Showing 6001 words to 9000 words out of 115235 words
gashi da gaske yake jin ya kamata ace ya huta, yakamata ya karbe shi kamar yadda ya karbi Aji a lokutan baya. Sai dai d'an nasa sam be shirya hakan ba, abinda yasa yake dada jan lokacin sosai, burin sa kawai yasa a gaba tun bayan shigar sa jami'ah, in da ya kwallafa rai akan aikin tsaro, ya kuma samu cikar burin sa duk da ba hakan ne ya kasanci burin sa ba shi.
Kamal ne ya shigo wajen, ya gaida kowa cike da girmawawa sannan ya samu gefe ya zauna yana fuskantar Muhammad din, kallon juna suka yi ba tare da wata magana ba, murmushi kawai Kamal din ya sakar masa wanda ya kasa maida masa domin ya san ma'anar sa, be damu ba ko kad'an, da ace Bubu zai ji shawarar sa da ya jima da yiwa Kamal din abinda yake muradi, amma shima kemaimai yaki, ya kwallafa rai akan Muhammad din, ko me yasa? Oho. Ya dage kafadarsa alamun baya da bukatar ya sani ma dai.
Duk batutuwan da aka tattauna a wajen be tsinci komai ba, zuciyar sa ta lula chan zuwa in da ya baro, tunanin halin da take ciki ko abinda take aikatawa kawai yake har kusan kowa ya gama ficewa ya zama na daga shi sai Aji, da Bubu.
"Muhammadu." Yayi firgigit sai kuma ya hau sosai kai yana murmushi
"Barka da rana Bubu."
"Kalli shigar ka fa Muhammad, kalle ka? Hakan ya dace a matsayin ka da gidan nan? Haka kaga dan uwanka Kamal yayi shiga irin ta masarauta?"
"Wallahi Bubu garin sauri ne, kuma gashi ba wani iya nada rawanin nan nayi ba wallahi, infact ciwon kai wallahi yake sani, amma za'a gyara ba za'a sake ba."
Murmushi Aji yayi me dan sauti, ya kalle shi yana sake fadada fara'ar fuskar sa.
"Ayi hakuri ranka ya dade munyi kuskure ba zamu sake ba." A duk sanda irin hakan ta faru Ajin ne ke yin uwa yayi makarbiya ya hana ayi masa fad'a, hakan yasa ba kasafai Bubun ke korafi gaban Ajin ba, sai ya tsuke bakin sa kawai be sake cewa komai ba.
Tashi yayi, ya dan russuna a gaban mahaifin nasa
"Zan shiga ciki Bubu!"
"Ka same ni a shashe na bayan sallar magriba."
" In sha Allah. A tashi lafiya."
" Aji sai na shigo wajen yar tsohuwa ta."
" Tana nan tana jiran ka da manshanun ta da yajin daddawa."
Murmushi yayi, ya fice suka raka shi da ido. Yana fita Bubu yaja tsaki
" Na rasa me yake damun yaron nan wallahi, ace yaro ya taso a cikin abu amma sam ya tsane shi? Wannan wanne irin abu ne?"
" Mu cigaba da hakuri kawai Ahmadu, komai zai wuce ne."
" Allah yasa, kowa jira na yake, mutanen gari da manyan mutane kowa ya zuba ido yaga me zanyi akai, ga Kamal da gaske yake son mulkin nan, gashi sam be chanchanta ba, na rasa yadda zan."
"Shima ka barni dashi kawai, ayi masa abinda yake so din, yanzu dai a zaman da zakuyi sai kayi masa maganar auren muji, a kalla auren zai taimaka masa ya zauna a cikin mu, kaga dole ya koyi komai."
" In sha Allah, idan ma bashi da yarinyar da tayi masa ni zan nemo masa."
" Kul, Muhammad ba irin yaran da za'a yi musu haka bane, mu da muke son amfani da soyayyar shi ga yarinyar, abi dai komai a sannu."
" Shikenan in sha Allah, Allah yasa mu dace."
