Showing 39001 words to 42000 words out of 115235 words

Chapter 14 - Halin Girma Hausa Novel Complete

ka shirya zaka kaita wajen uwarta kenan bayan na gama cin wahalar ta, duk abinda nayi baka gani ba. "

" Kiki tsoron Allah, na gano duk irin rikon da kika yi wa Ummi, kinci amanata kin ha'ince ni, Ashe ke din fuska biyu ce dake ban taba sani ba."

" Da yake yanzu hankalin ka ya koma wajen tsohuwar matar ko, ko nace tsohuwar karu... "

A wani irin bacin rai ya daga hannu zai Kai mata mari, fasawa yayi yaji kamar an rik'e hannun zuciyar sa na tafasa, ba ya cikin mazan da zasu daki matar su,baya kuma fatan hakan duk da irin yadda Maman ta bata mishi rai.

"Dukana zakayi Ibrahim? Dukana? Akan na fadi gaskiya, waya san auren da kukayi na gaske ne ko kuwa? Tunda mu dai babu wanda ya shaida, shine zaka dauki hannu ka dake ni akanta ko?"

Ji yayi kansa yana sarawa, be taba tunanin tashin hankalin mAman ya kai haka ba, juyawa yayi da nufin barin kitchen din amma sai yaji ta rik'e masa riga ta baya

"Wallahi ba zaka je wajen ta ba, wallahi ba zan yarda ba."

Tsoro ne ya kamashi jin ta daga murya sosai, da sauri ya fizge rigar sa ya daga kafarsa wajen ficewa daga gidan ma gaba daya, ba zai biye mata ba, har a jisu a gidan abinda zai zamar masa abun kunya a wajen yan uwan sa .
Shashen Gaji ya wuce da ya hango Iman tsaye da Musaddik a chan wajen gate din. Sako ya kawo mata daga Muhammad ya juya ita kuma ta koma cikin gidan.
Tana shiga Mama dake tsaye a falo tana huci ta fisgota, saura kad'an ta fadi amma ta tsaya akan kafarta, kallon Maman take a tsorace dan bata dauka abin nata ya kai haka ba

"Zan ga uban da ya isa ya fita daga gidan nan wallahi, wato kece munafukar kina so ki hada uwarki da ubanki ko? Toh wallahi baki isa ba na gama cin wahalar ki."

Matsawa baya tayi ganin kamar dukanta Maman zatayi, kamar daga sama sai ga Habib kaamr an jeho shi, yayi saurin shiga tsakani yana wa Maman magana,

" Lafiya Mama? Me tayi?"

Bata jira amsar Maman ba ta yi saurin ficewa.
Abinda Abba ya guda sai da ya faru, magana har gaban gaji, mama ta dage ba zai tafi ba shi kuma yace bata isa ta hana shi ba, haka sukayi ta kai ruwa rana karshe ya je da kansa ya dauko kayan Iman din ya bawa Habib ya saka masa a mota sannan suka tafi tana kallo ta cigaba da haukanta.



***Jingina tayi ta rufe idonta a lokacin da suka shiga jirgin, karon ta na farko kenan shiyasa take jin tsoro tsoro amma ta dake dan da wuya kaga abinda zai sa kaga weakness dinta, rashin tsaron da ake fama dashi a k'asar ya saka Affan yi musu booking flight kawai zuwa Abujan dan ba zai yi risking tafiya da Iman din a hanya irin wannan ba. Lokacin ma da Moh yaji labarin tafiyar tata sai da yaji tsoro Allah yasa ba a mota zasu ba, dan har ya gama shirya yadda zai siya musu ticket din kawai ya aikawa abba amma kuma baya so a san shine sai kuma tace masa a jirgin zasu, hakan ya saka shi samun relief. Tafiyar su Dubai ya saka basa waya sai dai chatting dan kar tayi saurin gano shi. Da zata tafi ya saka Musaddik kai mata dubu biyar a cikin envelope, sai da ya jinjina kudin kafin ya aika, kyautar sa ta farko kenan amma sai yake jin kunyar kai mata, tana bukatar manya manyan abubuwa a wajen sa amma akwai sauran lokaci.
Tunawa da tayi da envelope din ya sakata cirota a cikin handbag dinta ta bud'e, murmushi tayi ganin kudi ne sai wani dan karamin note an rubuta I love you da shape din heart a k'asa. Sosai taji dadin kyautar tayi ta kallon note din tana jin dadi sosai.
Cigaba da rikewa tayi a hannun ta har zuwa sanda zasu sauka sannan ta maida cikin handbag dinta tana jin wani irin feeling, she's nervous bata san wanne irin tarba zata samu ba. Tana ganin sanda Abba ya dauko waya bayan sun sauka yayi kira.

