Showing 21001 words to 24000 words out of 115235 words

Chapter 8 - Halin Girma Hausa Novel Complete

hankalin sa ya kasa kwanciya da abinda ya karanta. Tashi yayi ya fito zuwa falon gidan, ya k'wala kiran Iman din. Zeenat ce ta fito

" Ina Ummi? "

" Ina ga tana wajen Gaji. "

" Je ki kira min ita. "

Fita tayi shi kuma ya cigaba da tsaiwa awajen har suka shigo a tare.

" Ki same ni a daki na. " Yace yana juyawa tabi bayanshi, dariyar mugunta Zeenat tayi a tunanin ta wani laifin Iman din tayi dan sosai yanayin Abban ya nuna bacin rai.

A gefen gadon sa ya zauna, ta samu chan gefe daga kasa ta rakube tana tunanin dalilin kiran.

" Kina jina Uwata? Kina da wata matsala wacce ban sani ba? "

Girgiza kanta tayi

" A ah Abba babu. "

" Kalle ni nan, ni ne mahaifin ki, baki da wanda yafi ni bayan mahaifiyar ki, ki fad'a min gaskiya idan akwai wani abu da yake damunki."

Zuciyar ta ce tayi rauni, taji kuka na taho mata, ta k'asa rike shi kawai ta fashe da kuka. Dafe kansa Abban yayi, ya shiga tunanin me yake faruwa? Wanne irin abu ne haka da har shi ya kasa ganewa?

"Fatima..." Ya kira ainihin sunan ta a karo na farko a rayuwar ta

"Na'am." Ta amsa cikin muryar kuka

"Kowanne bawa da irin yadda rayuwa take zuwar masa, kiyi hakuri zanyi bincike, sannan akwai shiri da nake yi na kaiki wajen mahaifiyar ki da zarar maganar bikin ku ta tabbata, nayi mata alkawarin kai mata ke da zarar lokacin auren ki yayi, mahaifiyar ki na son ki fiye da yadda take son kanta, ki rik'e wannan."

" Tashi kije kinji, ki daina kukan haka."

Tashi tayi bayan tace

" Nagode Abba." Ta fice ya bita da kallo yana jin kamar be kyauta mata ba.

Dakin su ta wuce ta tarar da Zeenat na waya har da shewa, juyawa tayi zuwa store ta zauna a gefen katifar ta, tayi kuka sosai har sai da taji babu abinda yayi saura a zuciyar ta. Tsawon lokaci ta sauka a ciki har sai da taji maganar Mama tana fad'a a waya anan ta gane ta dawo dan dazu bata gidan. Tashi tayi ta fice ta kofar baya bayan ta gyara fuskar ta a sink din kitchen.

***Zama Mama tayi tana sababi akan tafiyar Khalil din babu sanarwa, sai dai a k'asan zuciyar ta taji dadin hakan domin a kalla hankalin sa zai dauke daga kan Iman din har a gama magana da shi dayan da yazo. Abba ne ya shigo ya sameta tana zaune , ya zauna a gefenta sai tasha jinin jikin ta musamman da ta gama sanin halin sa tsaf.

"Me yasa kika ce min Ibrahim ba da gaske yake akan maganar Ummi ba, sannan shi kuma yaje ya samu Yaya da maganar."

Yadda ta zabura yaso bawa Abban mamaki.

"Khalil din ne yaje wajen Yaya? Yaushe akayi haka? Me yayan yace masa?"

"Duk ba wannan na tambaye ki ba, baki bani amsa ta ba."

"Toh toh ai gani nayi shi Khalil ba yanzu zai yi aure ba, su kuma yaran nan yanzu ne muke so mu aurar dasu, bana so Zeenat ta tafi da bar Iman tunda kaga tare suke komai, shiyasa nace gwara wanda ya shirya."

"Haka ne kuma." Yace yana mata wani irin kallo da ya sakata tunani sosai

"Toh hakan yayi ai, Ina fatan dai zeenatu ta sallami yaron nan Bashir ko? Dan ina nan akan bakana ba zan bashi ba."

