Showing 105001 words to 108000 words out of 115235 words
Chapter 36 - Halin Girma Hausa Novel Complete
take."
Kafin ma ya karasa tuni Moh ya firgice, yasan an ce akwai mutum uku bayan iman da Ummimi, daya an harbe shi ma aamma sam be kawo tunanin komai ba, be ma kara tunawa ba saboda damuwar da ta danne shi, yana so dai yaje ya tabbatar da Musaddik na cikin wadanda aka samo din amma sai yake ganin kamar idan ya matsa daga wajen ta komai zai iya faruwa.
"Yana ina?"
"Yana chan emergency unit har yanzu bamu ji komai daga garesu ba, su Abba dai suna chan?"
"Innalillah wa inna ilaihi rajiun, muje."
Sauri sauri ya dinga yi kamar zai tashi sama, idan wani abu ya samu yaron fa? Ya zai da ransa wai? Ba'a barin kowa ya shiga wajen nasa saboda yadda case din nasa ya zama very complicated case, bayan sun yi nasarar cire bullets din amma sam jinin ya ki tsayawa, ana kara wani, wani yana fita, su kansu abin ya basu tsoro ganin yadda yake zubar da jini, shiyasa suka hana kowa shiga, su Abba da suka dawo wajen tun da suka samu labari jikin kowa ya gama sarewa da al'amarin Mahfuz din.
Moh na isa wajen dr na fitowa daga ciki, jikin sa babu kuzari ya nufo wajen da su Abban suke, ya kalle su daya bayan daya kafin yace
" Sai dai muyi hakuri... "
Wani irin zubewa Moh yayi a wajen, kirjin sa na masa wani irin suya, ashe Ajali ne ya kawo shi k'asar? Ashe dama shine sanadin mutuwar sa, me yasa yayi masa wannna tsawar, me yasa ya ci masa mutunci bayan be san wani abu dangane dashi ba,
"Nooo Dr... No be mutu ba, Dan Allah karka ce min ya mutu dagaske, ban kyauta masa ba, be kamata ya mutu ba, he's innocent be kamata yayi facing irin wannan mutuwar ba, me yayi? Menene nasa a ciki?"
"Get hold of yourself Capt, kullu nafsin za'ikatul ma'ut, hakikaa kowacce rai sai ta dandani zafin mutuwa, shi da ya tafi be yi sauri ba, mu kuma bamuyi jinkiri ba, addu'a kawai yake bukata."
Dr yace ya juya ya barsu a wajen, babu wanda ya iya motsi a wajen saboda tsabar kaduwa, yaro me zumunci me shiga rai, me son yan uwan sa, ya Yaya zataji? Labarin mutuwa irin wannan mara dadi, kullum korafin ta akan Nigeria shine rashin tsaro, ko waya sukayi ta kan ce musu Nigeria ta zama abinda ta zama, rai ba abakin komai yake ba. Kullum maganar ta kenan, tsoron ta kenan, ashe bata tsira ba, Ashe zaman ta a chan bashi ne zai sauya kaddara ba? Innalillah wa inna ilaihi rajiun kowa yake maimaitawa babu hargitsi ko hargowa, saboda dauriya irin ta maza, sai dai kana kallon su zaka san mutuwar ta dake su, musamman Habib da Moh, kafin kace kwabo labarin ya zagaye ko ina, kowa sai da ya tausaya wa Mahfuz irin kaddarar da ta fad'a masa.
Zuwan Aji da Bubu ne ya dawo da Moh cikin hayyacin sa, babu hawaye ko digo a fuskar sa amma ya daku, ya kadu da zaka iya rantsewa ya dade a kwance yana jinya me tsanani.
Baya magana bayan amsa gaisuwa sai dai kawai ya amsa maka da ka, har zuwa lokaci itama bata farka ba, yaje yaga Musaddik wanda yake da sauki sai ciwuka a jikin sa yawanci na duka ne. Sai kuma yunwa da ta ramar dashi sosai, driver da Ummimi babu abinda ya same su dama su ba sune targets din ba.
