Showing 84001 words to 87000 words out of 115235 words
Chapter 29 - Halin Girma Hausa Novel Complete
da uwargidan tasa suka fado, sai da k'yar suka daidaita dan shima jan wuya yayi mata ganin idan ta biye masa zai iya cewa su rabu yasa ta kyale shi, taga kansa rawa yake ya samu yarinya karama shiyasa ta kwantar da kanta ta cigaba da bin sa tana so taga iyakar limit din iskancin nasa, tasan sarai yana zuwa dakin da dare amma ta share bata taba nuna masa ba, wani zubin ma akan kunnenta komai yake faruwa amma ta daure dan plan dinta akansa ba na yanzu bane, shigo shigo babu zurfi tayi masa sai ya gama sakankancewa zatayi maganin sa.
Ranar ma kamar yadda ya saba kawo mata waya suyi magana da Mama haka ya kawo mata, ta karba tana daga kwance da babu wani aiki da takeyi yanzu matar gidan ta rage takura mata, dattijuwar me aikinta da ta tafi gida ta dawo shiyasa aikin ya rage mata sai dai taci ta kwanta ga uban kasalar da take fama dashi ga shegen nacin Bashir da yake hanata sakat, tana shan wuya sosai a hannun sa dan baya daga mata kafa ko kad'an, tun tana masa rashin kunya har tazo ta kyale shi yayi uwar da zai yi, ranar da zata samu hanya kawai take nema wallahi ta tafi ba zata dawo ba ko me za'a yi mata kuwa.
Wayar ya mika mata bayan ya gama amsawa da toh, suka gaisa da Mama ta take fad'a mata haihuwar Aunty Bilki, tayi murna sosai ana take jin gobe suna kuma a gidan su za'a yi sunan saboda akwai fili sosai
"Ki lallaba shi ya kawo ki na dai gaya masa."
"Toh shikenan, zan kira." Ta katse wayar ta mika masa
"Dan Allah ka barni naje suna gidan mu gobe."
"Ki shirya da safe zan mika ki sai na wuce garari na, idan na gama sai nazo mu dawo."
Yace ya sa kai ya fice da bishi da kallon mamaki, bata taba tunanin zai yarda haka kai tsaye ba, murna ta hau yi ta dinga zagaye dakin tana jin kamar wahalar ta, ta kare kenan dan ko giyar wake take sha idan taje gida ba zata dawo ba sai dai Abba ya kashe ta.
Murmushin mugunta yayi yana barin dakin, shi kadai yasan tsiyar da ya shirya ya kuma tabbatar da ko taje gidan toh sai ta dawo da kanta ko Maman ta sakota gaba ta dawo da ita.
***Waya suka gama yi da Ya Maryam ta cigaba da shiryawa a tsanake saboda safiya ce, sannan yace ta jira shi ya fita toh dole sai ya dawo zata tafi, tana so taga Abban ta da Marwan da Gaji da sauran yan gidan, shiyasa ta tashi tun wuri ta hau shiryawa yadda zata samu zuwa da wuri ta dade kuma.
Tana zaune taji shigowar motocin sa, ta yaye curtains din dakin ta ga wasu motoci guda biyu da bata san su a gidan ba, sakin labulen tayi, ta sake fesa turare ta fito suka hadu a falo.
Tafi ya shiga yi mata dan ba karamin kyau tayi ba, lace ta saka me orange da black yayi mata kyau ya dace da kalar ta, zaunar da ita yayi ya dauke ta hotuna masu kyau sannan yace idan ta gama ta ga driver nan idan yaso zai zo da daddare su dawo tare. Jakar ta, ta dauko ya rakota har wajen motar ya bud'e mata ta shiga, sannan suka fita daga gidan yana tsaye yana kallon su. Tasa motar ya fad'a shima ya bar gidan dan yana da important abun da zai yi. A daidai lokacin Zeenat suka fito da Bashir, ya kunna machine din da ya aro a wajen abokin sa dan Hajiya ta fita da motar ta, kamar tace ba zata hau ba, sai kuma ta hau dan bata da ko biyar din da zata dauki adaidata sahu, tunanin idan taje gida ta karbo masa sam be zo kanta ba.
_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D'aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/12/22, 11:31 - Buhainat: Halin Girma
33
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
*******�?
A kusan jere suke tafiya da motar Abba da Habib ke ciki shida mama, kasancewar tint ce ya saka basu gane Iman din bace a ciki, suna shigowa layin su Habib ya sake kallon motar yace
"Ina tunanin fa Iman ce a motar nan."
"Wacce motar? " Mama tace tana waigawa, gabanta ne ya fadi ganin dalleliyar mota a bayan su,
" Ta ya akayi ka sani?"
