Showing 99001 words to 102000 words out of 115235 words

Chapter 34 - Halin Girma Hausa Novel Complete

da sau goma, har ya gano abu daya a cikin sakon, akwai kiyayye me zafin gaske tsakanin duk wanda ya turo sakon, duk wanda yake son ranka ba karamin kiyayye yake maka.
  Girgiza kai yayi ba tare da yayi magana ba,

"Idan ka gamsu da maganganun da mukayi, lallai muna da bukatar Kamal a binciken mu, domin idan har ka tattara bayanan baya da na yanzu zaka gane akwai wani abu da yake a boye a bayan dukkan cases din, case din ka da Laila, evidence din da ya wanke ka, sannan matar ka, zai iya yiwuwa wani ne da yake son ta tun ba yanzu ba, ko kuma wanda yake da matsala da kai ne amma shi da kansa yake son daukar fansa shiyasa har yayi kokarin wanke ka a baya, duk wannan tunani na ne, ban ce ya zama gaskiya ba, amma ina ji a raina, cases din suna da alaka da juna."

Zama ya kuma yayi a kujerar da ya tashi yana tattare bayanan dukka a kwakwalwar kansa, jiya baki daya ranar a cikin bincike yayi ta, babu mutum daya da binciken sa ya nuna masa sai Kamal. Evidence din farko shine sanda ya shiga bangaren sa, sai na biyu da suke zaune suna magana da wani mutum ya sunkuyar da kansa, wata mace a gefen sa itama babu fuskar ta, fuskar Kamal din ce kadai ta nuna wanda ya tabbata shi be sani ba, yana kyautata zaton gadar zare suka danawa Kamal din sukayi amfani da son mulkin sa suka samu abinda suke so sannan suka yi dumping din sa.

"Duk abinda ya kamata ayi, ayi Sir."

"Zamu fara da Kamal, ina fatan hakan ba zai zama matsala ga Maimartaba ba."

"In Sha Allah." Yace yana mikewa, jiri ne ya debe shi, yayi kamar zai fadi da sauri CP ya tashi yana riko shi

"Subhanallah, Capt akwai matsala ba, sai ka daure saboda tana matukar bukatar taimakon ka a wannan gabar."

Gid'a masa kai yayi yana rik'e kansa da yake mugun sarawa, be runtsa ba tunda ya diro garin Kano, ba kuma yajin idan ka cire ruwa ya sakawa cikin sa wani abu, sai da ya dawo daidai sannan ya mike yayi masa sallama, ya rakashi da ido yana yaba wa kwazon sa.

***Gidan su Iman din ya wuce kai tsaye, dan sunyi waya da Abba da safe yake ce masa bashi da lafiya, kamar ma bp din sa ne yayi sama, yasan batan Iman din ne ya saka shi shiga matsalar.
   A kofar gida ya tarar da Habib da saurayin nan na ranar nan, dauke kai yayi kamar be gansu ba, sai da Habib din ya taso yazo wajen sa yana kokarin kiran waya.

"Sannu da zuwa."

"Ah... Babban Yaya."

Ya mik'a masa hannu suka gaisa, sannan yayi masa jajen abinda ya faru, suna maganar Mahfuz ya karaso wajen, ya mik'a masa hannu kansa tsaye, kamar ba zai bashi hannun ba, sai kuma ya mik'a masa a dakile suka gaisa.

"Zanga Abba."

"Owk Bismillah."

Yayi gaba, shi kuma suka biyo bayan shi tare da Mahfuz har part din su, Abba na kwance a falo kan doguwar kujera, Mama ta shiga ciki dauko Hijab suka shigo, ya durkusa har k'asa ya gaida Abban, wanda yake kallon sa ciki da tausayawa, ya ga dauriyar sa sosai dan kana kallon sa zaka gane yadda ya tabu, ya rame sosai amma be karaya ba, be kuma zauna ba tun da ya dawo.

"Akwai labari ne muhammadu?"

"In sha Allah Abba, ana iyakar kokari."

"Toh basu kira ba har yanzu ko?"

"Basu kira ba Abba."

"Shikenan Allah ya dawo mana dasu cikin koshin lafiya."

