Showing 57001 words to 60000 words out of 115235 words
Chapter 20 - Halin Girma Hausa Novel Complete
ni, sunana Laila, gimbiya Lailah."
Yawu me karfi ta hadiye, ta hau kokarin daidaita kanta waje daya, shigowa taji an sake yi, ta daga idonta da sauri wannan karon wata babbar mata ce ta shigo a hargitse, tayi saurin yin kan wadda ta kira sunan ta da Laila tana rik'e ta, tana kallon yadda Lailan ta cigaba da rusa kuka kamar Allah ya Aiko ta, matar na bata baki jikin ta na rawa sosai. Daga ta tayi da sauri, ta yafa mata mayafi ta rik'e hannun ta, suka zo daidai in da Iman din take tsaye, matar tayi mata wani mugun kallo, ita kuma Laila tayi mata murmushin da ta tsaya mata a rai. Fita sukayi tayi saurin zuwa ta sakawa kofar key, ta dawo ta durkusa a k'asan falon ta shiga kuka, kukan da take ta kokarin rikewa dan bata son su ga weakness dinta, dama chan ita mutum ce me taurin zuciya da wuya kaga weakness dinta, shiyasa yanzun ma ta daure har suka fita.
Sai da tayi kuka sosai sannan ta tashi ta share hawayenta, a kalla zata so taji ta bakin shi, kar ta yi judging dinsa da abinda ko a musulunci babu hujja, dan bata gansu suna aikata wani abu mara kyau ba. Duk da ta na kokarin karfafa jikinta da zuciyar ta akan ta bari taji komai, amma kuma jiki da zuciyar ta ta sunyi sanyi, sanyin da take jin kamar komai ya kare mata, kasan zuciyar ta tana jin zafin sa, tana jin haushin sa amma kuma bata da damar yanke masa hukunci.
A yan awannin da tayi a cikin gidan nasu ta fuskanci akwai wani Babban al'amari da ya shafi Moh dinta. Tana jin kamar gadar zare aka hada masa har ma da ita. A nutse take duk da abin ya kadata, dan babu matar da zata ga wata mace a dakin mijinta cikin yanayin da taga Laila ba tare da taji komai ba, sai dai ta yarda da addu'a dan haka ta dage sosai har ta soma jin nutsuwa na saukar mata.
Bata san dadewar da tayi a wajen ba, taji kamar motsi a dakin, ta tashi ta dubo cikin rashin sa'a ta cire takalmin ta, ta taka glass din da yake fashe a wajen, kara tayi hakan ya farkar da Moh gaba daya, ya mike da sauri kansa yayi wani irin sarawa da be taba jin irin sa ba, jiri yaji yana neman kayar dashi yayi saurin komawa ya zauna yana dafe kan, bayan kamar sakan goma ya mike a hankali ya fito.
A durkushe ya ganta tana rik'e kafarta da har ta fara jini, da sauri ya karaso ya durkusa a gabanta yana kama kafar
"Me ya same ki? Me kika taka."
Kokarin janye kafarta tayi, ya sake kama kafar ya rik'e yana kallon kafar cikin tausayawa.
"Cika min kafata."
Tace ba tare da tasan me yasa ba, kawai ganin sa ya sakata jin haushin sa. Kin cika mata kafar yayi, sai ma daukar ta da yayi gaba daya duk da yadda yake jin sa babu kwari, ya ajiye a gefen gadon ya dauko first aid box din sa yazo ya durkusa a gabanta ya gyara mata kafar Allah ya taimaka kwalbar bata shige ba.
"Yaushe kika zo nan? Ya akayi nayi bacci? Me ya faru aina aka samu kwalba a wajen nan har kika taka? Ina masu kula da wajen?"
