Showing 78001 words to 81000 words out of 115235 words

Chapter 27 - Halin Girma Hausa Novel Complete

Duk da bata da yawan magana amma tana masifar son kananan yara, musamman jarirai zuwa 4years haka, ko magana sukayi sai taji dadi, shiyasa take son kaninta Marwan ba kuma tajin komai idan Mama ta sakata aikin sa.
   Daukar number aunty bilkin tayi, ta kirata tayi mata murna sosai, suna wayar kiran Abba ya shigo, ta katse na Aunty Bilkin ta daga nasa suka gaisa, anan yake fad'a mata labarin haihuwar ta nuna kamar bata sani ba tayi farin ciki sosai, bayan sun gama wayar ne ta kira Mamma take fad'a mata zuwan su, amma bata san ko a yau din zasu iso ba ko sai gobe dai, murna tana jiyo su Amaan ta wayar kamar zasu shigo ciki saboda karadin su.
  

***Tana idar da sallar la'asar sai gashi ya shigo, ba kayan da ya fita dasu bane a jikin sa, wasu ne daban da sukayi mata kama da sababbin da ba'a taba sakasu ba, gaishe shi tayi a ladabce tana daga kan sallayar, ya amsa yana zama, yanayin sa ya nuna a gajiye yake, sai ta tashi ta ninke sallayar ta ajiye ta nufi kitchen ta dauko masa ruwa da soft drink, akan tray ta doro ta dawo falon ta ajiye masa tana rissinawa, saurin tayata yayi yana hadawa da hannun ta da tray din, sukayi dariya a tare ta zauna a gefen sa tana zuba masa ruwan. Karba yayi yasha, sosai saboda tunda ya fita be saka komai a cikin sa ba, gashi sam baya jin yunwa so yake kawai su tafi.

"Ga abinci akan dinning ko na kawo maka nan?"

"Waye yayi?"

"Nice."

"Owk zanci, amma ki zubo min a plate ba da yawa ba, sai ki taimaka min da fruit please,."

"Ok." Ta mike bayan ta karbi cup din ruwan ta ajiye, taje ta zubo masa abincin ta kawo ta koma ta yanko fruits din ta kawo, yana kwance ya mike kafafunsa, har sai data zauna a gaban abincin sannan ya sakko yana saka spoon din a gaban sa ya soma cin abincin hankalin sa a kwance, sosai yaci dan beyi tunanin zai ci kamar haka ba, sannan ya sha fruits din kadan, bayan ya gama yace

"Thank you...Abincin yayi dadi."

Blushing tayi cikin jin dadin yabon da yayi mata, ta hau tattare kayan zata kwashe ya rik'e mata hannu

"Ki barshi yaran chan zasu gyara idan mun tafi."

"Ai ba wahala, bari na kwashe kawai."

Sakin hannun nata yayi, ta dauki tray daya, cikin takun da bata san tana dashi ba, ta shiga takawa zuwa kitchen din, kallon ta yake har ta kule kafin ya dawo hayyacin sa, yana kallo ya sake dawowa ta kwashe sauran ya sake bin steps din nata da kalllo, ba zai iya hakura ba, musamamn idan ciki ya dauka, ga kuma abunka da sabon angon da be san ya isa ba, tashi yayi har da dan saurin sa, ya sameta a kitchen din tana tattare dattin plates din, sam bata ji shigowar sa ba, sai ji tayi an rungume ta, ta baya. Ta juyo a dan tsorace kafin kamshin turaren sa ya mamaye ilahirin kitchen din.
   Manne bayan su yayi waje daya, ya dora kansa saman gadon bayanta, ya shiga goga mata bayanta da kan nasa.

"Ba... Bari... Na karasa gyara kayan."

"Barshi, ai dama ba aikinnki bane, ga aikin lada me yawa."