"Amin Abba"

"Sannu da kokari, kai ma Allah ya biyaka, Allah ya tona asirin azzalumai, tun jiya ban runtsa ba, na rasa in da zan saka raina naji dadi, shikenan mutun bashi da daraja a k'asar nan tamu? Ace satar mutum tafi satar kaza sauki? Wannan wacce irin musiba ce... Allahumma ajirni fi musibati..."

"Allah ya bayyana su."

" Amin ya Allah. "

Suka hada baki gaba daya, shigowar Mama da Zeenat a bayan ta ne ya katse maganar da Moh yaso yayi, ya dan kalle su sai ya dauke kai ya maida wajen Abba da alamun sa ya nuna yana jin jiki. Gaisawa sukayi da Mama sama sama tayi masa jaje, sannan Zeenat da gaishe shi itama ya amsa yana mikewa.

"Bari na koma Abba, duk yadda ake ciki zan kira dan Allah ka kwantar da hankalin ka."

"Shikenan, Allah yasa muji alkhairi."

" Sai anjima." Ya dan kalli gefen da Mama take ya fad'a sannan ya fice Habib da Mahfuz suka bi bayan sa, sun kusan kai gate din gidan Mahfuz yace

" Zan iya taimakawa."

Tsayawa chak Moh yayi da tafiyar da yake ya juyo.

"Idan har zaka yarda zan iya taimakawa."

"How? Ta yaya?"

"Security ne from an intelligent agency a UK."

"Sounds good."

Moh yace yana dan rage hadewaar fuskar sa. Sai ya bud'e hannun sa alamun babu matsala yace

"Idan har zaka iya taimakawa, shikenan sai muje ko?"

"Let me freshen up, zan zo daga baya. Ina zan same ka?"

" Habib ka rakoshi gida na, don't take long please."

" In Sha Allah."

Juyawa yayi ya fice su kuma suka koma ciki don Mahfouz ya shirya, anan suka tarar da Gaji a part din ta saka Abba a gaba tana ta rusa kuka, bata samu labarin ba sai da Moh yazo yanzu sannan tasan abinda yake faruwa, taji zancen a radio har ta tausaya amma bata kawo Iman bace ,bata ma fuskanci zancen ba kwata kwata ma gaba daya. Baki Abba yake bata akan tayi hakuri amma taki, sai kuka take ita lallai sai an kaita gidan Iman din, a dole haka Abba ya saka tabi su Habib din ko ta barshi ya ji da kansa shima kawai dauriya ce irin ta namiji.
   Yana shiga gidan ya tarar da motocin masarauta, ciki ya shiga kansa tsaye, da mamaki yake kallon Fulani a zaune a falon nasu, tare da mummy da Mamma sai wasu matan, suna zaune jingum jingum cikin alhini da jimami, daga gefe hadiman Fulanin ne suma a falon, kallo daya yayi ma duk matan falon, ya karasa gaban Fulanin ya durkusa ya gaishe ta, ta amsa muryar ta na rawa alamun  bata dade da gama kuka ba, juyawa yayi ya gaida su mummy wanda sai a lokacin ya samu ganin su, ta fad'a tayi fayau amma kuma a nutse take sosai, sai yace ma Mamma ta fita fita hayyacin ta, wuce su yayi zuwa ciki, suka rakashi da kallon tausayawa.
   Dafe kansa yayi bayan ya zauna a gefen gadon, komai nata yana nan a dakin hatta da handouts din da ta fito dasu ranar da zata tafin gasu nan a saman gado, be san me yasa abubuwan suka juye masa a yadda be yi zato ko tsammani ba. Wayar sa ce tayi kara, ya dauka yana kallon sunan, Bubu ne

"Menene alakar Kamal da batan matar ka?"

"Barka da rana Bubu..."

"Barka dai, ya mukaji da alhinin? Allah ya bayyana su cikin koshin lafiya."

"Amin ya Allah."

"Ina jin ka, menene alakar Kamal da batan matar ka?"

Saman goshin sa ya shafa kad'an, kafin yace

"Bincike ne ya kawo hakan Bubu."

"Shikenan, Allah ya sa muji alkhairi."

