Showing 90001 words to 93000 words out of 115235 words
Chapter 31 - Halin Girma Hausa Novel Complete
ta zauna a wata kujerar roba, tace zuwa tayi zaman cikin ya ishe ta, nan fa suka hau murna suka cigaba da hirar tana sauraren su, a kalla sun debe mata kewa dan bata dawo ciki ba sai bayan da aka kira sallar magriba.
Washegari ta tashi da murnar zuwa school bayan tsawon lokacin da sukayi a gida, jin ta take tamkar sabuwar shiga dan wasu abubuwan ma ta mance su, tasan da yawa duk yau zasu koma saboda dai kowa ya gaji da zaman gidan. A tsanake ta shirya tsaf, sannan tasaka madaidaicin mayafi akan doguwar rigar atamfar da ta saka brown da touches din blue, ta dauki jaka da takalmi da suka shiga sosai ta saka, tayi shigarta ta mutunci ta fito ta nufi kitchen in da ta hanyar ne ake bi zuwa bq, a kitchen ta tarar da Ummimi, tana karasa hada breakfast dinta, ta russuna har k'asa ta gaishe ta, ta amsa a sake tana dudduba aikin.
"Zan je school ba jimawa zan ba, idan an gama komai sai a jera a dining, zanyi bakuwa anjima da rana."
"Allah ya dawo dake lafiya gimbiya, idan kina bukatar abu ba sai kin zo ba, kira kawai zakiyi ranki ya dade."
"Babu komai karki damu."
"A dawo lafiya, Allah ya bada sa'a."
"Amin."
Tace ta juya ta fita, ta samu driver ya gyara motar, sai kawai ta fad'a baya tana tuna rayuwa yadda take a shekarun baya, shekarun da basu gaza biyu ba. Tun da suka isa makarantar duk in da suka wuce sai an kalle su, a department dinsu kuwa kamar an ga nama ko wata sabuwar halitta, dama labari ya riga ya karad'e ko ina amma dama ance gani ya kori ji, wasu takanas suke zuwa su tabbatar da gaskiyar abinda suka ji. Tayi ta zuba ido ko zata ga Zeenat amma ko me kama da ita bata gani ba, har suka gama abinda zasuyi suka koma gida.
Tun daga ranar kullum sai taje school din ta dawo, sai zaman gidan ya zama mata kad'an, duk dare kuma suke shafewa suna magana da shi a waya, ba wani sosai take jin kadai ta ba, sannan kuma duk sanda take free da rana ko ta dawo da wuri tana zama ta koya wa masu aikin karantun al'qurani da ta lura kusan rabin su basu iya ba, kawai rayuwar su sun taso ne akan hidimtawa gidan sarautar, tun iyaye da kakanni suke a haka har zuwa yanzu babu wani sauyi da ya samu rayuwar su. Hakan ba karamin dadi yake mata ba, a kalla ita ma zata samu lada me dinbin yawa.
Wasa wasa sai gashi yayi sati uku cif da tafiya, duk sanda ta tambaye shi yaushe zai dawo sai yace mata surprise zai mata kawai, haka take hakura ta kyale shi, kullum cikin shiri take dan tasan zai iya zuwa mata bakatatan, wasu magunguna da momma ta bata wanda yawancin su na fruits ne da madara su take ta faman sha, dan sosai suke mata dadi har ta kanyi mamakin kanta a lokacin da Mamman ta bata , bata wani ji dadin su kamar yanzu ba.
