Showing 81001 words to 84000 words out of 115235 words

Chapter 28 - Halin Girma Hausa Novel Complete

da suka shiga wajen, mutane ne masu yawa kai kace wani gagarumin biki ake, kowacce kofar shiga wajen dankare take da jami'an tsaro, ji tayi ido yayi mata yawa, gashi duk sun tashi da shigowar su. Mafiya yawancin su ba hausawa bane, sai yan daidaiku da tayi hangowa daga in da take. Wajen zaman su waitress dake tsaye a wajen ta nuna musu, basu wuce chan ba kai tsaye sai da suka je wajen manyan kusoshin, suka kwashi gaisuwa in da taga yayi wata irin gaisuwa tasu ta daban, sannan suka samu wajen zama suka zauna sai a lokacin ya sakar mata hannu.

"Sannu Amarya!"

Wata bahaushiya a kusa da ita tayi mata magana, amsawa tayi tana maida mata murnushin da tayi mata, sai kuma suka gaisa da sauran matan wasu hausawa wasu ba hausawa ba, kafin kuma a fara gabatar da abinda ya hada su.
  Captain Is'mail ne a gaba gaba akan komai shi da George, su ne ma organizers din event din shiyasa ko zama sun kasa yi, har sai da lokacin cin abinci yayi sannan suka zauna shima na wucin gado,ana gama ci aka cigaba da gudanar da event din. Sun sha kyaututtuka sosai har sai da Iman ta gaji da karba, idon ta yayi nauyi kwanciya take so kawai yayi, yana lura da ita, yasan ba karamin aikin su bane su kai fiye da biyu a wajen babu kuma wanda zai damu, ita kuwa akwai rashin sabo, tashi yayi yana zura hannunsa cikin aljihun wandon sa, ya nufi wajen da Is'mail yake ya jashi gefe, yayi masa magana kana ya dawo wajen zaman sa ya zauna. Sai da aka kara kamar mintuna ashirin sannan isma'il din ya bada sanarwar amarya bata jin dadi zata je ta huta, da haka suka samu suka sulale daga wajen suka nufi masaukin su. Dukkan su a gajiye suke dan haka babu abinda suka kara bayan sauya kayan jikin su sai bacci, cikin kankanin lokaci bacci yayi awon gaba dasu.

    Da wuri ta tashi, ta shirya ta zauna tana duba lokaci, baccin sa yake tsakanin sa da Allah tun bayan dawowar sa sallar asubah gashi ta matsu ta ganta a gidan, gashi babu alamun zai tashi har past 10, an kawo musu breakfast daga reception din taci kad'an ta ajiye masa sauran ta cigaba da zaman jiran sa. Wasa wasa lokaci ya dinga ja, babu abinda yake sai chanja kwanciya da juyi daga nan ya koma nan cikin jin dadin baccin. Ganin da gaske ba zai tashi ba, ya sakata zuwa daidai saitin kansa, ta dan rankwafa da niyyar tashin sa, hannu takai kan sajen fuskar sa, ta taba kadan, juyi taga yayi ya sake maida kansa dayan barin, sake durkusowa tayi ta bayan nasa ta kai hannun ta jikin sa, kam taji ya riko hannun ya makale shi tsakanin hannun sa da jikin sa, ja tayi taji ya makale shi kam, gashi sauran kad'an ta fado kansa gaba daya, dayan hannun ta saka ta taba shi,

"Please ka tashi zamu makara."

"Uhum..." Yace cikin muryar dake cike da nauyin bacci, ya sake kankame hannun nata a jikinsa wanda ta jawo mata fadawa kansa ta gefe daidai saitin bayan sa.
   Sun jima a haka tana jin shi yana fitar da numfashin bacci, kafin yayi motsi ya bud'e idon sa da suke cike da bacci sosai, ya juyo bangarenta yana sakin hannun nata.

"Ka tashi dan Allah."

"Um um..."

"Ka manta zamu fita?"

