Showing 12001 words to 15000 words out of 115235 words
Mama tayi mata, tayi kwafa ta mike sannan ta kalli Zeenat da ta soma kuka wiwi tace
" Ki same ni a daki."
Kamar wadda zata fadi saboda kuka haka ta tashi, ta kusan fadowa Iman din aka, a ranta tana jin babu abinda zai hana ta auren Bashir, duk tashin hankalin da za'a yi sai dai ayi shi, amma babu wanda zai hanata abinda zuciyar ta take so.
***Cikin wani yanayi bayan ya gama jin komai ya gaida Abban da ya fito, yayi masa adawo lafiya sannan ya juya zuwa wata hanyar ya fasa shiga dakin. Idan har abinda yaji gaskiya ne, wannan me zubin yan boko haram din aka bawa damar turowa kenan, ba zai taba yarda yayi biyu babu ba, ba aiki ba Iman, shi zai fara isa wajen Yayan idan yaso ayi wacce za'a yi, yasan ba zasu taba hanashi ba, domin shi ya chanchanta ba wani bare ba, da ba'a san daga ina yazo ba.
***
Tashi zaune yayi zaune bayan ya ajiye wayar, ya kalli Musaddik da ya zauna a gefen sa
"Ya akayi ne?"
"Na shigo kana ta waya"
"Eh wallahi, ni da Wifey ne."
"Wifey kuma? Yaushe kayi aure ba labari?"
"Bana son iskanci, kasan wa nake nufi ai."
"Toh ai sai kace aljanar ka da ka nacewa, amma kace wifey bayan bamu shafa fatiha ba."
Jefa masa dan pillow din da yake kusa dashi yayi
"Dan iska, ka jira ka gani ai."
"Wai karo maka yaran ka akayi ne? Naga gate din naka ya sake cika ga wani uban iyayi kamar basu san mutum ba?"
"Sai hakuri kawai, ya ake ciki ne?"
"Normal, shiru ne ko ina, ya ka baro su Ammi?"
"Lafiya lou wallahi, Bubu yayi min maganar aure ai, nace zan zo musu da magana in less than a month, kafin nan mun gama daidaitawa da Wifey."
" Ya zakayi toh idan aka ce ka turo?"
" Shine matsalar wallahi, amma zan san yadda zan dai."
" Toh Allah ya sa muji alkhairi angon Fatima."
" In Sha Allah." Yace yana dafe saitin heart dinsa, dai-dai lokacin kiran ta ya shigo wayar, yayi saurin dora hannun sa akan baki alamun Musaddik yayi masa shiru, wurga masa pillow da ya jefe shi dashi yayi ya fice yana cewa
" Ka same ni a kasa idan ka gama zan kalli laliga."
Da kai ya amsa masa yana kara kiran a kunnen sa
" Nagode sosai da kika kirani, na zata ba zaki kira ba."
" Haba! Zan kira ai."
" Nagode sosai, bari na kira ki toh."
" A ah ba komai, muyi magana akwai kati kar a cinye maka naka kai kadai."
Murmushi yayi me sauti
" Kinga kuma 200 nasa dazu har ta kusa karewa, bari na fita sai na sake siyo ko na 100 ne sai na kiraki."
" Allah ba sai ka fita ba, ga sanyin nan da ake yi ma."
" Shikenan Nagode."
" Me kikayi a wajen Abba."
" Abinci naci."
" Iyeeeee, yar gata! Har abinci abba ke baki? Allah sarki ni."
" Kaima ai dan gata ne."
" Ni din? Tab ni ba dan gata bane, gashi ke har abinci Abba yake baki, niko kin ganni a dan shago na sanyin nan duk a kaina zai kare, babu me tausayi na ya bani abinci."
" Allah sarki."
Tace cikin tausayawa, da ace sun saba sosai da tace yazo ya karbi abinci, ta hada masa har da abin rufar ta idan yaso ita sai ta samu wani wajen Gaji, amma ba zata iya ba, sai kawai tayi shiru tana tunanin ta yadda zata fad'a masa Abba yace yazo ya samu yayansa.