Wajen azahar ya dawo dakin da take, har lokacin bata tashi ba, mummy ce kawai a dakin tana zaune gaban gadon da Iman din take, idon ta yayi ja sosai, addu'a take tofa mata ya shigo ta tashi a kunyace tana kokarin barin dakin
"Dan Allah mummy ki yi zaman ki, dama nazo na duba ko ta farka ne, zanje station din na dawo."
Komawa tayi ta zauna shi kuma ya fita, ya shiga mota ya nufi station din. Direct office din CP ya wuce ya samu DSP yana press conference akan case din, kokarin fita yayi amma babu dama sun riga sun ganshi, sukayi masa cha kuwa kowa na son masa tambayoyi, be basu dama ba dan yanzu ba wannan ne a gaban sa ba, da kansa zai shirya ya basu lokaci amma ba yanxu da be ma san me yake masa dadi ba sam. Hakuri aka basu, aka kuma sallame su sannan ya samu ganin CP din sukayi magana, ya kuma shiga wajen da aka ajiye Jabir din. Yayi matukar laushi sosai saboda ba karamin duka sojajin nan sukayi masa ba, dama yasan ba zasu kyale shi ba, hakan ba dan dai basaso a samu matsala ne amma tsaf zasu iya kashe shi a wajen.
Baya jin a yanzu akwai wata halitta da ya tsana sama da Jabir din, shiyasa ya tsaya daga kofar be shiga ba, dan idan ya shiga zai iya shake shi har sai ya daina numfashi. Wani dan sanda ne a gaban sa rik'e da wani katon katako, yana masa tambayoyi, sai kuma wasu yan sandan suma daban daga gefe cikin fushi suke interrogating dinsa yana rokon suyi hakuri. Juyawa yayi ya bar wajen ya koma suka karasa magana da CP sannan ya bar station din ya dawo asinine, in da ya wuce kai tsaye wajen Musaddik, ya samu dakin da yan sanda suna daukar bayanai daga wajen sa, wucewa yayi ya koma bangaren Mahfuz da har yanzu ba'a saki gawar sa ba, sai an gama bincike tsaf sannan za'a basu suyi masa sutura. A chan ya zauna tare da su Habib dasu Abba har bayan Magriba sannan aka basu gawar tasa, suka dauke ta suka nufi gida da ita don yi masa sutura a mika shi gidan sa na gaskiya.
Zuwan su ya saka gidan rikicewa, dama kowa ya iso ana zaman jira cike da alhini, ba karamin taba kowa mutuwar tayi ba, nauyi da kunya ya Moh shiga ciki, sai yake ganin kamar shi ya jawo, da be saka shi a cikin maganar ba, da duk hakan bata faru ba, a daren aka hada shi, aka kuma rakashi gidan sa na gaskiya. Allah sarki.
Mutuwa darasi ce babba, Rayuwa bata da tabbas, Allah ya bamu ikon amfani da lokacin mu kafin ya kure mana,Allah kasa mu cika da imani. Amin 😭
***Wani irin juyawa cikin Samha yayi lokacin ta samu labarin an kama Jabir, tsoron ta daya kar sunan ta ya shigo ciki, itace ta bawa Jay din shawarar kidnapping Iman din, kuma ita kadai ce tasan plan dinsa duk da itama bata san amfani yayi da ita ba. Wayar ta ce tayi kara da take gefen ta,dan tsorata tayi, sai kuma ta kai hannu ta dauka tana kallon number, Kamal ne yake kiranta, dagawa tayi ta saka wayar a handsfree
"Ashe dama abinda zaku aikata kenan ke da dan iskan chan shine kuka shigo dani ciki kuka samu duk wani bayani akan shi, daga karshe kuka watsar dani."
"Ai kai ba karamin kidahumi bane, idan banda gara irin ka, waye yake da amana a wannan zamanin, kowa kansa ya sani bari kaji, dan haka karka dameni ka kyale ni naji da abinda yake damuna."
