Showing 9001 words to 12000 words out of 115235 words
A dawowa ma haka ta sake yi shima bata ga kowa ba, ta dawo gida ta chanja kayan ta kenan aka shigo aka ce tazo inji Muhammad, Hijab ta dora a saman kayan jikinta ta fito. A tsaye yau ma ta hange shi wajen kujerar, ya rataye hannayen sa a bayan sa yana tsaye kyam akan kafafun sa.
"Assalamu alaikum." Tayi masa sallama tana jan kujerar.
"Sannu da zuwa, nan akwai rana bari na saka maka a chan." Taja kujerar zuwa k'asan wata yar bishiya ta ajiye,
" Bismillah." Tace masa tana nuna masa kujerar, be zauna ba, ya zaro hannun sa daga bayan sa, ya dawo dasu gaba ya rungume su a kirjin sa,
" Bismillah." Ya nuna mata kujerar da baki
" Zauna babu matsala." Yace mata
" A ah dan Allah ka zauna, be kamata na zauna kana tsaye ba, ance bakon ka..."
" Kyale fadar hausawan nan, zauna dan Allah."
Allah da taji ya ambata yasa ta zauna a kunyace, ya zura mata ido har sai da ta dan ji wani iri.
" Na cika kallo ko? Kiyi hakuri." Yace mata yana murmushi,kallon ta kadai yayi jin sa yake kamar yafi kowa sa'a a duniya
" Ba komai." Tace tana gyara wayar hannun ta
" Ina wuni?" Ta gaishe shi yana dan zamowa
" Lafiya lou, sai kika jini shiru, tafiya nayi zuwa kauye Baba ya kira ni, naso ma na zo kafin na wuce toh tafiyar ce tazo a gaggauce, sauka ta kenan ma."
" Allah sarki... Allah yasa lafiya."
" Lafiya lou, sai godiya. "
" Ka baro su lafiya?"
" Alhamdulillah. Nagode da kulawa."
" Ba komai." Tace tana wasa da hannun ta.
Turo gate din akayi, Habeeb na gaba yana bin sa a baya, wani irin daukewa yaji ganin sa na neman yi. Iman zaune tare da wani suna hira, a cikin gidan kuma? Be san sanda ya isa wajen ba, sai ganin mutum sukayi a gaban su.
Wani kallo Moh yayi masa, yayi murmushi yana taune gefen lips dinsa na kasa
"Yaya sannu da zuwa." Yace yana mika masa hannu, kin bashi hannu Khalil yayi, sai Habeeb ne suka gaisa, ya daki kafadar Khalil din
" Muje ko?"
" Yi gaba ina zuwa." Yace masa,
"Ok." Ya wuce ya bar Khalil din a tsaye
" Iman shiga gida." Yace a gadarance, ta dago ta kalle shi da sauri, ya hade girar sama data k'asa tamau irin ba wasa din nan.
"My heart, ki shiga gida ki huta dama naji ba zan iya zuwa gida ban zo na ganki ba, shiyasa na taho nan kai tsaye, zan kira ki anjima ki ajiye waya a kusa dake kinji?"
Kunya ce ta kamata ta noke, ta mike da k'yar tace
"Ka gaida gida." Sannan ta wuce ciki, tana barin wajen ya hade fuskar sa sosai.
" Da tsakar ranar nan ka taso yarinya, kazo zaka ishe ta da uban surutu, ku dama talakawa haka kuke, da kunga yar hanya sai kuzo kuce kuna so, kai kanka kasan ba sa'ar ka bace, ba sa'ar auren ka bace shishigi dai, toh ita din matata ce, ni zan aureta an gama magana, sai kaja tsumman kafafunka a koma in da aka fito, ka samu daidai da kai."
" Zaka ga tasirin talaka da talauci kuwa, baka da ikon tsarawa kowa rayuwa, haka arziki ba wani abu bane face fitina, wadatar zuciya itace mutum..." Ya dan matso gaban sa
" Mark my word, a gaban idon ka, right under your noses, talaka zai baka mamaki, mamakiin da har ka kare rayuwar ka zaka fita daga cikin sa ba, count down dinka ya fara daga yanzu."
" 1,2,3!" Sai na jika.
Ya juya ya fice daga gidan cikin takun da ya tsayawa Khalil a rai, cikin wani irin yanayi yayi cikin gidan yana jin yanzu ba sai anjima ba, zai yi abinda ya dace, gida be koshi ba, babu yadda za'a yi a bawa dawa.