"Dama... Dama...Abba ne yace."
"Me?" Yace cikin zakuwa
"Wai ka fara zuwa ka samu Abba (Baban yayansu) ka nemi izinin zuwa kafin ka cigaba da zuwa."
"In Sha Allah zanzo, yaushe ake samun sa a gida?"
"Kamar da yamma haka zuwa bayan Magriba."
" Ok in sha Allah zanzo, nagode sosai da wannan karamcin na Abba, duk da ni din ba kowa bane, amma har aka bani wannan damar, nagode Sosai."
" Ni dai dan Allah ka daina cewa kai ba kowa bane, a islamiyya an fad'a mana, babu wanda yafi wani sai wanda yafi tsoron Allah."
" Haka ne, wai kinga ina nufin ni din ba kudi ne dani ba, amma..."
" Kudi ba sune farin ciki ba ai, wadatar zuciya itace mutum, dan Allah ka daina wannan maganar kana sani jin wani iri."
"An daina ta daga yau, ba zaki sake ji ba, kiyi hakuri idan na bata miki rai."
" Babu komai."
" Yawwa, kiyi min murmushi naji toh."
Shiru tayi
" Kinji mana, pleaseee."
Yace sai kuma yayi saurin daidaita kansa ganin zai zarme da yi mata shagwaba har ta ranfo wani abu
"Nayi fa, ai baka gani na."
"Tam shikenan, idan naje na nemi izini wajen Abban mu, zanzo na gani a zahiri."
"Uhum." Tace tana jin zuciyar ta na sake nutsuwa dashi, ko ba komai ta samu wani da yake dauke mata damuwar ta da kadaici
"Bari na barki haka kar na cinye miki kudi..."
"Goodnight, sweet dreams of meeeee."
"Allah ya tashe mu lafiya." Tace tana yin dariya k'asa k'asa
"Amin ya Allah, bye inji turawa."
"Bye." Tace mishi ta ajiye wayar.
"Yess!" Yayi tsalle ya dire kafin ya fice yana saka hannun sa cikin aljihun dogon wandon sa. A falon ya tarar da Musaddik da tea yana sha, ya zauna ya diba shima yana murmushi.
_"You don make me fall in love, you don make me fall in lov, Baby I love you."_💕
Dariya sosai Musaddik ya saka
" JJC kawai, zaka cika mana kunne da wata wakar ka."
"Idan fitsari abin banza ne, kaza ma tayi mana?"
"Okh haka ne, shikenan ai.Wait and see. Ni yanzu ba wannan ya kawo ni ba, me yasa ka saka aka dakatar da gayen nan ne?"
Tashi yayi rik'e da cup din yana bata fuska
"Kaga dacewar ya nemi irin abinda nake nema?"
"Kamar ya?"
"Ba'a takara da Sarki, be chanchanci karawa dani ba, bashi da qualities din da zai iya neman auren ta, cika bakin sa ya saka na nuna masa iyakar sa, anyways warning ne kawai, zan sake gwada hankalin sa , idan yayi hankali fine, idan be ba kuma sai muje a haka, sai a karbi application din wasu."
Gid'a Kai Musaddik yayi be sake cewa komai ba, yasan waye Moh, yasan bashi da matsala ta kowanne bangare, amma bashi da dadi idan har kayi crossing din sa, zai nuna maka shi din babba ne a cikin manya!
"Ka fahimta dai ko?"
"Yes Captain!" Ya mike sannan ya sara masa.
"Aje waya!" Yace masa suka kwashe da dariya a tare.
HALIN GIRMA
Hafsat Rano
WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*
*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*
*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*
*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*
*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar .
___________
1/6/22, 17:52 - Buhainat: *HALIN GIRMA*
7
*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*
I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
***
Kukan ta ne yake karuwa Mama na tsaye a kanta, ta ja tsaki tace
"Bana son shirman banza kina ji na? Akan namiji zaki zauna kina rafka wannan kukan kamar uwarki ce ta mutu ko ubanki?"