"Ai wallahi kadan kika gani, asirin ki ya gama tonuwa dan na gama zayyane komai a gaban yan sanda, abubuwan da kuka sakani nayi duk na fad'a sai ki jira hukunci, wallahi ko shi MOH ya kyale ki wallahi ni ba zan kyaleli ba kinji na rantse!"
Kit ta kashe wayar ta jefar da ita,
"Wannan wacce irin masifa ce?"
Da sauri ta ja jakarta ta fito, bata tarar da maman ta a falo ba dan haka tayi saurin ficewa ta dauki mota ta bar gidan, tana tafe tana gwada kiran Laila amma bata dagawa, ta rasa abinda yake mata dadi, sai kawai ta wuce gidan ta sameta suyi magana ko zata taimaka mata, amma tana zuwa gate sai aka hanata shiga, tayi mamaki sosai hadda fitowa tayi musu bayanin kanta, amma kemaimai suka hanata bayan sun tabbatar mata da sun gane ta, umarni ne aka basu kar su sake barin ta, ta shiga masarautar.
_ZAFAFA2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D'aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/24/22, 08:08 - Buhainat: ©®*Hafsat Rano*
_Halin Girma_
*41*
***Ruwa ta fara ambata sanda ta farka, da sauri Mamma tayi wajenta itace take tsaye dama, Mummy na kan sallaya tana lazimi ta mike da sauri cikin tsananin farin ciki.
"Alhamdulillah." Ta furta tana karasa kusa da Mamma da take jera mata sannu, da ido kawai take bin su tana son tuna abinda ya faru karshe. Murmushi tayi cikin dauriya tace
"Mamma."
"Na'am Iman, sannu kinji?."
" Alhamdulillah mun auna arziki. " Ta juya tana fadawa Mummy da ta kasa boye farin cikin ta
"Fatima. "
"Mummy. "
" Sannu kinji, akwai abinda yake Miki ciwo? "
Da hannu ta nuna cikin ta, taba cikin Mummy tayi kila saboda wankin cikin da akayi mata ne,
" Bari nayi musu magana tunda ta farka. "
" Bari naje. "
Mummy tace tana yin gaba, ta bar su da mamma tana tambayar ta. Tare suka shigo da nurses su biyu, mamma ta matsa suka duba ta, sukayi mata tambayoyi sannan suka ce a bata ruwa tasha da abinci sannan suka fita daya ta sauki file din ta daya kuma ta tafi kawo mata magunguna daga pharmacy.
Taimaka mata mamma tayi tunda an cire drip din ta kai ta toilet, ta gasa mata jikin ta, ta taimaka mata tayi wanka da brush kafin ta fito Mummy ta hada mata tea me kauri da kidney pepper soup da aka kawo daga fada.
Daure da alwala ta fito bayan ta sauya kayan jikin ta zuwa doguwar riga mara nauyi ta saka Hijab ta zauna a gadon ta biya bashin sallolin da suke kanta, sai da ta idar sannan ta dan ci abincin kad'an ta koma ta kwanta lamo tana jin jikinta babu kwari ko kad'an.
Abba ne ya shigo tare da wasu mutane masu rawani, suka dubata sukayi mata ya jiki sannan suka tafi, Abba ya rakasu ya dawo ya zauna yana sake dubata. Tsam Mummy ta bar dakin ta koma waje ta bar Mamma a ciki suna magana da Abban, ya dan jima a ciki sai da yaga alamar ba zata dawo dakin ba bayan kuma ita ta kirashi da Iman din ta farka sai ya tashi kawai yayi sallama ya tafi akan zai dawo anjima.
