Showing 75001 words to 78000 words out of 115235 words
Chapter 26 - Halin Girma Hausa Novel Complete
ciki?"
" Wai hakuri? Wallahi ban ba,kinsan yadda nake son Capt tun muna school haka shima kinsan kaunar da yake min ba kad'an bace, ba zan iya rayuwa da kowa ba sai shi, bayan haka kinsan matsala ta da Dr. Bryan Ford."
" Haka ne, toh shikenan yanzu menene next move dinki?"
" Har yanxu ban dawo daidai ba, I need time to recover nasan me zanyi."
" Shikenan, duk abinda zakiyi dai kiyi informing dina, zan baki shawara yadda ya kamata."
" I know I can count on you, Nagode Bestie!"
"DM!"
Tayi murmushi yana relaxing sosai akan kujerar, tana tunanin yadda zatayi amfani da Laila ta samu cikar burin ta!
Sai wajen tara sannan suka tafi, bayan Maman sun gama zantawa da Ammi, babbar aminiyar ta ce sama da kowa a kaf adamawa dan da ita ta fara sabawa lokacin da aure ya kawota, sannan yaransu ma tare suka taso ita tana da yara biyar compared to Ammi da take da guda daya tal...
Zuciyar ta fari kal sanda suka isa gida, ta san ko babu komai zata dinga samun duk information din da take so ta bakin Laila, tunda tayi masifar yarda da ita fiye da yadda ma ta yarda da uwarta mahaifiya. Bata da kirki ko kad'an idan har ka shiga gonar ta, amma kuma tana masifar ganin mutuncin Samha din, dan itace tafi mata kowa a yanzu, gani take ma babu me kaunar ta sai Samha din kawai. Ko Kilishi ta san ta Kamal kawai take yi ba tata ba, shiyasa itama bata wani sanar da ita idan zatayi abu sai dai daga baya, daga Samha sai amintacciyar hadimar ta guda daya wadda zata iya bada ranta fansa ga Laila din saboda tsabar biyayyar da take mata.
Wurgi tayi da tarkacen da ta debo daga mota tayi a saman gadon ta, ta kwanta tana kallon sama ba tare da ta cire dogon takalmin kafarta ba, murmushi take ita kadai duk kuwa da abinda Muhammad din yayi ya bakanta mata rai, amma kuma ta raina yarinyar da ya kira ta da matarsa, a shekaru ba wata babba bace haka ma wayewar rayuwar duniya sam bata cikin sahun amma kuma tana da nutsuwa a yanayin ta, da kuma iya handling abu dan yadda tayi da taji da wanda take waya ya matukar bata mamaki, kamar bata fahimci komai ba bayan sarai ta gane, kuma bata ko bi takanta ba ,ko ta tuhume shi ko ta chanja masa fuska sanda ya shigo, sai ma ta tarbi mijinta da fara'ar da ta mantar dashi komai da kowa.
Tashi tayi tsaye ta soma zagaye a tsakanin dakin tana jin kamar taje ta jawo ta da karfin gaske ta fidda ta daga gidan, duk yadda suka kai da wayewa amma ya tsallake su ya dauko wadda bata kai ko rabin ajin sa ba, adah Laila kawai take jin haushi amma yanzu na Laila ya daina damunta, dan tasan babu wani abu da zatayi sai da sanin ta, yarinya karama ce yanzu take neman zame mata ciwon ido.
***Suna shiga part dinsu tun daga kofa ya daga ta sama, ta saki siririn ihu tana kankame shi, da gaske taji tsoro dan bata yi tunani ba, sai ji tayi anyi sama da ita, kin ajiyeta yayi sai da ya kai karshen falon sannan ya zaunar da ita ya bita ya zauna a gefenta yana dariya
"Kin fiyaa tsoro Allah!"
"Ai it was unexpected shiyasa."
"Ba wani, tsoro dai kawai, ki yarda, you have to be strong, kinsan dai ance a wife of a soldier is a soldier!"
" Wasa suke suma wallahi." Ta saka dariya
" Haka dai aka ce." Yayi dariyar shima
"Yawwa... Dazu na gani a WhatsApp wai anyi calling off strike?"