"Mafita nake so mu samawa kanmu, saboda anga zaki huta shine aka shiga aka fita ake so ayi mana bakin ciki, idan ba haka ba, me ya kawo wadannan zantukan?"
Cikin kuka tace
"Wallahi Mama nasan Iman ce taje ta samu Gaji da maganar tunda dama ita yace yana so ai, shine dan taga wanda yazo wajen nata talaka ne shine zata min bakin ciki, toh wallahi babu wanda ya isa ya hanani auren Bashir, naji na gani kowanne hali ne dashi."
Shiru Maman tayi tana kallon yar ta ta, idan har ta bari maganar ta sha ruwa akwai matsala, sanin cewa Zeenat din ba wani farin jini bane da ita, dama dai jamaar Iman din ne tun farko take sanin yadda zatayi, dole ta san abinda ya kamata amma duk da haka ba zata nunawa Zeenat din komai ba
" Kina jina? Ki tashi ki tafi dakin ku, ki daina wannan kukan tunda ba ubanki bane ya mutu, zan san yadda zanyi komai ya daidaita."
Da bayan hannun ta ta goge kukan, ta fice tana rangaji, tana sake kudurewa a ranta babu gudu babu ja da baya a auren ta da Bashir din.
Tana isa daki ta tarar da missed calls din sa, ta bi kiran da sauri tana sake daidai ta kanta.
" Gani a waje." Yace tana dagawa.
" Mu hadu a bayan layi akwai matsala karka zo gida."
" Me ya faru?" Yace a kidime.
" Babu komai gani nan zuwa."
Kashe wayar ta, tasan zai ta tambayar ta menene gwara kawai taje suyi magana su sama wa kansu mafita dan ba zata iya hakura dashi ba.
Ficewa tayi ta kofar kitchen bayan ta gyara fuskar ta, ta bar gidan cikin sauri tana tsoron haduwa da Ya Habib ko wani.
A chan bayan layin ta hange shi jikin motar sa, a tsaye yake yana ta jijjiga jikin sa daga gani baya cikin nutsuwar sa, tana isa ya juyo da sauri.
" Lafiya baby?" Yace yana riko hannun ta. Kuka ta saka da sauri yace
" Na shiga uku, me ya faru?"
" Abba ne yace wai na rabu da kai, wai yayi bin..."
" Shisshsh..." Yace da sauri yana dora hannun sa a saman bakin ta
" Kinsan dai hakan ba gaskiya bane ko? Sharri akayi min ko menene akace domin a hana mu aure, duk wanda ya yi min wannan sharrin na bar shi da Allah kawai." Yace yana girgiza kansa
" Shikenan yanzu rabuwa zaki dani? Nasan rayuwata shikenan ta kare, idan har zaki iya yarda mahassada su shiga tsakanin mu, bakya so na baby, rayuwata shikenan ni."
" Ni ban yarda da duk abinda akace ba ai, kawai sharri ne na sani, amma ya zanyi da Abba? Bayan shi din kaifi daya ne akan maganar sa."
" Dan Allah Zeenat karki yarda a raba mu, wallahi Ina sonki , bansan ya zanyi da rayuwa ta ba idan har baki aure ni ba."
Hawaye ya fara yi tayi saurin sa hannu ta goge masa
"Zanyi duk yadda zanyi, ba zan bari a raba mu ba..."
" Da gaske? Kinyi alkawari?"
" Nayi maka alkawari."
" Dan Allah karki saba alkawari dan Allah, ki taimaka wa rayuwa ta, kinji?"
" Karka damu." Tace tana jin wani karfin zuciya,
" Ba zan taba yarda su yi min abinda bana so ba, Kai nake so kuma duk yadda kake ina son ka a haka.*
"Nagode nagode baby, in sha Allah ba zakiyi dana sanin amincewa dani ba."