Da kai ya amsa mata da eh, kokarin tashi tayi zaune ya daddanne ta, ta hanyar dora kafarsa a jikin ta

"Kinsan fa jiya bamuyi wani bacci ba, please muyi bacci idan muka tashi sai mu fita."

"Past eleven fa, please please please."

"Ohhhh! Ni dai gaskiya, gaskiya bacci nake so nayi, anjima sai muje idan mun tashi, bari kiga."

Ya sake kadannade ta da kafafun nashi da sukayi mata nauyi ta kasa janye su,gani tayi yana maida idon sa zai rufe tayi saurin rik'e fuskar sa

"Dan Allah!"

"Shikenan." Yace yana sauke kafarsa, ta samu ta mike tana murmushi

"Amma da sharadi, ke zaki min wanka ki shirya ni, ki kuma bani abinci a baki."

"Ahhhh." Ta bud'e baki cike da mamaki

"Fine, bari na koma bacci na sanda na gama mun fita."

Da sauri ta rik'e blanket din da zai sake rufa

"Zanyi."

"Good girl."

  Yace yana mata murmushin mugunta. Janye blanket din tayi, ya zuro kafafun sa k'asa yana mika mata hannu, kama hannun tayi ya tashi, yayi kamar zai fadi ya fado jikin ta, nauyi sosai taji, amma ta daure dan taga take taken sa zai iya cewa ya fasa, a haka suka isa toilet din, ya zauna a gefen bathtub din ta hada ruwan, ta dauko masa brush da toothpaste ta matsa masa ta bashi, kin karba yayi ya bud'e mata bakin wai tayi masa, sake mika masa tayi ya noke yana tashi alamun zai bar toilet din, da sauri ta riko shi, ya koma ya zauna ta fara yi masa, dariya ce take kamashi amma ya kanne, yadda ta daddage kawai zai baka dariya, hannun sa ya dora a saman nata ya karbi brush din, ya karasa, ya bata ta cilla shi a dustbin din toilet din daga nan tayi hanyar fita

"Kina fita zan fito nima."

Tsayawa tayi ta dawo tana tura baki, ya hau cire kayan sa a gaban ta, tayi saurin juyar da kanta, murmushi yayi ya shiga ruwan da yayi masa daidai da yadda yake so, sai data tabbatar ya shiga ciki sannan ta juyo tana cigaba da dauke kanta ta dauko sponge da sabulu ta bud'e ta ajiye a dan wajen da aka tanada, zama tayi a gefen bathtub din,  taki kallon gefen sa ta juyar da kanta gaba daya hanya, bata yi aune ba taji ya jawo ta cikin ruwan, ta saki kara, ya hade bakin su waje daya ya hana karar tata tasiri.

   Sai da suka bata lokaci mai tsawo a ciki sannan suka fito, ta dinga turo baki tana jin kamar tayi masa kuka, ta riga ta gama shiryawa tsaf har kayan da ta saka dama su tayi niyyar sawa amma ya jawo sai ta sake sabon shiri, a wajen shiryawar ma haka tayi ta fama dashi da ya janye mata towel ta nan sai ya janye mata ta nan haka dai yayi tayi har sai data gama cika fam, zata fashe kafin ya kyaleta su shirya a nutse.
   Kasancewar ciki da falo ne dakin, sai tayi ficewar ta, ta barshi a ciki yana karasa shiryawa ta hada masa breakfast din ta ajiye da yazo ci kawai zai yi su tafi. Da waya a makale a kunnen sa ya fito, yayi zaman amsa wayar da ta fuskanci da Musaddik suke magana, sai da ya gama wayar tsaf sannan ya jawo abinci ya soma ci a yangace kamar ba jiran sa take ba, bata dai ce komai ba, ya gama duk bata lokacin da zai yi, sannan ya tashi yana goge bakin sa da tissue. Tashi tayi itama dama tayi ready har da jakarta a kusa da ita, gaba yayi ta bishi a baya, ya murda kofar sojan da yake jiran sa a wajen ya karbi Notepad da wayoyin sa, shi kuma ya zuba hannuwan sa a aljihu suka shiga takawa zuwa wajen da aka tanadar domin parking motoci.
   Bud'e mata kofa yayi, ta shiga ya rufe sannan shima aka bud'e masa nasa bangaren ya shiga suka fita daga harabar hotel din!