Wata rana a cikin ranakun da take zuwa school ta kai yamma, ta tashi duk jikin ta babu dadi, ciwo take amma bata san takamainai me yake mata ciwo ba, kamar kar taje school din amma sai ta daure dai, ta shirya ta kira Ummimi ta rakata, tunda dama sai da yace lallai ta dinga tafiya da masu rakata amma bata tafiya dasu. Tare suka tafi yau haka nan taji bata son tafiya ita kadai, suka jirata tayi lecture ta fito wajen biyar na yamma, a gajiye likis gashi ko ruwa bata saka ma cikin ta ba, kaidar tace bata cin abu a school tun da ma, sai dai idan zata dade irin haka taci ko snacks ne shima ba ko yaushe ba, dan mafiya yawancin lokuta rage kudin da Abba yake bata Mama take ta bata kadan, shiyasa ta koyi yadda zata yi karatun haka,sai kawai ya zame mata jiki ko yanzu da take da komai bata damu taci din ba
Da sauri Ummimi ta karbi Jakarta da kayan hannun ta, ta tayata bud'e mata motar ta zauna sannan ta zagaya ta shiga bangaren ta, bata lura da su biyu ne a gaba ba, har da wani sai da ya gaishe ta
"Amarya barka da rana."
"Barka dai, ai ban ma lura ba, ina wuni?"
"Lafiya lou wallahi, dama wannan gajiya da kuka kwaso, dama munyi waya dashi ne yace na biyo ta makarantar taku sai mu wuce, zasu sauka da karfi shida da rabi, sai mu dauko shi a airport, amma fa yace kar na fad'a miki dan wai so yake yayi surprising dinki."
Dariya ta saka
"Lallai, ina ta tambayar sa yaushe zai dawo yaki fad'a min, so yayi kawai yanzu ma sai dai na ganshi kenan."
" Ai irin wai surprise din masoya."
Dariya kawai tayi, bata kawo komai a ranta ba, ganin Musaddik ne, haka kuma sai taji wani yanayi na dokin ganin mijinta, wanda yau ya cika sati uku da kwana biyar cif da tafiya. Hanyar airport din suka dauka, ta kwantar da kanta a bayan da yake saramata sosai.
**A word of encouragement to All TTC mother's (Trying to conceive) do not lose hope, Allah yana tare daku, ku cigaba da addu'a, Allah ya baku 'yaya masu albarka da mu baki daya. Baa debe tsammani daga rahmar Allah.
_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D'aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/17/22, 09:45 - Buhainat: Halin Girma
36
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
*******�?
Cikin wani yanayi taji kamar bacci yana fuzgarta, ta sake gyarawa sosai Ummimi ta matsa mata sosai ta kwanta a bayan, nan take kuwa bacci ya dauke ta. A tunanin Ummimi tsabar gajiya da wahala ce ta saka ta baccin, dan tun safe suka fito kuma tana lura bata saka komai a cikin ta ba sai ruwa, ita dai ta bata kudi taje cafeteria ta siya abinci taci, amma ita kuwa bata ci komai ba, dole ne ko ba karatu kake ba, ka jigata balle. Tausayin ta taji, musamman da ta gama fuskantar halin kirkin da, bama ita kadai ba duk ma'aikatan gidan na murna da samun ta a matsayin uwargijiyar su, babu hantara balle tsangwama, gaba dayan su son ta suke da gaske.
Tafiya suke tayi babu alamun zasu tsaya, har duhu ya fara mamaye sararin samaniya, kallon ta Ummimi tayi taga har lokacin bacci take da gaske, shiru kake ji a motar babu wanda yake magana a cikin su, a tunanin da za'a samu ko yar karamar hira ce tsakanin driver da na gaban amma babu wani wanda yayi magana a ciki, jakar dake kusa da Iman din ce ta fadi kasa, Ummimi ta sunkuya da nufin dauka, abinda ta hango a hannun shi ya saka hantar cikin ta kadawa, a firgice ta dago tana dunkule jakar a hannun ta, juyowa yayi ya dube ta, ya sake dago mata hannun nasa da kyau dan ta gani sosai, bindigar ce kuwa, tsoro ne ya kamata,
"Idan kika sake kika bud'e bakin ki a wajen nan, sai na fasa kanki da alburushi."
Da sauri ta rufe bakin ta da hannun ta, juyawa yayi kan driver yace
" Idan ka kai karshen titin zaka gangara haggu."
