direbobin Masarautar Kano wanda ya sanshi sosai saboda kaudin sa da hayaniyar sa, kafin ya auri wata mata wadda ake kyautata zaton auren jari yayi, tun daga lokacin kuma ya bar masarautar sai jefi jefi yakan je ya gaida Fulani idan ta kama. Yayi mamakin ganin sa da zabgegiyar mota amma da ya bincika ya gane komai, sai yaji hakan yayi matukar yi masa dadi, yayi Kuma daidai da tsarin da yake son dora su akai.
Dawowa yayi daga tunanin jin kamar an taba shi, ya kalli wanda ya taba shin sai ya fad'ad'a fara'ar fuskar sa,

"Aji!"

"Tunanin me kake haka Muhammad?"

" Babu komai, mun same ku lafiya?"

" Lafiya lou, ya aikin? Amma kazo kenan ko? Zaka dade?"

" In Sha Allah!"

" Sannu da zuwa." Yace yana mikewa

" Zuwan ka dana ji ne ya sakani zuwa , Ina fatan idan ka huta zaka shigo, akwai batutuwan da nake so mu tattauna."

" Muje na taka maka, dama nima akwai maganar da nake so muyi."

" Toh toh madallah."

" Muhammad."

Bubu ya kira sunan sa yana daga zaune

" Na'am Bubu!"

" Naji dadin ganin ka da shiga irin wacce ta dace da kai, Ina fatan dorewar hakan."

" In Sha Allah Bubu, zan kokarta."

" Madallah da kai."

" Allah ya kara girma."

Tashi yayi suka fice tare da Aji, hannun su cikin na juna, Maimartaba ya jinjina kansa yana mamakin tarin kaunar da suke wa juna, har suka bacewa ganin sa sannan ya sauke ajiyar zuciya yana tafiya tunanin abubuwan da aka tattauna don cigaban al'umma. Sai dai yana fara tunanin, tunanin ta ya shigo ya katse masa duk hanzarin sa, ya rasa dalilin da ya saka a duk sanda ya tuna da maganar yake jin duk wata walwalar sa da farin cikin sa ya ragu, musamman a dan tsaikon nan, sai yake jin tamkar ana dakatar dashi da yin wani yunkuri. Shi din mutum ne me riko da addini matukar gaske, baya taba bawa maganganun da za'a zo a fad'a masa muhimmanci ko kad'an, sai dai a duk abinda ya shafi Muhammad baya wasa, yana ji a ransa kar fa abinda tsohuwar matar ta sanar masa ya zama gaskiya, tsoron hakan ya hanashi gabatar da komai cikin sauri yake bin komai a hankali, ba kuma wai dan ya gasgata maganar ta dari bisa dari ba, sai dan yana ji da tsoron sharrin masu sharri, be san me suke shirya wa dan nasa ba, sai dai be gaza ba, babu dare babu rana kullum cikin nema masa kariya yake a wajen ALLAH, ko ma menene tabbas zai zo masa da sauki.

***A falon Ajin ya same shi yana zaune fuskar sa kamar gonar auduga, da kansa zai je amma sai Bubun yace ya bari yazo kawai ya huta. Bayan ya zauna ne fadawan suka fice suka jawo musu kofar.

"Na matsu na sanar da kai wannan albishir din, abinda muka dade muna jira ne, Muhammad dai yazo da magana, har yana neman aje ayi masa tambaya!"

Fuskar Bubu ta fad'ad'a,farin ciki ya mamaye shi

" Masha ALLAH! A kanon ne kamar yadda Takawa yace?"

" Eh har binciken da mukayi, nan din ne in Sha Allah."

" Sai a sanar wa Takawa babu jira, in Sha Allah gobe duk abinda ya kamata ayi sai ayi, jibi sai aje musu da magana, da tsayayyiyar rana domin Takawa ya bukaci ayi komai a cikin kankanin lokaci."

" Madallah...Hakan yayi."