Ya sake chusa kansa sosai, tsam ta dauke hannun ta, sanda taji hannun sa na yawo a daidai tsakiyar cikin ta, yana shafawa har zuwa kasan rigar ta, rik'e jikin kitchen cabinet din tayi dan ji tayi kamar zata fadi, Allah yaso ta dafe wajen. Daga ta yayi sama chak, ya wuce falon zuwa bedroom dinsu, ya dire ta yana mata murmushin mugunta,  a matukar tsorace take dashi amma kuma ba zata hanashi ba, dan ba zai taba bata damar da zata hanashin, yabi ya kanainayeta da salon kaunar shi me tsayawa a makoshi!
   Sai da suka bata lokaci sosai, dan har wani dan guntun bacci yayi bayan nan, da k'yar ta tashe shi yayi wanka ya shirya, suka fita a mota zuwa wajen Ammi, daga nan suka fice daga masarautar da magribar fari!

***
Tun bayan fitar sa bata tashi daga wajen da take ba, sai da taji yunwa na neman kai ta k'asa, ta tashi ta jawo ledar da ya bari ta cinye ragowar,tasha ruwa ta kwanta a wajen.
   Har wajen takwas na dare Hajiyan bata dawo ba, turo dakin akayi, ta dago tana kallon sa, tashi tayi zaune da sauri tana kare jikin ta, murmushi yayi ya zauna a kusa da ita, ya ciro wayar sa a aljihu ya rik'e a hannun sa yace

"Zan kira miki Mama,dan ta kira tana son magana dake nace mata wayarki ce ta lalace, idan kika kuskura kika fad'a mata wani abu sai ranki ya baci."

Banzan kallo tayi masa, ta warci wayar lokacin da taji tana ringing, bata jira Maman tayi magana ba ai tana jin ta daga ta rushe da kuka,

"Lafiya Zeenat, wannan kukan fa?" Tace a kidime tana saka handsfree dan Habib yaji shima

"Mama dan Allah kice wa Abba yayi hakuri na tuba, dan Allah!"

" Ki nutsu ki fad'a min abinda yake faruwa, menene?"

" Bana son auren nan Mama, dan Allah kizo ki tafi dani wallahi zan mutu!"

" Mutuwa? Me yayi miki Bashir din?"

Shiru tayi ta rasa me zata ce, dan bata isa ta fadi abinda ya faru tsakanin ta da Bashir din ba, a sanyaye tace

" Mama yana da Mata, kullum sai ta sakani aikin wahala babu dare babu rana, ga tsangwama, karshe ma Mama a BQ nake wallahi." Sai ta sake fashewa da wani kukan,salati Mama ta saka, ta kama zagaye a dakin tana jin bayanin Zeenat din

" Yana ina, bashi wayar."

Tun kafin ta bashi ya karba yana mata murmushi,

" Hello Mama."

" Kana ji? Wallahi tun muna shaida juna da kai ka dawo min da 'yata, wannan ai wulakanci ne, wallahi ka dawo min da ita kafin kasha mamaki na."

" Kiyi hakuri Mama, amma Zeenat matata ce,a yanzu nine nake da iko da ita,dan haka kiyi hakuri dai."

" Kan bala'i, ni kake fadawa haka Bashir?"

" Ayi hakuri Mama, gaskiya ce, sai mun sake kira mu gaishe ki."

Kafin ta sake magana ya kashe kiran, ya kuma kashe wayar gaba daya ya jefa ta aljihun sa, yayi gaba zai bar dakin ta chakumo shi ta baya

" Na rantse da Allah sai ka rabu dani,sai ka sake ni wallahi ba zan zauna ba, na tsane ka bana son ganin ka."

Maganganun ta sun masa zafi kwarai, amma sai ya danne ya jawota ya hadata da bangon dakin, ya dalle mata baki sannan ya bi ta da kiss me zafi.

"Idan kika sake yi min ihu wallahi sai nayi fata-fata dake, aure na dake babu saki ko yaji, auren mutukaraba kenan, ko nace miki auren zobe, idan bakiyi wasa ba sai na tabbatar miki da haka a yau din nan, ta hanyar zuba miki ajiyar da baki isa ki guje min ba."