" I can't say, bari na kira naji, amma zaki koma ne? Ko a samu wata school din daban?"
" Duk yadda akayi yayi."
" Owk toh bari naji." Yace yana ciro wayar sa daga aljihu, yayi dialing number wani lecturer abokin sa, suka gaisa sannan ya tambaye shi, baa gama daidaitawa ba amma dai akwai yiwuwar komawar nan kusa. Ajiye wayar yayi ya fad'a mata yadda sukayi
"Matsalar k'asar nan kenan, yanzu fisabilillahi fiye da 9month ana strike amma gwamnati tayi shiru? Shikenan karatun yara ya lalace akan wani dalili mara tushe, it's so unfortunate gaskiya."
"Wallahi har sai mutum ma ya gaji da zaman, babu dadi sam."
"Dole ai, Allah ya kyauta."
"Amin." Tace sai sukaayi shiru, chan kuma yace
"Bari muga idan basu daidaita ba, kawai sai mu chanja ko Base ne, ko kuma wata private uni din na Kano."
"Owk Allah ya zaba mana mafi alkhairi."
" Amin Matata!"
*** Tare suka shiga ciki bayan sun kammala duk abinda ya kamata su kammala a falon, zama yayi ya kunna system ya shiga aiki ita kuma ta wuce toilet dan ta watsa ruwa tazo ta kwanta. Sharp sharp tayi wankan ta fito sanye da rigar da ta cire , be kalle ta ba, har ta isa gaban wardrobe ta dauki wata mara nauyi iyakar ta kasan guiwa, dan duk sauran kayan da take dasu anan ba zata iya kwanciya dasu ba, idan ma ta saka tasan shi, zai iya yin karfa karfa ya hanata yayi amfani da damar yayi mata wayo. A gajiye take jin ta yau din ba wai don tayi wani aiki ba, bata san dalili ba gaba daya jikin ta ciwo yake mata, wankan da tayi take saka ran zai dan saka taji dama-dama.
Kallon ta yayi bayan ta sako rigar, yayi mata alamar tazo, ta taho ta zauna agefen sa, ya cigaba da aikin da yake na hada kan wasu takardu masu muhimmanci sosai, yana lura da ita yadda jikinta yayi sanyi sosai, jawo ta yayi bayan ya dan matsar da system din, ya kwantar da kanta a jikin shi
"Goodnight sweet dreams." Ya rankwafo yayi mata peck a kunci, lumshe idon ta tayi bacci na cin karfin ta sosai. Be san iya adadin awoyin da ya dauka a wajen ba, ya dade sosai har sai da ya fara jin bishi-bishi, sannan ya rufe system din, ya gyarata a hankali sannan ya tashi yana mika, alwala yayi yazo yayi sallah raka'ah biyu, ya lura da ko shafa'i da wutri da ta saba yau bata yi ba, be san wanne irin bacci take ji haka ba, dan har ya gama aikin sa ya tashi ko motsawa batayi ba. Taimaka mata yayi zuwa gadon ya kwantar da ita ya lullube mata iya kafarta, sannan ya kwanta bayan ya rage kayan jikin sa ya rage daga shi sai boxer kawai.
Cikin dare sosai taji ishirwa, irin wadda bata taba jin irin ta ba, tashi tayi ta lallaba ta fito bayan ta duba fridge din dakin ta tuna babu ruwa a ciki, ta manta kuma bata kawo ba dan bata bar kowa cikin masu aikin sun taba shigar mata dakin ba, iyakar su falo shima dan babu yadda zatayi ne amma ko yaushe suna BQ sai wani abu me muhimmanci sannan take kiran su.
A kitchen ta samu ruwan, tasha sannan ta dauko karamin katan na ruwan ta taho dashi. Falon yayi dim amma kuma akwai dan haske kadan da ya hasko ta corridor din kitchen da yake a kunne, kafarta take sawa a hankali tana tafiyar har ta kai tsakiyar falon, da yake falo ne katon gaske da sai kayi tafiya tsakanin kitchen da corridor din bedrooms din, motsi taji kad'an kad'an, tana matsowa yana karuwa har ta kusa kai wa corridor din abinda ta gani a wajen ya sakata daskarewa a wajen. Chak ta tsaya ta kwalla wata irin kara da ta tashi Moh daga bacci, ya mike a firgice yana kiran sunan ta, sai kuma yayi hanyar fita daga dakin da sassarfa kirjin sa na bugawa da karfi!