A waje suka hadu da Mummy din, ya sameta har wajen da take zaunen yayi mata magana, ta amsa masa sama sama kamar tana jin haushin sa ko wani abu, be gane dalilin ta ba, ganin a waje ne ga kuma Moh da ya nufo su ya saka shi kyale ta ya tafi, suka gaisa fuskar sa fayau alamun ya samu labarin farkawar Iman din. Komawa yayi ya raka Abban har mota sannan ya dawo, ya tarar da mummy da Mamma din duk a waje, kila Mummy din ce ta sanar mata da zuwan sa shiyasa suka fito ba sai ya shiga su hau fita ba, gaishe su yayi da tambayar ya mai jiki sannan ya danyi jim a wajen sai da Mamma tace ya shiga sannan ya tashi ya nufi dakin da daukin ganin ta.
Ko sallama ya maita yayi sai da ya tura kofar ya shiga sannan ya tuna yayi sallama ta dago daga kwanciyar da tayi ta kalle shi. Da sassarfa ya karasa kuwa, ya haye saman gadon ya tattaro ta zuwa jikin sa, ya rungume ta tsam damuwar da yake ciki na raguwa. Luf tayi a jikin nasa tana jin nutsuwar da ta rasa tsawon kwanaki, bata san haka tayi kewar sa ba, sai yanzu da suke tare, kuka ta saka masa ya sake rungume ta yana jin shima kamar ya rushe da kukan. Sai da yaga kukan nata na neman zarcewa sannan ya dakatar da ita ta hanya shafa bayan ta ya shiga magana a kunnen ta
"Shssh... Karki karawa kanki wani ciwon please, you are safe now. Babu wani abu da zai sake faruwa, I will protect you with my life."
Shiru tayi tana jan numfashi, ya cigaba da shafa bayanta har sai da yaji tayi shiru gaba daya, sannan ya dago ta daga jikin sa yana kallon fuskar ta, murmushin ya sakar mata ta maida masa itama.
" Me yake miki ciwo yanzu? "
" Kai na.. " Tace a hankali
" Sannu zai daina a hankali, komai zai wuce, ba zan sake tafiya ba barki ba nayi miki alkawari nan."
Maida kanta tayi jikin sa ta kwantar ya gyara mata kwanciyar yadda zata ji dadi, ya saka hannu yana mata tausa a hankali.
Sun dade a haka har sai da akayi knocking a kofar, ya zameta ta kwanta sosai akan gadon ya sauka sannan yace
" Bismillah a shigo."
Bataliyar yan gidan su ce, tun daga kan su Ya Maryam da matan gidan hadda Dadah da wasu ma da be san su ba, a gurguje ya gaisa dasu ya bar musu dakin dan dakin ma yayi musu kad'an.
Dakin da Musaddik yake ya wuce, ya sameshi a zaune ya gama cin abinci, yayi fes dashi jikinsa kuma yayi kyau, kanin sa ne yake kula dashi suka gaisa da Moh din sannan ya basu waje dama yana so yaje ya siyo abu a shop sai yayi amfani da damar ya tafi.
"Jikin ka yayi kyau sosai friend."
"Wallahi Alhamdulillah, mun gode Allah, ya jikin Madam din?"
"Itama Alhamdulillah wallahi, ta samu sauki."
"Masha ALLAH. Allah ya kara mana lafiya baki daya. "
"Amin, ka tabbata kana cikin abokai na gari, Allah ya hada mu tare a inuwar al'arshi, bansan da wanne baki zan gode maka ba, ban kuma san da wanne ido zan kalle ka na gode maka ba, ta ya akayi na kasa ganewa? Na kasa banbance ka da wani daban? How long ka zauna a wajen sa.? "
" Mu daina tunawa dan Allah, tunda ya shigo hannu shikenan nasan dole zai girbi abinda ya shuka. "
" Still dai inaso nasan komai... "
" Ka bari mu koma gida, zan baka labarin komai, for now kayi fucusing akan case din cikin gida, yau saura kwana uku su juya komai, kana bukatar gabatar da evidence din nan."