Ya jero mata tambayoyin cikin son tuna wani abu, da Ido kawai yake bin sa kamar me son karantar sa, sai dai bata ga komai ba sai tsantar gaskiyar sa a yadda yake maganar. Janye kafarta tayi ta mikar da ita a saman gadon, ya dawo ssman gadon ya zauna yana jan kafar ya dora akan cinyar sa.
"Bacci ne ya dauke ni bayan na sha juice daga nan kuma bansan me ya faru ba, kin dade kina jirana? Da baki tashe ni ba?"
"Bana so na katse maka barci ne." Tace ganin duk ya damu, ajiyar zuciya ya sauke yana matsowa ya gyara mata kafar yadda zata ji dadi, ya mannu a jikinta.
" Kiyi hakuri, kaina ne naji yana min ciwo sosai shine kawai nazo na dan huta bansan zanyi bacci ba."
" Ba komai."
Tace tana rufe idon ta
" Bacci?"
" Umm."
Tace a gajarce dan bata son doguwar magana tana son tattara bayanan da ta samu ta hade su waje daya kafin wayewar gari.
Tashi yayi ya fita bayan ya maida rigar sa, ya hau k'wala kiran ma'aikatan wajen, da sauri ya shigo yana raba ido, masifa ya fara yi masa akan dalilin barin kwalba a hanya, hakuri yayi ta bashi yayi saurin gyara wajen sannan ya fita.
Ji yayi duk jikin sa yana masa ciwo, chan k'asan zuciyar sa kuma wani irin feeling ne da be san dalili ba, ji yake kamar idan har be samu abinda yake so ba zai iya rasa ransa, yana wanka yana tunani har ya kammala ya fito daure da towel iya ka guiwar sa, kallon in da take kwance yayi, ta dunkule waje daya kamar me jin sanyi.
Kaya ya saka sannan yayi sallah ya duba wayar sa yaga misscalls da yawa, ganin dare yayi ya saka shi ajiye wayar ya hawo gadon yana juyo da ita tana kallon shi. Hawaye ya gani a saman kuncin ta, ya saka hannu cikin mamaki yace
"Kuka?"
Kamar wadda take jiran kiris ta shiga rera shi sai dai babu sauti, rikicewa yayi ya hau tambayar ta menene, bata amsa masa ba, ta cigaba da kukan ta wanda ita kanta bata san me yake sake tunzura ta take kukan ba, da farko ta zata zata iya daurewa sai daga baya ta gane duk dauriyar ta wannan ya wuce in da take tunani, kishin mijinta ne ya sakata kuka. Magiya ya cigaba da yi mata akan ta fad'a masa dalilin kukan ta amma taki, rungume ta yayi a jikinsa yana lallashin ta amma kamar kara ingizata yake, ya rasa yadda zai, ga wani irin abu da yake jin yana taso masa. Kasa daurewa yayi ya hade bakin su waje daya, da karfi tayi kokarin turashi ta amma ta kasa!
Rano💕
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
1/31/22, 19:15 - Buhainat: Halin Girma
23
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
*******
A hankali ya shiga bin ko ina na jikinta yana aika mata da sakonnin shi, kukan da take na taba shi, yana jin har cikin kansa, sai dai ba zai iya controlling kansa ba, abinda yake ji yafi karfin ikon sa, ba kuma zai iya tsere masa ba.
Da fari ta dauka babu wani abu da zai mata sai son ganin ya rarrashe ta, amma daga baya sai taga abin yana chanja salo. Jikinta ne ya hau rawa ta ko ina, ta sauya akalar kukan nata zuwa magiya da rokon sa, baya jin ta, idan ma yaji ta baya tunanin zai iya yi mata abinda take so din.
Juyo ta yayi ta zama a saman sa, ya sake hautsina ta zuwa kasansa , ya ajiye mata dukkan karfin sa, ji tayi kamar numfashin ta na janye wa daga jikin ta, ta dinga jansa tana kuka tana kiran sunan sa, yadda yake kissing dinta kamar mayaunwacin zaki ya sake tsorata ta,shi kansa jikin sa rawa yake,ga wani karfi da yake ji ya zo masa wanda be taba jin irin shi ba. Kayan jikin ta ya shiga janyewa yana wurgi dasu ta kowanne angle, har yayi nasarar rabata da komai. Idanun sa da suka rine sosai ya zuba mata yana kallon ta, wani abu yana kaiwa da komowa a tsakanin wuyansa.