BIYAN BASHI ⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️😂😂😂😂😂
2/7/22, 19:06 - Buhainat: Halin Girma
30
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
******* �?
A durkushe ya ganta tana kuka ta rik'e kanta, saurin durkusawa yayi a gabanta yana janye hannun nata
"Menene?"
"Miciji!"
Tayi maganar tana nuna masa wajen, saurin kalla yayi amma be ga komai ba, ya yunkura zai tashi ta kankame shi sosai tana fashewa da kuka. Hannun ta ya kama zuwa wajen switch din falon, ya kunna haske ya bayyana a ilahirin falon, wurwurga idonsa ya dinga yi a gaba dayan falon amma be ga komai ba,
"Aina kika ganshi?"
"Adaidai nan zai shiga dakin chan!"
"Tsaya ." Ya tsaida ita yana sake dubawa amma babu komai. Riketa yayi ya kaita daki, tayi saurin rikeshi ganin zai fita
" Dan Allah karka fita ka barni."
" Kinaji? Calm down babu abinda zai faru, yanzu zan dawo.".
Sakin sa tayi, ya fita ya taso securities din a gaba, suka zo suka hau bincika falon da ko ina na part din,ciki ya koma ya sameta ta kudundune a saman gadon still jikinta be bar rawar da yake ba, tana addu'a kasa kasa, daga gani kasan ta tsorata sosai dan bata taba ganin shi haka a zahiri ba. Jawota yayi jikin sa, ya mannata da kirjinsa yana shafa mata baya kad'an kad'an.
" Babu abinda zai faru kinji? Ki kwantar da hankalin ki."
Da kai ta amsa masa, zuwa lokacin ta fara dawowa nutsuwar ta, sai wani uban juyi da taji cikin ta nayi,ta dora hannun ta a saman cikin yana yatsine fuska, kallon hannun nata yayi, ya dauki nasa ya dora a saman nata yana tayata shafa cikin,
"Ciwo?"
"Eh."
"Sannu zai daina, bari na dubo ko sun gama dubawar."
Ya kwantar da ita ya fita, a tsaye ya same su rik'e da abu me kama da maciji, matsawa yayi yana dubawa cikin son karin bayani
"Macijin roba ne ranka ya dade!"
"Roba?" Yace cikin yanayin mamaki
"Me ya kawo shi nan? Me yasa bamu ganshi ba tun da rana sai yanzu..."
"Waye da waye suka shigo part din nan?" Ya fad'a yana daure fuskarsa tamau. Rantse rantse suka hau yi, kowa na son kare kansa, wata uwar tsawa ya daka musu, duk suka nutsu suka kame suna masu saukar da kansu k'asa
"Kwana daya tal na baku, ku gano wanda ya shigo part din nan har ya ajiye wannan shirmen, koma waye sai ya fuskanci hukunci me tsanani!"
" Yes sir!"
Har ya juya sai kuma ya tsaya.
" Get ready, we are leaving tomorrow in the afternoon!"
" Yes sir!"
Suka kara hada baki wajen fad'a sannan ya juya ya bar su a wajen da sassarfa. Dayan dakin ya shiga, ya hau bincike wasu kaya da sauri da sauri, ba zai yarda a taba masa ita ba, idan har ba zasu iya tsayawa iya kansa kawai ba, toh zai yi abinda zai girgiza su matuka. Ya dan dau lokaci a dakin, sai da ya tuna ya barta ita kadai ya kuma san tsoro take ji, sannan ya koma da sauri, ya tarar bacci ya dauke ta, ta takure waje daya tana fitar da numfashi kad'an kad'an. AC din dakin ya rage, zuwa low ya dawo ya gyara mata kwanciyar, ya kura mata ido yana jin son ta na kara ruruwa a zuciyar sa, ba zai bari banzar al'adar gidan su ta taba ta ba, zai yi duk abinda zai yaga ya kareta da dukkan karfin da yake dashi.