Bashin Jiya....so sorry banajin dadi ne

_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D'aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107
2/12/22, 11:07 - Buhainat: Halin Girma
      32

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

*******�?

Address din drivern ya dinga bi har suka isa gidan, tun kafin motar ta gama daidatuwa a harabar gidan take kokarin fita, chapko ta yayi yana bata fuska

"I'm jealous!"

Da mamaki dake kallon sa

"Yes I'm jealous, I want my share of love too, inaso naga same action na murna anytime mukayi nisa da juna, inason soyayya, inaso a gatata ni, aji dani sannan a damu dani please."

Dariya ma ya bata, ya saki hannun ta yana sake bata fuska shi a lallai yayi fushi, girgiza kanta tayi cikin muryar lallashi tace

"I'm so sorry toh, kawai I'm eager ne, ban wani zauna dasu sosai ba, shiyasa kawai."

"Shikenan reason din?"

"Shikenan, ko baka so naga Mama ta? Kullum fa kai kana tare da Ammi fa, nifa?"

"Ba haka bane, banda Mummy ai nake nufi, Mamma, Amaani, Amaan and rest, su nake kishi dasu."

Dariya ta sake yi, ta rik'e kofar ta bud'e, ya zuba mata ido kamar bashi da niyyar fitowa, sai da tayi masa alamar da hannu sannan ya bud'e ya fito ta dayan side din, yana karewa gidan kallon.
   Kofar shiga part din suka nufa, yana biye da ita a baya hannun sa sakaye a cikin aljihun sa, daf da zasu kai kofar ta bud'e, Amaani ce a gaba da shegen gudu, tayi kanta tana ihun wallahi itace, kamar zata kada ita, sai da k'yar ya nutsu tana numfarfashi, hango shi da tayi a baya sai kawai tayi wajen sa , ta rik'e masa hannu ta fara zuba masa surutu kamar tayi shekara da sanin sa. Cike da sha'awa yake duban ta, ta rik'e shi gagam har ciki tana bashi labarin da be gane kan sa ba.
  Mamma ce ta fito daga wani corridor, tana sanye da lullubi akanta, fuskarta cike da farin cikin ganin su,

"Sannun ku da zuwa."

Tace sanda ta karaso falon, idon ta akan Iman dake zaune da Amaan a kusa da ita. Russunawa yayi cikin ladabi ya gaida Mamma din, a daidai lokacin Mummy ta fito itama, ya gaishe ta a kunyace dan kallo daya yayi mata yaga tsantsar kama da Fatin sa, amsawa tayi ita din ma a yanayin kunya irin tamu wadda aka gada tun iyaye da kakanni. Iman ce ta gaishe ta,  ta amsa daga tsaitsaye ta juya ciki, murmushi kawai Mamma tayi dan tasan yadda ta matsu da zuwan nasu, amma ba zata taba nunawa ba, yadda tayi zaka dauka ma bata damu ba sam,nan kuwa tsantsar kara ce irin tata da har take nema tayi yawa.
   Abinci aka shiga jere musu, yayi mata alama da ido akan tafiya zai, ya dauki bottle water guda daya ya mike yayi musu sallama akan zai dawo, mamma ce ta hau korafin me zai sa ba zai tsaya yaci abinci ba, hakuri ya bata akan zai dawo akwai wanda yake jiran sa ne. Shikenan tace ya fice ta harari Iman

"Haka ake wa miji? Tashi mana kije kiji."

Tashi tayi tana dariya, ta bi bayan sa ta same shi har ya kai wajen mota, tsayawa yayi ganin ta fito ya choge jikin motar sai data karaso sannan ya shiga, ya sauke glass din motar yana kallon ta

"Kwana zanyi ko?"

"Inji waye? Da yamma zan dawo zuwa magriba."