Da ka ya amsa, daga gani a tsoroce yake, rashin sani ya hanasu ganewa tun shigowar su motar. Kallon Iman take ganin da gaske bacci take, bacci me nauyi da ya hanata jin duk abinda ya faru, mamaki ne ya kama Ummimi, dama ta saba irin bacci haka ko kuma dai akwai matsala, da sauri ta dan taba ta, sai taga ta motsa kad'an tamma kuma bata tashi ba, ajiyar zuciya ta sauke, hawayen da take ta makale shi ya gangaro zuwa fuskarta, me yasa mutane suka lalace haka? Labarin da suke ji a gidan radio yau shine ya faru dasu? Idan har masu sarauta da masu hannu da shuni basu da tsaro toh waye kai kuwa talaka? Anya rayuwar zata tafi a haka?
Cikin tsananin fargaba take har suka karaso wani gida, karami a cikin gungurmin jeji, babu gida gaba babu baya, ba zaka taba tunanin halitta irin ta mutum zata rayu a wajen ba, tana jin yadda suka dinga shiga kan tudu da kwari alamun sam hanyar bata mota bace, ko tace mota bata taba bi ba. Murfin motar ya bud'e yana nunawa driver bindiga, suka fito a tare ya zagayo wajen sa ya rik'e kugunsa. Fito yayi da bakin sa, sai ga wasu kartin maza su biyu sun fito, tare da wata mace a bayan su, tafawa sukayi da daya daga ciki sannan yace
"Kayi babban aiki, aikin da zai firgita ilahirin k'asar har ma da ketare, tana ina?"
Bayan motar ya nuna masa, ya tafi zuwa wajen ya bud'e yana leka ciki
"Baccin ne be sake ta ba har yanzu?"
"Eh!"
"Tasha ruwan kenan!" Yayi murmushi yana rufe kofar
"Tasha sanda ta shigo motar."
"Kayi kokari sosai... Kudos!"
"Thank you sir."
"This is a shame to the Nigerian Armies, The royalties, government, gaba daya ma, duk sunyi failing, ta yaya kake tunanin mutane zasu sake yarda dasu? Bayan sun damka hakkin kulawa rayuwar su garesu, sai ya zama sun k'asa tsare kan su?"
Sai ya kwashe da dariya
" Yaron nan a bayan mu yazo, yaron nan ta dalilin sa na rasa komai, ciki harda aikin da na kwallafa rai, saboda shine shafaffai da mai? Saboda shi din dan gata ne, shiyasa aka fifita shi akan kowannen mu, me yafi mu? Mulki?"
"Oga!"
" Haka ne mana!" Ya fad'a da karfi
"Haka ne. Kullum cikin favoring dinsa ake, kullum cikin yabon sa ake, na kai mataki Babba amma yaron nan, ta dalilin sa komai ya baci, ya kake tunanin zan iya hakura?"
"Kunsan shekarun da na dauka ina gina rayuwata har na kawo wannan lokacin?"
"A ah." Suka girgiza kai dukka
" Shekara goma sha daya, amma cikin sakan da be wuce goma ba, ya kwace komai, khaki na, rank dina, mutunci na a idon duniya, na muzanta, na zama abin gudu da k'yama."
Duk sun yi shiru kowa na sauraren sa, shirun shima yayi dan bashi da abin fad'a kuma
" Ku shigar dasu ciki, idan princess ta tashi a fad'a min."
Sai ya juya ciki ransa fari tas, ya tabbatar saura kiris bomb ya tashi, bomb din da zai tarwatsa duk wani farin cikin Muhammad Ahmad Santuraki da duk wani makusancin sa, shekara biyar kenan yana bibiyar sa, ya kuma samu nasarar samun duk abinda ya samu a yanzu, wanda yake tabbatar da su kadai sun isa su tarwatsa duk wani farin cikin sa. Matsala daya da ya samu, bashi kadai ne yake son ganin bayan sa ba, nasa kawai yafi zafi ne, sai ya hada guiwa dasu, yayi amfani dasu wajen samun abinda ya samu akan sa, ya kuma tabbatar da babu wata alaka da zata sake hada su a nan gaba, ya datse duk wata hanya da zasu neme shi.