" Number na duba. "
Ya amsa mata yana tsayawa a daidai kofar gidan, daidai lokacin motar Iman din itama ta tsaya, yayi daidai da isowar Zeenat a saman machine din Bashir. Mutuwar zaune Mama tayi ta kasa bud'e murfin motar balle ta fito, idon ta yana kan motar da ta gama gane wacece a ciki, ta saitin ta Bashir ya zagayo bayan ya faka machine din, ya leko yana cewa
" Sannu da zuwa Mama. "
Wani abu taji, ta kalle shi a kaikace kamar ta falla masa mari, tayi dauriya ta danne zuciyar ta ta amsa tana jan kofar ganin yana kokarin bud'e mata, matsa wa yayi ta fito idon ta akan Zeenat da tayi wani irin haske, hasken da tana kallon ta, ta gane na menene, kamar wadda aka sage wa guiwa haka ya shiga jan kafarta zuwa cikin gidan, suka rufa mata baya a jere Iman din na magana da Zeenat da take ta kokarin maida hawayen da take jin zasu zubo mata wanda bata san dalilin su ba
"Ashe zaki zo?" Tace a sanyaye
"Wallahi, ya gida? Ko waya bamuyi ba."
"Wayata ta lalace ne. "
" Ayya." Kawai tace suka karasa ciki, nan da nan mutanen dake harabar gidan sukayi kan Iman, kowa so yake ya ganta, duk sun rude babu wanda yabi ta kan Zeenat, ganin haka yasa ta sulale ta gudu bangaren su, ta samu Mama a zaune tana kuka wiwi, kukan bakin ciki, kukan dana sani da aka ce keya ce wadda bata da amfani, ta tuna watarana da aka zo akayi sallama da Iman, ranar ce ta farko da aka fara zuwa kuma wajen Iman din, tun basu kai yanzu ba, da kanta ta saka Hijab ta koreshi irin korar wulakanci, ba tare da kowa ya sani ba sai Habib, wanda bayan ta kore shi ne Habib yake gaya mata waye shi, da kuma gidan da ya fito,. Tun daga lokacin ta dauki alwashin dakushe Iman din, ta kara maida ita mara yanci cikin rashin sanin cewa gata tayi mata, babu in da zata shiga rayuwa ta bata wahala musaman irin abubuwan da suka shafi kula da gida.
Taba ta Zeenat tayi ganin sai sallama take amma bata amsa ba, firgigit tayi tana dawowa tunanin ta, suka rungume juna Zeenat din ta fashe da kuka, bata hanata ba, sai da tayi me isar ta dan tasan kukan zai rage mata abinda take ji, gwara ace kishiyar uwa ke gallaza maka akan ace kishiyar ka ce zata hanaka sakat da sukuni, abinda tayi ne ya juyo kanta amma ta siga ta daban, sigar da bata taba tunani ko tsammani ba.
Yan uwan Abba ne suka biyo Zeenat din har cikin gidan nasu, da mitar me ya faru zata shigo ta wuce su babu ko gaisuwa, Mama na jinsu bata ce komai ba, dan tasan da biyu suka zo maganar, tana jin Zeenat din tace suyi hakuri, wanda ya saka su jin nauyi da kunya kuma, suka tafi cike da borin kunya.
Suna fita Iman ta shigo, ta russuna har k'asa ta gaida Mama kamar yadda ta saba, ko ba komai ita a uwa take kallon ta, dan itace tayi mata komai na mahaifiya idan aka cire shekarun haihiwa zuwa yaye, ita ta sani, ko ma menene dai tayi mata wani abu.
A chunkushe ta amsa, har yanzu akwai haushin Iman din a zuciyar ta, wanda bata jin zata daina sai ko ranar da ta bar duniya, har gobe tana kallon Iman din ta tuna cin amanar da akayi mata, wanda take ganin da gaske Itace baa kyautawa ba.
Ta dan zauna a bangaren nasu, babu me magana a cikin su, sai jefi jefi da suke magana tsakanin ta da Zeenat wadda take cike da mamakin sauyawarta, tayi sanyi sosai kamar ba ita ba, ta kuma hangi wani abu a idon ta, da take da yakinin damuwa ce. Tashi Mama tayi ta barsu a falon tayi shigewarta daki, domin ta samu damar yin tunanin abinda ya kamata tayi akan auran Zeenat din.
Bin ta Zeenat tayi, ganin haka ya saka Iman ficewa ta koma bangaren Gaji in da anan me jegon take, ta shiga yan uwa aka cigaba da kuranta ta da yaba ta, kowa yana so ya samu ya kafa kansa ganin cewa yanzu ta wuce duk wani matsayi ta kai in da basu taba tunani ba, shiyasa kowa yake kokarin chusa kansa dan idan wata dama ta taso ko da ta aikin Hajji ne, toh Iman din zata tuna da mutum.
