Showing 102001 words to 105000 words out of 115235 words
Chapter 35 - Halin Girma Hausa Novel Complete
rufa asiri ya sa mu gama lafiya
2/21/22, 08:16 - Buhainat: Halin Girma
39
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
****
"Capt... Yaron nan ya bata min rai, ya za'a yi ya zarge ni haka?"
Sassauta fuskar sa yayi, ya dafa shi
"Karka damu yarinta ce."
"Naga alama, waye shi? Aina yake?"
"Bansan shi ba, abokin Habib ne I guess!"
"Amma ka barshi ya zage haka, naji ma kamar hausar shi bata fita."
"Eh, born and raised a UK ne, dole zaka ji banbanci, anyways ya wuce na masa fad'a kuma."
"Shikenan, yanzu menene next? Da ya kamata muyi?"
Daga kafada Moh yayi cikin halin ko in kula yace
"Babu komai for now, muna cigaba da addu'a."
"Bari na wuce, I'm sorry akan maganar missing files din nan."
"Karka damu."
Da kallo ya bishi har ya fice daga wajen, ya daga waya ya kira waya, sukayi magana sannan ya kashe. A kalla Mahfuz ya zama wani haske a binciken sa, kowa da yanayi da tsarin aiikin sa, ya san aikin sa sosai ya kuma masifar burgeshi, he's smart and intelligent daga ganin shi,kuma da yake akwai banbancin yadda k'asar mu take da tasu sun fi mu skills da kayan aiki.
Shugaban su ya kira, ya fad'a masa abinda ake ciki, ya kuma tabbatar masa da zasu yi duk yadda zasuyi, a yanzu za'a binciki layin mudassir din a nan za'a gane da wadanda yake waya, yana ajiye wayar ya kira Ammi sukayi magana sannan ya kira Aji da yake ta avoiding kiran sa tun ranar, yana dagawa kuwa ya haushi da fad'a akan kin daga wayar sa da yayi, hakuri ya bashi kawai sukayi magana ya kashe.
Bayan kamar awa daya aka kirashi, ya shirya a gurguje ya fita cikin tawagar yaran matasan sojoji, kowanne a cikin su a kalla zaka gane babu sauki a tattare dashi, bakin glass ne a fuskar Moh, baka ko ganin kwayar idon sa. A wani waje suka hadu, ya tarar da taron jami'an tsaro birjik kowannen su cikin shiri, babu kalar da babu na jami'an tsaro tun daga kan police, DSS, civil defense, uwa uba sojoji. Gaisuwa ya dinga amsawa daga kananan ma'aikata har ya karasa wajen manyan da suke kasan wata rumfa suna magana. Details din bayanan da aka samu ta wayar Musaddik din suke dubawa, in da ya nuna babu wata waya da yake yi illa da mutum uku, Moh din sai wata number da take kiran sa kullum a private number sai kuma Samha Bello Turaki, da Kamal Abubakar Santuraki
Kansa ne yayi masifar daurewa, menene alakar Samha a cikin case din? Karba yayi ya sake dubawa sosai ya tabbatar da abinda yake a rubuce. Yasan Laila ce take son shi ba Samha da take kawarta ba,menene akalar Samha da Iman dinsa da har za'a hada kai da ita a sace ta?be san dalili ba, abu daya ya yarda dashi, dukkan su anyi amfani dasu ne, domin a samu galaba akan sa, su kuma idon su ya rufe, suna son ganin bayan din suka fadawa gadar zaran JABIR!
"Mun gabatar da duk binciken da zamuyi akan shi, mun kuma tabbatar da ba Musaddik bane, yayi amfani da fuska ne, sannan yayi amfani da wata na'ura da take kwafar murya, wadda take da masifar tsada Kuma alamu sun nuna ya jima tare da kai, ba zaka taba ganewa ba idan har ba sani kayi ba, Musaddik yana da kusanci da kai shiyasa har sukayi amfani dashi wajen samun kanka, da weakness dinka, sai kuma dan uwanka Kamal da suka taimaka musu don cimma tasu bukatar da hadin guiwar Samha da bamu san wata alaka dake tsakanin ku ba."