"I'm so sorry."
Ya furta mata da k'yar kafin ya shiga aiwatar da abinda yayi niyya.
Sama sama yake jin ta, cikin muryar da ta shige ciki saboda kukan da ta sha, kamar mafarki haka yake jin abun, juyowa yayi da k'yar ya dune ta, tana kwance agefen sa taci kuka har ta gode Allah.
"Subhanallah!"
Ya furta yana tashi, abinda ya faru ya shiga dawo masa akai, ya akayi haka? Bayan yayi ma kansa alkawarin zama so gentle, yadda yasan ba zai bata wahala sosai ba, what has gotten in to him? Me yayi mata?
Rik'e ta yayi yana kokarin daidaita kansa ya samu damar kwantar mata da hankali
"I'm so sorry dan Allah, dan Allah kiyi hakuri ki yafe min, bansan me ya hau kai na ba, this is not me, bani bane ba."
Bata da karfin da zata kwaci kanta, sai kawai ta lafe a jikin sa tana jan numfashi. Kanta ya dinga shafawa a hankali a hankali, yana jin wani irin son ta, na saka shigar sa. Idan har abinda kwakwalwar sa ta dawo mata dashi gaskiya ne, toh lallai sai yaci uban Lailah, dole ne yayi mata abinda ko a hanya ta hadu dashi ba zata nuna ta sanshi ba.
Idonsa a rufe yana tariyo abinda ya faru, tabbas ya ganta a tsaye a kansa, lokacin da baccin da be san na menene ba dauke shi da sauri. Tunanin sa ne ya koma baya, zuwa sanda ya shigo ya tarar da juice akan table din da ake ajiye masa, a gajiya yace amma ya tsaya ya sha daga nan ne ya fara jin wani abu me karfin gask yana taso masa, sai wani irin bacci me nauyi da be taba jin irin sa ba.
"Desire pills?"
Ya furta yana kokarin tashi, k'ara tayi mara sauti ya tuna tana jikin shi, yayi saurin komawa ya zauna yana sake gyara ta.
" I'm sorry."
Ya saka hannu ya goge mata hawayen da suke sauka a fuskar ta. Tsawon minti talatin yana a haka yana tunanin abubuwan da suka faru a daren, tabbas koma menene an shirya masa abu ne, be san ya akayi ya bada kafa ba, har aka yi galaba akansa. Tashi yayi bayan ya gyara mata kwanciya, ya shiga toilet ya gyara jikin sa, sannan ya fito, ya taimaka mata, ta tashi tana ciccijewa sai dai taki yarda su hada ido, ta hade fuska sosai a dole haushin sa take ji, haushi biyu ne suka hadu waje daya, ta kasa manta abinda ya faru farko da na karshen.
Toilet din ta shiga sai taga ya biyo ta, ta dube shi tana tsaye gaban bathtub din, ta marairaice fuska, yi yayi kamar be ganta ba, ya rufe kofar ya karaso ya durkusa yana taba ruwan.
"Ka fita."
Ta fad'a muryar ta babu karfi, banza yayi kamar be ji ta ba, ya ciro towel a cikin jerin sabbin towels din dake jere a cikin wata drawer, sannan ya dauko brush da toothpaste ya saka mata a jiki ya ajiye a gefe ya hau nannade hannun rigar sa. Kamar ta rusa ihu haka taji, ta rasa yadda zatayi ta hanashi, bata ga alamar ma zai hanun ba, sai kawai ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido, bata san rashin kunyar namiji ta kai haka ba. Sai da ya gama abinda yayi niyya ya tabbatar yayi mata yadda zata ji dadin jikin ta sannan ya kyale ta ya fito yana jawo mata kofar.