Tofar da yawu tayi ta durkushe a wajen tana sakin kuka gwanin tausayi. Tsallake ta yayi, yayi ficewar sa yana dariyar mugunta, yana son Zeenat din da gaske, amma kuma ba zai dauki rashin kunyar ta ba, ko kuma ya kyale iyayenta su taka shi ba, sai abinda yaga dama zai yi da ita tun da dai shine me iko da ita a yanzu.


_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D'aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107
2/8/22, 07:39 - Buhainat: Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb


_________________________


31

    ×××Ya fada a can 'kasan zuciya yana yamutsa fuskar sa. Yanayin yadda ya yamutsa fuskar tasa ne hakan yasa Zaraah sake matse tata fuskar. Ta wulkita idanu ta dankara masa harara. Hade da kokarin bude murfin motar cikin fushi da takaicin sa.

Ledar ya dora mata akan cinya. Tare da sake rufe murfin motar .

"Budemun. "Ta fada a hankali.

Hade da kaudar da fuskar ta zuwa kan murfin motar. Don sam batason kallon fuskar Maheer. Domin tamkar sudeis yayi kaki ya tofar. Saboda tsananin kamar da suke.

"Tsiwar ki ta bude miki" Ya fada cikin muryar umarni . Ya kuma bata rai don karta dauka da wasa yake.

‘Kunkuni ta fara yi ahankali . Maheer ya saki siririn tsaki,

“Dauka ledan ki fita. Kuma this should be the very last time da zaki tsallake dokata kinji na gaya miki.�?

Ya karasa ransa a matukar bace . Cikin zuciyar sa na masa zugi.

“Toh ina ruwanka da rayuwata.�?

“Ni kike gayawa haka?�? Yana kokarin jefa mata wani kallo mai dauke da kalamai.

“Ni dai ka budemun na fita…�?
Ta karasa fada tamkar zatayi kuka.

. Hade da sake kiciniyar bude murfin motar. Hannun sa d’aya ya dora akan nata da zummar hanata kokarin fitar da take.

Wani Irin electric shock ne ya ziyarce ilahirin jikin su da kwakwalen su. Da sauri ya janye itama ta dauke nata hannun.

“Dauki kayan ki fita . Kuma su zaki dinga amfani dasu wajen fita unguwa da sauran su. Kar ki kuskura ki kawo wani abun a zuciar ki. Amanar da dan uwana ya bani nake zartarwa.�? Ya karasa hade da jan kasan leben sa ahankali .

Lock din ya cire, Ta fice da sauri har tana tuntube. Ya sauke zuciya kawai hade da girgiza kai. Ya ja motar zuwa bangaren sa.

Ya sha mamaki kwarai matuka wajen ganin masu aikin gidah nata rushe rushen bangaren nasa ana sake kawata shi.

Zai yi magana kenan sai ga fitowar Addayo daga ciki. Fuskar ta kumshe da murmushi. Gayar da ita Maheer yayi ya na mata kallon karin bayani game da gyaren bangaren nasa.

“Addayo�?

“Na’am na ikko dan albarka. Kaga bangaren ka ya fara sauyawa ko?�?

Ya daga kai alamar eh hade da susar keyar sa.

“Toh me zaa jira, Aure an rigada an daura, Sai tariya kadai ta rage. Ina ita kishiyar tawa ne.�?

“Ta shiga sashen su.�?

“Yauwa inason ganin ku an jima da yardar Allah.�?

“Tohm Addayo! Saukar yaushe?�?

“Tun dazu fa nazo. Dan na tsaya gidan Harisu ne.�?

“Okay Masha Allahu.�?

“Allah ya maka albarka, Allah ya jikan mahaifan ku da dan uwanka.�?
Ta karasa fada tana mai goge hawayen dake tsiyaya a idanunta


“Aaamen Addayo�? Ya bata amsa yana runtse idanun sa.

“Muje bangare na nan aka mayar maka da kayan ka kafin a kammala nan din.�?