"Layin da yake private mun saka an bud'e mana shi, kuma mun tabbatar da ana kira da layin ne daga wani bangare ma dajin falgore! "
"Yana ina yanzu? "
" Yana ciki, idan an gama shiryawa shine zai shige gaba, kaine team captain din da zai jagoranci tafiyar daga bangaren mu. "
" Ok sir! "
Yace yana sara masa, wucewa yayi zuwa in da aka ajiye fake Musaddik din, yana so ya tantance banbance banbancen dake tsakanin sa da Musaddik dinsa da ya kasa ganewa, yana durkushe a k'asa bayan dukan da ya sha, ya tabbata dai da JABIR ya tantance shi sosai kafin ya kawo shi, dan hatta tsawo da yanayin sa irin ma Musaddik din ne, fuskar sa ya dago, ya kare masa kallo zuciyar sa na tafarfasa, kamar zai daure amma sai ya k'asa, ya dunkule hannu ya naushe shi a baki, nan da nan kuwa sai jini, ya saka kafa ya hambare shi. fitowa yayi ya tsaya a filin yayi bayanin yadda zasu yi idan sun isa, duk suka amsa suka shiga motocin su a gurguje suka dauki hanyar dajin falgore.
Gudu suke kamar zasu tashi sama, haka suke a duk sanda suka fita operation amma kuma na yau yasha banban da sauran operation da suka taba zuwa, yau abun nasu ne, su aka taba kai tsaye shiyasa kowa yake ji kaamar abin ya shafe shi sosai, cikin kankanin lokaci suka isa saboda masifar gudun da suke, barbazuwa sukayi a dajin kamar yadda yake according to plan. A daidai lokacin Dr da zai kawo maganin ya iso, tana kwance kamar kullum ta gama galabaita sosai ya shigo rataye da jakar sa, tana ganin sa ta mike da sauri, bata ma san tana da ragowar karfin nan ba sai data ganshi, ya ajiye jakar ya ciro magungunan a ajiye su, sannan ya koma gefe ya tsaya yana jiran shigowar ogan, jim kadan sai gashi ya shigo, ya duba magungunan yayi masa bayanin yadda za'a sha.
"Tashi!" Ya daka mata tsawa yana tamke fuska
"Dan Allah kayi hakuri, dan Allah."
"Wallahi sai kin sha."
"Dan Allah kayi hakuri." Ummimi tace tana kuka
"Shut up munafuka, idan na sake jin bakin ki sai na sheke ki har sai kin daina numfashi. "
Gefe ta koma jikin ta yana ta rawa, bindiga ya ciro ya nuna Iman dashi
"Karbi kisha kafin na harbe ki. "
Hannu ta miko ya zuba mata, ya kafe ta da jajayen idon sa, yana nuna ta da bindigar, ta sha sannan ya juya yana murmushin mugunta ya fice likitan yabi bayan sa. Dakin da ya ajiye Musaddik da driver ya shiga, ya tarar da Musaddik din a kwance amma kuma sallah yake daga haka, kwafa yayi ya fito bayan ya rufe kofar, yazo wajen yaran nasa da suka cika harabar wajen dauke da manyan bindigu cikin shirin ko ta kwana.
"Zan shiga na kwanta, ku kula sosai bana so a samu matsala."
"An gama Oga."
Suka hada baki wajen fad'a, ciki ya shiga su kuma suka cigaba da tsaiwa a wajen.
Zagaye gaba daya dajin sukayi, kowa ya kama stand dinsa, Moh da sauran zaratan sojojin suka kutsa kai ciki, sai da suka dan shiga sosai sannan suka hango bukkokin dake wajen, wanda suka tabbatar da nan suke. Sake rarrabuwa sukayi waje waje, suka sake zagaye bukkukin.