Kwanciya ta sake yi a cikin tub din ruwan na ratsa ta, gefe tana tuna abinda ya wakana tsakanin su. Murmushi tayi, duk kalaman sa na dawo mata daki daki, abu daya ne ya tsaya mata har take kokarin alakanta shi da abinda ya faru kafin nan, idan har shi din ba mutumin kirki bane, idan har wani abu ya faru tsakanin sa da Lailah, ba zai sha wahala wajen neman hanya ba.
Saurin kawar da tunanin tayi kunyar kanta na kamata kamar yana wajen, da wanne idon zata koma wajensu Mamma ma wai tukunna, da wanne idon? Kwankwasa mata kofar yayi ganin ta dade, sai ta tashi tana karfafa jikin ta, ta dauro towel din bayan ta goge jikinta ta fito kanta a k'asa. Ajiyar zuciya taji ya sauke bayan ya kare mata kallo, hankalin sa yaki kwanciya tunanin sa ko yayi mata illa ne, sai yaga akasin haka, be sani ba ko duk cikin dauriyar da ya gane tana da ita bane. Lokacin sallah ake kira a cikin masallacin cikin Masarautar, daga jikin kofar ya tsaya be fita ba, yana kallon ta har ta gama ta saka doguwar jallabiyar sa daya ajiye mata a gefen gadon, murmushi yayi ya fice kansa sanye da farar hula da ake kira da tashi ka fiya naci ya dora doguwar riga irin wadda ya dauko mata.
A sahun farko ya samu Kamal, daga liman sai shi, hakan ya bashi mamaki amma ya share, bayan an idar suka gaisa a tsattsaye ya fice yana son komawa ya ga halin da take ciki. Sun hadu da Bubu amma be masa magana ba, ya dai ce masa ya sameshi idan garin ya gama wayewa, sai dai yanayin fuskar Bubun ta saka shi tunanin akwai wani abu me girma.
A saman sallayar ya tarar da ita, ta kwanta akan hannun ta ta mik'ar dashi, karasawa yayi ya daga ta, ya maida ta saman gadon yana zama a gefen ta. Rufe idon ta tayi da sauri jin ya matso da fuskar sa daidai saitin tata. Iska ya fitar me zafi, ya tashi ya kashe wutar dakin ta dawo ya hawo gadon ya kwanta.
"Me ya faru?"
Yayi mata tambayar kai tsaye, yadda yayi sounding zaka gane daga muryar sa, maganar yake so suyi, shiru tayi bata ce komai ba, dan bata san me zata ce ba, tace masa ta same shi da wata a daki ko me? Ta yaya ma zata fara?
"A lokacin da kika zo dakin part din nan, wani ya shigo? Ko kinga wani a ciki?"
Nan din ma shiru ta sake yi masa, kasan zuciyar ta na ce mata kar ta yarda,kawai zai yi amfani da innocent dinta ne ya nuna mata kamar be san komai, daga gefe kuma wata zuciyar na ce mata ta fad'a masa watakila be sani ba, watakila so ake a hada su, tunda har yanxu bata san komai akan sa ba, ba zata iya dorar da wani abu ba balle har ta iya judging dinsa, kawai dai a matsayin ta na mutum me tunani , tana kyautata masa zato.
Birkitota yayi da karfi muryar sa na fita da dan karfi akan dazu yace
"Tell me, me ya faru? Wani abu ya faru? Kin samu wata ko wani da kika zo? Wani ya fad'a miki wani abu ne? Me ya faru!"
Kuka ta samu kanta da fashewa da, ya tashi da sauri yana kunna wutar dakin, ya dawo ya tashe ta zaune suna fuskantar juna, zuwa lokacin ya ji yana neman loosing temper dinshi.