"Mun sauka." Taji yace sai kuma yave

"Owk tura min number shi."

Suna tsaye ya sake duba wayar, number aka turo ta text message ya ciro ta ya kira ya fad'a masa yadda zai gane su kafin ya kashe yana cewa

"Ummi muje gashi chan ma."

Matse jakar hannun ta tayi, taja akwatin ta zuwa wajen wanda yake nufo su.

"Welcome Sir."

Yace cikin girmamawa, ba bahaushe bane jikin sa sanye da wasu uniform navy blue an saka number 5 a daidai aljihun.

"Thank you."

Karbar kayan su yayi ya zuba a booth sannan ya budewa Abba gaban motar ya zauna ita kuma Iman ya bud'e mata baya sannan ya jasu suka fita daga airport din. A daidai wani hotel suka tsaya Abba ya juyo bayan ya kalli Iman yace

"Zanzo da safe in sha Allah, ki gaishe su, idan kina bukatar wani abu ki kirani."

"In Sha Allah Abba, Nagode sai da safe."

"Allah ya kaimu." Ya fice ya rufo kofar ya tsaya daga gefe yana kallo suka bar wajen.

Ta cikin dark tinted glass din motar Iman take karewa garin kallo tana admiring ko ina musamman da dama magriba ta kawo kai dan wasu masallatan suna kokarin fara kiran sallah.
A wani babban gida cikin jerin gidajen Babbar unguwar nan ta Maitama yayi horn, a hankali gate din ya shiga zugewa har ya karasa budewa gaba daya. A gefe daya yayi parking kafin ya gama daidaitawa wasu mata su uku da wasu maza biyu suka fito ta wata kofa suka nufo su dukkansu fuskar su dauke da farin ciki mara misaltuwa.
1/21/22, 12:57 - Buhainat: Halin Girma
16

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

*****************
Yana zaune a daki kiran Aunty Faty ya riske shi, dagawa yayi yana tashi dan yasan dalilin kiran

"Mun shirya tafiya kawai zamuyi kana ina ne?"

" Ina cikin gidan bari nazo."

Yace yana cire wayr, takalmin sa ya zura ya fito falon, fadawan dake wajn part din suka yunkuro jin motsin sa, da hannu yayi musu alamar kar su bi shi ya shiga takawa zuwa shashen Fulani da ya san a chan zai same su.
Babban falon ta ya nufa in da ya tarar da su da yawan su, daga gefe akwatuna ne masu yawan gaske, da ido ya bi kayan kafin ya zauna suka hau tsokanar sa da ango ango, yawancin su yan uwan Ammin sa ne,sai dangin Bubu da matan abokan sa da badu da yawa sosai, komai Takawa yace sai Bubu yace masa ba sai an zo ba, ayi komai a nan din kawai. Yanzu ma dan dai abun kamar al'ada ne, shiyasa kawai Takawa yace ya kyale su idan yaso sai ya zama ba kowa da kowa ba.
Anty Faty ce ta tashi ta hau nuna masa yadda kayan suke

"Wannan saitin na Takawa ne, gasu nan 12 ne cip, kaya ne na alfarma komai da kasan ya kamata a saka an saka ciki, sai wannan masu pink din su kuma saitin Ammi ne, suma Sha biyun ne kamar na Takawa, wadannan kuma masu purple din na Hajja ne da dan tsohon mijin ta Aji, guda shida ne gasu nan ko? Sai masu maroon din nan na karshe, namu ne dan muma ba za'a bar mu a baya ba, suma guda 6 ne idan ka hada set nawa kenan? "

" 36!" Yace yana sake bin kayan da ido.