Da asubah ya tashe ta, sukayi sallah a dakin, sannan ya fita ya shigo mata da micijin robar yana mata dariya
"Matsoraciya, nina fa na shigo dashi jiya by mistake, abun wasan yaran chan ne suka bani, ashe sai na yar dashi ban ma lura ba."
Shiru tayi tana kokarin daidaita maganganun nasa da abinda ta gani, idan har ba gizo idon ta yayi mata ba, toh tabbas tafiya ta ganshi yana yi, har ya kai kofar dakin kafin ta daina ganin sa.
"Common!" Yace yana son dauke tunanin ta
"Babu komai fa I promise you."
"Amma na ganshi fa yana motsi!"
"Imagination ne kawai nothing else, karki damu ki kwantar da hankalin ki."
Shiru tayi tana kallon sa, yanayin sa yayi mata kama da na wanda yake so ya dauke hankalin ta, amma idan ba haka ba babu yadda za'a yi taga abu yana tafiya da idonta ya zama imagination kuma, hore mata idon yayi yana jawo ta jikinsa
"Karki yi ta tunani kinji? Anjima zamu wuce ma, Abuja zamu fara zuwa na gaida Mummy, daga nan muyi tafiyar mu gidan mu mu sha soyayyar mu."
"Da gaske?"
"Da gaske mana, are you happy?"
"Naji dadi sosai, bari na fara hada kaya na, da wuri zamu tafi ko? Ko sai da yamma."
"Yamma!"
Komawa tayi ta zauna tana jin kamar yamman ya mata tsayi
"Zanga Aji ne, sannan bana son kowa yasan mun tafi sai Ammi kawai, shiyasa ba zamu dauki yaran chan ba, i mean ma'aikatan gidan, akwai screening da za'a yi musu kafin su biyo mu."
" Owk Allah ya kaimu."
" Amin my beautiful wife."
Murmushi tayi, ya dauko musu al'qurani me girma suka shiga karantawa, ya dinga admiring muryarta da yadda take bawa kowanne harafi hakkin sa, cikin nutsuwa da fitar da tajweed a duk in da ya dace. Sai da rana ta fito, sannan sukayi wanka, suka shirya a tare suka fita don karyawa, bud'e warmers din yayi, ya kakkala sannan ya saka aka kwashe masa su daga wajen, ya aika part din Ammi aka karbo musu breakfast din, taso ya barta tayi amma ya hanata, ya kuma ki gaya mata dalilin da ya saka shi sawa a kwashe abincin da aka girka a part din, bata ce komai ba, ta barshi a zuwan kawai zata ji koma menene daga baya, dan ta lura yadda ya boye masa kanta kafin aure akwai abubuwa da yawa da yake boyewa a yanzu ma, duk da haka ba zata zarge shi ba, zata bashi lokaci sosai ta kara fahimtar shi, jikinta na bata akwai wani abu da shi kadai ya sani, sai ko Aji da take ganin kusancin su yafi na kowa hatta mahaifiyar sa da mahaifin sa.
Bayan sun gama breakfast din ne ya fita, cikin shigar kayan sojoji da suke masifar yi masa kyau, cikin rakiyar yaransa ya nufi part din Kilishi, wanda tun kafin ya karasa sakon zuwa nasa ya ishe mata, tana zaune ta gama karyawa, tashi tayi da sauri ranta na baci, tasan zuwan sa babu abinda yake jawo mata sai bacin rai. Daki ta shiga ta chanja kaya, ta zauna tana jiran sanarwar isowar sa. Tana jin sanda ya shigo, dan har falon ta na ciki ya shigo, ya zauna fuskar sa fes dauke da farin ciki, idonsa na kan kofar da zata fito, ya dan dauki lokaci a zaune har ya fara tunanin ko ba zata fito ba, agogon hannun sa ya kalla, ya daga kai ya kalli na jikin bangon dakin, a tare suke tafiya dakiya daya, sauke idon sa yayi yana murza agogon nasa, takun tafiya yaji, yaki d'agowa amma yasan itace,sai da ta zauna sannan ya dago yana dubanta, yayi murmushi cikin salon girmamawa yace
"Barka da gida ranki ya dade."
