Showing 51001 words to 54000 words out of 115235 words
Chapter 18 - Halin Girma Hausa Novel Complete
saurin dawowa ta manne kusa da ita hakan ya saka ta dan ji dama dama. Mukullin motar da Abba ya damka mata a hannun ta da wasu abubuwan ya sakata shiga yanayin da ta shiga, har yanzu bata bar mamakin yadda abubuwan suka sauya salo ba, wanda bata taba tunani ko hasashen hakan zai faru da ita ba.
Bayan kamar minti biyar sai ga Mamma nan ta dawo ta kalli sauran tace
"Matar nan bata da kirki sam, bansan me yake damunta ba, amma ni dai na fad'a mata lallai ta shirya tazo ta kai Iman dakin ta, idan ma wani abun ne yake damun ta ko hassadace ita ta sani, na dai bata girmanta."
"Toh ai Mamma kina gani kinsan bakin ciki take, dama kin kyale ta kawai mu kadai mun isa."
"Ai ba haka ake ba, mu muka zo muka same ta kuma duk tsiya dai itace marikiyar Iman din."
" Toh yanzu zata je din ko yaya?"
" Ban san mata ba wallahi, na dai fita ai ni dai,ruwanta taje ruwanta taki zuwa, babu abinda za'a fasa."
" Wallahi kuwa, Allah ya kyauta."
" Amin." Tace tana zama.
Kayan Iman din aka gama fitarwa, aka saka a booth din motocin, sannan suka shigo da kansu su uku, suka ce sun zo daukar amaryar su, akayi barkwanci dai tsakanin su da su Mamma sannan suka fita su kuma su Mamma suka fito da Iman din.
A harabar gidan suka hadu da Mama, ta yafa mayafi ita da Aunty Muhibba, kallo daya Mamma tayi mata ta dauke kai suka fice, bayan su suka bi, suka tarar an gama tsara mutanen kowa ta samu mota ta shiga, kowacce mota da kayyadadden mutanen da za'a saka kuma kowa ya samu an shirya komai yadda ya kamata.
Motar amarya ce kawai ta rage sai guda daya da tazo a karshe, wasu ne suka shiga dayar tare da Aunty Muhibban sai Mamma da Mama suka shiga ta amarya suka sakata a tsakiya kamar yadda ake yi. Chan jikin kofar motar Mama ta makale taki yarda ta rabi Iman din, jawo ta sosai Mamma tayi jikin ta ta dora kan Iman din a saman kafadarta ta kwanta sosai.
Lamido Crescent suka nufa in da nan ne ainihin gidan Iman din, sojojin da ke zube birjik a gaban gidan ya saka mutane sake jinjina lallai Babba ne Muhammad din, gida ne hadadden gaske wanda dama chan a nan Muhammad din yake amma an masa gyara sosai da ba zaka taba cewa ba a lokacin aka gina shi ba. Tsaruwar gidan da yadda aka kawata faluka da dakunan gidan da kaya na alfarma ya kusan saka Mama shan k'asa, ta rik'e hannun Aunty Muhibba dan da gaske ta tsorata da yadda taga gidan. Falo biyu ne daya sama daya k'asa sai dakuna biyu a sama, uku a k'asa kuma kowanne Masha Allah kaya ne aka zuba na alfarma, kar Azo batun kitchen wanda duk yadda Mama ta kai ga kure siyayyar ta sai taga ta raina kanta, komai na ciki unique ne ga wasu shegun electronics wasu ma bata san menene amfanin su ba. A daddafe ta daure ta shiga ko ina dan yadda kowa ya zura ido a kanta kowa so yake ya ga yadda zata shiga dimuwa ko ma ta kasa rik'e bakin cikin ta har ta nuna a samu abin fad'a.
Basu wani jima a gidan ba suka fito, dama saboda dai su san gidan Iman din tunda yanzu ba anan za'a fara kaita ba, masarauta zash dan suna da shagalin bikin da zasuyi su ma.