" Wadannan kwandunan kuma, gasu nan guda 24 kowanne da ka gani, abokin Bubu Maimartaba sarkin Ghana ne ya aiko dasu."

" Allah sarki." Yace yana murmushi

" Kilishi fa?"

" Auw kaga na manta ko? Gasu chan fito dasu Harira."

Tayi wa daya daga cikin bayin dage tsaye daga gefen kayan magana,

" No a barsu bana bukatar su, a barsu anan zan duba su daga baya, akwai kayan da za'a kai na rabon da zasuyi a dangi, suna cikin Ford 2 nasa an saka su, zaku duba kafin ku wuce, komai yayi in sha Allah."

" Owk shikenan, kaga wadannan boxes din da kasa aka yi musu design a dubai da hoton ku?"

" Na gani aunty sunyi kyau sosai, su nake so a fara fitowa dasu, dan Allah aunty ayi duk yadda nace."

" An gama karka damu."

" Shikenan, Musaddik zai shige muku gaba, ya za'a yi tafiyar?"

" Eh da wai kamar motoci goma haka, sai wanda za'a zuba kayan Hilux din Takawa masu rufin bayan nan, idan yaso sai su biyo baya ko?"

Murmushi yayi me aji, ya girgiza kansa yana ayyana kalar tsiyar da ya shuka yana kuma jinjina abinda zai faru nan da wasu yan awoyi. Bed room din Fulani ya shige, ya sameta da yan uwata da suka zo, ya zaune tsakanin wasu tsofaffi biyu ya dinga tsokanar su ya hanasu sakat, kowa ya ganshi yasan yana cikin farin ciki mara misaltuwa, yanayin sa kadai zaka san ba karamin murna yake da auren ba, su kuwa basu san harda murnar hawan jinin da ya tabbatar zai kama Mama, dama ita hassada ga mai rabo taki ce, idan kuma zaka gina ramin mugunta toh ka gina shi gajere baka san ko kai ne zaka fad'a ciki ba.


****Mama babu zama tun da taga yamma tayi ta tabbata suna hanya ko sun kusa zuwa, tayi nan tayi nan duk farin ciki ya hana mata sakat, karar tsayawar manyan motoci a kofar gidan ya saka kowa nutsuwa aka hau sake gyara wajen, kowa ya zauna ana dakon shigowar su.
Gate din gidan me gadi ya bud'e da sauri, aka shigo da motocin da akwatunan suke ciki, sauran aka bar su a waje saboda babu wajen da zasu shiga dukka.
Sauke akwatunan aka fara yi a harabar wajen, kafin su gama sauke su dukka guda talatin da shida, sai baskets din suma. Boxes din da Anty Faty tayi masa magana akai suka riko kowacce mace ta rik'e daya a hannu dama yan kanana ne, matan da Mama ta wakilta da idan sun zo su tare su ne suka karaso kowanne fuskar sa dauke da fara'ar suka tare su sannan suka yi musu jagoranci zuwa ciki, Mama na zaune an sha lullubi da kayan alfarma suka shigo, ta bisu da kallo ta kasan Ido, mata ne hamshakai wanda suka amsa sunan su mata, hutu da jin dadi ya kama jikin kowacce kai ba sai an fad'a maka ba. Rawar jiki jamaar Mama suka fara su a lallai an zo wajen su, dangin su Abba na gefe sun zama yan kallo, akwatunan aka dinga shigowa dasu Mama ta hadiye wani yawu me karfi, cikin al'ajabin uban kayan da ake ta shigo dasu, gaba daya ma sai ta bata lissafi suka dinga yi mata gizo, kamar ta tashi ta hau bubbudasu taji, wani farin ciki na ziyartar ta. Duk gaishe gaishen da ake tsakani bata wani fahimta saboda yadda ta tafi tunanin kalar hutu da gatan da Zeenat zata shiga, gashi alamu sun nuna dangin mijin nata masu karamci ne, basu da nuna kyama ko wulakanci ko kadan.