"Barka dai, ya iyali?"
"Lafiya kalou kalou, kamar yadda kike fata a kowanne lokaci."
Yak'e tayi, tasan magana ya fad'a mata, dan ya saba gasa mata ita dama, murmushi ya sake yi yana lankwasa hannayen sa baya
" Haka ake so ai, sai a sake kula sosai."
" In Sha Allah, za'a kula kulawa me kyau, duk wani me sharri Allah zai maida masa kansa ma, saboda addu'a itace makamin mumini, kuma matakin duk wata nasara."
" Haka ne!" Tace tana gid'a kanta. Mikewa yayi cikin salo na burgewa, ya dan rankwafa yace
" Na barki lafiya!"
" Nagode!" Tace tana danne zuciyar ta, bayan sa tabi da kallo har ya fice gaba daya,
"Ahhhh!" Tayi kara tana jifa da trow pillow din dake kusa da ita,kamar ta shako shi haka taji, gashi kamar masifa yasan duk wani shirin ta, ta rasa yadda zatayi dashi ya zame mata tamkar kadangaren bakin tulu! Ya kuma zame mata ciwon ido, da za'a bata makami ace ta kashe mutum daya toh tabbas shi zata kashe, bata son ko ganin wulgawar sa.
Laila ce ta shigo, ta tarar da ita cikin halin da take ciki na bacin rai, bin ta tayi da kallo har ta dauki jakar ta, ta bud'e ta dauki ATM cards din Kilishin, ta juya zata bar dakin.
"Laila!" Tsayawa tayi ta juyo
"Ina zaki? Me kuma zakiyi da Atm dina?"
"Haba Mah, tunda har na dauka ai amfani zan dashi."
" Shine ba zaki iya fada min ba?"
" Da ma fa na saba dauka kuma bana fad'a miki, why now?" Sai ta juya ta cigaba da tafiyar ta
" Zan dawo dashi wani payment kawai zan." Sai data kai karshen kofar sannan ta fad'a, ta saka kai tayi ficewar ta, kwafa Kilishin tayi ba tare da ta sake cewa komai ba.
****Bayan fitar sa ne tana zaune da waya a hannun ta suna chatting sama-sama da Ya Maryam,rabin hankalin ta na kan Tv sai tana duba sakon lokaci zuwa lokaci, ta kira Abba bata same shi ba, kila ko ya fita ko kuma baya kusa da wayar. Kara wayarta tayi a tunanin ta Abban ne, sai taga number Ya Maryam ce, dauka tayi tana tashi zaune
"Ina ta magana a whatspp kin sauka, yanzu aka kira ni a gida Aunty Bilki ta haihu!"
" Dan Allah!"
" Wallahi yanzun nan kuwa ta haihu."
" Masha ALLAH, me aka samu?"
" Ina ma na tsaya tambaya? Murna ta saka ni kiranki, kinga al'amarin Allah, bayan ta cire rai, dama ba'a cire rai da rahmar Allah."
" Wallahi, kai Masha ALLAH, nayi murna sosai Allah ya bata lafiyar shayarwa."
" Amin ya Allah, zuwa kano ya kamaki."
" Gaskiya, dama yau zamu bar nan din, amma Abuja zamu wuce daga nan zamu dawo Kanon."
" Ah shikenan ma, ki kirata toh kafin nan, bari na kira Amira itama na fesa mata."
" Owk ki tura min number ta, Inaga kamar bani da ita yanzu."
" Ok tam, zan ajiye miki a WhatsApp."
" Yawwa."
Ajiye wayar tayi farin ciki na kamata, after all a karshe dai itama ta samu nata babyn, shekara ashirin da aure amma bata taba ko batan wata ba, sai yanzu Allah yayi, dama dai sunji kishin kishin din ciki ne da ita musamamn da bata zo bikin da akayi ba, sai mutane suka kara tabbatar da zargin su, boye labarin sukayi sun fi so kawai aji haihuwa daga sama.