“Toh Addayo.�?

Tana gaba da yar sandar da take dogarawa, Shi kuma Maheer yana biye da ita a baya yana tunanin yadda zasu kwashe da Zaraah idan suka tare. Dubada ganin su duka biyun ba kaunar junan su suke ba. Gwara gwara ma shi yakan ‘daga mata kafa awasu abubuwan saboda amanar ta da Sudeis ya bashi.

••�?. ••�?.

Tana shigewa parlorn nasu bakinta dauke da sallama ta ajiye ledar hannunta akan kujera. Hadi da kwaye hijabin dake jikin ta, Ta ajiye a kusa da ita.

Dadaa dake daki tafito tana jijjiga baby sudeis daya tashi a bacci.

“Dadaa barka da yammaci.�?

“Barkan mu..�?

“Love of my life�? Zo nan.�? Ta karbu baby sudeis a hannun ta tana kallon sa. Har cikin bargon jikinta take kaunar baby Sudeis. Idan ta dauke shi ji take nutsuwa da kwanciyar hankali ta dabaibayeta.

Dadaa na hankalce da ita, Ta zauna akan kujera hade da janyo ledar da Zaraah ta ajiye.

“Wannan kayan fa?�?

“Yaya Maheer ne ya sayo�?

“Na waye?�? Dadaa ta tanbayeta tana dudduba hijaban da su safa hadi da sabuwar wayar.

“Wai nawa ne�? ta karasa cikin kasa da murya.

“Yauwa zo ki zauna anan Zaraah. Ki bani hankalin ki da nutsuwar ki. Abunda zan gaya miki abune mai muhimmanci a rayuwar ki. Kinga saura kwanaki kalilan ku fara jarabawar kare makaranta ko? Dan haka inaso kafin lokacin ki samu nutsuwa ki kuma sa aranki hukuncin da aka zartar akan ki shine mafificin alkhairi agare ki.�?

“Tohm Dadaa. �? Ta fada, Hadi da zama a gefen kujera . Tuni hawaye suka shiga reto a idanun ta.

“Allah yasa ba laifi nayi ba Dadaa da aka yankemun hukunci�?

“Aa wallahi ko d’aya! Hasalima nina bada hadin kai wajen yanke hukuncin. Illa dai kiyi hak’uri na rashin neman yarjewar ki da bamu yi ba. Kina sauraro ko?�?

“Toh Dadaa. Ina ji�?

“Ba wani abu bane fyace daurin auren ku da akayi da Maheer. Maheer dai yayan Sudeis marigayi…�?

Dadaa na karasa fada, Maheer ya doka sallama ya shiga parlorn. Don sanarwa Zaraahn nema su da Addayo take�?

Zaraah ta daga idanunta da suke zama tamkar garwashi saboda tsananin yadda suka rine sukayi ja. Ta sauke akan Maheer. Hawaye d’aya na bin d’aya suka shiga kwarara a fuskar ta.


Unedited
Sorry for the late post
Thank you ❤️❤️



*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar


XOXOWRITES🤩
2/9/22, 20:30 - Buhainat: Halin Girma
      31

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

******* �?

Lokacin da suka isa Abuja dare yayi dan basu suka bar Yola ba sai wajen karfe takwas na dare, sun dan samu delay ne shiyasa, direct Hotel suka nufa ta dinga masa magiya akan ya kaita gida amma fafur yaki, yayi mata kunnen uwar shegu har suka huta bata bar mitar ba, yi yayi kamar be ji ta ba, shima akwai gidan Bubu da suke sauka duk sanda suka zo ko shi yazo kawai akwai dalilin sa na zuwa nan din. Waya taga yana ta faman yi, da mutane daban daban duk akan maganar zuwan nasu, sai da ya gama tas wajen takwas da rabi sannan ya tashi ya nufi kofa ya bud'e, ya karbi sakon ya rufe ya dawo yana ajiye ledar a saman makeken gadon hotel din.