Wajen azahar sai ga Yaya Maryam tazo, sai da ta biya ta asibitin da take ANC sannan ta tawo shine dalilin rashin zuwan nata da wuri. Jan Iman tayi suka koma gidan su, suka zauna su isu matasa aka hau hirar aure da yadda rayuwar auren take ma baki daya, sosai Iman take daukar haske, tana karuwa da wasu abubuwan tunda sun fita jimawa, bata saka musu baki ba, a tunanin Yaya Maryam ma bata jin su, nan kuwa ta haddace komai akanta.
***Tare suka shigo da Musaddik, wanda kallo daya zaka yi musu kasan a gajiye suke sosai, babu wanda yayi magana sai da suka huta sannan ne Musaddik ya mika masa wayar sa da ake ta faman kira tun suna hanya, karba yayi ya daga yana kishingid'a a saman kujerar
"Ya akayi? Kun duba yadda abun ya samu kansa a cikin part din?"
"Mun duba dukka CCTV footage na gaba daya area din, bamu ga kowa ba a kusa da wajen ma, har zuwa kofar shiga shashen, falon kuma babu CCTV kasan, time da za'a saka kace baka so. "
" Na sani, shikenan ba damuwa. "
Yace yana zare wayar daga kunnen sa, ya ajiye yana murmushi wanda ya saka Musaddik kallon shi
" Akwai wanda yake so yayi wasa da hankali na, ko ma waye yasan babu cameras a ciki, target din su iya na wajen ne kawai. "
" Me kake tunani? "
" I can't say exactly, amma dai akwai wani abun daban ba sarauta ba, ko ma waye yana da matsala da aure na, ba sarauta ba. "
" Laila fa? "
" Ba ita bace. "
" Toh me zasuyi benefiting anan, ban gane komai ba. "
" Guy, baka san wanne irin mutane ne suke zagaye da gidan nan ba, da kuma kudurin kowa, zaka sha mamaki amma. "
"Ka sansu? "
" Almost.. "
" Then why are you allowing them to walk over you? Bayan kana da duk damar da zaka yi musu abinda zakayi to get rid of them. "
" Ba zai yiwu ba, this is not a military war, wannan fad'an ba ma makami bane, ko na gwajin kwanji ba, sai ka zama very very careful da duk moves dinka, akwai bakin ciki a gidan sarauta, akwai kyashi, da hassada. Masu son kujerar ba mutane bane yan kad'an, suna da yawa kuma kowa zai iya komai domin ganin ya samu abinda yake so"
Gid'a kai Musaddik yayi yace
" It's harder than i thought. "
Murmushi Moh yayi, ya hade hannuwan sa waje daya, suka fitar da sauti me dan kara, ya mike yana zuba hannayen sa cikin aljihun sa
"Muje naga Takawa."
"Owk." Yace ya mike suka fita
***Be samu ganin Takawar ba kamar yadda ya saka rai, ya zauna zaman jiran sa dan yana so ya nema masa alfarma akan tafiyar da za'a yi akan wani aiki gashi har da sunan sa, baya son yayi nisa da gida dan a kalla zasuyi wata guda cif, yasan idan ya samu Takawar ya kira waya za'a iya cire sunan sa, duk da tun daga last yace ya daina nema masa alfarma, tun da shi yaji ya gani dole ne yabi dokar aiki, sai gashi ya dawo yanzu be kuma san yadda zata kaya musu ba, shi kansa kunyar neman alfarmar yake amma kuma baya son tafiya ya bar Iman ita kadai bata gama sanin komai ba.
Har sukayi la'asar suka dawo Takawan be dawo ba, cigaba da zaman jiran sa sukayi Muhammad har da dan baccin sa,ya bar Musaddik yana kallo dan dama shi mayen kallo ne. Sai goshin Magriba sannan suka ji dawowar sa, alwala suka daura suka fita zuwa masallaci aka yi sallah,.
Yadda ya dawo da irin wannan lokacin dama babu wani zama da zai kara direct ya wuce gida dan yana bukatar ya huta sosai.
Shawara sukayi akan kawai su dawo gobe da wuri kafin ya fito zaman fada. Da wannan shawarar sukayi amfani suka tafi, suka wuce kai tsaye gidan su Iman daukota. A ransa ya kuduri zai kaita ya nuna mata dakin da ya zauna har ya kwana aciki saboda ita!