"Amin ya Allah." Yace sannan sukayi sallama.
   A tsammanin sa Musaddik zai neme shi da zarar gari ya waye, ya kuma rakashi duk wani waje da zai je, amma kuma ga mamakin sa sai gashi har rana ta daga babu ko waya daga gareshi, bayan yafi kowa sanin muhimmancin da Iman take dashi a wajen sa, shine mutum na farko kuma na karshe da ya yarda dashi kaf duniyar nan idan ka cire mutane hudu mafiya kusanci dashi, Ammin sa, Takawa, Aji da Bubun sa, bayan su be yarda da kowa ba sai Musaddik wanda ya yarda da tsantsar kaunar da shi ma yake masa, fiye da wadda shi yake masa, say da yawa Musaddik ya sha shiga rigima saboda shi, ya kuma sha shiga tashin hankali saboda shi, amma kuma ya kasa gane dalili daya, da zai saka Musaddik din kasa jajanta masa kamar yadda ya saba a baya, duk wani abu masa tare sukeyi.
   Tashi yayi yana dan zazzagaya dakin, yana so ya dauke tunanin daga zuciyar sa,yana so yayi wa Musaddik din uzuri a karo na farko kasancewar dan Adam ajizi ne, watakila wani uzurin ne ya danne wannan din. Wayar sa ce tayi kara, ya matsa yana dubawa, sakon text message ne from an unknown number, da sauri ya dauki wayar yana dubawa.

_"Ka shirya?"_

Da sauri ya maida masa reply

"Waye kai, me kake so?"

Sai da aka dau lokaci sannan akayi reply da wata number daban

"Ashe har kana da lokacin tsayawa tambayar waye bayan rayuwar matar ka da ke cikin hatsari."

"Ina zamu hadu? Ka dawo da ita nayi maka alkawarin zan kawo maka kai na da kai na."

Nan ma sai da aka sake daukar lokaci kafin yayi masa reply da wata number daban kuma

_"Idan na shirya zan neme ka, karka bata lokaci wajen tracking din number, ba zaka taba samu ba." _

Kiran number yayi da sauri, amma sai yaji ta a kashe, ya bi sauran layukan da sukayi magana suma duk a kashe, text message ya turawa CP na numbers din dukka.
    Kira ne ya shigo wayar sa daga gate din gidan, kamar be zai daga ba sai kuma ya tuno da zuwan su Habib, dagawa yayi suka tambaye shi ko yasan su, yace a farsu su shigo brothers din Iman ne, da haka ya kashe ya sauya rigar sa zuwa mara nauyi saboda zafin da yake ji.

***Dagata Ummimi tayi ta taimaka mata bayan ta gama amai, ta gyara wajen ta dawo ta tsugunna a gabanta tana mata sannu, da kai ta amsa mata, ta rufe idon ta hawaye ya gangaro mata. Shigowa sukayi su hudu, shine a gaba suna bin bayan sa, ya zo gabanta ya durkusa ya saka hannu ya dago kanta.

"Fine Lady." Ya shafi gefen fuskar ta, ta saka ragowar karfin da take dashi ta ture shi, ya tuntsure da dariya yana kallon ta

"Ga Dr nan zai duba min ke, dan ina tunanin nine zan maye gurbin Capt bayan na aikashi barzahu, kina da kyau."

"Dr matso, a duba min da kyau idan har ciki ne, a cire shi ko ta yaya ne, ba zan iya jure ganin sa ba, kaga auren mu ba zai dau lokaci ba idan aka cire shi."

Matsawo likitan yayi, ya bud'e idon ta, sannan ya taba goshin ta, ya dauko wata roba a cikin kayan sa ya mikawa Ummimi.

" Gashi fitsari zatayi."

Kin karba tayi, na bayan ya daka mata tsawa, ta karba da sauri tana daga Iman din, dukkan su hawaye suke amma babu me bud'e baki yayi musu saboda tsoro. Tare sukaje tayi fitsarin suka fito ta dawo ta kawo masa, ya karba a wajen ya duba, ya kuma tabbatar da ciki ne, yan tambayoyi yayi mata akan period dinta ta amsa tana kuka.

"Ciki ne oga, na sati shida."

"Ya za'a yi dashi?"

"Ba zai wahalar fita ba, tunda karami ne. Yanzu dai zan dawo sai nazo da maganin da zata sha."

"Yayi kyau, rakashi yaro." Rik'e masa jaka wanda aka kira da yaro yayi suka fita, sannan shi ma suka fita.

"Hello... Samha baby." Ya fad'a da yaji ta daga wayar

"Eh tana hannu har yanzu."