Kin yarda Mama tayi ta koma motar amarya ta fad'a wajen Aunty Muhibba dan komai zai iya faruwa idan ta zauna gata ga Iman din. Bata taba tunanin kalar wannan daukakar ga Iman din ba. Sai gashi in da Iman din taje ko zata je nan gaba bata isa ta taba kai wa wajen ba har abadah. Tayi mata nisan da za'a iya cewa ya kai tsakanin nisan sama da kasa.
Bata kara raina kanta ba sai da ta gansu a cikin masarautar, babbar masarauta irin ta Kano, da bata kawo kanta a ciki ko da wucewa tazo yi kuwa bata taba hasashen kasancewar ta ba.
Wani tsari akayi na tarbar su, wanda ya sake bawa mutane mamaki, kana kallon fuskokin kowa zaka tabbatar da yadda suke ciki. Sanda suka isa bangaren Fulani kakar Moh din da kanta ta taso ta rungume Iman a jikinta, ta kuma zaunar da ita a kusa da ita, jikokin ta sauran suka hau dariya suna tsokanar ta, ta biye musu suka dinga yi kamar ba matar sarki ba, duk da ba kowa ne aka bari ya shiga wajen ba, iya makusantan Iman din ne daga Mamma sai Mama sai dangin Abba su biyu sai Amaani da take makale da Iman din, sauran mutanen a wani babban falo aka ajiye su aka shiga gabatar musu da nau'ikan abinci kala-kala na gida dana kasashen ketare.
Sun dan jima a shashen Fulanin mutane daban daban manya wanda suka zo bikin suka dinga zuwa suna ganin Iman din, kunya kamar ta nutse ta dinga boye kanta wanda hakan ya saka suka kara son ta kowa ya dinga yabon ta yana yaba sa'ar da Moh din yayi.
Rakasu bangaren Moh din Fulani ta saka akayi, wanda dama chan aka ware wa Iman din da wanda zasu tayata zama kafin gobe yan uwan ta su dawo shagalin da za'a yi a babban Hall din gidan da tun a ranar an gama tsara shi an kawata shi.
Two bed room ne sai falo da kitchen, tuni masu kula da shashen sun gyara komai, daya daga cikin dakunan aka kaita, sannan su Mamma sukayi mata sallama aka bar mata Amaani, khadija, Zahra sai su Amira, duk dai yan matan aka bari a zuwan su Mamma sai su dawo gobe. Kamar zatayi kuka haka taji da zasu tafi amma kasancewar ta me dakiya ta daure kawai tayi shiru tana cigaba da kallon komai tamkar almara.
A falon su Amira suka zauna bayan sun raka su Maman sun dawo suka dasa kallo da hirar gidan Iman din da irin yadda aka karbe su a masarautar. Tana jin su sama sama bata fito ba sai ma tayi kwanciyar ta saman gadon dakin tana shakar kamshin da ta tabbatar da kamshin sa ne dan shine kamshin da ko da yaushe take jin sa yana yi.
Tana kwance taji kamar motsi, ta daga kai ta duba, sai taga kofa a jikin karshen bangon dakin wanda sai ka lura sosai zaga gane don ta saje da kalar curtains din dakin. Budewa taga kofar tayi, ta mike daga kwanciyar da tayi da sauri kafin ta gama daidatuwa har ya shigo, cikin shigar bakin dogon wando da riga armless, cikin mamaki take kallon sa har ya shigo cikin dakin gaba daya. Mikewa tayi tsaye lokacin da ya karaso daidai in da take. Ya saka hannu ya shafi gefen fuskar ta.
"Wai tsoro kika ji?"
Da ka ta amsa, ya rik'e ta ya zauna a gefen gadon sannan ya zaunar da ita a daidai kusa dashi, k'asa kallon sa tayi, ya zuba mata ido yana kallon ta kamar a ranar ya soma ganin ta. Farin cikin da yake ciki a yau din mara misaltuwa ne, ba zai iya tafiya adamawa be sake ganin ta ba shiyasa kawai ya hakura da zuwan sai da safe.