***Akwai Yayar su Abba da take turai tare da iyalin ta, sukan dade basu zo ba yawanci sai dai waya suke yi, akwai dan ta Mahfuz zai yi sa'an su Habib ko ya dan d'ara su da kadan, duk ciki shine me zumunci me son dangin sa, tun da ya girma idan ya samu lokaci ya kan zo yayi wata biyu ko daya ya koma, karshen zuwan da yayi ya jima sosai be dawo ba, sai wannan lokacin da yazo. Yaso ya samu bikin da aka ce masa za'a yi, duk da ba wani sanin su yayi ba saboda yawansu sai kuma aka samu yar matsala da ta dakatar da zuwan sai yanzu. Yana da wasa sosai da sakin fuska , abu daya yake hada shi da kowa shine yadda dabi'un sa da al'adun sa suka sha banban da na Malam bahaushe, gashi dama bahaushe ko yaya ka kuskure wajen al'ada wadda ba irin tasa ba be kuma karbe ta ba,toh fa zaka samu matsala dashi. Hakan ce ta kasance ga Mahfuz, yadda yake mu'amular sa tasha banban da tamu, dole ne za'a ga banbanci wanda shi tsakann sa har ga Allah ba da wani abu yake ba
Tun da ya shigo falon ya dora idon sa akan Iman ya kasa daukewa, be kawo matar aure bace sam, gefen ta yaje ya zauna daf har sai data dan matsa, suka gaishe shi dukka ya amsa idon sa na kanta.
"You are beautiful." Yace mata kan sa tsaye, gabanta ne ya fadi, ta kalli Yaya Maryam ta kalli sauran yan dakin, sai kawai ta mike tana tattare jakar ta.
"Bari naje wajen Gaji kafin ya zo."
Bata jira amsar su ba tayi gaba, ya tashi da sauri ya bi bayanta ya jera da ita yana yi mata surutu, da hausar sa da ba wani ganewa take ba, tana shiga part din Gajin text din Moh ya shigo wayarta,
"Muna waje." Yace a text din kawai, sallama tayi wa Gaji kawai dan kuma babu zama, ta juya zuwa nasu gidan ta tarar da Zeenat a zaune tana cin tuwo, nan ma tayi wa Maman sallama tace ta gaida gida. Fitowa tayi rik'e da hannun Marwan, ta koma wajen su Yaya Maryam tayi musu sallama, suka firfita zasu rakata, anan suke ganin ana sauke kayan abinci a irin motar da Iman din ta gani dazu a gida, ranta ne ya bata lallai aikin sa ne, tana jin su Maryam suna maganar sai dai idan shine ya aiko dan cikin surukan gidan babu wanda zai aiko da kayan abinci haka masu yawa. Har gate suka rakata sannan suka juyo, Mahfuz na ganin zata bita ya tashi ya sake bin ta suka rankaya zuwa waje, kamar tace masa ya koma amma sai ta kasa tana jin nauyin sa. Tun da suka fito idon Moh akan su, ya gama tabbatar da ba Habib bane, ba kuma Khalil bane dan ba zai kara gangancin da yayi a baya ba. Ransa ne ya baci, ganin yadda suke jerawa yana mata magana da yanayin yadda yake maganar. K'asa hakuri yayi, ya balle murfin motar ya fito daidai lokacin da Mahfuz yake kokarin kai hannu ya bud'e mata kofa, gashi yayi kusa da ita sosai.
"Dalla malam baka da hankali ne?" Ya daka masa tsawar da ta saka Iman sakin yar jakar hannun ta, tsayawa Mahfuz yayi yana kallon sa yace
"Pardon?"
Wani banzan kallo yayi masa, ya zagayo ya kama hannun ta, ya jata zuwa dayan side din motar ya turata ciki, be lura ba sai data bigi ya rufe kofar da karfin sannan ya dawo wajen Mahfuz din dake tsaye rik'e da jakar Iman din da ta fadi cikin mamakin abinda ya harzuka gayen.
"Wannan shine last warning dinka akan matata, ko waye kai komai alakar ka da ita, kar na sake ganin ka haka kusa da ita, idan ba haka ba wallahi sai na balla kafarka, nonsense."
Be jira abinda zai ce ba, ya bud'e motar a fusace ya shiga ya rufo, Musaddik dake gaba ya juyo zai magana yaga yanayin sa, sai kawai yayi shiru, yace ma driver ya ja, jan motar yayi suka bar wajen.
_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D'aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/14/22, 19:05 - Buhainat: Halin Girma
34
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
*******�?
Tun da suka dauki hanya babu wani wanda yayi magana a cikin su, ransa a bace yake matuka. Manne da jikin kofar take, cike da mamakin dalilin fushin sa haka, a kalla ya tsaya ya fuskanci abinda yake faruwa kafin ya yanke hukunci haka, abun ma dariya ya so bata, yadda ya jata zuwa cikin motar, lallai da gaske sojoji akwai su da temper, idan ba haka ba, menene abun tashin