Ta jima tana bacci sosai, Ummimi dake durkushe a gabanta tana kuka sosai taga ta motsa, ta cigaba da motsawa tana yamutsa fuska kafin ta bud'e idon ta da kad'an kad'an da sukayi mata matukar nauyi, saman dakin ta fara kalla, sai kuma ta shiga jujjuya idanunta tana son gano a in da take, da sauri ta yunkura zata mike, Ummimi ta taimaka mata tana rik'e ta
"Karki tashi da sauri jiri zai iya daukar ki, ina tunanin sun zuba miki magani ne.". Ta fad'a cikin muryar kuka
"Ina ne nan? Me muke anan Ummi?"
"Ni ma ban sani ba, wanda kukayi magana dashi, shi ya kawo mu nan, sun sato mu!"
"Musaddik?"
"Eh."
"Innalillah wa inna ilaihi rajiun." Ta furta a hankali, kanta da yake jujjuyawa ta saka hannu ta dafe, amai ne taji yana taso mata, ta yunkura da nufin tashi amma kafin ta kai kofar har ta soma aman, wanda babu komai a cikin sa sai zallar ruwa, tun tana yi har ta koma kakari kasancewar babu abinda yake cikin ta tun safe, rik'e ta Ummimi tayi tana kuka, tana jera mata sannu, sai da taga ya lafa sannan ta taimaka mata ta maida ita gefen tabarmar da ta tashi,
"Bari na samo miki ruwa, sannu."
Ta tashi ta fito, su biyu ne a zaune suna karta, suna ganin ta suka tashi
" Ruwa take so dan Allah. "
Da Ido sukayi wa juna signal, kafin daya daga ciki ya shiga wani daki, ya dawo da ruwa ya mik'a mata, ta karba ta juya ciki, ta tarar da ita tana ta juyejuye akan tabarmar, ta rik'e cikin ta da yake murda mata kamar zata amayar da kayan cikin ta. Dagota tayi, ta bata ruwan ta kuskure bakin ta, sannan ta sha, ta koma ta kwanta tana sake rik'e cikin ta.
***Kwanan Zeenat biy babu Bashir babu alamar sa, Abba kuma ya zuba musu Ido be sake cewa komai ba, ko Mama be sake mata maganar ba, shirun nasa yayi masifar bata tsoro, dan bata san me yake shiryawa ba, ranar suna zaune Zeenat din na cin wainar fulawa, ba wani dadin ta take ji ba amma itace kadai take mata dadin ci, sai nama da tuwo idan ta same su kamar wata tsohuwar mayya, jigum jigum suke kowa da abinda yake damun sa. Kofar falon ce ta bud'e duk suka kalli kofar a tare, Abba ne ya shigo, ya wuce dakin sa, k'asa k'asa Zeenat din tayi masa sannu da zuwa be ma ji ba, ya shige jimawa kadan ya fito, ya dubi Mama da tayi tsam tana kallon sa yace
"Tunda har ban isa na saka ko na hana Zeenatu abu a gidan nan ba, kin nuna min ban isa ba tun fil'azal, na bar miki ita, idan har tana so mu shirya da ita lallai ta koma dakin ta, ke kuma, hakuri na ya gaza, kije gida kya dawo duk sanda kika shirya gyara auren yarki, idan har Zeenatu bata koma dakin mijinta ba, toh zaman mu ba zai cigaba ba. "
Daga haka ya saka kai ya fice, ba don darajar yaran dake tsakanin su ba, ba kuma don darajar zaman da tayi dashi na dadi a baya ba, da zai sauwake mata ne kawai, amma hakan ba zai yiwu ba, har yanzu yana sonta yana kuma son ta gyara halayenta.