" Amin ya Allah."
***Bangaren Ammin sa ya wuce, yana tafe yana amsa gaisuwar da ya tsana, ayi ta gaida mutum kamar wata tsiya, hakan na daya daga cikin abinda yake hada shi da gidan su, ya gwammace yayi guduwar sa waje daya kawai ba tare da hayaniyar mutane ba.
Tana zaune ta dora kafarta a saman dan tumtum din dake falon, kafar na damun ta sosai shiyasa ko yaushe zaka ganta a mike ana dan mammatsa ta. Yana tura kofar duk suka mike, har rige rigen gaishe shi suke kowa yasan yadda Ammin ke masifar ji da tilon dan nata, mace me kirki da sanin yakamata, shiyasa ta karbe kowa a gidan daga ma'aikata har dangi kowa nata ne, wajen Bubu ma Itace star,itace kuma uwar gidan sa dan dai Allah be bata yawan haihuwa bane.
"Barka da zuwa yarima, sarki me jiran gado, uban mara uba me uban ma kaine gatan sa, shalelen Gimbiya da maimartaba, ka tsare gaba ka tsare baya, Allah ya kara maka daukaka da girma, Allah ya ida nufi.. sai..."
Da sauri ya dakatar da ita, sai ta juya sum-sum-sum ta fice, ya kalli Ammi yayi mata murmushi kafin ya zauna a daidai saitun kafafun nata ya tankwashe kafafun sa
"Ashe zaka zo." Tace masa tana murmushi itama
" Na isa naki zuwa Ammi? Barka da gida mun same ku lafiya?"
" Lafiya lau Alhamdulillah , shiru daga cewa zaka je wani aiki Kano shikenan kamar an aiki bawa garin su, su ba labarin su da suka bika kaima ba labari, gidanka da kake sauka ma an ce min ba chan ka sauka ba."
" Wani babban aiki ne ai Ammi, ki tayani da addu'a kawai in sha Allah zakuji labari me dadi."
" Allah yasa toh, ya aikin naku?"
" Alhamdulillah wallahi, muna ta fama, ba dadi amma haka dai za'a cigaba da lallabawa."
" Tunda kana so ba." Tace.
Dariya ya saka kawai be ce komai ba. Ya dan jima a tare da Ammin tasa kafin ya tashi ya yi mata sallama zuwa shashen shi, da yake kusa da na Bubu.
Yana shiga ya tarar da kayan abinci a jere a falon nasa, sai kamshin turaren wuta dake fita ta cikin yar karamar burner din dake makale a jikin wani dan karfe.
Wuce komai yayi zuwa bedroom dinsa, ya kwanta rigingine a saman gadon ya jawo woyoyin sa, ya shiga cikin contact dinsa, number farko da yayi saving dinta da emoji din heart da padlock ya danna kira ya kwanta sosai yana lumshe idanun sa lokacin da ta soma ringing...
****Da safe ta tashi kamar kullum tayi duk abinda tasan wajibin ta ne, har zuwa sanda rana ta fito sosai, kayan ta na wanki dana Marwan ta hada ta zagaya baya ta hau wanke su, daga gefe ta ajiye wayarta tana jin karatun alkur'ani me girma, tana wankin tana bi har ta gama tsaf, ta tattare su ta shanya sannan ta dawo ciki ta chanja kayan ta, ta fice zuwa shashen Gaji.
Fitar ta kenan Khalil ya shigo, maigadi na bin sa janye da katotuwar trolly din sa a baya. Da Habib suka ci karo yana kokarin fita, ya bashi hannu suka chapke cike da murnar ganin juna
"Welcome welcome." Yace masa yana juyawa suka shiga ciki. Da sauri Mama ta fito jin hayaniyar su..
"Wa nake ji kamar Khalil, inyee lallai yaron nan Ashe dai da gaske kake."
"Gani dai, ai dama na gama shirin zuwa kawai ban sanar dake bane sai jiyan."
"Maraba lalle da manyan yan jarida."
