Showing 54001 words to 57000 words out of 115235 words
Chapter 19 - Halin Girma Hausa Novel Complete
shiga kamar jira dama suke matar da ta shigo da ita ta wurgar da ita a saman kujerar har sai da kanta ya bugu da bango, tayi kara saboda zafin da taji kafin wadda suke kira da Hajiya Lay (Layuza) ta rankwafo akanta tana mata kallon tsana tace
"Ke dan yar iska ce ke, har kin isa mu hada miji daya? Kin isa nayi sharing dake? Karamar yarinya da bata fi sa'ar yata karama ba, kece kishiyata ko? Toh ni ko a zamanin kuruciya ban zauna da kishiya ba balle yanzu da nasan ciwon kaina nasan abinda nake so, dan haka nan dakin da nake ajiye masu aiki nane kuma na sallame su dan yanzu basu da amfani, sai ki cigaba daga in da suka tsaya, shara wanke wanke, wankin undies dina da girki, komai ma dai da kika sani."
Gaba daya kwakwalwar Zeenat ta gaza gane me matar take cewa, ji tayi kamar wani yare take mata na daban da bata sanshi ba, ta dinga jujjuya kanta tana son gasgata abinda taji akan Bashir din, yana da mata dama? Mata babba kamar wanna da ta yi sa'ar uwarsa? Abba ne ya fado mata, sanda ya kirata yake mata magiya kamar ba Mahaifin ta ba, ya kaskantar da kansa yana rokon ta akan ta rufa masa asiri ta hakura da Bashir amma ta shafawa idon ta toka, ta kekeshe kasa tace taji ta gani, yanzu ta yaya hakkin Abban ta zai barta? Tun a ranar farko ta fara fuskantar wannan tashin hankalin.
Firgigit tayi sanda taji saukar abu kamar ruwa asaman fuskar ta, ta saka hannu ta shafa da sauri tana daga kanta
"Kinji abinda na fad'a miki ko?"
A hankali ta daga kanta alamar eh, ta daka mata tsawa tace
"Baki zaki bud'e kiyi min magana bana son rainin wayo."
"Naji." Tace tana barin kwallar da ta taru a idonta ta shiga sakkowa saman fuskarta. Dariya suka kwashe da ita, suka juya suka fita suna cigaba da zantuttukan su mara sa dadi ji.
***Bangaren amarya Iman kuwa komai na tafiya daidai, ta dade batayi bacci ba tana tunanin Moh da kalar soyayyar sa me tsayawa a zuciya, koman sa abin so da birgewa ne tun daga maganar sa har yadda yake tafiyar da ita. Da k'yar ta samu bacci ya dauke ta bayan ta gama tunanin nasa. Tun asubah da suka farka basu koma ba, kana jin yadda hayaniya take tashi a masarautar kasan akwai gagarumin shirin da ake yi. Shiryawa suka hau yi ita ta fara wanka sannan su Khadija suka yi. Suna fitowa falon suka tarar da abinci a jere na alfarma yana jiran su, nan suka hau kai suka ci suka yi nak, sannan aka turo tafiya da Iman din shashen Fulani. Alkyabba aka sake saka mata sannan suka fito kanta na k'asa tana jin yadda take shan gaisuwa kamar ta tsaya ta amsa amma yan matan nan sunce mata ksr ta tsaya amsawa haka sarautar take.
Da murna Fulani ta tarbe ta yau din ma, ta saka aka kaita har uwar dakin ta in da mutane suka dinga shigowa suna ganin ta wanda suke da kusanci da gidan. Ta jima sosai anan har suka soma jin tashin kidan kwarya in da adaidai lokacin su Mamma suka iso sai dai babu Mama, gaisuwa aka sake kafin a rakasu in da ake kidan kwaryar aka nuna musu wajen zaman su, kafin daga bisani a rako Iman din wajen itama.
Da yamma kuma aka dawo ciki aka sake shiryawa in da aka nufi hall din dan gabatar da bikin da kuma kyaututtukan da aka shiryawa Iman din.