D'agowa tayi da nufin ta ga abinda yake, tayi saurin sake maida kanta k'asa ganin yadda idanun sa sukayi k'asa sosai. Hannun ta ya kamo ya rik'e a cikin nasa yana murzawa, yana kokarin danne abinda zuciya da gangar jikin sa ke wassafa masa. Yadda yake murza hannun nata da yadda suka samu kusanci sosai ya saka ta a yanayin da bata taba samun kanta ba, shi din ma hakan ce, dan yadda yake ji yayi imani idan aka dauki lokaci me tsawo baa bashi matar sa ba toh komai zai iya faruwa. Lissafin ta yaji sunayi ya saka shi jin gaskiya ba zai iya bari har tsawon kwanakin da su Ammi da nan Kano kowa ya diba na shagalin da zasuyi ba. Kwana daya ya isa anan ko biyu chan kuma daya idan yaga zasu ki yarda zuwa zai ya samu Aunty Fatima ya karanta mata komai a taimaki dan maraya a bashi matar sa ko kuma yayi musu aika-aika.
Turo kofar akayi, su dukka suka kalli kofar, da sauri Khadija ta juya tana fadin
"Dan Allah kuyi hakuri."
Tashi yayi tsam bayan ta fitan, ya sakawa kofar key ya dawo ya mikar da ita, ya cire mata alkyabbar da take jikin ta har lokacin, saurin runtse idon ta tayi saboda yadda dinkin fitted gown din jikin ta ya kamata sosai dan sai da suka kusan haurawa sama da Mamma kafin ta yarda ta sakaa. A abuja aka mata duk dinkunan nata kuma kaf babu wani dinkin arziki a duk kayan da Maman ta bayar akayi mata tace idan tazo kayan lefen ta sai ayi mata wasu na fita amma ita nata duk na zaman gida ne ayi wa Moh kwalliya. Dogon numfashi yaja, a karo na farko ya ganta haka babu hijabi balle mayafi. Kayan su zauna das a jikinta,ta wajen hips din sun zauna kamar a jikinta aka dinka su. Idon sa ya shiga rarraawa daga tsakanin kirjinta zuwa kasan hips din ta, yabi flat tommy dinta da kallo wanda zaka rantse ba'a saka masa abinci saboda shafewar sa.
"Masha ALLAH!"
Ya samu kansa da furtawa, kunyar da take ji kamar ta haka rami ta shige gashi ya hanata sakat ya rik'e ta babu damar ta zauna. Sai da ya more kallon ta tsaf sannan ya dawo samar fuskar ta ya matso daf da ita har tana jin hucin numfashin sa a saman fuskar ta, tayi saurin runtse idon ta ya kura wa lips dinta ido, ya kai bakin sa daidai kan nata ya shiga kissing dinta passionately ba tare da ya shirya ba.
Jikinta ne ya hau rawa tayi kokarin hanashi amma sai ya sake matso da fuskar ta sosai, ya tallafo ta ta baya ya sakata a jikin sa ssosai ya cigaba da aikin sa. Ta saman bayanta taji yana neman abu, har ya kai wajen da zip din ta yake, ya shiga jan shi zuwa k'asa, da sauri ta rik'e hannayen nasa tana girgiza masa kai hawaye har ya fara sauka a idon ta.
"Pleaseeeeee." Ya furta cikin muryar da taji kamar ba tasa ba, ta shige ciki sosai.
"Dan Allah kayi hakuri." Tace tana sake rik'e hannun nasa, dan taga kamar ma baya gane me take cewa.
Wayar sa dake cikin aljihun wandon sa ce tayi kara, ya janye ta yana murmushi ya ciro wayar yana daidaita kansa.
"Zan kira ka Bashir."
Kawai yace yana kashe kiran. Lokacin ta koma ta zauna tana kokarin daidaita kanta dan ba karamin yanayi ta shiga ba.