Zama yayi a cikin kujerun falon, itama maman ta zauna tana gyara dan kwalin kanta.
"Wai dama kinsan zaizo Mah?"
"Nima sai jiya na sani, na zata kuma halin nasa ne Ashe da gaske yake shiyasa ma ban fad'a ma kowa ba."
"Ina wuni Anty?"
" Lafiya lou Khalil, yaso Hajiya da kowa da kowa?"
" Duk suna nan lafiya, itama tayi mamaki da nace zanzo, gashi kuma zan dade sosai dan aiki ne ya kawo ni."
" Ahaap ko da naji, Ashe zuwan dai da dalili, jairi dama nasan akwai abinda ya kawo ka."
" Abubuwa dai Anty, karki manta da wannan maganar tamu hadda ita ma."
Tsaki taja ta harare shi
" Zaka fara ko?"
" Nayi shiru." Yace yana dora hannun sa baki
" Yafi maka dai."
" Ina su Zeenat ne? Banji duriyar su ba."
" Zaka ji su ne ai ba dai kananan ba, ka tashi ku shiga ciki ka huta kaci abinci, sannu da zuwa."
Tashi yayi, yabi bayan Habeeb suka wuce dakin sa suna hirar yaushe gamo, idanun sa da kunnuwan sa na jiran yaji ta inda zasu bullo, he can't wait to see her beautiful face, ko me Anty zatayi masa kuwa ba zai fasa bawa zuciyar sa abinda ta dade tana so ba. Kishin ta daban soyayyar sa daban. Period!
****Zaman ta a bangaren Gajin yafi komai yi mata dadi, abu daya ne kawai yake dan takura ta yawan maganar Gajin, duk da haka take daurewa tana amsa mata, gashi ta manta wayar ta a kitchen bayan ta gama wankin nan, gashi taji alamar Khalil din yazo ta tabbata idan taje dauka zasu iya haduwa, ta kuma san me hakan ke nufi a wajen Mama.
Zaman ta ta cigaba kawai har sanda taji ana kiran sallar, alwala tayi ta zauna ta jira a tayar, tana jin sanda za'a tada sallar ta fita zuwa bangaren nasu, lokacin tasan sun tafi sallah Maman ma kuma ta shiga ciki tayi sallar itama, ta baya ta bi, ta shiga kitchen din a daidai lokacin da ya saka wayar a kunnen sa
"Waye?"
Yace yana gyara rikon da yayi wa kofin hannun sa, tashi zaune Moha yayi da sauri, ya kalli screen din wayar ko be kira number daidai ba? Kai Anya? Daidai yadda ta fad'a masa ne
"Fatima nake nema, ko tana kusa?" Yace jin me maganar ya sake tambayar waye a karo na biyu.
"Fatima? Malam Waye kai din da kake neman ta?"
"Sanin waye ni ba zai taba maka dadi ba, idan tana kusa ka bata zanyi magana da ita."
" Ba zan bata ba, abun yar karfi ne kazo ka karba idan kana dashi, mtsw.".
Yaja dogon tsaki hade da kashe wayar, kafar ta ta sako a kitchen din zata shigo domin ta karbi wayar ta da ya daga mata ba tare da izinin ta ba, muryar Mama ta dakatar da ita, ta juya da sauri ta bar kitchen din.
" Kai kuma me kake anan kana jin an tada sallah?"
"Ruwa nazo sha."
Yace yana juyawa ya bar kitchen din, kofar bayan ta leka ta tabbatar babu komai a wajen, tayi kwafa ta juya bayan ta jawo kofar ta ciki.
Wani irin tashin hankali ne ya ziyarce shi, ya tashi da sauri yana jawo dayar wayar tasa, cikin kankanin lokaci ya birkice ya koma Captain Moh din sa na ainihi, a yau ba sai gobe ba zai juya, dan ba zai taba daukar rainin hankali ba, ba dan ganin da zai wa Bubu ba, da babu abinda zai hanashi daukar hanya a yanzu, amma dole ya hakura zuwa lokacin da ya dauka masa duk da yana ganin yayi masa masifar nisa.