"Dan Allah Dr ka bar wannan maganar, tunda tana son shi kayi hakuri kawai ayi tunda an wuce zamanin da za'a yi wa yara auren dole."

Girgiza mata kai yayi yana dakatar da ita

"Wannan maganar taki shirme ce, musulunci mu ya bawa damar zaba wa yayanmu mazaje na gari, dan haka ban yarda da Bashir ba, idan akwai wani ta kawo shi."

Ya tashi ya fice ransa na baci da yadda maganar Bashir din taki karewa, sam Hajara bata shirya gane abunda yake hango musu ba, eh hango musu tunda duk in da aka je aka jawo ita uwa sai tafi cutuwa da abinda zai samu yarta.

***Text message biyu ya tura a lokaci daya, address din sa da Abba yace ya tura masa ta message sai kuma message din da yayi wa Abban Iman din, wanda yake ganin shine kadai hanyar da zai bi wajen hana Maman sanin duk wani abu akan Iman din, ya tabbata daga lokacin Abban zai saka ido sosai, ba kuma za'a dau lokaci ba zai gano komai, shi kuma sai yayi amfani da wannan damar ya nemi alfarmar barin komai ya zama sirri a tsakanin su iyaye maza, domin dama su iyaye maza baa sansu da ratatin zance ba, ba kasafai ma suke zama suyi ta magana anyhow ba, ya tabbata idan har hakan ta yiwu toh zai samu abinda yake so, zai kuma tabbatar da Fatiman sa ta samu gatan da bata taba tunani ko hasashen samun sa ba.

***Tunani Abba ya fad'a ganin address din da Muhammad ya turo masa a matsayin in da yake,Emir Palace Kano, Emir Palace Adamawa-Yola, me hakan ke nufi? Kiran Abban su Fatiman yayi yazo ya same shi a part din sa, ya nuna masa message din sannan ya kira sauran yan uwan su Abba Musa suka hau tattaunawa akan abinda ya kamata su yi. Dama chan Abba Musan yana siyasa sosai, sai sukayi shawara akan shi ne zai wuce gaba wajen binciken waye Muhammad din a cikin kwana uku kachal. Haka kuwa akayi, washegari ya same su da maganar da ta yi matukar basu mamaki. A yadda suka sani idan wani daga cikin irin wannan yaga yarinya yana so, kawai aikawa ake iyayenta suzo ayi magana a fadar sarkin, a matsayin shi sarki dama uban kowa ne, sai suga ga banbanci inda Muhammad din yazo kai tsaye ba tare da ya nuna shi din waye ba, ba kuma tare da ya nuna karfin iko na mulki ba, hanyar da ta dace da kowa yake bi wajen neman aure shima ita yabi.
  A cikin su babu wanda be yi amanna da maganar ba, musamman binciken da Abba Musan yayi da irin yabon da Muhammad din ya samu daga wajen mutane da dama musamman mazauna masarautar.
    Shiru Abba yayi bayan kowa ya gama tofa albarkacin bakin sa, aka bashi dama a matsayin sa na mahaifin Iman din,

"Bakwa ganin idan iyayen yaron nan suka san in da yazo neman aure zasu kyale shi, duba da mu din ba wasu bane akan irin girma da nasabar gidan da ya fito."

"Idan har a yadda bincike na ya nuna min ne, iyayen sa basu da matsala masu son talakawan su ne, dan haka muyi addua kawai in sha Allah alkhairi ne."

"Shikenan, Allah ya tabbatar mana da alkhairi,."

"Yanzu kayi magana, Amin ya Allah."

" Ina neman alfarma daya, da mu bar maganar nan a tsakanin mu zuwa muga abinda Allah yayi."

" Hakan yayi, Allah ya shige mana gaba."

Suka hada baki a tare, sai kuma suka shiga wata hirar tunda daman su dan dade basu yi irin wannan zaman ba, anan duk suka ci abinci a tare sannan kowa ya tafi zuwa sabgar sa. Aka bar Yaya a zuwan zai kira Muhammad din da daddare ya sanar dashi ya bashi izinin yazo yaga Fatiman su daidaita, da daddaren bayan ya gama komai ya turawa Muhammad din text message akan ya cigaba da zuwa. Muhammad na zaune shi da Musaddik suna kallon video da ya saka akayi wa Khalil suna kwasar dariya text din ya shigo, tashi yayi ya daka tsalle kafin yace

"Yess!!!