Zatayi magana wayar sa tayi kara
" Sorry." Yace mata kafin ya daga yana rage volume din wayar sosai
" Malam tun dazu nake jiran ka, ka dawo min da mota zan fita, wai ina ka tsaya ne?"
" Gani nan yanzu in sha Allah."
Ya kashe kiran ya ce
" Baby bari naje, urgent call daga Baba, zamuyi waya kinji?"
" Tam shikenan." Tace a sanyaye
" Yawwa ga sakon ki..." Ya bud'e murfin motar ya fiddo da ledoji, hannu tasa ta karba tayi godiya, ta juya ta soma tafiya shi kuma ya shiga motar ya tada ita da sauri ya bar wajen, yasan ba zasu kare kalou ba da ita, amma kuma hakan shine kadai zai kankaro masa mutuncin sa.
***Daki ta koma ta ajiye ledar bayan ta bud'e taga ice cream ne da Pizza, sai charger waya da yake ta lalace ta ta, sai wasu tarkachen alawoyi. Bata taba komai ba sai charger din ta jona wayarta a jiki sannan ta fice zuwa bangaren Gaji dan ta samu Iman a yi wacce za'a yi.
Iman din ce kuwa kadai a falon tana karanta hisnul muslim. Sai ganin mutum tayi a kanta, bata tanka mata ba ta sauke kanta ta cigaba da karatun ta kawai.
"Saboda kina bakin ciki kin samu fakiri talaka shine zaki kai munafurci kice Bashir bashi da hali ko?"
"Wacce irin magana ce wannan Zeenat?"
" Malama karki pretending kaman baki sani ba, idan bake kika fad'a ma Gaji wata magana akan Bashir ba waye ya samu Abba ya fad'a masa Bashir bashi da hali me kyau?"
Tashi tayi zaune tana kallon ta, ta girgiza kanta kawai kafin tace
" Kinsan bani da lokacin batawa akan irin wadannan maganganun, dan haka please bana son maganar."
" Zaki ce bakya so mana kina min bakin ciki, toh wallahi sai dai ki mutu da bakin ciki amma aure na dashi babu fashi, kije chan kiji da wanda zaki aura, mutum kamar shi ya kawo talauci duniya."
Tashi kawai tayi ta bar falon zuwa bedroom din Gaji dan ba zata iya irin wannan shirmen na Zeenat ba, sai dai da gaske maganar ta taba ta, har taji ta rasa gaba daya walwala da farin cikin ta, kwanciya kawai tayi ta rufe idon ta tana hasaso rayuwar ta nan gaba!
***Cikin shigar Khaki pants da wata jibgegiyar rigar sanyi da ya saka a saman armless rigar sa ya fito, kansa da yake a kwance yasha gyara ya tsaya yana sake dubawa a katon mudubin da yake ajiye a falon, yasan Takawa zai saurare shi ya kuma bi abinda yake so sai dai baya son ko kad'an karya ko wasa ya shigo a cikin maganar auren sa. Kallon kafar sa yayi, sai ya koma ya sauya takalmin zuwa wani daban sannan ya fice yana tura hannun sa cikin aljihun dogon wandon nasa.
Suna tsaye k'yam suna jiran fitowar sa, kowanne su cikin shigar da take nuna shi din waye, bud'e masa motar akayi da sauri ya fad'a yana makala bakin glass din sa yasan yau zai same shi a wajen hutawar sa, in da ya dace da maganar da zasu tattauna, shiyasa ma yayi shigar sa da yasan Takawan bazai masa surutu ba, dan ya riga ya san shi, ko yace kowa ya san shi da tsanar manyan kaya musamman a lokacin zafi sai yace wai takura masa suke.
Da yake sun san in da zasu, kai tsaye suka wuce dashi Family house din, in da Takawan ke hutawa a duk ranaku irin wannan ba tare da shigowar wani shaani na mulki ba. Iyakar abinda ya shafi kansa da iyalin sa kawai yake tattaunawa a rana cikin saukakakkiyat shiga da ba zaka taba cewa sarki bane duba da ko yaushe yana nannade cikin rawani da manyan kaya.