Tattaunawa suka shiga yi har dare yayi sosai,kafin ya koma bangaren sa cikin jin dadin labarin auren Muhammad din.

***Jifa tayi da kofin hannun ta, ya fashe a wajen gaba daya kwalbar ta wawwatsu a dakin, wani irin bakin ciki take a duk lokacin da taji wani abu da ya danganci Muhammad din. Yau Itace a turakar Bubu amma tasan ba zata taba samun kansa ba, idan ma ta zafafa zai iya cewa ta bar masa dakin shiyasa ta yanke wa kanta hukuncin ko da yadawo daga wajen Aji ba zata je ba zatayi zaman ta tayi tunanin menene mafita a gareta.

"Ranki ya dade, Yarima Muhammad yana waje yana neman iso."

" Uban me zai min!!"

Ta daka mata tsawa tana huci, sai kuma ta hau kokarin daidaita kanta

" A shigo dashi babban falo gani nan."

Da sauri baiwar ta fice tana mamakin uwar dakin nata.

Zaman sa yayi yana karewa falon kallo, an sabunta komai ba kamar zuwan sa na karshe ba. Murmushi ne a fuskar sa, yana da yakinin bata da bukatar ganin shi, ko da gilmawar sa ne balle har ya kai ga zama a falon nata, yana sane yazo domin ya kara tabbatar da abinda ya sani tun tuni.
A yadda ta fito, da yadda ta zauna kadai ya isheshi amsar abinda yazo nema, yana kallon yadda take satar kallon sa cikin kallon da yasan na tsantsar tsana ne tun da ya riga da ya dade da sanin bata kaunar sa ko daidai da minti daya ne

" Barka da gida, mun sameku lafiya?"


Ya fad'a da yanayin da yasan zai sake tunzura ta.

" lafiya, ya aikin naku?"

"Babu dadi, na gudo ma na dawo gida cikin yan uwa!"

"Ka kyautawa kanka." Tace a gajarce

Mikewa yayi yana zuba hannayen sa cikin aljihun sa, ya yi mata kallon cikin ido tace

"Bari na koma."

"Baka Sha ko ruwa ba." Tace tana daga zaune

"Na yafe, bani da bukata."

Ya dage gira yana juyawa, da kallon bakin ciki tabi bayansa har ya fice daga falon, ta yarfe hannunta tana jin kamar ta kamo shi ta tayi ta jibgar shi har sai taga ya daina motsi.