" Haka ne, kuma abinda ya faru yanzu ya saka na kara jin kowanne abu akwai good side da bad side dinsa, abinda na tsana nake ganin shine kawai matsalar ta, har naki bin umarnin Bubu akai,shi zan yi facing yanzu, zan karbi abinda ya zama mallaki na, zan farantawa mahaifi na kamar yadda ya dade yana burin ganin ranar. "
" Da gaske kake? "
" Da gaske nake. "
" Kai masha ALLAH, Bubu zai fi kowa murna shi da Aji. Dama a komai alkhairi ake nema ba son zuciya ba,nayi murna sosai aboki na, Allah ya baka sa'a. "
" Amin. " Yace yana daukar ledojin maganin sa
" Kana shan magungunan nan kuwa?"
" Ina sha. "
" Good, da baka sha da sai na saka ka... "
" Frog jump. " Ya karasa masa suka kwashe da dariya suka tafa
" Wallahi ka raina ni, Capt guda, Capt Muhammad Ahmad Santuraki, babu wani respect ko? "
" Ayi hakuri tsohon Capt! "
Duka ya kai masa a kafadarsa, ya goce suka sake kyalkyalewa da dariya.
***Baki daya ta rasa abinda yake mata dadi, ta rasa in da zata tsoma ranta taji sanyi, cikin jikinta yayi masifar takura mata, babu abinda take so take kulafuci sai mijinta Bashir, takanas ta aika aka samo mata irin turaren da yake amfani dashi amma duk a banza, watarana sai ta shiga daki tayi kuka gashi Abba yayi shiru da maganar, ko dan abinda ya faru a kwanakin ne? Babu irin kiran da batayi wa Bashir amma sai yace mata ta kara jira zaizo,. Takanas ta samu Mama a daki da ita ma kanta ta gaji da zaman Zeenat din ta kuma damu da shirun da Abban yayi dama Bashir din. Da kallo ta bita har ta zauna a kusa da ita, tun ma kafin tayi magana ta riga tasan me ya kawo ta
"Yau zan samu Abban ku da maganar, ni kaina hankali na ba akwance yake ba, kema kuma duk alamu sun nuna dakin mijinki kike so, ki tattara ki koma Allah ya baku zaman lafiya, me afkuwa ta riga ta afku shiyasa yayi biris damu shima Bashir din yasan ya gama damu, sai ki koma kawai ya zamuyi?"
"Nima dama maganar da nazo muyi kenan."
"Ai na sani, oh Zeenatu ana son miji. "
Da sauri ta rufe idon ta, ta tashi ta bar dakin a kunyace, ita kanta bata san menene ya hau kanta ba, yadda take ji idan bata koma ba, komai zai iya furuwa da ita. Ga wani masifaffen son cikin jikin ta da take ba zata so ya taso ba tare da mahaifin sa ba, ta taba karanta wani littafi da yarinyar ciki tayi gangancin kashe aurenta ashe akwai ciki, karshe haka ta haife dan a gida kuma ta cigaba da rainon sa a cikin bakar wahala, gashi duk wanda yazo auren ta sai yace ba zai rik'e mata da ba.
Text message ta sake tura masa na ban hakuri, kamar yadda take masa kullum amma baya reply, ko ranar da yazo gaisuwa gidan taso suyi magana amma kemaimai ya ki bata dama karshe ma ya daga wayar Hajiyar sa yayi tafiyar sa ya barta a wajen.
*Adamawa-Yola*
Ayi maneji😢😢🙌
_ZAFAFA2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D'aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/24/22, 08:09 - Buhainat: ®*Hafsat Rano*
_Halin Girma_
*42*
***
*Adamawa-Yola*
Dukkan su sunyi shiru da abinda yake sak'awa a rai, idan har ta tabbata Muhammad yana da evidence akan su, toh gaba daya lissafin su ya sauya. Amma kuma akwai abin mamaki ace yasan komai tsawon wannan lokacin amma be taba fadawa kowa ba, hatta mahaifiyar sa da yafi kusanci da ita akkowaan kowa.
Sanarwar shigowar sa masarautar ya sake