"Eh ya tabbatar da ciki ne, amma za'a cire shi tunda baki da bukatar shi."

"A ah... Babu fa abinda zan yi wa masoyinki, kawai wata yar harkalla ce zamu karasa ta. "

" Yawwa toh" tace tana jin dadi.

" Sai mun sake magana ko? "

" Amma ai bana samun ka kwata-kwata a waya, me yasa?"

" Babu komai, idan akwai bukatar muyi magana ni zan kiraki da kai na."

" Shikenan."

Dariya yayi sosai bayan sun gama maganar, be san bata da tunani ba kwata-kwata sai yanzu, amfani yayi da ita ya samu abinda yake so, ba kuma zai kyale wanda ta kwallafa rai akai ba, ba zata taba samun cikar burin ta ba in dai yana numfashi.

***A waje ya tarar da su Habib din bayan ya gama parker motar, ganin tare suke da Gaji ya sakashi saurin karasawa ya taimaka mata ta fito, sannan suka gaisa ya saka aka rakata ciki su kuma yace su biyo shi garden dake baya. Kujeru ne a wajen, ya zauna sannan suka zauna suma, yana karantar yanayin Mahfuz din, sai a lokacin yayi masa kallon tsaf, ya kuma fahimci hakan yanayin sa ne, ku kuma yanayin environment din da ya taso kamar yadda Habib yayi masa bayani dazu.

"Ta yaya zaka iya taimakawa?" Yace bayan ya gama nakaltar yanayin sa, gyara zama yayi sosai, yayi murmushi sannan yace zai masa yan tambayoyi,da ka ya amsa masa ya bashi go ahead.

"Babu wani message ko kira da ka samu daga wajen kidnappers din?"

"Akwai."

"Zan iya gani?"

"Why not?" Ya mik'a masa wayar, ya karba ya duba messages din dukka, ya jima yana sake dubawa kafin ya mik'a masa wayar sa

"Kayi tunani sosai, wanene kake da matsala dashi, irin wadda kasan lallai da zai samu dama akan ka zai iya aikata maka komai?"

"Babu shi, bansan waye ba gaskiya."

" Babu ko old friend? Ko abokin aiki?"

Shiru yayi cikin tunani

" Think... "

_" Zan dawo komai daren dadewa, sai na dauki fansa akan ka, ko da zan karar da komai da na mallaka ma duniya sai na maida rayuwar ka abun kwatance! "_

"JABIR! " Yace yana mikewa tsaye da sauri, tashi Mahfuz yayi shima yana kallon sa

" Waye shi. "

" Aboki na ne, abokin aiki na ne. "

" Recently na samu labarin ya zama babban terrorist kuma yana da connection da manyan k'asar, bayan shi bana tunanin akwai wanda zai bukaci rayuwa ta, babu. "

"Ya akayi na manta? Ya akayi? "

" Kasan in da za'a same shi? "

Girgiza kai yayi,

" Ban sani ba. "

Komawa sukayi suka zauna, Mahfuz ya ciro biro da paper ya rubuta wani abu, daidai lokacin da Moh ya daga wayar Musaddik yace ya same shi a garden, yana ajiye wayar sai gashi ya zagayo dama chan yana cikin gidan, da kallo Mahfuz ya bishi kafin ya karaso wajen yace

"Waye shi?"

"Best friend dina ne."

"Ok." Yace a gajarce ganin ya karaso, ya mik'a musu hannu suka gaisa amma da ya bawa Mahfuz hanun sai ya rik'e hannun nasa har sai da suka kalle shi dukka, sai ya saki yana murmushi ya jingina da kujerar da yake kai, wani kallo Musaddik yayi masa ya zauna yana maida hankalin sa kan Moh.

"I'm very sorry Capt..."

"Babu komai, nasan wani uzuri ne dakai." Ya katse shi kafin ya karasa.

"Babu wani progress ko?" Yace

"Babu."

"Allah ya bayyana su."

"Amin."

"Ya aiki?" Mahfuz ya tambayi Musaddik unexpectedly

"Aiki Alhamdulillah."

"Wanne aiki kake?"

"Harkar kwangila, kaifa?"

"Detective!"

Wani kallo Musaddik yayi masa, yayi shiru,.sai kuma ya kalli Moh

"Naga kamar kana da baki, dama inaso muyi maganar flash din nan ne tunda naga ka dawo."