"Baki ne daga gidan sarki, mun kawo lefen dan mu, jikan Maimartaba sarki, sannan d'a ga sarkin Adamawa Alhaji Ahmad Santuraki,Ina mahaifiyar amaryar tamu take?"

Mama tayi firgigit sanda taji wata cikin matan na tambaya, murmushi ta yi tana sake kama kanta ita a dole akwai surkutar nan. Aunty Faty ce ta tashi tsam, ta isa gaban Maman ta mika mata akwatin hannun ta, dake dauke da hoton Moh da Iman da ita kanta Iman din idan ta gani zatayi mamakin yadda ya same shi, hoton yayi masifar kyau zaka rantse tare suka dauka, yana sanye cikin shigar babbar riga da rawani, yayi wani murmushi da zaka kalla ka sake kalla. Wani irin shock Mama taji lokacin da ta karbi akwatin a hannun ta hoton da yake jiki ya shiga cikin idon ta ya aikawa da kwakwalwarta sako a take.

"Wannan itace kyauta ta farko ga yar mu Fatima, akwai sauran kyaututukan da bazasu kirgu ba, amma dai ita wannan din ita ce zamu iya cewa ja gaba ga sauran."

Kamar mutum mutumi haka Mama ta dinga kallon matar da take mata wani yare da sam kwakwalwarta ta gaza dauka balle ta fassara mata abinda matar take cewa.

"Wadannan kayan kad'an ne daga cikin abubuwan da muka tanadawar Fatima, in sha Allah ba zata taba dana sanin amincewa da dan mu Muhammad ba.


" Dan sarki jikan sarki kuma sarkin gobe idan me dukka ya kaimu."

Wata mata tace daga gefe, duk suka amsa da in sha Allah.


Guda aka saka a wajen, gudar da Mama taji kamar an saka allura ne ana chacchaka mata a tsakiyar kanta, kokarin sakin box din hannun nata take, wata kanwar su Abba da take lura da ita tuntuni ta taso da sauri ta karbe tana ma yan uwan Maman kallon banza.

"Masha ALLAH, lallai mun ga Halin Girma da karamci na wannan babban gida, mun kuma tabbatar da yar mu ta shiga hannu na gari"

Ta fad'a bayan ta koma wajen zaman ta, ta kuma mikawa wata babba a dangin box din. Murmushi matan sukayi dukka, sannan aunty Faty tace

" Sai a bude kayan ko?"