"Dan Allah..." Girgza mata kai yayi tun kafin ta karasa.

"Zaki dawo next time, sai na dawo bye."

Ya daga glass din ta dan ja baya tana kallon motar har ta fice daga gidan, kamar zatayi kuka haka taji, taja kafarta a hankali ta koma ciki ta samu Mamma ta zuba mata abincin mummy kuma ta dawo falon ta zauna tana wa Amaani fad'a akan rawar kanta.
   Taji dadin zuwan ta gidan sosai, kamar tayi ta zama haka taji, amma tasan tun da yace zai dawo toh zai dawo din, amma taso ya barta ko zuwa da safe ne sai yazo su tafi ko ya turo a dauke ta.
  Ta idar da sallar magriba kenan a dakin Mummy, Amaani ta shigo tace ya dawo, har ga Allah taji babu dadi, ta tashi ta nannade sallayar ta ajiye a gefe ta zauna a saman sofa tana ciro wayarta. Tana zaune har wajen minti talatin babu wanda yazo kiranta, har ta kishingida sai ga Mamma ta shigo, tace ta tashi su tafi yama fita,

"Na zata zai barni na kwana."

"Kul... Dududu yaushe akayi auren? Kar ma ki soma yi masa maganar kina ji na? Watarana da kanki zaki zo ma"

" Wuce muje kar suyi ta jira." Tace tana sakata a gaba suka fito falon, uban kaya ne jibge a gefen falon dangin su shinkafa kayan abinci dai masu yawa, Mummy na zaune tana juya kudi a hannun ta

" Kinga wahalar da yayi ko? Kiyi masa godiya nace ba za'a karba ba amma ya dage dole." Tayi maganar tana ajiye kudin a saman center table, bin kudin Iman tayi da ido wanda a kalla zasuyi hundred thousand, sai kayan abincin da yake a dankare awajen, jinjina kanta tayi cike da mamakin sa, ko alama be nuna mata ba balle ta gane shirin sa, dadi ne ya kamata ta fito bayan sun yi sallama da Mummy tana zuba masa ido ta cikin hasken compound din gidan, duk da motar tint ce, amma tana iya hango inuwar sa, cike da karsashi ta karasa wajen motar, dai-dai lokacin da kofar ta bud'e, ta shiga da sallama tana dagawa su Iman hannu.
   Suna fita daga gidan ya matso kusa da ita cikin lallashi yace

"I'm sorry na hanaki kwana, kinga gobe da wuri zamu tafi amma next time da kaina zan kawo ki har sai kin gaji."

"Laa ba komai fa, dama wasa nake yi, su Mamma ma ba zasu barni ba ai, wai dududu yaushe akayi auren?"

"Haka suka ce ko?"

"Eh..."

"Yawwa kin gani."

"Babu komai fa, ni nama manta ma ma na tambaya, I'm sorry."

Ta kama kunnenta, zare hannun nata yayi yana jawo ta jikinsa.

" Thanks dear."

****
Washegari suka dauki hanyar Kano, tun kafin su isa an gama gyara musu gidan su, dama dai ba wani baci yayi ba saboda akwai masu aiki da kula da gidan banda sojojin da suke waje suna gadi, suna isa ya fice tare da Musaddik, anan ta tarar da uban kayan lefen ta, tayi zaman kallon su cike da mamaki, idan kaya na yawa toh ita dai sun mata mugun yawa, ya zatayi dasu? Shine kuma har da siyan mata wasu kayan saboda dai ba'a san wahalar kudin ba. Gajiya tayi da kalla ta saka masu aikin suka kwashe su, suka maida su wani daki guda kafin ta kira Mamma taji abinda ya kamata tayi dasu da mutanen da ya kamata a bawa.
   Slippers ta zura ta zazzagaya gidan nata, wanda yasha kaya na alfarma, har da wani babban garden a baya da pool daga chan gefe shima, gidan yayi kyau amma yayi girma ace mutum daya kwal dan ma ma'aikata masu yawa wanda yawanci daga masarauta suke sai wanda aka turo su daga adamawa. Daki ta koma ta haye gado tayi kwanciyar ta dan bata jin yunwa tasha cornflakes suna zuwa sai kawai ta kwanta da niyyar ta tashi wajen azahar ta dafa masa simple dish dan wata gajiya take ji na nukurkusar ta.
   Ta jima batayi irin baccin da tayi ba, ga sanyin AC da kamshin fresheners masu dadin kamshi da ya cika dakin, hakan ya kara taimaka mata jin dadin baccin sosai har sai da taji ana mata knocking sannan ta tashi bakin ta dauke da addu'a ta yane kanta ta fito ta bud'e kofar, daya daga cikin masu aikin ce Atine, ta russuna ta gaishe ta sannan tace tayi baki ne a falo. Ok tace ta rufe kofar ta koma ta gyara fuskar ta, ta fesa turare ta dauko wayarta ta fito. Yan mata ne su biyu kyawawa dasu masha ALLAH, suna zaune suna kallon TV ta fito,