Sai da suka gama shiryawa tsaf, sannan Moh ya basu signal na su yi attacking dinsu, nan fad'a musu ta sama ta ka, nan suka rikice suka shiga kokarin maida martani, sai dai yawan Jami'an tsaron ya ninninka yawan su,. Cikin baccin da ya soma dauke shi yaji alamun yamutsewar wajen, kafin ya kai ga mikewa aka bugo kofar dakin aka shigo, Moh ne a gaba yaran sa na take masa baya, dukkansu a shirye suke su bada rayuwar sa dan ceto Madam din Oga. Kasancewar be shiryawa zuwan su ba, sai ya zama kamar sun ci galaaba akansa ne, babu bindiga ba babu komai a hannun Moh, ya matse shi a jikin bango ya shiga bugun sa, bugu ba na wasa ba, sai da yayi masa laga-laga ya sake shi cikin jini ya fadi kasa, ya bi ya take kansa da kafarsa cikin tsananin bacin rai ya soma magana.
"Kafin kaga karshe na, ni zan ga karshen ka da duk wanda ya goya maka baya..."
" Oga an samu Madam, she's bleeding so badly." Da sauri ya juya yabi bayan dan sanda da ya shigo, ya bar yaran nasa da JABIR.
Jini ne sosai yake zuba, da sauri ya karasa gabanta, idon ta da yake kokarin rufewa da kalle shi. Rawa jikin sa yake ya tallafota jikin sa
" Bude idon ki, dan Allah ki bud'e idon ke, me sukayi miki? Me sukayi miki?"
Karasa rufewa idon sukayi ruf, ya dagata ya fita da ita jikin sa na rawa, idan har wani abu ya same ta, sai ya karar da dangin JABIR kaf.
_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D'aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/24/22, 08:05 - Buhainat: Halin Girma
40
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
****Wasu daga cikin sojin ne suka bi bayan sa, in da sauran jami'an tsaron suka cigaba da dudduba bukokin har suka samu nasarar ganin Musaddik da driver a wani daki, sai makamai masu yawan gaske suma daki gida, dukkan su suna bukatar taimakon gaggawa musamman Musaddik da yake cikin mawuyacin hali.
Karar harbi suka ji, daga baya wanda basu san dalilin harbin ba, a zaton su sun kama duk yaran JABIR din, da shi kansa JABIR din bayan dukan da Moh yayi masa. Zagayawa baya sukayi, suka ga mutum a kwance cikin jini, bashi da alamun yana tare da sauran yan iskan amma kuma basu san me ya kawo shi wajen ba.
"Mu taimaka masa."
"Waye ya harbe shi?"
"Akwai sauran yan iskan a baya, let's check, ku dauke shi ku tafi dashi zamu biyo bayanki. "
" Ok. "
Suka ce suka taimaka masa, da k'yar yake numfashi saboda tsabar wahala, a motar da aka saka Musaddik suka saka shi, suka bi bayan motar da Moh suke ciki dan basu taimakon gaggawa. Rik'e yake da hannun ta yana kuka wiwi kukan da ya kasa dauriyar rik'e shi, gani yake kamar motar bata sauri duk kuwa da irin gudun da suke tsulawa, idan har wani abu ya same ta, ba zai bar kowa ba wannan alkawarin sa ne.
Sanda suke karaso asibitin tuni iyayen gulma yan jarida sun iso domin samun na watsawa, kofar baya suka koma suka bi, suka shiga asibitin dan a yanayin da take ciki ba zai yarda wasu yan iska su dauke ta a hoto su yada wa duniya ba, duk ma wata gidan jarida ko talabijin da tayi gangancin haka sai ya yi shari'a dasu.
Da sauri nurses din suka karbeta, daidai lokacin da Babban likita ya karaso cikin tawagar sauran manyan likitoci mata da maza, aka shiga da ita ciki domin bata taimakon gaggawa.