"Tashi ki shirya akwai dinner da Chief of Army Staff, da sauran manyan soldiers na k'asa, a madadin wanchan event din kawai aka hada wannan dinner din kowa da family nasa."

" Owk." Tace tana mikawa, ya nuna maya ledar da hannu yana shigewa toilet. Daukar ledar tayi me dauke da tambarin wani babban Mall, ta bud'e doguwar riga Abaya ta gani me kyau, ciro ta tayi tana ware ta, sosai tayi mata kyau ta ajiye a gefe ta ciro sauran tarkacen kayan hadda wata kar karamar jaka da tafi kama da purse sai takalmi hills amma ba chan ba. Shiryawa ta hau yi tana yi tana kallon toilet din har ta gama be fito, ta matsa wajen yar trolley dinsu da ciro perfumes ta faffesa sannan ta zauna tana dauko wayarta da take haske alamun kira ne ya shigo, Mamma ce, tasan cewa zatayi taji su shiru,ita kanta batayi tunanin nan din zasu zarto ba dan tasan an gama shiryar su kada ma Mamma taji labari tasan ba zata huta ba har sai sun iso. Dagawa tayi daidai lokacin da ya fito daga shi sai gajeren wando, faffadan kafadarsa ta kalla da take a mummurde, ta sauke kanta tana jin wani yanayi da bata san na menene ba, a gabanta ya tsaya yana rik'e k'ugu, yana, hannun sa daya rik'e da karamin towel, ganin ta dauke kai kamar bata ganshi ba, ya saka shi yarfa mata ruwan da yake hannun sa a fuska, yi tayi kamar zata tashi amma da daure ta cigaba da wayar, ta bawa Mamman hakuri yana ji ta gama ta ajiye wayar tana tashi da sauri.

"Kinyi kyau Matar Muhammad."

"Nagode." Tace a kunyace bubbude hannayen sa yayi, ya ja baya yana tattare fuskar sa.

"Shirya ni..."

"Na'am?"

"Eh ki shirya ni, ki shafa min mai ki saka min kaya..."

"Kamar dan baby?"

"Toh da mene? Ai babyn naki ne ni."

Dariya ta saka tana sake gyara zaman ta

"I'm serious fa, kinga we are running late, kar suyi ta jiranmu."

Ganin da gaske yake, ya sakata tashi ta dauko man, ta shiga shafa masa yana lullumshe ido, da gangan ya dinga sata komawa baya yana cewa be yi ba, nan fa. Da dai daga alamun so yake ayi tayi sai ta tattara man ta mayar, ta dauko masa suits din da ta gani tare da abayar ta, ta mika masa ya noke yana sake bararrajewa. Girgiza kai tayi, ta shiga saka masa, yana sake narke mata kamar wani karamin yaro a gaban mahaifiyar sa, sai data gama tas ya rage saura necktie sannan ya karba ya karasa sawa a gaban mirror, ya kalli kansa yana hango ta ta cikin mirror din,da hannu yayi mata alamar tazo, ta tako ta tsaya daga kuibin sa, ya matso da ita jikinsa yana kara kansa a jikin fuskar ta.

"Perfect!" Yace yana dariya, wayar sa dake kusa da wajen ya dauka, yayi musu hoto me kyau a gaban mirror din, sannan ya daga kiran da George yake masa.

"We are on our way."

Kawai yace ya katse kiran, ya rik'e hannun sa cikin nata suka fito, duk da suka hauro reception din suke shan kallo, tana jin shi yana jan tsaki k'asa-k'asa har suka shiga wajen da yake a cikin hotel din ne dalilln da ya saka ma suka sauka anan din kenan saboda already an riga anyi booking dakin tun kafin ranar ma. Duk in da suka wuce sojoji ne a tsaitsaye sun yi shirin ko ta kwana, cikin girmamawa suke gaida su, har suka kai babbar kofar shiga wajen.
  
    Wata iriyar kunya ce ta dabaibaye ta lokacin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login