Tashin hankali ba'a saka maka rana, da girman ta da komai gotai gotai zai ce taje gida, zagaye ta dinga yi a falon kaamar tayi hauka, duk tsawon shekarun da sukayi da Ibrahim be taba nuna mata ko yatsa ba, sai gashi a yanzu da girma ya soma hawa kansu, tayi abinda gaba daya mutuncin ta ya zube a idon sa, har yana cewa zaman su ba zai yiwu ba.
" Mama dan Allah kiyi hakuri, zan koma wallahi ba zanzo ku samu matsala da Abba akai na ba, zan jure koma menene dama ni na jawo ma kaina. "
" Ba laifin ki bane, babu abinda zai faru , sake gwada kiran Bashir din idan be daga ba sai kawai na saka Habib ya kaiki chan gidan su, daga nan sa neme shi ai dole yazo ya dauke ki."
Da sauri ta dauko wayar, ta kira amma sai taji alamar anyi blocking number, ajiyewa tayi jiki a sanyaye tana fadawa Maman, kira mata Habib tayi, tace yazo maza gida yanzu duk abinda yake yi, be dau wani lokaci ba sai gashi, ta fad'a masa abinda take so yayi,yace mata babu mota Abba ya fita, sakashi tayi yaje ya kira musu napep yazo suka tafi, suka fita ta ja ajiyar zuciya, ba zata iya jure tafiyar ko ina ba, ta riga tayi girman da zaman gidan su zai mata wahala sosai, idan kuma ta tafi bata san ta yadda zata dinga ji daga wajen Zeenat din ba.
***Yana zaune bayan sun gama wani taro da sukayi, ba zaka iya tantance yanayin da yake ciki na bakin ciki bane ko na farin ciki, kiran layin Musaddik yake amma still amsar daya ce, switch off, sunyi dashi kafin su taso zai kirashi, gashi babu wani isashen lokaci da zasu sake batawa, su biyu ne suka shigo, suka sara masa sannan suka koma gefe suka tsaya
"It's time sir."
Mikewa yayi be ce komai ba, ya shige cikin dakin, ya dauki jacket dinsa da dayar wayarshi, sauran kayan nasa sun riga sun fitar dasu tun dazu,gaba yayi suka bishi a baya, yana cigaba da kiran Musaddik din, ganin da gaske ba zai same shi ba, shiyasa ya sauya akalar kiran zuwa kiran ta. Jiya basuyi magana ba gaba daya, yasan tana kaiwa yamma a school haka kuma yasan ta dawo a gajiya, ko da ya kirata no answer sai kawai ya kyale ta, a zuwan suyi magana a yau kafin ya taho. Ringing wayar tayi tayi ba'a daga ba, bayan ta katse ya sake kira amma still no answer, sai ya kashe wayar tasa baki daya ya tura ta cikin aljihun wandon sa, sanda suka karaso wajen motocin da zasu dauke su, tuni duk sun shiga shi kadai ake jira, dama kuma shine Captain din tafiyar. Yana shigowa duk suka mike tsaya, irin doguwar babbar motar nan ce, sai da ya zauna sannan duk suka zauna, driver ya jasu suka bar harabar wajen.
Tun daren jiya labari ya kai fadar Maimartaba na rashin dawowar Iman din daga makaranta wanda ma'aikatan gidan ne suka kai labarin, kamar wasa da kowa ya dauka, a tunanin su ko wani wajen ta biya, amma ganin har dare ya soma yi ya saka hankali ya fara tashi, zama ma neman gagarar Fulani tayi bayan an tabbatar da bata je gidan su ba, ba kuma wani da zata je wajen sa, number driver da tata duk suna shiga amma kuma babu answer. Waya Maimartaba yayi a dare ya sanar da yan sanda abinda yake faruwa, a take ya tashi jami'an tsaron ko ta kwana, suka bazama neman, in da aka samu wayar Iman din da ta driver a cikin makarantar in da aka ajiye a waje daya cikin wata farar leda.
Tsawon daren babu wanda ya