" Ya akayi?"

" Karfe nawa yanzu?"

Yace yana kallon agogon falon

" Opss Ashe dare ya fara, ba dan ba dan ba da yanzu zanje na ganta, amma ba komai kafin na wuce Abuja zan tsaya na fara ganin ta."

" Me faru wai."

" Karanta!" Ya mik'a masa wayar

" Ah congratulations angon fatiti, Allah ya tabbatar mana da alkhairi."

Rik'e k'ugu yayi yana hararar sa

" Allah ka sake bata mana suna sai na saka frog jump, kaji ma na ratse."

" Kut! Allah fa ka raina ni Moh, komai sai kace zaka sani frog jump an fad'a ma nima kamar wadanchan dogs din naka ne na bakin gate."

" Ka dai kula, kana magana ne da Captain Muhammad Ahmad Santuraki, Captain Moh!"

" Whatever, ni dai muhammadu na sani, ba wani bragging da zaka min."

" Zaka gane ne idan na dauke ka na je na jefa wa mayunwatan zakunan nan na barack, ba zaka sake kiran sunana gatsal ba."

" An gaya ma kowa irin khalil ne? Lusari!"

Dariya suka saka Muhammad ya shiga gwada yadda Khalil din yake, suka sake tuntsurewa da dariya suka tafa

" Ashe farar kura ce a wajen, sai uban cika baki dan iskan yaro, gobe ma ya sake, naso ka dan saka su sun sassama masa jiki wallahi,."

" A hakan ma nasan sai sunci zalinsa ai."

" Wicked soul!" Yace yana dariya

" Naji, bari naje na kira Baby na, naji voice dinta me dadi kafin gobe naje na ganta, dan yanzu ina da license, na matsu na ganmu tare, muna yawo a garin nan cikin mota my hands in to her's, ga cool music na tashi Malam, wow love in the air."

" Toh Mr Romeo, Allah ya kaimu dai zamuyi kallo, yadda kake son ta Allah yasa tana maka ko rabin sa ne."

" I don't care, as long as munyi aure, zan koya mata yadda zata so ni."

" We shall see."

***Ruwan zafi ne a katon bawo, Khalil na zaune a gaban ruwan hajiyar su na danna masa bayansa, gaba daya jikin sa ciwo yake kafarsa kamar zata cire yake ji, babu irin tambayar da batayi masa akan me ya same shi ba amma yaki fad'a mata, haka Mama ta bugu tana fad'an tafiyar Khalil din hajiyar ta fad'a mata a yadda ya dawo, kuma yaki cewa komai. Yana jin su har suka gama ya tashi ya koma dakin sa ya kwanta yana tariyo abinda ya faru cikin tausayin kansa. Shi ya jawo yana takama da shegen bakin sa ya je ya kaishi ya baro, dama an fad'a mutum ya kiyayi harshen sa, akwai hadisi guda da akayi magana akan harshe da kiyayar sa, yaga izina a kansa, gashi bashi da damar fadawa wani abinda ya faru domin yasan shi za'a yi wa dariya, ko da muhammadu a iya soja ya tsaya matsayin da yake kai ya isa ya taka shi son ransa ba kuma wanda ya isa yace dan me? Balle ganowar da yayi waye Muhammad din, anan ya gane bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane, shi din ma ganganci ne da kuruciya. Eh toh kuruciya mana tunda dai yasan a girme Muhammad din zai girma shi dole ya fishi hankali da komai. Abu daya ne zai hana shi walwala, yadda zai yi da tarin soyayyar ta, gashi yayi masa kashedin ko a hanya babu shi babu ita, ya kuma tabbatar idan har ya kuskura yayi wani abu, za'a iya neman shi ma baki daya a rasa, dan masu kudin nan yasan ba wani abu bane a wajen su su batar da mutum bat, har abada a daina jin labarin sa.
   Tagumi ya rafka yana jin kamar yayi ta kurma ihu ko yaji sassaucin radadin da zuciyar sa ke masa. Allah sarki Khalil 😂
1/9/22, 10:17 - Buhainat: Halin Girma
    10

*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* 

I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb


***Be ji sallamar ta ba, sai ganin ta yayi kawai a dakin bayan a zahiri tayi sallamar amma saboda baki daya hankalin sa na ga tunani shiyasa be ji ba sam.