**A tsaye ya tarar da Habib yana ganin shi yace
"Kaiko me ka tsaya yi ina ta jiran ka."
"Abinda ka kasa yi, kana ganin kanwar ka da mutum a tsaye, kana ganin sa kaga mara gaskiya, wa ya sani ma ko dan boko haram ne da wannan uban kasumbar, amma baka damu ba kayi tafiyar ka, hakan ba daidai bane."
Kallon sa Habib yayi, mamaki na kamashi,
" Yaushe hakan ya zama ba daidai ba khalil?"
" Habib, maganar gaskiya ina son Iman, son da ni kaina bansan adadin sa ba, zan iya komai akan na sameta, dan haka ba zan iya jure ganin ta da kowa ba, musamman mutum irin wannan da ya nuna alamun rashin gaskiya, gashi fakiri jibi shigar jikin sa, no ba zan iya ba, rakani wajen Gaji ayita ta kare."
" Idan har kai din jinina ne, idan har na isa da kai babu kai babu Iman Khalil, na rasa kafiya irin taka, na rasa dagiya irin taka, bayan maganar nan mun dade da gama ta, na gaya maka ba zai taba yiwuwa ba."
" Akan me? Dan Allah Anty ki gaya min hujja me karfi a musulunci da ya haramta min auren ta, na daya ni ba muharraminta bane tunda ita din ba ke kika haife ta ba, toh sai menene? Akan dalili mara tushe?"
" Akan duk abinda zaka kira shi Khalil ka kirashi, amma idan har ina numfashi ba zamu hada jini ba wallahi, ga mata nan bila adadin, me yasa sai ita, wannan da yazo shi ya dace da ita, shine daidai da matsayin ta, inaso auren da zatayi ya zama sakayyar aure min miji da uwarta tayi, ta saka yayana samun yan Uba!."
" Ohh shit! Kin kasa fuskanta ta Anty, kiyi hakuri wannan karon zabin raina zan bi, zanje na samu Gaji na sanar da ita, gwara kowa ya sani a san me yakamata ayi."
" Khalil!"
Ta k'wala masa kira, ya juya da sauri yayi hanyar fita, wayar sa tayi kara, ya tsaya chak jin layin da yake ajiye numbers din manyan mutanen sa ne, ciro wayar yayi sunan Sir ya bayyana a wayar, ya daga da sauri yana daidaita numfashin sa
" Kana ji Ibrahim? Sako ne daga sama ba daga ni bane, an dakatar da kai aiki zuwa wani lokaci, za'a neme ka idan bukatar hakan ta taso." Be jira yace komai ba , ya katse kiran. Da sauri ya dafe bangon da yake kusa dan ji yayi jiri na neman kadashi, gaba daya rayuwar sa akan aikin ta dogara, yana da passion sosai a Kai sannan yana iyakar kokarin sa wajen aikin sa, maganar promotion dinsa ma ake idan har ya kammala wannan assignment din da ya kawo shi Kano, shikenan sai dakatarwa haka nan ba wani dalili?
" Ya akayi?! Habib ya matso ya taba shi ganin kamar ya shiga coma
🔥🔥🔥🔥🔥
*_LAST BONANZA_*
*_farincinku shine namu,ZAFAFAN DAI,sun sake amsa kokenku,sun sake rage muku kaso 20 cikin 100_*
*_Daga yau 29 ga wata,har zuwa 31 ga watan nan,xaku iya biyan 800 a amadadin 1000 na kudin litattafai biyar_*
*_za'a fara posting in sha Allah 1st January da yardar Allah_*
*HANZARTA KI BIYA NAKI KAFIN RANAKUN SU QARE*
*XAKI BIYA TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
SAIKU TURA SHAIDAR BIYA
08184017082
GA MASU TURA KATIN WAYA KO KUMA VTU,SAIKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYANKU
09134848107
1/2/22, 22:47 - Buhainat: *HALIN GIRMA*
6
*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*
_ASSALAMU ALAIKUM BEAUTIFUL PEOPLE!! ZAFAFA BIYAR FAMILY💯💯🙌🏽❤️_
_MUNGODE DA ZABIN LITTAFAN ZAFAFA BIYAR. ALLAH YA KARA BUDI YA KUMA BAR ZUMUNCI_
_KAMAR KO DA YAUSHE, WANNAN KARON MA MUNZO DA KOKON BARAR YOUTUBE CHANNEL DIN YARON MU, SUDEIS MASOYI KUMA MAKARANCI, MAHADDACIN ALKUR’ANI MA GIRMA_
_WANNAN KARON MA DAN ALLAH A TEMAKA ADANNA WA CHANNEL DINSA KARARRWA DOMIN KASANCEWA DA MU A DUK SANDA MUKA DORA FEFAN BIDIYON SA, A TALLAFA A KALLA A KUMA DANNA MASA SUBSCRIPTION. HAKAN NA KARAWA SUDEIS KWARIN GWIWAR SAKE DAGEWA YA KUMA KARA KAIMI WAJEN YIN KARATUN SOSAI. MUNGODE KWARAI💯🙌🏽❤️_
_GA CHANNEL DIN DAKE YOUTUBE NAN👇🏾_
https://youtube.com/c/sudaiskura
_Sudais is a young boy who has passion in recitation of the Holy Qur'an at a very young age._
_Please help him grow his YouTube channel by subscribing and liking his videos to encourage the little boy. Jazakumullahu khairan🙏🏻_
***
Girgiza kai ya hau yi da sauri da sauri.