Kaiwa da komowa ya dinga yi a tsakanin dakin, zuciyar sa tamkar zata hudo daga kirjin sa saboda tsabar kishi.
_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*
*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*
*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*
*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*
*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar
****
1/2/22, 22:47 - Buhainat: *HALIN GIRMA*
*_Hafsat Rano_*
*5*
*_Last free page!_*
****
Tana zaune ta idar da sallah, bata tashi daga kan abun sallar ba taji shigowar sa shashen Gajin, gabanta taji ya fadi, tayi kamar bata ji sallamar da yayi ba, tayi tsam a kan sallayar tana kallon gabanta. Da kallo ya bi bayan ta ya samu waje ya zauna a cikin kujerun falon yana kokarin daidaita yanayin da yake ciki. Gajin ce ta fito,
"Wa nake gani kamar Ibrahim?"
"Nine nan wallahi Hajiya."
"Lale marhabin, barka da zuwa. Saukar yaushe?"
"Dazu na shigo, mun same ku lafiya?"
"Lafiya lou wallahi, yasu Hajiyan da yan uwanka?"
"Kowa lafiya suna gaida ku."
"Muna amsawa, sannu da zuwa."
" Yawwa." Yace yana yawo da idon sa akan ta,
" Iman ba magana?" Yace yana son Gajin ta tanka
"Kaji sokonci, wai bata gaishe ka ba?" Tayi maganar da sauri
"Ina wuni?" Tace a gajarce
" Lafiya lou, kina lafiya?"
Shiru tayi bata amsa ba, Gaji ta hau sababi tana mata fad'a, tashi yayi hannun sa cikin aljihu ya zaro wayar ta
"Gashi na tsince ta a kitchen."
Ya mik'a mata sannan yayi wa Gajin sallama ya fice yana raya ta yadda zai bulowa Iman din, ya gama gane yanayin ta ba irin nasa bane, shirun ta yayi yawa amma duk da haka shi ba damuwar sa bace, yadda ya shiga zuciyar kowa a gidan nan da hakan zaiyi amfani ya kafa kansa, ba zai wani ja lokaci ba zai gabatarwa Gaji da kansa, baya jin ma zai wuce gobe, zai sai fara tuntubar Yaya Hajara idan yaga ba ta goyi bayansa ba zai yi gaban kansa, iya ka tayi masa fad'a shikenan ya wuce. Be koma shashen ba, sai ya fice daga gidan a kafa yana adana number da ya dauka a wayar ta ta, so yake ya saka number a truecaller yaga ko zai samu wani information akai.
Cikin call log dinta ta shiga ta duba amma bata ga number da aka kirata ba, taji babu dadi dan bata so yaga kamar tana sane ta bayar aka daga wayar tasa. Ko da tafiyar su ba zatayi daya ba, ba zata so yaji a ransa dan yana lacking wani abu bane shiyasa hakan ta faru. Kwantar da kanta tayi a saman hannun kujerar ta rufe idon ta tana tariyo zuwan da yayi wajenta, akwai wani abu me girma a muryar sa sai kuma abu daya da ya tsaya mata shine kamshin turaren da taji yana yi, wanda yayi kama da me tsada ne irin ajin farko, domin Allah ya hore mata kaunar kamshi, shiyasa ta kan yi saurin ganewa. Sai dai akwai irin tuurare yan durin nan da suke da kamshi me dadi har ka kasa tantance su, kila irin su ne, abunda ya kara burgeta dashi kenan, duk da yana cikin yanayin da zaka ce kai tsaye babu, amma be bar kansa a wulakance ba. Juya kanta tayi daya gefen ta dora wayar a saman cinyarta ta cigaba da tunani.