"Ya Khalil wai a kawo maka abinci..."

Ai kafin ta karasa ya daka mata uwar tsawa

"Uban abincin, dallah Malama karki dame ni."

"Toh... Me yayi zafi? Hajiya ce ta aiko ni ai."

"Fitar min daga daki!" Yace yana tasowa, da gudu ta juya tana dariya, sai da ta ga ta fice sannan ta daga murya tace

"Bani na kar zomon ba..."

Ransa ne ya sake baci, ya bigi kofa yana komawa ya fad'a saman katifar sa yana jin kamar yayi ta cizon kansa.

A falo ta samu Hajiya ta zauna tana haki

"Allah ya taimake ni na kusa cin duka, daga tambaya kawai ya hayayyako min Hajiya."

"Toh wai ko dai Khalil tsokana yayo ne aka tattaka shi, kinsan fa Khalil ba dai tsokana da cika baki ba."

"Alamu dai sun nuna Hajiya, fad'a ya takalo da yafi karfin sa wallahi, gashi nan yaki fad'an abinda ya faru."

"Toh Allah ya kyauta " Hajiyan tace tana tashi ta fita zuwa dakin nasa.

***Tana tsaye a bayan kitchen dinsu, wanki ta gama tana ta sauri saboda kwana biyu bata maida hankali zuwa islamiyya saboda abubuwan da suka sako kai, tana wankin tana tunanin maganar da sukayi da Abba da ta zama tamkar bitar karatu haka take yin sa, takun tafiya taji, ta juyo sai taga Abban a tsaye yana duban ta, da sauri ta dan russuna,

"Abba sannu da zuwa."

"Wanki ake ne?"

"Na'am.?" Tace tana zaro ido sanin cewa ba da sanin sa take wankin ba, musamman ya samu almajiri yake wanke musu kaya ita da Zeenat da Marwan yake biyan shi ta hannun Mama, duk da yasan dole zasuyi wanki irin kayan ciki da abubuwan da ba za'a iya bawa me wanki ba, amma kuma tarin kayan da ya gani a wajen da ya gane na Marwan ne sai wasu na Maman ya saka ransa mummunan baci, har a jiya sai da Maman ta karbi kudin wanki a wajen sa da zumar yau me wankin zaizo karbar kudin sa ya kuma bata babu musu. Yanayin sanyin garin zai yi wuya wajen wanki musamman da tun da dadewa yasan fatar Iman din bata son wahala idan tayi wanki hannun ta kanyi ja sosai, shi kuma Allah ya hore masa son yaya Kuma gasu ba wai yawa ne dasu ba shiyasa duk wani aikin wahala baya son siyi duk da ba wai kwata kwata ba zasuyi komai ba, amma kamar wanki yana ganin be kamata shima a saka shi a cikin aikin mata ba, mata na wahala da aikin gida kula da yara da girki wankin aka dauke musu zasu samu sassauci. Matsowa yayi ya sake leka kayan kafin ya girgiza kansa ya juya bayan yace

"Ki bar wankin nan kizo ki wuce ciki."