"Habib aiki na, innalillah wa inna ilaihi rajiun."
"Me ya samu aikin naka?" Mama ta matso da sauri tana rik'e shi
"Wai sun dakatar dani, babu wani kwakkwaran bayani kawai wai daga sama ne."
"Innalillah wa inna ilaihi rajiun, zo ka zauna, rik'e shi Habib ya zauna."
Zaunar dashi Habib yayi, yayi saurin dauko masa ruwa ya mik'a masa
"Sha ko zaka ji sauki a zuciyar ka, ba wani abu bane babba in sha Allah, wata yar matsala ce zasu gyara da yardar Allah."
Jujjuya kansa yake ya kasa magana, shi kadai yasan hakan me yake nufi, shi kadai yasan yadda yake ji a halin yanzu, tabbas idan suka hana mishi aikin nan sun yi masifar cutar sa, akan me? Me yayi haka da ya chanchanci wannan hukuncin? Bayan irin kokarin da yake ganin ya rik'e aikin sa, tsawon lokacin da ya dauka kafin ya samu aikin, da irin wahalar da yasha kafin ya kawo matsayin da yake, sai yanzu? Daga sama ta ka kawai ace an dakatar dashi? Innalillah wa inna ilaihi rajiun. Ya sake maimaitawa.
"Kalle ni nan Khalil, karka ce zaka daga hankalin ka akan abinda kasan baka da iko dashi, kayi hakuri ka kwantar da hankalin ka, in sha Allah ba wata matsala bace, kaji?"
Gid'a mata kai yayi kamar karamin yaro, ya kwantar da kansa yana jin kamar ya zubar da hawaye saboda bacin rai. Shiru sukayi kowa yana jimamin abinda ya faru, ya ma manta da abinda yake shirin aikatawa. Shigowa Zeenat tayi dauke da wasu manyan ledoji,uwar ta bita da kallo bata ce komai ba.
"Daga ina kike?" Habib yace yana bin hannun ta da kallo
"Bashir ne yazo."
Kallon Mama yayi, yaga ta dauke kanta
"Mama fa Bashir din nan naji wasu maganganu akan sa marasa dadi, ya kamata a duba sosai kafin a barta tana fita wajen sa."
"Bana son maganar nan yanzu, dame zamu ji? Da abinda ya faru da Khalil din ko da naka zancen?"
Tsuke bakin sa yayi be sake cewa komai ba, ya tashi ya bar falon ma,
"Me ya samu Uncle Khaly din Mama?"
"Babu komai, ki wuce ki bani waje uwar yan magana."
Da sauri tayi gaba da ledojin ta, ta shige dakin uwar ta rakata da kallo kafin ta sauke ajiyar zuciya tana tuna abinda ya faru daren jiya ita da Abban su.
***
"Ya ake ciki da yaran nan?"
"Name fa?"
"Akan maganar yaran da suke zuwa wajen su, Yaya yayi min magana akai yace ya kamata asan abinda ake ciki, kindai san tsarin gidan nan ba'a wani daukar dogon lokaci ana zance."
"Eh toh, ita Iman akwai wani wanda yazo."
"Zuwan sa biyu kamar ko?"
"Ashe ka sani?"