***Kiran sallar magriba ya sashi fita daga sashen nasa zuwa masallaci, achan yayi alwala ya shiga sahun farko sukayi sallar. Bubu na ganin shi yaji dadi sosai. Bayan an idar ya wuce bangaren nasa domin ya jira shi, yana zaune sai gashi ko ya shigo, ya tashi tsaye har sai da ya zauna sannan ya zauna shima a k'asa cikin girmamawa ya sake gaishe shi, ya amsa masa sake yana nazarin sa.
"Muhammadu!" Ya kira sunan sa, gyara zaman sa yayi ya tattara hankalin sa waje daya cikin son ganin be yi wani abu a gaban Bubun ba
"Kana ji na Muhammad?"
"Inaji Bubu."
"Madallah, Muhammad ka san dai a tsarin gidan nan kana cikin lokacin da ya kamata ace ka ajiye iyalin ka kaima, ka nutsu waje daya a kalla hakan zai taimaka maka wajen cikar kamalarka."
Kansa a kasa yana jin Bubun yayi ta bayani yana gida kansa cike da gamsuwa,
**A kofar ta tsaya tana kallon takalmin Muhammad din dake zube a wajen, ta samu labarin zuwan sa a wajen Kamal amma bata tsammaci irin wannan ganawar da Maimartaba ba, shiyasa ta kasa hakuri tazo ta nemi iso wajen Maimartaba din wajen sarkin kofa amma sai ya nuna mata ba zai yiwu ba, domin an gargade shi akan barin kowa ya shiga shashen maimartaba din har sai ya kammala ganawar sa da Muhammad din, ranta a matukar bace ta koma sashen ta tana jin wani irin tashin hankali, tana tsoron kar Muhammad din ya amsa tayin mahaifin nasa a wannan zaman da zasuyi.
Safa da Marwa tayi tayi, har wajen sallar isha basu fito ba, tana hangen bangaren ta cikin nata shashen, ta kasa zama tana da yakinin ko menene suke tattaunawa haka me muhimmanci ne sosai.
Tana tsaye jikin window taga fitowar su, fuskar Muhammad din a sake yana takewa mahaifin nasa baya. Tsaki taja ta saki labulen tana juyawa zuwa gefen gadon ta, ta zauna tana sake jan wani tsakin, tsakin haushin Muhammad din da ya zame mata ciwon ido shi da mahaifiyar sa.
"Ranki ya dade, Maimartaba ya aiko yana da bukatar ganin ki bayan ya dawo sallar isha'i."
Bata amsa ba, sai ma juya fuskar ta da tayi wani sashen tana sake sakin siririn tsaki.
***Bangaren sa ya koma, ya tattaro abunda ya san zai bukata ya fito, sai kuma ya tuna da maganar Maimartaba ta karshe da suka tattauna, yana son ganin sa da safe kafin ya fito fad'a, komawa yayi ba dan yaso ba, ya ajiye komai ya zauna yana kirga lokacin zuwa wayewar gari. Nisan yayi yawan da yake jin kamar yayi loosing idan har ya kyale shi tsawon wannan lokacin.
Wayar sa dake ajiye a gefen sa ta dauki sowwa, ya daga ganin kiran da yake ta jira ne tun dazu,
"Oga na duba maka number din, akwai bayanan sa da komai har da wajen aikin sa, hoton sa da kuma location dinsa a yanxu, na tura maka ta mail sai ka duba."
"Ok! Thank you, zan neme ka. "
Ya katse kiran ya shiga mail dinsa, ya hau kan message din ya bud'e. Hoton sa ya bud'e yayi zooming sosai, sai kuma ya fita ya karanta information din. Karamin tsaki yaja ya ajiye wayar yana jin a ransa wannan din karamin kwaro ne be kamata ya hana shi walwalar sa ba, abu daya zai masa ya kama shi a hannun sa, sai dai ba zai hakan ba har sai ya je ya tabbatar da zargin sa.
***Anan sashen Gajin ta shirya, ta wuce islamiyya tana tafe tana satar kallon hanyar ko zata ganshi tunda yace mata yana zama ne domin yaga wucewar ta, har ta isa makarantar bata ga ko me kama dashi ba, sai kawai ta share tayi abinda ya kaita.