A kofar wajen motocin nasa suka tsaya, ya balle murfin tare da me bud'e masa ya fito yana kallon ko ina na harabar gidan. Kansa sanye da hular sanyi ya cire glass din idon sa ya shiga takawa zuwa ciki. Gaisuwar da ya tsana ya dinga kokarin kaucewa har ya dangana da inda takawan yake ya hange shi a zaune a cikin wajen yayi matashi da pillow yana kallon yadda yan yaran da suka kasance jikokin sa ke wasa a wajen.
Sarkin dogarai ne ya fara ganin shi,ya washe cikin farin cikin ganin shi yace
"Maraba da Yarima!"
"Sarkin dogarai..."
Muryar sa ta saka takawa d'agowa, ya gyara daga gishingid'ar da yayi, ya fad'ad'a fara'ar fuskar sa da tayi ma Moh iso har gaban kakan nasa. Russunawa yayi cikin girmamawa ya kai gaisuwa, hannu ya mik'a masa ya matso kusa dashi sosai, ya shafi saman kansa
" Sai yau kaga damar leko ni ko Muhammadu?"
" Tuba nake Takawa, ayyukan ne suka yi min yawa."
" Toh madallah, naji kace kana son gani na, toh gani ya akayi?"
" Dama magana ce akan abinda Bubu yayi maka magana."
" Auren ka? Jairi toh sai akayi yaya?"
Dariya ya saka sosai
" Toh kunce sai nayi aure yanzu kuma nazo da maganar kuma, sai na fasa auren ma gaba daya."
" Fasa mana, waya yayi asara? Kaji dan nema."
Dariya suka saka a tare, kafin Takawa yace
" Toh sai ka fadi a inda yarinyar take ko? Idan yaso sai a nemi iyayenta."
" A ah ni dai Takawa, ayi min aikin gafara a bari a samu wasu suje su nema min auren ta."
" Wasu?" Yace yana kallon sa
" Eh a dangi haka ba, ba manya sosai ba, Ina nufin ba cikin manyan masarauta ba, yan chan kasa kasan dai."
" A wanne dalili?"
" Kawai ni bana so suji tsoro su ga kamar mun fi karfin su."
Girgiza kai Takawa yayi
" A neman aure babu boye boye Muhammadu, a sak dinka zaka je, kai ne fa jika na farko a gidan nan, sannan a wajen mahaifin ka, wanne irin tunani ne haka ya shiga kanka?"
Sosa kai Moh yayi yana marairaice fuska
"Ni dai dan Allah takawa, a bar wasu suje."
"Sam sam kaima kasan hakan ba mai yiwuwa bane, dole ne su san kai din daga gidan da ka fito."
Shiru yayi yana jin kamar ya daure kansa da ya budewa Takawa zuciyar sa, yasan shi sarai da tsayawa akan ra'ayin farko, amma yayi tunani zai fuskance shi duba da irin son da yake masa, dama Musaddik ya gaya masa, babu me yarda da shirmen sa kamar yadda yake jaddada masa a kullum, babu me biye masa ko bashi goyon baya. Tun daga lokacin yasan sarai babu me tsayawa ya saurare shi, balle ya yarda da tsarin sa. Ammin sa ce kadai itama bata ja da maganar Takawa, ballantana Bubu da baya iya aiwatar da komai sai abinda Takawa din yace.
"Kana jina Muhammadu, maganar da kazo da ita bata kamawa bace. A tsari na gidan nan ma zamu iya aika musu suzo nan din domin muna da damar bada diyar tasu, sai dai ba zamuyi haka ba, zamu basu girman su da darajar su in Sha Allah, za kuma musu duk abinda Muhammad yake so amma banda shiririta."
Ya karashe yana murmushi, murnushin shima yayi kawai ba tare da yace komai ba. Suka cigaba da hira irin wadda suka saba har be san iya adadin awoyin da ya bata ba, sai da suka ci abinci da Takawar sannan ya lallaba