"Sannun ku da zuwa."

"Yawwa." Suka amsa a sake, suka gaishe ta sannan suka gabatar mata da kansu

"Fulani ce ta aiko mu, kayan gara ne dangin su alkaki dasu bakilawa da dublan, sai gireba da sauran su, tace gashi nan zaku iya tayin baki tunda kun dawo."

"Kai mun gode sosai, Allah ya saka da alkhairi."

Ta tashi ta bubbude, ta dawo ta zauna tana murmushi ta sake godiya, aikin gidan mace ne kayan gara amma basu bari anyi mata ko daya ba, dama tasan dai ko za'a yi sai dai a gayawa su Mamma suyi mata sai gashi sunce ba sai anyi ba,itama yar su ce kamar Muhammad din.
   Hira sukayi sosai tun tana nokewa har ta saki jiki dasu dan suna da hira ga faram faran kamar sun saba. Tare suka ci abincin da suka zo dashi alkubus da miyar taushe, suka bita kitchen da zata yi ma Moh dan abincin sa, suka tayata sai yamma suka tafi, bayan sun mata alkawarin zasu dawo basa so ya dawo ya same su dan tsaf zai kore su, jin su kawai tayi dan batayi tunanin zai aikata ba, bata san yadda yake tsare musu gida da daure fuska bane shiyasa har yake mamaki dan sun ce ba zasu zauna ya same su ba.
   Suna fita kuwa sai gashi ya shigo, yaga fitar motar su amma basu tsaya ba suka kara mai. Bud'e hannun sa yayi ya tsaya daga jikin kofa, ta tafi a sanyaye ta fad'a jikin sa, ya rungume ta yana shafa kanta.

"Sannu da zuwa yallabai."

Ta karbi rigar hannun sa suka rankaya cikin falon, sai da ya zauna sannan ya amsa mata sannun ya dora da

"Baki kikayi?"

"Su umaima ne, daga chan gida aiko su."

"Yan rawar kai, tun yaushe suka zo?"

" Wajen twelve din rana."

" Ah kice kin samu yan hira ko nace yan surutu dan bakin su sam baya shiru."

" Naji dadin zuwan su kuwa, sun tayani hira ai."

" Sun kyauta da suka tafi kafin na dawo, dan tsaf zan saka yarinya frog jump ba abinda ya damen."

Ya fad'a yana kai cup din ruwan da ta zuba masa bakin sa,

" Da gaske wai?"

" Da gaske mana, suma sun sani ai, kila ma sun fada miki ko?."

" A ah." Tace tana dariya

" Ya yau din? Ya gidan naki?"

" Alhamdulillah, komai yayi Masha ALLAH, Allah ya kara arziki, thanks for everything,

" Amin Amin, I'm glad you like it."

Yace cikin jin dadin addu'ar ta

" I love it!"

" Masha ALLAH."

***Tun ranar farko da Bashir ya samu damar shigowa dakin har yayi abinda yayi, tun daga lokacin duk dare sai ya lallabo, ranar farkon tana jin su suka haura sama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login