Sakalo tayi a tsaye tsoro na kamata

"Bakya ji ne?" Ya daka mata tsawa, da sauri ta bi bayansa har cikin gidan, dakin su taga ya wuce ya kwankwasa sannan ya tsaya

"Waye?" Zeenat tace tana daga kwance cikin rufa, a yadda tayi maganar zaka gane knocking din ya takura ta, sake kwankwasa wa yayi sannan ya tura kofar da sallama, be shiga ba, ya tsaya a kofar yana karewa dakin kallo, gadon zuwa katifar dake shinfid'e a kasa da ta tabbatar masa da ta Iman din ce. Tuna lokacin da ya bada kudin gadajen nasu yace a siyawa kowa nasa amma sai Mama tace daya ya ishesu me dan girma saboda hakan zai sake shakuwa tsakanin su,da wannan yayi amfani a ganin sa hakan ne ya kuma dauki hakan a matsayin soyayyar da Maman ke wa yar tasa. A yadda yake jin zuciyar sa a lokacin zai iya yin komai, sai kawai ya fice daga gidan gaba daya ba tare da ya koma daki ba.
Tsoro ne ya kama Iman musamman da bata san me zata ce wa Maman ba akan wankin, shiryawa tayi cike da fargaba ta tafi makarantar tana fatan koma menene ya taso ya zama daidia kafin ta dawo dan a rayuwar ta, ta tsani tashin hankali ko kad'an.
Rabi da kwata bata gane kan karatun ba, haka dai ta taho gidan tana ta zulumi, tana shigowa ta ganshi a tsaye ya harde hannayen sa a gadon bayan sa yana kallon kofar shigowar. Shigar jikin sa ta bi da kallo zuwa gyaran da yayiwa fuskar sa, murmushin da ta gani kwance a fuskar tasa, ya saka ta samun nutsuwa har ta karaso wajen da yake a tsaye.

"Ashe kina kusa da shigowa, naji a jikina."

Murmushi tayi kafin tace

"Sannu da zuwa."

"Yawwa, ya hanya?"

"Alhamdulillah wallahi.*

" Akwai wanda ya kalleki da kina tahowa? Idan akwai fad'a min naje na same shi."

Sosai ya bata dariya,

" Kai... Babu kowa fa, ya gida yasu Mama?"

" Mama? Ammi muke ce mata, tana nan lafiya tace ma na gaishe ki, na gaida wacce ta kwace mata yaronta kafin tazo haka tace."

Rufe fuskar ta tayi tayi yar dariya

" Allah sarki, ina amsawa nagode."

" Itama ta gode, tace ta matsu ta ganki."

"Watarana zata ganni in Sha Allah."

"In Sha Allah, very soon."

"Abba Babba yace idan kazo ka shiga ciki."

" Da gaske? Kice na zama dan gatan Abba."

Dariya tayi

" Naga alama kam, Abba ya yarda da kai sosai."

" Allah sarki, ai yana da kirki sosai."

" Sosai." Tace

" Bari na bud'e maka, chan ne seat room din sa."

" Owk." Yace ya harde a jikin ginin yana kallonta, har ta bud'e ta dawo sannan ya bita a baya yana admiring steps dinta zuwa ciki.
A kofar dake farkon kofar ya zauna ita kuma ta shiga ciki, yana zama Aliyu ya shigo da ruwa a tray, ya ajiye ya gaishe shi sannan ya fita, ruwan ya dauka ya sha sosai sannan ya kalle ta, gefe take kallo tana wasa da jikin kujerar da take kai.

" Zahraah, tafiya ce ta kamani, ba zan iya wucewa ban sanar miki ba, ba wani dadewa zan ba in sha Allah, inaso kafin lokacin da zan dawo mu sake fahimtar juna sosai, idan na dawo sai a shigo da magana me karfi, bana so a ja lokacin."

" Allah ya kiyaye ya tsare, ya dawo da kai lafiya."

" Amin ya Allah, Amin Amin Zahraah Nagode"

Shiru ne ya dan shiga tsakani, shi yana kallon ta yana sake ganin ainihin kyawun ta, ita kuma ta tafi tunanin Allah yasa ya dawo din kar taji shiru idan ya tafi, har zuciyar ta bata son tafiyar tasa, amma kuma ya zatayi? Ba zata hanashi ba ai.

"Ina wannan yayan naki da muka hadu ranar nan? Har ya korar min ke?"

" Uncle Khalil?" Tayi dariya

" Auw sunan shi kenan."

" Eh kanin Mama ne, a nan gidan ya taso kafin ya koma gida."

Gid'a kansa yayi kamar be sani ba

" Shiyasa ya nuna min iko kenan."

" Uhum." Tace kawai bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login