Sakon Maimartaba ne ya samu Fulani akan yana son ganin Matar Muhammad din dan a yau zasu wuce komai dare, mamaki ya kama Fulani dan a yadda suka shirya kwanaki uku zasuyi a nan din kafin su tafi adamawar, bata sani ba Muhammad din ne da kansa yaje ya samu Takawan ya roke shi akan a rage bidiar dan shi kam ya gaji sosai, take kuwa ya amince har ma ya sanar da Bubu tun a daren jiyan.
Maimakon a wuce da ita hall din sai aka fara kaita wajen Takawar. Kanta a k'asa sosai kwarjinin sa ya cika wajen ta yadda kowa ya kasa sakewa, nasiha ya soma yi cikin maganar sa da ta saka jikin kowa mutuwa, yayi musu fatan alkhairi sannan ya kare da sake jan hankulan mutane akan yadda rayuwar ta zama, basu dade a wajen ba, suka fito kowa na yaba karamci na Maimartaba da ya karbe su hannu bibiyu ba tare da nuna banbanci ko wani abu ba.
A gaggauce akayi taron, saboda tafiyar da zasuyi, sosai iman ta samu kyaututtuka masu tarin yawa a yan awowin da basu gaza biyar ba, kowa so yake ace shine yafi, kowa so yake ya burge Fulani da Maimartaba, dan kowa ya san yadda muhammad din yake a zukatansu.
***Motoci ne guda uku suka dauke su zuwa airport din daga su Mamma sai wasu yan uwan Abba su uku shikenan wanda zasu adamawar, shima saboda bikin da zasuyi ne suma badan haka ba da babu me zuwa. a lokacin Moh sun dade da isa suna zaune dasu Musaddik ana hira a wani kebantaccen wuri.
Zuwan su da aka dan suka dauki hanya babu wani bata lokaci. Ita kadai ce a wajenta, babu kowa a saman duk suna k'asa sai ita kadai kwal har ta dinga tunanin dalilin da ya saka aka kawo ta nan din ba abarta wajen su Mamma ba. Kamshin turaren sa ne ya amsa mata tunanin ta, ya karaso ya zauna kusa da ita yana kashe mata ido. Kayan jikin sa ta kalla wanda suka kasance na sarauta, sai takalmin kafarsa da akayi da fatar zaki yayi kyau sosai shigar gidan sarauta, babu hula akan sa ya rik'e ta hannun sa, sumar sa ta fulani ta sha gyara ya fito a bafulatanin sa sosai.
Shi din ma shigar ta yake kallo, yana kuma yaba yadda komai ta saka sai yaga ya karbe ta yayi dai-dai da ita.
"Ba magana?" Yace bayan ya gama kallon nata
Mirgina kanta tayi gefe tayi masa murmushi tace
"Sannu da zuwa toh."
"Yawwa."
Yace yana jingina da kujerar jirgin sosai, be sake magana ba sai dai yanayin sa ya nuna mata kamar akwai damuwa, tasan yadda yake mata dan haka yau din sai taga kamar bashi ba, bata sani ba ko sarautar ce ta motsa. Satar kallon sa ta dinga yi sai taga ya kulle idon sa yayi kamar me bacci. Duk sai taji ta takura ta kuma damu, taba shi tayi kad'an, ya motsa amma be bude idon nasa ba, sai kamo hannun ta da yayi ya sakalo shi ta tsakanin nasa hannun ya harde su waje daya, kusan rabin jikin ta ya sauka a nasa, bata sake attempting komai ba har zuwa sanda suka iso jirgin ya sauka suka fito still hannun sa na sarke da nasa.
***Kafarta a mike take tana sauraron bayanin da take mata, ko motsi batayi ba, kamar bata jin me take cewa har ta kai karshen bayanin tayi shiru tana kallon ta. Sai da ta dauki lokaci me tsawo kafin ta gyara zama, ta bud'e hannun ta, ta mik'a mata shi, jikinta na rawa ta ciro kwalbar da take nannade a gefen zanin ta, ta saka mata a cikin tafin hannun ta. Jujjuya shi tayi tayi a hannun nata tamkar me son gano wani abu.