"Eh ina sane da komai ai, kinga alamun zasu dai-dai ta ne? Naga zuwan nasa biyu dududu."
"Toh idan bashi ba waye? Babu kowa ai."
"Khalil din fa?" Yace yana mata kallon mamaki
"Wai Dr bar maganar Khalil din nan, ba da gaske yake ba wallahi."
"Ana wasa a maganar aure ne Hajara?"
"Shi dai yayi, gwara a tsayar da magana akan wanda yazo din dan da alama ba da wasa yazo ba."
"Toh shikenan, Zeenatu fa?"
"Eh ita ai Bashir ne dama."
Tashi yayi tsaye yana girgiza kansa
"Ban yarda ba sam, ban amince da yaron ba, binciken da nayi akansa be min dadi ba, kamar ance min ma kuma yana da mata duk da hakan ba zai hana a bashi aure ba, sai dai na samu labarin bashi da hali me kyau gaskiya, a wani labarin ma ance min har zaman prison yayi, sai ki fad'a mata nace banda Bashir ta kawo wani."
Hankalin ta a tashe tace
" Amma baka ganin sharri akayi masa? Don a hana a bashi?"
" Akan me za'a masa sharri? Akan wanne dalili kenan?"
Ya tsare ta da idanun sa, sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, tsoron yadda za'a kwashe da Zeenat din take domin ta san yadda ta saka Bashir din a ranta, gashi babu laifi yana mata hidima sosai, hakan ya saka Maman sake yarda dashi da yar ta ta.
"Bari na shiga ciki Anty." Khalil yace yana mikewa, ta daga masa kai kawai ya wuce ya barta tana cigaba da tunanin yadda zata bullowa al'amuran.
***Tana zaune a falon Gajin tana tunanin abinda ya faru tsakanin shi da Uncle Khalil, wayarta dake saman cinyarta tayi kara, ta kalli wayar ganin bakuwar number ya saka ta tashi, ta wuce zuwa bedroom din Gajin ta daga tana zama a gefen gadon ta
"Assalamu alaikum." Tayi sallama cikin muryarta da tafi komai tafiya dashi, lumshe idon sa yayi ya bud'e a hankali ya amsa sallamar ta ta
"Wa alaikisalam..."
"Ina wuni?" Ta gaishe shi jin muryar sa
"Lafiya lou Mi Love, na barki lafiya?"
"Alhamdulillah." Tace a kunyace ganin shi kai tsaye yake maganar sa.
" Kina jina Zahraaah na? "
" Na'am?" Tace tana mike kafafunta
" A zahirin gaskiya ba da wasa nazo ba, da gaske nazo neman auren ki ba kuma naso a dauki wani dogon lokaci in sha Allah, ni din dai ba wani bane kin dai ganni, bawan Allah ne me neman amincewar Fatima Zahra, ina fatan zaki bani dama dan Allah!"
" Hmm..." Ta sauke ajiyar zuciya maganganun sa na taba ta, me zata ce toh? Da gaske take jin ya kwanta mata duk da taga alamun ba wani shi nne dashi ba, amma sai taji yadda yake abu kai tsaye ya birgeta sosai, babu karya straight kawai yake maganar sa, bayan haka da gaske take son matsawa daga wajen Mama, ko ba komai ta samu yanci itama.
"Baki ce komai ba?"
"Allah ya shige mana gaba, Allah ya zaba mana abinda zai zamar mana alkhairi gaba daya."
Wani irin dadi yaji ya shige shi, ya rufe idon sa, ya dau yan sakanni yana jin sonta na sake ruruwa a zuciyar ta, yana tuna tsawon lokacin da ya dauka yana dakon soyayyar ta, a lokacin da shi kansa be san me ake nufi da so din ba.
Mahaifiyar sa 'ya ce ga sarkin Kano kuma shi jika ne a gidan, hakan ya saka yake da alaka me karfi da garin na Kano duk da mahaifin sa da mahaifar sa Adamawa-Yola ne, rayuwar sa bayan ya tasa yayi ta ne tsakanin Kano da Adamawa, shiyasa babu in da be sanin a Kanon ba, yake kuma jin kamar yafi zama comfortably a Kanon, musamman da bashi da son hayaniya sosai sai nan din yafi zamar masa peaceful wajen hutawar sa.