"Ciwon Ido, zanyi maganin ka!" Ta furta tana tashi ta koma ciki


***Daga nan bangaren Ammin sa ya wuce, yana jin kansa kamar sabon ango, farin ciki yake ciki shiyasa ma be wani damu da abinda ya faru ba. Dama yasan kafin ya isa ta samu labarin ko ta wajne Hajja ko Bubu, aikuwa yana shiga ta tare shi da murnar ta, ya zauna ya tankwashe kafarsa a gabanta tana jin yadda take lissafo masa abubuwan da za'a bukata na zuwa gidan su Fatiman. A farkon farko be so wani abu na sarauta ya shigo ba, amma kuma da ya tabbatar hakan ba zai yiwu ba, shiyasa yayi amfani da damar nan wajen hadawa Mama gadar zare, dalilin tafiyar ta da shine ya assasa bayan ya kira Khalil a waya ya karanta masa yadda duk yake so ayi, babu musu ya amsa kuma ya tabbatar masa da zai yi komai daidai. Dazu Kuma ya kira shi ya tabbatar masa da Maman ta iso tun wayewar gari. Da wannan ya yi gaba wajen aiwatar da saura shirin sa da ya tabbata zasu yi matukar girgiza kowa ba Maman kawai ba.
Har dare sosaii yana shashen Ammin, ta hada komai abubuwan da ya tabbata zasu dace da tsarin fatimar sa, shi din ma akwai tanadin da yayi mata amma ba yanzu ba, sai ranar da dubban mutane suka shaida, ya zama ita ta zama shi, a ranar zai nunawa duniya kalar gatan da take dashi a wajen sa.
Da sassarfa ya karasa part dinsa, Kai kace wani uban aiki yayi saboda yadda yake jin sa a gajiya. Kwanciya kawai yayi bayan ya aika mata da cool night text message ya kashe wayar sai bacci, baccin da yake yi a duk lokacin da ya samu kansa a dakin sa na cikin gidan.
Zai iya cewa ya jima beyi bacci me dadin na ranar ba, ko dan abinda ya faru a ranar ne? Ko Kuma dai dan ance gida daban yake, dama bahaushe na cewa kowa ya bar gida... wanka ya soma yi, ya fito domin ya karya dan yasan komai na kammale a ajiye yana jiran sa. Zaman karyawa yayi, yayi dialing number dinta yana kallon plate din da ake zuba masa abinci, da hannu yayi masa alamar ya isa, ya karba ya soma ci jin bata daga ba, a yar mu'amular da yayi da ita, ya lura tana da bawa kowanne abu muhimmanci idan har shi ta saka a gaba, misali idan tana aiki takan ajiye wayar ta waje daban ta kammala aikin, haka idan tana wani muhimmi abun bata hada shi da komai har sai ta gama. Tunanin sa ne ya katse lokacin da kiranta ta ya shigo nasa. Murmushi yayi yana jan tissue ya goge bakin sa, yayi rejecting kiran sannan ya bi bayan yana kishingid'a a jikin lallausan tumtum din dake kusa dashi.
Da sallamar ta, ta daga kamar ko wanne lokaci, ya amsa mata shima kafin ta dora da gaisuwa

"Ina kwana?"

"Lafiya lou, kin tashi lafiya?"

"Lafiya lou, yasu Ammi? Ka same su lafiya?"

"Kalou kowa, ya sister Maryam da jiki?"

"Gata ta samu sauki, inaga ma na tafi gida tunda naga ta warke sosai. "

" A ah kiyi zaman ki! " Yace da sauri

" Me yasa? "

" Amm kin gane, kinga tana bukatar ki, ki dan kara mata ko da kwana biyu ko uku ne, zata ji dadi. "

" Owk tam. "

" Yawwa. "

" Ina kika shiga dazu na kira no answer, kitchen? Ko shara? "

" Ya ka sani? Ina kitchen. "

" Na sanki ai, nasan bakya wuce wuraren nan biyu. "

" Lallai, kasan abubuwa da yawa akaina, amma ni bansan komai ba. "

" Zaki sani, karki damu zaki sani fiye da sanin da kowa ma yayi min. ".

Ya karashe maganar cikin sigar tsokana, bata ce komai ba, yasan kuma ba zata ce din ba, shima ba dan tace wani abu yayi maganar ba

"Zan zauna takanas, kiyi min duk tambayoyin da zaki yi min, zan amsa, amma kafin lokacin ina so ki san, nifa soja ne!"

"Soja!" Tace gabanta na faduwa sosai, bata son aikin soja ko miskala zarratin, bata kuma taba tunanin auren soja ba, dan tasan yadda suke very busy da aikin su

"Eh ni soja ne, amma fa irin kurtun nan."

"Soja dai ai duk soja ne, sunan daya ne."

"Amma rank din daban daban ba."

"Uhummm. " Ta ja ajiyar zuciya, ya sammace ta, kenan dai zaman kadaici be rabu da ita ba, dan sojoji basu da lokacin kansu balle na matan su, yanzu ita kenan...

" Karki damu, ba zan dinga nisa ba kinji? Zan zama ko yaushe kika bukace ni Ina kusa, nayi miki alkawari."

"Allah yasa, dan da gaske bana son aikin soja wallahi."

"Saboda me? Aikin taimakawa kasa ne fa, aikin lada ne idan har ka yi yadda ya dace."

"Na sani, ni kawai bana so ne, basu da time din kansu ballanta na ..."

"Na matan su? Haka ko yaushe aka cewa dama,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login