"Turare ne ranki ya dade, a jiki kawai ake shafa shi bayan haka babu wani abu."
"Kin tabbatar da abinda kika ce?"
"Allah ya taimake ki, yadda nayi miki bayanin haka yake, yace kar ayi wasa dashi, sannan kuma kar ayi sakacin da za'a samu matsala."
"Rik'e." Ta mika mata, da sauri ta karba tana damke wa a hannun ta sosai.
" Kin tabbata babu wani abu da ya faru tsakanin su?"
" Na tabbatar, sai da ya nuna min komai kafin ya bani, yau zasu iso sai kiyi kokari kafin su tare a sabon bangaren su dan naji rad'e rad'in bikin ba zai dau kwanakin da aka tsara ba, bisa umarnin Sarki."
Murmushi tayi me kyau, ta dawo ta zauna bayan ta ciro wata karamar riga ta karata a jikin ta,sai kuma ta ajiye tana mikar da hannun ta baya.
" Kinyi kokari, kina da kyauta me tsoka idan har na samu biyan bukata."
" An riga ma an samu gimbiya, ki kwantar da hankalin ki."
"Tukunna dai."
" Me yayi saura? Yan awoyi ya rage miki ki samu abinda kike so gimbiya ta."
Jikin tagar dakin ta karasa, ta daga labulayen tana kallon harabar gidan da yadda hadiman gidan ke kaiwa da komowa a tsakanin bangaren Moh din da na Ammi, tasan duk shirin tarbar bakin ake, hankalin kowa ya riga ya koma chan dan haka zatayi amfani da damar ta isa bangaren Moh ta yi zaman jiran dawowar shi!
Rano💕
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
1/31/22, 19:14 - Buhainat: Halin Girma
22
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
**********
Tamkar rana haka harabar masarautar take, komai an shirya shi an tsara saboda shirin tarbar su. Tafiya sukayi doguwa a ciki kafin su kai wajen manyan gine-ginen cikin masarautar.
Ba mota daya suka shigo daga airport din dashi ba, shiyasa ma bata ganshi ha a sanda suke fitowa daga mota. Cikin rakiyar hadiman shashen Ammi da na gidan ma baki daya suka isa babban falon nata, da aka kawata shi matuka ana jiran isowar su. Kamar yadda suka samu tarba ta musamman a Kano haka aka karbe su anan dinma. Hakan ya kara bawa su Mamma nutsuwa da tunanin irin yadda Iman din zata samu kanta a gida irin wannan wanda yake cike da abubuwan da ba lallai ta iya dauka ba.
Bayan sun huta an gabatar musu da abinci ne Ammi ta saka aka rakasu masaukin su, wanda aka ware musu tun kafin isowar su. A gajiya kowa yake dan haka suna zuwa kowa ya mike aka shiga maida maganar yadda aka karbe su da irin sa'ar da Iman din tayi.
Tana jin su bata tanka ba, hankalin ta ya tafi sosai wajensa tana son jin yadda yake dan ta tabbata da akwai wani abu da ya rage masa walwala.
***Tun isowar su ta samu labari wanda dama abinda take jira kenan, ta shirya tsaf babu Kuma abinda zai hanata aiwatar da abinda tayi niyya shiyasa ma bata bari Kilishi ta sani ba balle har ta hanata.
Shigar sa shashen nasa bayan ya bar wajen Bubu hadimar ta, ta sanar mata wanda dama ta saka ta ne ta saka ido tana ganin ya shiga ta fad'a mata.
Tashi tayi tana gyara gashin kanta da ta saka ribbon din tayi sako-sako dashi, ta daura babbar Alkyabba akan kayan da suke jikin ta da ya kasance karamar riga ce mara hannu iyakar ta guiwa kawai, sai dogon wando a k'asan da ta saka saboda yadda zai zama ko ina na jikinta ya rufe.