"Flash?" Mahfuz yayi karaf ya tambaya

"Let's talk about that later." Moh yace sai ya mik'a wa Musaddik hannu

"Suna ina?"

Sosa kansa yayi

"Dalilin da yasa kaga kamar ina janye kaina a case din nan kenan, wallahi bansan ya akayi ba, na rasa su gaba daya."

"What!"

"Kayi hakuri,ranar da aka sace wayata aka hada dasu gaba daya, bansan ya zan maka bayani ba, nasan kuma muhimmancin flash din a wajen ka, shiyasa na kasa nutsuwa."

Murmushi kawai Mahfuz yayi, ya dire pen din hannun sa akan dan deborin da yake gaban sa, ya dora hannun sa akai ya jingina yana masa kallon tsaf.

" Idan nace wani abu zaka yarda dani?"

Girgiza masa kai Moh yayi dan maganar batan flash din ba karamin bashi mam I'llaki tayi ba.

"Ina bukatar yara hudu cikin yaranka na gate."

" Me zasuyi maka?" Musaddik yace ransa a bace.

" Wait and see." Yayi murmushi, shi Moh ba gane kan maganar ba kwata kwata, yayi dai abinda Mahfuz yace ya kirawo su suka zo, suka tsaya daga gefe, tashi Mahfuz yayi ya zagayo ta bayan Musaddik,

"Take off your mask!"

"Kamar ya?"

"Me kake nufi Mahfuz?" Moh da shima ya mike ya fad'a cike da mamaki

" This man is deceiving you, ka kalli hannun sa, ka kalli fuskar sa, akwai banbancin skin color, he's definitely using a mask, idan har ya musa, zan tabbatar maka."

"Noo...you are mistaken, wannan Musaddik ne, trusted friend dina ba zai taba deceiving dina ba,you cannot accused somebody without a proof."

" Shine zan maka proving yanzu ai, wait and see, guys... Ku rik'e shi."

" Dakata!"

Moh yace ransa na baci, ba zai dauki wulakanta Musaddik yana kallo ba.

"Waye wannan Capt, waye zai zo ya shiga tsakani na da kai?"

"Calm down aboki na, misunderstanding aka samu amma zan masa magana..." Sai ya juya wajen Mahfuz din

"Let's call it a day, zamuyi magana gobe, Habib ku jirani a wajen mota."

"Muje Mahfuz." Wani kallo yabi Musaddik din dashi, sannan ya juya suka bar wajen da Habib.

Juyawa kan Musaddik yayi da ransa yayi masifar baci, ya shiga bashi hakuri akan abinda Mahfuz din yayi, yace ya jirashi yana zuwa bari ya sallame su. Yana barin wajen ya ciro waya, ya kira shi yana matsawa chan gaba.

"Akwai matsala." Yana dagawa yace

"Ya fara suspecting dinka ne?"

"Be fara ba, wani banzan yaro ne bansan daga ina yazo ba, yaso dole sai ya nuna masa gaskiyar mask da na saka..."

"Ya yadda?"

"Be yarda ba, kasan ya yarda dani sosai, so ba zai taba kawowa ba. "

" You have to be very careful, shi kuma yaron zan san yadda zan yi dashi. "

" Ok sir. " Ya kashe wayar yana juyowa, sukayi ido biyu da Moh da yake tsaye a bayan sa kamar mayunwacin zakin da ya shekara be ce ba.




***Assalamu alaikum sisters, masu korafi naga wasu daga cikin korafin ku, ina mai baku hakuri akan matsalolin da aka samu, dan gane da rashin posting halin girma shekaran jiya da jiya, hakan ya faru ne sakamakon ciwon hakorin da ya matsa min hade da zazzabi, wanda har ta kai ban iya samun duba sakonni ba balle har na iya zaman rubutu

Duk cikin zafafa biyar babu wadda a cikin mu take jin dadi a duk sanda batayi posting ba, Allah ne shaida ana iyakar kokari wajen ganin Anyi abinda ya dace. Sai dai idan abu ya sha kan mutum a ba yadda ya iya. Allah ya huci zuciyar duk wanda ransa ya baci ta dalilin jira ko wani abu, ba da gangan bane wani lokacin kuma ajizanci ne na dan Adam.

Allah ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login