Zagaye ya soma yi a wajen cikin yanayi na fitar hayyaci, wayar sa da take ta faman nemam agaji ya gaza fitowa da ita balle ya iya amsa kiran da ake ta faman doka masa da ba zai wuce daga makusantan sa ba, bashi da sukunin ciro wayar balle ma ya amsa ta, balle ya iya wata magana ba tare da yasan halin da Iman din sa take ciki ba.
Cikin kankanin lokaci asibitin ya cika da manyan mutane daga masarauta da kuma gidan gwamnati, Takawa ne ya karaso a karshe ya samu shiga wajen da Moh din yake shi kadai sai wasu sojoji daga gefe, sauran mutane suna ta dayan bangaren in da aka kai Musaddik da saurayin da aka harba wanda yake cikin yanayi mara dadi.
Yana ganin Takawa yayi saurin isa gareshi, sai kuma ya ja ya tsaya a gabansa ba, hannun sa ya kama, ya ji yadda hannun yake rawa sosai kamar wanda yake jin masifaffen sanyi.
"Kayi addu'a muhammad, babu abinda zai faru kaji?"
Da ka ya iya amsa masa, sai a sannan ya ga su Abba, ya matsa ya gaishe su, dukkanin su suna cikin tashin hankali, Abba kamar bashi ba saboda tashin hankali, sun riga Takawa zuwa wajen amma ba'a barsu sun shigo ba saboda tsoron da yake wajen sai da Takawa yazo sannan suka samu shigowa. Sunyi waya da Maman Iman din tun dazu ya kuma san zuwa yanzu sun karaso amma ba lallai su shigo kai tsaye ba, sai ya dubi Muhammad yace
"Mahaifiyar ta suna waje, nasan ba za'a barsu su shigo ba."
"Bari naje." Ya fad'a yana yin gaba, daya daga cikin sojan ya bishi suka tafi tare, daga chan baya ya hango su a tsaye suna magana da wani Soja da yaki fafur barin su, su shiga wajen, ganin Moha da kansa ya nufo wajen ya saka sojan sake kallon matan.
"Alhamdulillah." Mamma tace tana share hawayen ta
Bud'e musu sojan nan yayi tun ma kafin ya karaso, dan yayi masa alamar ya barsu, suka shigo suka sameshi, ya gaishe su, sannan suka tambaye shi Iman din, Alhamdulillah kawai yace suka bishi zuwa ciki duk jikin su ya kara sanyi sosai da lamarin.
Be barsu sun karasa wajen da su Takawa suke ba kasancewar duk maza ne, sai yasa aka kawo musu kujera suka zauna shi kuma ya karasa ciki.
An dauki tsawon lokaci kafin likita guda daya ta fito, har zata wuce sai ta ga Takawa, da sauri ta je ta durkusa ta gaishe shi, sannan tace suna kokarin su in sha Allah babu matsala, sannan ta je ta dauko abu ta dawo ta koma ciki.
Sun iya iyakar kokarin da zasuyi wajen ganin sun tsaida cikin amma kuma hakan be yiwu ba,saboda karfin maganin da aka bata ba zai bar cikin ba, Allah yaso babu wani illa da yayi mata bayan fitar da cikin. Wankin ciki suka hada sukayi mata sannan aka saka mata drip saboda ta rasa ruwa sosai a jikinta tsawon kwanaki tana amai sannan babu abincin da take ci. Numfashin da take fitar wa ne kadai zai baka tabbacin tana da rai bayan haka babu wani abu na jikinta da yake motsi, tayi fayau kamar ba ita ba, sai uban fari da tayi kamar babu wadataccen jini a jikinta.