A gabanta yayi kamar kneel down, ya tallafo fuskar sa yana mata kallon tsantsar kauna, turo baki tayi ta harare shi ya tuntsure da dariya
"Pretender kawai."
Ya saka hannu ya lakaci gefen hancin ta, murnushin ita ma tayi ta juyar da kanta daga kallon sa abinda ya faru yana cigaba da haskawa a idon ta.
"Kaje anan kiran ka."
Tace ganin yaki tashi ya kuma hanata sakat da kallon sa da idon sa da suke sake bata tsoro a game dashi.
"Kora ta kike? Wallahi sai naki tafiya na kwana anan din dama ai daki na ne."
" Ya hakuri ni dai dan Allah."
" Matsoraciya, kin fiye tsoro wallahi."
" Tsoro ai halak ne." Tace tana dariya
"Inyee kinyi baki haka? Yarinya zaki maimaita maganar nan ne, for now zan barki amma gaskiya zan dawo, kice ma su Amaani su kwana dayan dakin ke kadai zaki kwana anan, kinga dama akwai secret door dita kawai sai na shigo mu sha soyayyar mu."
" Tab!"
" I'm serious
#Rano💕
#Rano💕
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
1/31/22, 19:12 - Buhainat: Halin Girma
21
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
**************
Ta kofar ya koma ya fice bayan ya tabbatar da ya isar mata da sakon da yake son isarwa, yana kallon yadda tayi laushi sosai ta bishi da kallo har ya fice gaba daya.
Kai tsaye wayar sa ya dauka ya kira Bashir, ya daga yana tafiya zuwa shashen Takawa dan yana son ganin shi
"Ya akayi Bashir?"
"Barka da warhaka Ranka ya dade"
" Barka dai, ya taro?"
" Mun gode Allah, an kawo amarya yallabai."
" Yayi kyau, Allah ya baku zaman lafiya, ka kula da ita sosai kar naji wani abu mara dadi, karka kuma taba yarda mahaifiyar ta ko wani yace zai taka ka akan matar ka."
" In Sha Allah ranka ya dade, hakan ba zata faru ba."
"Yayi kyau, sakon ka na wajen Musaddik."
Godiya ya hau yi dan dama abinda ya saka kiran kenan. Cilla wayar yayi a aljihu sanda ya isa sashen Takawan da ya zata ya jima da isa a adamawa.
***A tsorace take tun bayan da mutane suka yaye, yan matan biyu da aka barta dasu suma basu wani jima ba suka cikawa wandon su iska dan ba zasu iya zaman ba, babu kalar ma da bata yi musu ba akan su zauna amma suka ki, a cewar su idan suka zauna basu san uban da zai maida su gida ba su ba samari masu mota ba ga unguwar da shegen nisa kafin kaje titi. Haka tana ji tana gani suka yi tafiyar su suka barta. Tasha kuka kuwa kamar ba zata mutu, ta dinga tsinewa Bashir albarka taji kamar ta gudu ta bar garin ma baki daya.
Tana nan a zaune cikin duhu taji ana saka mukulli a kofar gidan, tashi tayi da sauri tana zaro ido,a duhu take dan dama da wayar ta, ta haska kuma babu charge ta mutu tun dazu.
Shigowa yayi yana haske gidan da wayar sa, ya shigo ciki ya dalle ta, tayi saurin kare fuskar ta tana cewa
"Waye!" A tsorace
"Amarsu ta ango."
Wani abu ne ya tokare mata a makoshi jin muryar sa, tayi kansa da sauri ta hau kai masa duka tana kuka
"Allah ya isa ban yafe maka ba, Allah ya isa."
Rik'e hannun nata yayi da karfi ya juyar da ita ta dawo tana jingina da bayan sa
"Ni kike wa Allah ya isa? Lallai ma yarinyar nan."
"Allah ya isa na fad'a mugu, macuci maha'inci."