Akwai ranar da ya fito shi da abokin sa Musaddik, suna tafe a mota hanya ta biyo dasu ta area din su Fatima, a lokacin ya ganta duk da lokacin ba ta kai yanzu ba, be kuma taba jin abinda yaji akanta, shiyasa ya nace a lokacin suka yi ta bin ta har suka ga gidansu, suka kuma yi tambaya akan ta da komai. A lokacin yaso ya shigo da karfin sa, sai dai wani labari da ya samu ya sauya masa tunani da shawara, ya kuma yanke ma kansa shawarar da yake ganin itace zata daga masa darajar ta, a ranar da gaskiya ta bayyana.
Musaddik be aminta da shawarar ba duba da gidajen da Muhammad din ya fito, amma haka ya kafe akan bakansa, shiyasa ma kawai Musaddik din ya kyale shi amma fa kullum cikin masa korafi yake.
Bangaren aikin sa zai iya cewa yana cikin yan gata da sai abinda suka zaba da inda suka zaba zasu zauna, kasancewar gaba daya k'asar babu in da kakan shi mahaifin Ammi zai nemi alfarma ba'a masa ba, sannan gefe guda mahaifin sa yayi sunan da zaka yi mamaki sosai.
Duk da hakan be daina aikin sa ba, sai dai babu wani matsi ko takura tun ma be kai matakin captain ba, balle yanzu da yake da rank me girma.
"Kinsan me?"
Yace yana gyara kwanciyar sa sosai, sanda Musaddik ya murda handle din dakin ya shigo bayan yayi knocking ya bashi izinin shigowa.
"Ya Iman Abba na kira." Marwan ya fad'a mata yana tsaye a gefen ta, hannun sa ta riko shi kuma yace
"Yaya Iman ki gaida min da Abba, idan kin dawo ki kira ni please, zan fad'a miki wani abu." Murmushi tayi me sauti yana jiyo ta
"Ok bye." Ta ajiye wayar ta rik'e hannun Marwan din suka fito a tare..
"Yaushe Abban ya dawo?"
"Be dade ba, yana falo yana cin abinci."
"Owk." Tace suna karasawa.
" Abba barka da gida."
" Barka da Uwata, na dawo ban ganki ba, da zan fita ma ban ganki ba, shiyasa nace ya kira min ke."
" Ina wajen Gaji Abba."
" Eh haka maman ku tace, amma ai na ganki dai ko?"
K'asa tayi da kanta Mama ta karbe
" Tafi son zaman chan yanzu ai."
" Kuna shan hira da Gaji kenan ko?" Yace yana murmushi
" Ko kuma tafi jin dadin tayi wayarta a chan ba, ko 'yata?"
Maman tace cikin son a sako zancen Moh, shiru kawai Iman tayi Abba ma ya girgiza kansa kawai
"Allah ya kyauta, kinci abinci dai ko? Nasan ki da wasa da cikin ki."
" Naci Abba."
" Toh karbi nawa ki kara, nasan ba da wani yawa kika ci ba." Ya tura mata plate din gabanta
"Maza kirawo min zeenatu Marwan."
Gaban Mama ne ya fadi, ta zamo daga kujerar tana sakin salati a ranta. Tana gyara daurin dankwalin kanta ta shigo falon, ta zauna a kusa da Iman ta gaida Abban.
"Abinda yasa na kiraku ke da yar uwarki, akan maganar yaran da suke zuwa wajen ku ne, duk da shi wanda yake zuwa wajen Uwata bansan shi ba, inaso ki sanar dashi yazo yaga Yaya kafin ya cigaba da zuwa."
Abincin da ta diba ta hadiye da k'yar gabanta na dukan uku uku.
"Ke kuma..." Ya nuna Zeenat
"Ki kawo wani daban ba yaron nan Bashir ba, ki sake dubawa a cikin sauran ki nemo wanda ya dace da nasabar gidan nan, me Halin Girma mutumin kirki, kinji na fad'a miki."
Waro ido tayi cikin tashin hankali ta kalli Abban
" Hakan shine abunda ya kamata muyi a matsayin mu na iyaye, dan haka kiyi hakuri."
Tashi yayi, ya kalli Iman da tayi tsam a wajen, ya juya ya kalli Mama yayi mata alama da ido sannan yace
" Na fita!"
Da k'yar Mama ta bud'e baki tace
" Adawo lafiya."
" Allah ya kiyaye Abba." Iman tace yana kokarin fita
" Amin." Ya amsa kafin ya fice gaba daya.
Wani kallo