Turaren da yake cikin Jakarta ta ciro, ta dunkule shi a hannun ta, ta fita ta kofar bayan cikin rakiyar amintacciyar hadimar ta. Tafiyar dake tsakanin bangaren Moh din da nasu da akwai tazara dan haka yasa suka bi ta baya har suka isa. Idon ta, ta daga ta dubi bangaren bedroom dinsa amma sai taga dakin babu haske sai sauran dakunan. Zagayo wa sukayi zuwa gaban ginin masu kula da kofar suka tashi ganin ta, da ido sukayi magana da daya, ya girgiza mata kai alamar eh sannan yace
"Yarima na jiranki gimbiya Lailah."
Jin haka ya saka dayan saurin bud'e mata kofar, ta kutsa kanta ciki kai tsaye tana jin kamar anyi an gama ta samu cikar burin ta.
Tafiya ta ke a cikin falon tana kallon komai, yadda aka sauya komai kamar ba part din da take shigowa a duk sanda ta ga dama ba, babban hoton da ke manne a jikin bangon dakin ta kurawa ido tana matsawa gaban sa. Iman ce a jiki, ita da Moh ranar da aka daura aure, sunyi masifar kyau kamar kayi musu magana su amsa. Wani bakin ciki ne yazo ya tokare mata a makoshi, taji kamar tayi wurgi da hoton ya tarwatse a wajen amma sai ta daure, ta maida hannun ta baya tana nufar bedroom din nasa in da tasan zata same shi.
Kafin ta karasa ta hango glass cup a k'asa a farfashe, ta durkusa ta dauki ragowar tana kaiwa hancin ta, murmushi tayi tana da yakinin komai ya zama daidai, everything is in order kamar yadda ta tsara. Hakan ya saka ta wucewa Kai tsaye ta murda kofar dakin ta kutsa kanta ciki tana zare alkyabbar da take jikin ta, ta zame a wajen ta fadi.
Muryar sa da ta soma bacewa yayi kokarin cewa
"Waye!"
Yadda yayi maganar ya saka ta sake tabbatar da komai yayi daidai, basu yi mata shirme ko shiririta ba. Karasawa tayi jikin gadon, ta kai hannu ta taba shi ta hasken bedside lamp da ke kunne, take kallon sa, idon sa yayi masifar komawa ciki yana lumshe su tamkar wanda yake shirin yin bacci irin baccin da yafi karfin sa yake neman kai shi k'asa.
"Waye?" Ya sake maimaitawa da k'yar kansa da yake juya masa ya shiga kai masa sakon mayen kamshin da yaji ya karad'e dakin,kamshin da ya dauke shi zuwa wata duniya ta daban, a take yaji komai ya hargitse masa, ya mike da k'yar yana duban ta cikin ido, gaba daya komai ya chanja masa,ta juye masa Iman dinsa gaba daya. Hannu ya kai zai taba ta, ta saka karbi ta tura shi baya ya fad'a saman gadon!
***Text message ne ya shigo wayar ta, ta bud'e da sauri tana fatan ya kasance daga shi, kamar yadda tayi tsammani, shi din ne kuwa,
_"A rako ki shashe na."_
Haka kawai sakon ya kunsa, kifa wayar tayi tunanin yadda zata fara fadawa Mamma yace a rakota bangaren sa. Da kunya sosai bata kuma jin zata iya,shiru tayi tana wassafa abun a ranta, zuciyar ta na ce mata kawai ta kira mamma ta fad'a mata ai ba wani abu bane, wata zuciyar kuma na ce mata a ah. Ta na nan zaune har aka dau tsahon wani lokaci, sakon ya sake shigowa irin na dazu a karo na biyu, sai dai banbancin lokaci. Amaani ta kira suna zaune suna cin snacks da juice, ta bata wayar tace ta kaiwa Mamma. Sai ta kifa kanta tana jin nauyin Mamma. Tana jin sanda Mamman tazo kanta, tana sababi
"Yanzu haka ake gaya miki anayi Iman? Mijinki yana kiranki tun dazu kika yi shiru. Kunyar me? Zamani ya chanja kinji? Tashi maza ki gyara jikin ki, ga masu kula dake nan da yawa daya sai ta rakaki, tashi maza kina kara bata lokaci."