"Kalle ni, look at me! Menene? Me ya faru da ban sanshi ba? Tell me, waye yazo?
" Maimartaba ne yazo."
" Maimartaba!?" Ya furta da dan karfi cikin yanayin dake nuna tsantsar mamakin sa
"Me yazo yi a part dina? Me yace? Me ya faru? Wani abu ne ya faru while i'm sleeping?"
" Eh." Ta daga masa kai, tsugunawa yayi a wajen yana tattaro dukkan nutsuwar sa, gabansa na faduwa da abinda zata ce dan yasan ba karamin abu bane zai kawo Bubu part din sa.
" Believe me, bansan komai ba, kamar yadda babu alkalami akan me bacci, na rantse miki bansan me ya faru ba."
Goge fuskar ta, tayi da hancin ta a jikin sa, ta dago tana kallon kasa tace
" Naga wata Laila a nan."
Ta nuna wajen da Lailan ta zauna
" Lailah!? "
"Eh."
"Ehen, sai me?"
"Tana zaune a wajen tana kuka sosai, daga nan sai Maimartaba ya shigo, sannan ya tafi sai kuma wata mata ta shigo ta daga ta suka fita
Abu ya hadiye me karfi, ya yi kokarin ganin be yi wani abu ba, a hankali yaji kamar ana masa rad'a
_Be calm Moh, be calm."_
Kamar wanda aka saka abu aka bubbuge ma guiwa haka ya zube a wajen, zai tolerating komai amma banda fushin Bubu, shi za'a wa wannan kazafin? Abinda be taba tunani ko shaawar aikatawa ba, Zina? Shi Muhammad shi aka yiwa wannan sharrin? Saboda yayi kamar be san wani abu yana faruwa ba, shine har aka samu damar yi masa wannan kullin?
Tana ankare da yadda ya shiga kaduwa, tana kuma ganin yadda Adam apple dinsa ke hawa da sauka tsakanin makogwaron sa, idon sa kadai zaka kalla ka tabbatar da ransa yayi masifar baci.
Sai da yayi kusan minti goma be ce komai ba, ba dan bashi da abinda zai ce din ba, sai dan yadda mamakin Iman din ya hanashi komai, be zaci haka daga gareta ba, idan wata ce, ba zata iya daukar abinda ta gani ba, har ta tsaya jiran shi, ya ga kokarin ta sosai kuma ya jinjina mata, hakan ya kara mata matsayi a zuciyar sa.
Girgiza mata kai yayi yana kama hannun ta
"Kin yarda dani?"
" I don't know." Tace tsakanin ta da Allah
"Bansan yadda zan dauki abun na ajiye ba, all I know shine I'm hurt, more than yadda nayi tunanin I ll be."
Folding hannun nata yayi a cikin nasa ya damke.
"I promise to make everything right, koma menene we will over come it, in sha Allah, together we will build tomorrow, I promise you that!"
Shiru sukayi babu wanda ya sake magana, ko be ce ba, ko be ba ita zata gano komai, zata gane kafin ma ya gane, tana da kaifin tunani, sannan tana karantar komai kafin tayi judging din mutum.
Kwanciya tayi ganin suna zaune kowa da abinda yake tunani, ganin ta kwanta sai ya mike ya fita, ya nufi part din Ammi duk da lokacin garin ke karasa yin haske. Ya san tana zaune har lokacin tana azkar kamar yadda ta saba a ko da yaushe.
Yadda ta ganshi ya shigo jikin ta, ya bata babu lafiya, katse abinda take tayi ta mike tana kallon sa har ya karaso
"Lafiya Babana?"
"Ina kwana Ammi?" Ya duk'a k'asa ya gaishe ta, kafin ya amsa mata tambayar ta
"Ba lafiya ba Ammi, yarinyar nan Laila tayi abinda zan nuna mata ko ni waye, ganin kamar ban san me take ba ya bata damar aikata abinda ta