Juyo da ita yayi ransa na soyuwa amma ya danne kamar be ji komai ba, ya dalle mata baki da bayan hannun sa, yayi murmushi yana sake haske ta
"Duk abinda ma zaki ce ki fad'a amaryata."
Kuka ta shiga rusa wa da karfi, ganin zata iya jawowa a jiyo su a makota ya sakashi jawota ya shiga sumbatar ta, ta dinga dukansa tana harbin sa a kafa amma ko a jikin sa, sai da ya gajiyar da ita sosai sannan ya saketa yana murmushin, a kalla ya rage zafi dan yasan ba lallai Hajjaju ta yarda ta barshi ba.
A wajen ta duk'a tana kuka, ta dinga jin kamar ta mutu ta huta da abinda take ji, tana jinshi yana waya har ya gama kafin ya dagata tsaye ya rik'e hannun ta a cikin nasa su shiga barin gidan.
Mota ce a kofar gidan irin wadda yake zuwa wajen ta zance, bud'e mata gaba yayi ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ya shiga mazaunin driver ya tada motar suka bar unguwar.
Tafiya sukayi da dan nisa har suka iso unguwa, gangarawa taga yayi zuwa wata doguwar hanya suka dinga tafiya kafin su isa kofar wani babban gida, horn taga yayi da sauri me gadin ya bud'e gidan ya shiga da motar ciki. Tunanin ta ne ya tafi wani waje daban, ko dai Bashir gwada ta yake yana so yaga yadda zatayi idan ya kaita wanchan gidan shiyasa ya kai ta? Ko kuma dai duk shiri ne. Murmushi ya sakar mata ta cikin hasken da ya hasko cikin motar bayan ya tsaya a gaban ginin gidan.
Sauri taga yayi ya bud'e motar sanda wata babbar mata hamshakiya ta nufo su cikin wata irin kwalliya, ta sha ado sosai tana walwali, katuwar gaske ce dan zatayi biyu ko ma ukun Bashir din idaan aka hade shi da Zeenat din waje daya.
Kafin ta kai ga garasowa Bashir din ya isa wajenta. Yayi kamar zai zube a k'asa a gabanta, ta riko shi tana masa murmushi, ware ido sosai Zeenat tayi tana tunani toh ko Maman shi ce? Karasowa tayi daidai kofar da Zeenat din take ciki ta bud'e mata tana sakar mata murmushi
"Amarya."
Ta kira ta tana sakin hannun Bashir din ta kama na Zeenat din tana jawo ta daga ciki.
"Sannu da zuwa kanwata, sannu sannu."
"Kanwata?"
Zeenat ta maimaita sunan tana bin Bashir da kallon neman karin bayani amma sai taga ya fuske kamar be ganta ba. Takawa suka shiga yi har zuwa cikin gidan wani babban falo da yasha kawa sosai. Wasu mata ne hamshakai suma kamar matar farkon suka tarbi Zeenat din suna tafi, ita dai Zeenat gaba daya kanta ya kulle jira take su samu kebewa da Bashir ta tambaye shi me yake faruwa. Zaunar da ita matar tayi ta ja hannun Bashir din sauran mstan suka hau shewa da dariya, bin su Zeenat tayi da ido har suka haura sama, zuwa anjima kad'an sai gata ta sakko ita kadai babu Bashir din cikin shigar kayan bacci ta karaso falon ta kalli sauran matan tace
"A rakata dakin ta ko?"
"An gama Lay, an gama."
Suka tashi gaba daya, daya ta kama Zeenat din suka nufi wata hanya da take a bayan kafar benen dake falon, wani dogon corridor ne suka bishi har zuwa bayan dakunan gidan, sai wani daki guda daya a wajen da kofar sa tana kallon kofar da suka fito, nan taga an bud'e, sannan sun shiga gaba daya ciki.
Katifa ce a k'asa karama kamar ta yan boarding sai wata karamar kujerar roba fara, suna