Tura ta akayi zuwa dakin da aka kwantar da ita, sannan Drs din suka fito wajen da su Takawa suke, suka kwashi gaisuwa sannan sukayi bayanin yadda al'amarin ya kasancewa pills din da aka bata ne yayi karbi sosai, jiri ne ya kwashi Muhammad yayi kamar zai fadi wani bafade yayi saurin taro shi, ya rik'e shi jikin sa. Hakuri kowa na wajen ya dinga bashi, kafin a bada damar a shiga a ganta, Takawa ne ya fara shiga sannan su Abba suka shiga tare dasu Mummy, sannan suka fito aka bar Muhammad din ya shiga. Tunda ya shigo ya hangi yadda take fitar da numfashi a wahalce, jikin sa ya kara sanyi sosai, shine duk ya jawo mata wannan matsalar tana zaman zaman ta. A da ya dauka matsalar sa kawai gidansu ne, shiyasa gaba daya ya taso da tsanar mulki tun bayan da yaga abinda ya faru da Baban su Laila lokacin bashi da wani girma sosai amma hakan be bar kwakwalwar sa ba, ya taso da tsanar mulkin da ganin cewa duk wata masifa tana cikin gidan sarauta.
Sunyi aiki tare da JABIR zai iya kiransa da abokin sa mafi kusanci dashi a wanchan lokacin, bashi da hannu a matsalar da JABIR din ya samu daga sama har aka sallame shi aka kuma karawa Moh din matsayi irjn wanda ya Jabir din ne ya chanchanta, bayan nan duk wata alaka tasu ta yanke, har ya manta dashi sai lokaci zuwa lokaci yake tunashi,be taba saka wani abu a ransa game dashi ba, rayuwar sa yake kansa tsaye ba tare da sanin akwai babban makiyinsa da yake burin ganin bayan sa ba.
Maganar Takawa ce ta fado masa wadda yayi masa ita dazu kafin ya bar asibitin
_"Ka sani bawa baya taba wuce ko ketare kaddarar sa, dan haka ka dauka wannan din kaddarar ka ce kayi addu'a Allah ya baka ikon cinyeta. Sanin kanka ne mutum be isa ya hana ko dakatar da kaddarar ka ba, kafi kowa sanin yaran da suke tare da kai suna tsaron ka gida da mota ba wai na matsayin da kake dashi bane a aikin ka, alfarma tace ya saka aka baka su har haka, wanda duk munyi hakan ne saboda mu baka kariya a gida da waje, sai dai yanzu na kara tabbatar wa babu dan adam din da ya isa ya tsare ka face Allah, kuma duk abinda Allah ya kaddara zai faru toh fa sai ya faru ko da a gaban idon mutum ne."_
Gaban gadon ya ja ya tsaya cikin tsananin tausayin ta, be taba kawo tunanin wani abu zai faru da su haka ba a dan kankanin lokaci nan, ya zata shikenan ta rabu da duk wata matsala tun da suka riga sukayi auren su, ashe ba haka bane. Hannun wanda babu drip a jiki ya rik'e, ya zauna a gaban gadon yana karewa fuskar ta kallo, daga gani kasan ba jin dadin baccin take ba, bacci ne me cike da wahala iri iri.
Ya jima sosai a dakin, babu motsin komai, kamar babu kowa aciki, knocking akayi, ya cire kansa da k'yar ya kalli kofar ba tare da yayi magana ba, sai da aka sake kwankwasawa sannan yace
" Bismillah. " Turo kofar akayi, Zeenat da Habib ne a gaba sai Mam, sai sauran jama'ar gidan da sai yanzu suka samu damar shigowa wajen, tashi yayi daga zaunen, ya mikawa Habib hannu suka gaisa, fuskar sa ta dan daga alamun yayi kuka, ya mai jiki yayi masa sannan suka gaisa da sauran matan, suka fita tare da Habib din waje,
"Ina Mahfuz?"
Yayi karfin halin tambayar sa dan yayi tunanin tare zasu zo. Dan duban sa Habib din yayi kamar me tunani, sai kuma yace
"Ai tare aka fito dasu daga wajen da Iman din take."
Kallon rashin fahimta Moha yayi masa yace
"Ban gane ba?"
Kwalla ce ta zubowa Habib din yayi saurin sharewa yana daurewa yace
"Dazu da safe ya fito daga gida akan zaizo ya same ka, nace zan raka shi amma ya bari anjima yace zai gane ma ai, shikenan ya tafi, bansan ya akayi ba, sai gashi shima an same shi a chan in da Iman din