Tashi tayi kunya na nukurkusar ta,ta dinga sunne kai taki yarda su hada ido da Mamman, tana kallon ta, ta fito mata da wasu kayan tace ta sauya, sannan ta kawo mata wani abu a cup da madara ta bata ta shanye, ta faffesa mata turarurruka masu kamshi sannan suka fito in da yan matan ke zaune, da sauri suka tashi su biyu, suka sakata a tsakiya suka nufin bangaren Moh din da yake da dan tazara da wanda aka sauke su.
Babu kowa a kofar, kai tsaye ta shiga su kuma suka samu waje daga wajen suna jiran ta dan tace musu ba jimawa zatayi ba, babu kowa a falon babu motsin komai, dakin farko ta bud'e da sallamar ta, baya ciki, sallama take amma ba da karfi sosai ba, a tunanin ta ko ya shiga toilet ta zauna jiran shi, shiru shiru babu alamar sa, ta kasa kunne ko zata ji karar ruwa a toilet sai taji kamar shesshekar kuka, sake kasa kunnen tayi sosai ta tabbatar da abinda taji, sai ta fara tunanin aina take ji, dakin da yake karshen falon ta kalla, babu alamun haske a ciki amma kuma tabbas da ga nan ne sound din yake fitowa. Tashi tayi ta nufi dakin tana taraddadin abinda zata tarar. A hankali ta tura kofar, ta leka da kanta kafin ta shiga da jikin ta gaba daya, tana gama shiga wutar dakin ta kawo, kwakwalwarta ta dauke kamar yadda ake dauke wutar nepa, idanun ta suka sauka akan Moh yayi ruf da ciki a saman gado yana bacci cikin kwanciyar hankali, boxer ne kawai ajikin sa dgaa shi babu komai. Da sauri ta maida kallon ta kan matar dake zaune a kasan tiles din dakin, kanta babu dankwali gashin kan nata da ya hargitse ya barbazu har zuwa saman fuskar ta, shigar jikin ta kawai ta kalla tayi saurin dauke kanta tana kokarin barin dakin, sai dai bata kai ga barin wajen ba dan ko taku biyu batayi ba, taji sanarwa shigowar Maimartaba, bayan sanarwa ne taji shigowar sa.
Karuwar kukan Laila ya sake sakata cikin yanayin da ta shiga, har Maimartaba ya karaso bakin dakin tana tsaye kamar an dasa ta, bata san me zatayi ba. kallon ta yayi kafin ya maida kallon sa cikin dakin, yayi musu kallo daya wani abu me dacin gaske yana tokare shi a goshi. Juyawa yayi sai a lokacin kwakwalwarta ta kai mata sakon waye wanda ya shigo din, da sauri ta zube a wajen ta gaishe shi cikin muryar ta da take rawa sosai.
Be amsa mata ba, sai daga mata kai da yayi ya juya ya fice yan rakiyar sa suka bi bayan sa cikin tunanin dalilin zuwan Bubun shashen Moh.
Kasa daga kafarta tayi daga wajen, ta jingina da bangon dakin tana karanto duk addu'ar da tazo bakin ta, ji tayi kamar ana mata magana, ta dago tana kallon cikin dakin
"Amarya! Kinyi farin gani ko?"
Me zata ce? Shiru tayi tana maida idonta ta rufe shi ruf tana kokarin ajiye abinda ta gani din da kuma abinda zuciyar ta take haska mata waje daya.
"Anya? Anya kuwa? Muhammad? Me ya faru? Me yake shirin faruwa? Wacece wannan din?"
"Karki wahalar da kanki tunanin wacece