Da karfin guiwar su dangin Abba suka tashi, aka fara bud'e box din farkon nan, kowa ya shiga mamaki, mukullaye ne wajen guda uku na mota, sai mukullin gida da takardun su, sai kuma wani babban set of gold masu girman gaske. Wata irin guda da tafi ta dazu aka sake saki, jira ya soma dibar Mama, ta kasa gane komai sai hajijiya da take ji kamar zata kayar da ita daga zaunen da take, me yake faruwa? Me yake shirin faruwa.
Daya bayan daya aka dinga bud'e kayan, tun mutane na irgawa har kowa ma ya gaji aka zuba ido ana kallon tarin dukiya, dukiya me sunan dukiya, dangin Abba da Mama ta dinga dagawa kai sai suka zama kamar sune kawai a wajen, farin ciki suke dama kowa yaji haushin abinda Maman tayi a dan tsakanin gabatowar bikin, sai kuma yadda ta dinga yada habaici a ranar da za'a kawo kayan wanda suka tabbatar dasu take shiyasa suka ji haushin ta sosai, amma yanzu da haka ta faru sai suka hau murna suka dinga yin abu da gayya dan su kara haukata Maman.
Tashi sukayi bayan an gama ganin kayan, aka damka duk wasu abubuwan da suke da muhimmanci sosai kamar golds da takardun gida da keys a hannun kannen su Abba sannan suka yi musu sallama, abubuwn da aka shirya da sunan Zeenat suka je suka dauko aka saka musu a mota, basu ma so karba ba amma yadda suka dinga insisting yasaka suka karba dan kar suga kamar sun raina musu ne.
Suna gama fita daga gidan masu kawo kayan Zeenat ta shigowa, mata ne kwantsam masu mugun yawa, masu goyo ne, gasu nan harda wanda suka ciko bus suka zo. Ana kokarin daga Mama a maida ta cikin daki sanarwar zuwan su ya katse su, a sanyaye suka dawo suka zauna, suka shigo bayan an matsar da kayan Iman an tura wasu dakin Abba da dakin Maman.
Da kallon bakin ciki Mama take bin su, kamar ta tashi ta hau bugun su haka taji, yaran da suka zo dasu suka dinga ihu na goyen sai da aka sakko su, na hannu kuwa suka hau wasa a falon. Gaisawa akayi suka gabatar da kansu, kafin ma su dire sunan Zeenat din Mama ta ja numfashi da take jin kamar zai fice daga jikin ta.

"Kuyi hakuri asthma ce da ita nema take Kuma ta tashi tun dazu, tashi Yaya mu shiga ciki ki huta."

Aunty Maimuna kanwar Maman tayi saurin rufawa ta janye Maman dan ta hango matsala babba, kamar ma kokawa take da numfashiin ta. Suna shiga dakin ta kurma ihu, ihun da kowa ya ji shi, da tayi sauri ta saka hannu ta rufe mata baki

"Haba Yaya Hajara, ai sai aji kunya, dan Allah kiyi hakuri."

"Kutmar uban hakuri, kike ce min nayi hakuri? Bayan kinga abinda ya faru? Kinga yadda Ibrahim ya munafurce ni da yan uwansa? Bayan duk halaccin da nayi musu ? Amma kike cewa nayi hakuri, ke kinsan me nake ji? Innalillah, wayyo Allah na."

" Ni dai kiyi hakuri, ko ma menene ki bari a gama taron nan, kinga mutane zasu tafi dake a baki."

" Taro? Ke kina ganin za'a cigaba da taron nan?"

" Toh me za'a yi Yaya?"

" Ba zai yiwu ba, wallahi sai dai a fasa auren, amma ba zan bari bakin ciki ya kashe ni ba a banza." Sai ta sake fashewa da kuka, kuka irin wiwi din nan da kana gani zaka tabbatar da ba karamin kuka mutum yake ba. Duk yadda Aunty Maimuna taso ta bata baki tayi hakuri ta kasa, sai kawai ta fito ta rufo mata kofar ta dawo wajen bakin, lokacin har an soma bud'e kayan, akwatu na guda hudu sai kit daya, da kayan ta masu kyau daidai da tsarin akwatunan, amma ganin da mutane sukayi wa kayan Iman ya saka zasu ga na Zeenat din kamar bola, a daddage kowa ya kalla, suka dauko dubu ashirin suka ce gashi nan ta kai dinki ba'a samu an dinka ba saboda kurewa lokaci. Daga haka sukayi musu sallama aka je dakin Mama a dauko ragowar kayan da suka rage ta ce idan an basu ko ruwa ba'a za'a basu ba, da k'yar Aunty Maimuna ta bata hakuri aka saka musu ruwa da lemo a bayan mota suka tafi.

Daya bayan daya yan uwan Abba suka zo suka kwashe kayan iman suka maida su bangaren Gaji a cewar su kar bakin ciki da kishi ya saka Mama ta saka wuta ta kona su.
Hauka hauka Maman ta soma da suka shigo, kowa yayi mata banza suka dinga dariya suna yada mata da magana, suka kwashe komai suka yi tafiyar su.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login